Showing 90001 words to 93000 words out of 161948 words

Chapter 31 - ABU - MALEEK Book Complete BY SARAUTA.txt

05 Jan 2025

6613

idanunsa akan Julde wacce ta ɗan juya tana gyaran kwanciyarta can cikin baccinta kuma tace.


"Ballowo!!!! Shine ka gudu kaƙi dawowa ko? Ban ƙara kulaka"
Ta faɗa tana kwaɓe fuska, wani irin janye idanunsa yay tare da komawa ya narke a jikin kujera,
Ganin haka yasa Oumuu-Ayman faɗin.
"Go to har please zaki, tun ɗazo take sambatun ka gudu, tunda idanunta suka buɗe kaƙi tsayawa"
Luff yay ba tare da yace komai ba,
Domin shi kansa tsoran tsayawa inda take yake tunda idanunta suka buɗe.
"Zaki!!"
Oumuu-Ayman ta ƙara kiran sunansa kafin tace.
"Ni ka masshe Shara? Eh? Ko halin ko in kula ɗin zaka nunawa Yarinyar daka buɗewar idanunta? To babu ruwana tunda Nima yanzu ban isa na faɗa maka kaji ba"
Miƙewa zaune yay yana ware firgitattun idanunsa akan Oumuu cikin sanyin murya tare da ƙarya wuya gefe yace.


"Ayyah! Oumuu nima abin a duba ne, bana jin daɗi"
Ya faɗa yana sauke numfashi tare Lumshe idanunsa yana tsotsar laɓɓansa,
Wata hararan wasa Oumuu ta watsa masa kafin tace.
"Eh! I see, kai Dr ne ita kuma matar Dr so wane ya dace ya kula da wani? Look! Jalal lokacin yayi da zaka Fahimci rayuwa, ka gane abinda yake dai-dai,
Mata akewa faɗan kula da miji, sai kuma akanka za'a fara yi maza faɗa? Ni yanzu na daina maka komai, everything you need ask your wife zata maka abinda yafi nawa"
Ta faɗa rai ɓace ganin yadda ranta ya ɓaci ne yasa yace.


"I'm sorry Oumuu, me kike so nayi i promise zanyi amma kada kici naje wajanta please!!!"
Ya ƙare maganar yana juya mata kansa tare narke fuska,
Kallonsa tayi tana tsare sa da idanunta tana son fahimtar abinda yake nufi ganin bata fahimci komai bane yasa tace.


"Why? Ko itama ta maka wani abune? Kai bari kaji mata rahama ne, farin cikin namiji baya taɓa dauwama sai da mace a kusa dashi,
Mace tana da matuƙar sauƙin kai idan ta samu kula kuma sai abinda kace mata,
Mu mata soyayya itace raunin mu, Hawwa'u bata San waye kai a wajanta ba, amma look at her face? Ba kaga farin ciki ba? Ba kaga yadda ta sauya ba? Eh? Baka lura da yadda fuskarta take kullum cikin annuri ba? Ka san Meye Dalili?"


Girgiza mata kai yay kamar ƙaramin yaro, kafin a hankali kuma
Ya juya idanunsa yana sauke ganinsa a saman fuskarta, ƙuri yay mata yana ganin wata zallar kamannin a saman kamilalliyar fuskarta,
Bai san kamar wace ba amma Tabbas fuskarta yana masa tsananin kama dana wani ko wata to su waye?
A hankali yace.
"Uhm"
Jin yadda ya faɗa ne yasa Oumuu-Ayman faɗin.
"He's happy just because of you Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal, Hawwa'u she's in love with you, soyayya mara algus, wacce ita kanta bata sani ba, yaya kake ganin farin cikin da zata shiga duk sanda ta fahimci kai ne mijinta?, Ka ɗauki min tuna 30 a cikin mintocinka na alfama, show her some love nasan zaka ban labari U most"


Ta faɗa sakin murmushi,
Domin ita kaɗai tasan tarin albarkar dake tattare da rayuwar su duka biyun, amma rashin sabo da kuma rashin sanin gin shiƙin abun yasa suka fahimtar hakan!


A hankali Julde ta shiga buɗe idanunta, da sauri kuma ta rufe idanunta tare da sakin ƴar ƙara, saboda hasken da yaywa idanunta yawa wanda bata saba dashi ba,
Daga Oumuu-Ayman har Abu Maleek ɗaga kai sukai tare da kallonta, kafin Oumuu tace.
"Bari na kira Dr Jemeal stay with her"
Ta faɗa tana fita daga room cikin nutsuwa.


Abu Maleek kam gyara zama yay sosai, tare ɗura narkakkun gajiyayyun idanunsa akanta,
Yana kallon yadda take janye duvet ɗin a hankali, cikin nutsuwa kuma tai saurin mayar da Idanunta ta rufe, tana sauke ajjiyar zuciya,
Hakan nan taji fargabar buɗe ido musamman da Zuciyarta ta gama bata cewa yana wajan.


Gently ya miƙe tare da ajjiye wayoyinsa a inda ya tashi, walking slowly yake tafiya yana fesar da iska daga cikin bakinsa
A hankali yaja ya tsaya a kanta, yana kallon yadda Jikinta ke rawa a hankali yaji ƙafarsa ta kaza ɗaukan gangar jikinsa,
Zubewa yay tare da zama dai-dai kanta har hannunsa na sauka gefen fuskarta,
Idanunsa ya buɗe sosai akanta kafin a hankali ya miƙa hannunsa tare da manna shi a saman goshinta,
Da sauri ta buɗe idanunta ƙirjinta na matsanancin bugawa idanunta dake a rufe ta buɗe, a hankali ta cilla idanunta a saman fuskarsa,
Numfashin ta ya kusa tafiya, Yasubuhanallah! Aminci Allah ya tabbata ga Ubangiji daya halicci wannan surar,
Bata taɓa ganin movie ba da tabbas babu abinda zai hana ta haɗa kyan Abu Maleek dasu, Karan nutrah (dheerajdhpoor) ko Jalal Muhammad Akbar, Ko Sameer (KapurShab)
All her life bata taɓa ganin halitta mai tsananin kyau tare da ɗaukan hankali irinta Abu Maleek ba, ko dan shi ta fara gani?
A hankali ta sauke ajjiyar zuciya tana ƙara ware idanunta a kansa kamar yadda shima yake kallonta,
Shi mamakin kallon da take masa yake, ita harga Allah bata yadda shi ne Ballowo ba, muryarsa kaɗai zai sanya ta aminci gashi har yanzu yaƙi magana,
Hannunsa dake saman kanta yay baya dashi a hankali tare da tura sumar kanta baya, yana jin wani masifafan ƙamshi na ratsa hancinsa,
"Uhm ahhhhh!!!"
Ta sauke ajjiyar zuciya tana ƙara kallon sajan fuskarsa wanda yake ta ƙyalli, a hankali ta fara ƙoƙarin miƙewa zaune,
Amma rashin ƙwarin jiki da kuma kyan Abu Maleek wanda ya ƙara zautar da ita ya sanya ta kasa koda motsi ne.


Lumshe idanunsa yay a hankali kana ya buɗe kafin a hankali ya gyara zamansa tare da ranƙwafawa dai-dai kanta, Julde wacce Jikinta yake rawa ga hannunta daya ƙwaɗaitu da son taɓa ƙwantaccen sajansa nasa,
Da wani irin sauri ta san yafin hannunta mai sanyin gaske ta manna a kan sajansa wajan laɓɓansa,
Da wani irin sauri ya ɗan kalleta kafin a hankali kuma hannunsa ya goce gaba ɗaya ya kifa kanta.


Nauyin da yay mata ne kuma ya sanya tace.
"Auchhhiiii ƙirji na, zaka fasa nono"
Da wani mugun ƙarfi ya runtse idanunsa lokacin guda kuma tsigar jikinsa ta shiga zubewa tana mimmiƙe wa tsaye,
Wani irin magaɗisun abune yake masa yawo a saman fatar jikinsa, yayinda kuma zuciyarsa take bugawa da ƙarfi, a hankali kuma wasu fararan taurari suka fara gilmawa cikin idanunsa.


Idanunsa ya buɗe ganin yadda laɓɓansa suka sauka akan nata, tsantsin laɓɓanta da kuma danshin yawon bakinsa a dalilin tsotsar laɓɓansa da yake,
Suka haɗu waje guda suka bada wani sauti na musamman, bakinsa ya ware da niyyar magana,
Da Sauri ya runtse idanunsa,
Wani irin razanan nan ihu Julde ta sanya, saboda wasu abubuwa da taji sun gilma, ta cikin tafin ƙafarta zuwa tsakiyar ƙwanyar kanta,
Dalilin shigewar lips ɗinsa cikin bakinta.


Wani tsuma yaji lip's ɗinsa da yake manne cikin nata, ya fara tamkar wanda yake cikin dusar ƙanƙara,
Haka laɓɓansa suke rawa yayinda ya kejin gaba ɗaya zuciyarsa da ƙwaƙwalwarsa suna sauya linzami da kuma alar jikinsa zuwa ga nata, a karo na biyu kenan daya kejin wani fitananan bahagon yanayi yana kusu masa,
Idanunsa da suke a tsume da wani ruwan ya tsurawa fuskar ta, gam gam Julde ta manne idanunta jin wani sabon yanayin game da Ballowo ɗinta, wani irin wahaltaccen numafashi ya sauke, tare da sanya laɓɓansa duk biyun ya matse nata dake manne cikin nasa, a hankali ya haɗe teeths ɗinsa tare da sakar mata wani nagartaccen cizo a tsinin tongue ɗinta,
Ƙara ta saki da sauri shi kuma ya janye jikinsa yana ɗan fidda numfashi,
Kafin ya zauna tare da gyara zamansa.


Dai-dai lokacin ne kuma Oumuu-Ayman da Dr Jemeal suka shigo cikin room, da sauri Oumuu-Ayman ta ƙarasa wajan Julde tare da faɗin.
"Daughter"
Sai kuna ta nemi waje ta zauna tare da kallon Abu Maleek tace.
"Me kai mata"
Kallon Oumuu yay da idanu yay mata alamar "me kowa zan mata"
Dr Jemeal ya shiga duba Idanun Julde kafin yace.
"Allahamdulillah, congratulations Mrs Aremo Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal, for now baki da wani problems ga medical glass ɗin ki, sai medicine nan da 6mnt zasu sake dubawa zaku iya tafiya"
Miƙewa Oumuu-Ayman tayi tace.
"Thank you so much Dr Jemeal",
Murmushi Yay mata yace "it's my pleasure Ma'ah"


Dai-dai lokacin Aremo Adams ya shigo cikin shigar Alfarma, Julde wacce aka sanyawa farin glass na ƙarin gani yay mata masifar kyau, ya ƙara haska fuskarta
"Hamma Adams"
Ta faɗa tana washe masa bakinta, Murmushi Yay mata yace.
"Congratulations Cute ido yazo"
Murmushi tai masa ba tare data sake magana ba,
Idanunta ta juya ta kalli Abu Maleek zare mata ido yay hakan yasa itama ta zare masa ido ta ɗauka wani abu ne domin komai kuya take,
Wani irin kasalallan Murmushi ne ya suɓuce masa da sauri yay waje yana ɗaukan Wayarsa.
"Oumuu ya tafi"
Kama hannunta tayi tace.
"Muma tafiya za muyi, Adams muje ka sauke mu, nasan zaki bazai tsaya ba"
Tuni Abu Maleek ya shige motarsa da wani irin speed yabar cikin hospital ɗin.
Haka ma su Oumuu
Kafin su isa ya daɗe ta shirya kansa cikin kayan bacci, ya ɗauki Strowbeery ya cilla a bakinsa tare da rungome sweet bacci ya ɗauke sa.


Washe gari
Ko fituwa bai ba, saboda kwanan fargabar da yay haka nan yaji zuciyarsa babu daɗi gaba ɗaya,
A hankali ya miƙe daga shi sai 3gauther da Armless ya nufi art room ɗinsa,
Zama yay tare da ɗaukan pencil ya rufe idanunsa a hankali ya fara zane, yana gamawa ya buɗe idanunsa,
Sa wani irin sauri ya miƙe tsaye daya gani a saman zanan, a wannan karan idanunta a buɗe suke suna fidda wani haske mai masifar ɗaukan hankali,
Cikin tsananin mamaki da kuma tarin Al'ajabi ya sake duba zanan ƙarara kamannin.....












*_65-66_*
Julde, tsananin mamaki ya da tarin Al'ajabi daya kada ɓoyuwa a saman fuskar Abu Maleek, ya saki maki yana kallon zanan da yay, wanda gaba ɗaya zanan Zallar kamannin Julde ne ya bayyana, fuskarta ɗauke da wani ni'imtaccen Murmushi.


A hankali yay baya, tare da lumshe fararan idanunsa, yana sauke wasu tagwayen ajjiyar zuciya,
Wanda da ace wani yana kusa dashi babu shakka zai iya jiyu sautin fitar Numfashinsa.


Wato dalilin bai taɓa ganin ƙwayar idanun ta a zanan nasa ba, shine ya sanya ya kasa tantance zaman photon kamannin waye ya zana.


Gently ya Mike tsaye tare da fitowa daga cikin art room ɗin hannunsa ɗauke da Sweet dake faman ɗaga masa jela,
Kai tsaye bathroom ya shige ya sakarwa kansa shower tare da yiwa kansa handrayer, nan da nan gashin kansa yay wani irin murmurɗewa sai ƙyalli yake gwanin sha'awa.


Kansa ya shirya cikin wani farin cotton ɗin voyal, mai taushi da kuma santsin,
Ɗinkin half body ne, mai short ɗin hannu, hakan nan yaji yau yana son yin traditional dressing na Yaruba, hakan yasa ya ɗauki wani manyan murjani guda biyu, babba da ƙarami ya sanya a wuyansa, Wow! So ma sha Allah,
Ba ƙaramin kyau Abu Maleek yay ba.


Wayarsa ya ɗauka kana yay waje yana ɗan fidda numfashi,
Yana zuwa ya tsaya cak Saboda ganinta da yay a tsaye kusa da fridge,
Tana ƙoƙarin ɓalle murfin fresh milk,
Da wani irin hargitsastsan kallo ya bita dashi, a hankali kuma ya fara ƙare mata kallo frm head to toe,
Tun daga kan yatsun ƙafarta har zuwa saman ƴan cinyoyinta dake cikin wata ƴar,
Yaloluwar riga mara nauyi,
Idanunsa yaja ya lumshe yana wani sanyi na ratsa dukkan jikinsa, gyara tsaiwarsa yana ƙara ware rikitattun idanunsa masu ɗauke da wani irin sinadari a cikinsu.


Yarrr yarr! Haka Abu Maleek yaji tsigar jikinsa na mimmiƙewa, wani sihirtaccen sanyi na ratsa dukkan kofufin jikinsa, yana ratsa cikin ƙashin sa, dama ɓargwan sa baki ɗaya,
Yayinda ya kejin kamar ana sanya mayan ƙarfe ana fisgar zuciyarsa dashi zuwa gare ta!


Wani masifafan kyau tai masa a cikin idanunsa,
Ga wani ƙwantaccen gargasa da suke kwance a saman fatar jikinta,
Su kaɗai zai sanya mutum ya zauce.


Julde wacce bata san mene ke faruwa ba, tun sanyin safiya da Oumuu-Ayman ta shigo ta bata maganinta,
Ta fita bata sake shigowa, yunwar dake shirin galabaita da ita ne yasa ta fito ɗaukan fresh milk domin ta sanya a cikinta.


A hankali ta juya da niyyar zama a kujera taji tayi karo da mutum, da sauri tai baya tana ɗan zaro idanunta da suke cikin farin glass, wani mugun ɗagawa ƙirjinta da yay lokacin da idanunta ya sauka akan Abu Maleek,
Wanda yay tsaye yana kallon surar Jikinta,wacce take gab da zautar dashi, wani irin mayataccen kallon yake binta dashi, musamman saman wuyanta kasancewar rigar nada faɗi kana daman na net ne, shiyasa gaba ɗaya saman fararan fatar brest ɗinta suka bayyana,
Har shatin nipples ɗinta yake iya ganuwa.


Idanunta da shape ɗinta kaɗai ya isa zautar da mutum, but even her lips are looking luscious, succulent and irresitable every tensed man.....


Ajjiyar zuciya ya sauke a hankali kuma ya shiga takawa tare da matsawa inda take tsaye,
Kawo lokacin tuni Julde tayi ƙasa da idanunta, sam ba zata jure wannan kallon da yake mata ba,
Gashi gaba ɗaya ta kasa surutun da take yawan yi masa, ashe dan bata taɓa sanin waye shi a fuska ba,
Duk rashin kirki da surutun ku, baka isa kaiwa Abu Maleek ba, domin no way da zaka samu damar yin hakan.




Idanunta dake cikin glass ta rufe ruff, Jikinta ya shiga ɗan kyarma a hankali kuma ta fara ja baya,
Abu Maleek still idanunsa yana kanta duk inda yasu ya kuma ga dama cilla idanuna yake babu wani shamaki tsakaninsa da jikinta.


Ganin hakan yasa ta runtse idanunta gam gam,
Tana jin wata matsananciyar faɗuwar gaba na shigarta, yayinda linzamin dake juya akalar Zuciyarta yake ƙoƙarin bada gangar Jikinta zuwa garesa.


Ƙwayar idanunsa maƙale akan dugwayen wuyanta, wanda yake maƙale da wata farar siririyar necklace mai red ɗin stone,
Cak ta tsaya lokacin da bayanta ya hannu da bangon parlon, idanunta dake ɗan kawo ruwa ta buɗe tare da kallon jajayen laɓɓansa domin bata jin zata iya kallon cikin tsinin idanunsa,
Tunda idanunta ya buɗe ya kuma fahimci cewa shine Ballowo ɗinta,
Taji wani mugun nauyinsa ya shigeta, idanunsa suna haifar da mutuwar jikinta, ha wani kwarjini da yay mata a idanunta, saboda tsananin cikar haibarsa da kuma tarin Ilhama dake a gangar jikinsa.


Bakinta na ɓari laɓɓanta na rawa yayinda haƙuranta suke haɗuwa dana juna suna bada wani sauti ƙass ƙasss!!! A cikin kunan Abu Maleek,
Cikin wata raunatacciyar murya mai amsa kowa tace.


"Bal.. Ballowo!!"
Saukar Muryarta da kuma da ɗinta, haɗi da amonta suka taru waje guda suka haifar masa,
Da wani irin kasalallan yanayi a jikinta, al'amarin daya haddasa rufewar idanunsa ba tare daya shirya hakan ba,
Daƙiƙo, da seconni, haɗi da shuɗewar wasu mintunoni ya ɗauka idanunsa a rufe yana sauke wani irin numafashi..


Slowly kuma ya buɗe idanunsa wanda suka gama janyewa sosai, tare da yin ciki ya manna a saman wuyanta, kafin ya yi sama da kansa zuwa saman fuskarta,
A hankali kuma ya sake kusantuwa gareta kafin ya miƙa duk hannayensa ya ɗura saman shoulder ɗinta.


Ganin hakan ya sanya Julde cikin sauri tai ƙasa da idanunta tare da cure Jikinta waje guda bakin na rawa tace.
"Ballowo..me...me zaka min??"
Jajayan rikitattun idanunsa ya juya mata ba tare da yace komai ba, ya matsa kusa dashi, ganin yana shirin haɗa jikinsa da nata ne yasa ta ƙara mannewa da jikin bangon, tana sauke wasu masifaffun numfashi, as he coming closer and closer yasa ta ƙara narkewa Hawayen da suke maƙale da idanunta suka samu damar sakkowa.


Siririn tsaki yaja daga can cikin zuciyarsa hakan yasa babu mai fahimtar abinda yay,
Da ɗan rayuwar ƙarfi da Muryarta ta bar masa, ya ƙara matse shoulder ɗinta tare da jawota kusa dashi sosai, ya manne ƙirjinsa da nata, tare da yin ƙasa da hannunsa ya manna a saman ass ɗinta, kafin a hankali kuma ya riƙe hannunta tare da ɗura shi saman west ɗinsa, kana kuma ya tura sosai jikin gadon...


Wani irin masifafan harbawa zuƙatansu sukayi, a cikin daƙiƙon da bazai huce ɗaukewar numafashi da dawo dashi ba,
Lokaci guda haka kuma daƙiƙa guda suka lumshe idanunsa, kana a hankali kuma bugun zuciyoyin nasu yake yin wani irin sauya salo daga tafiya a hankali zuwa da sauri da sauri..


Gam ta riƙe west ɗinsa saboda rawar da jikinta yake mata, ƙasa yay da hannunsa dake bisa ass ɗinta tare da murzawa,da wani irin sauri taja numafshinta jin yana neman barin gangar Jikinta.


Idanunsa akan wuyanta wanda yafi tafiya dashi, kafin a hankali ya haɗe hannayensa da suke bayanta ya kama igiyoyin rigar da suka kunce rigar tana ƙoƙarin zamewa daga Jikinta, gashi kallon farko da yay mata, yasan babu bra a jikinta dalilin daya sanya kenan yay very close to her domin ya gyaran mata rigar.


Yana gama ɗaure igiyar rigar ya saki sauran Jelar, tare dayin ƙasa da kansa zuwa wuyanta, wani fitananan numfashi ya sauke lokacin da wani haɗaɗɗan ƙamshin turaran Al'ajabu daya ratsa dukkan kofofin hancinsa, a hankali ya furta "uhmsheyyyyyyhhhh!!!" Kafin ya manna softness lips ɗinsa a fatar wuyanta kana ya haɗe lips ɗin ji kake "Muuu'ahhh" ya saki wani sound mai kama da kiss sound.


Sanyin laɓɓansa da kuma taushin sajansa ya sanya Julde ƙara riƙesa tare da buɗe bakinta dake rawa wanda ya hawaye ya gama jiƙasu tace.
"Auchhhiiii, hyyyyyyyh Ballowo"
Zare fuskarta yay tare da ɗan haɗe gira kana ya zare daga jikinsa, tare dasa hannu ya tallafo haɓarta, idanunta a runtse a hankali ya saketa.


Cikin wata kasalalliyyar murya mai ɗauke da emotional sound yace.
"Cowardddd!!"
Ya faɗa a sanyaye tare fesar da iska daga cikin bakinsa.


"Yasubuhanallah!!"
Shine abinda Hawwa'u kawai ta iya faɗa kafin ta sulale a wajan ta zauna, saukar Muryarsa ba ƙaramin sauya mata akalar Zuciyarta tayi ba,
Ajjiyar zuciya ta sauke tare da buɗe idanunta,
Ga mamakin ta ko mai kama dashi babu, kamar walƙiya haka ya fice daga cikin Parlon..


Abu Maleek yana ɗan cije lips ya shige part ɗinsa, domin ya lura bata ma san cewa ya juye masa dukkan fresh milk ɗin a jikinsa bisa dole ya fara sutale kayan jikinsa tare dayin wulli dasu cikin datti clothes..


Bai fito daga cikin bedroom ɗinsa ba sai zhur prayer, yana dawowa kai tsaye Lambunsa ya shige,
A hankali yaja jikinsa zuwa haɗaɗɗan kujerar ya zauna,
Kana ya cikin nutsuwa ya zura fararan ƙafafuwansa cikin ruwan yana ɗan wasa dasu tare da yin playing vedio a Wayarsa.


Mostin da yaji ya sanya ya ɗaga idanunsa, a hankali ya sauke wani lamintaccen numafashi,
Saboda idanunsa daya sauka akan ta, mamakin abinda ya Kawo ta Lambunsa yake,
Ba tare da yace komai ba ya gyara zama tare da ƙurawa bayanta idanu tamkarey samu tibi.


Tsalle ta sakeyi saboda sam ta kasa ciro Fasadabir wanda yay mugun nuna ya kuma bata sha'awa, tsayawa tayi tare da kwaɓe fuska kana ta ƙara miƙa hannunta, tare da yin wani sabon tsalle, dai-dai lokacin data ciro Fasadabir ɗin ne kuma dai-dai lokacin da wata tsotsa ta sauka a saman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login