Showing 141001 words to 144000 words out of 161948 words
ya nufi inda yake hangen ruwa kwance, yana zuwa ya sanya hannunsa a cikin ƴar ƙaramar ƙoramar ya ɗebo ruwan da sauri ya ƙarasu wajan ya zuba mata a saman fuskarta, wata sassanyar Ajjiyar zuciya mai nauyi ta sauke hakan yasa Abu Maleek riƙe ta ya shiga faɗin "Mami what happened to you? Mene yay maki" girgiza kai kawa Queen Roomana take kafin ta zabura da sauri tana ƙara nuna Arɗo da yake zaune cikin irin mawuyacin hali, sai dafe kansa yake.
Mai Babban ɗaki tun kallon farko da tayiwa Arɗo taji wata iriyar mummunar faɗuwar gaba ta riskesa, duk yadda takai da daure abun gagara tayi, gashi dai babu kamannin amma tsantsar nutsuwa da kuma ƙyakkyawar lafazin sa ya riga daya bayyana waye shi.
Jiki a matuƙar sanyaye ta zame a wajan tare da kifa fuskarta a saman cinyoyinta, ganin hakan yasa Hadima Zubaida ƙarasawa wajanta da sauri tana riƙe ta.
Tashin hankalin data shiga itama ba'a magana Tabbas wannan Arɗo ne, amma yaci ace Arɗon rugar su yafi haka tsuma da kuma manyan ta waye wannan ɗin? Arɗo ne ko kuma wa ne?..
Kwacewa Queen Roomana tayi daga hannun Abu Maleek ta nufi wajan Arɗo tana faɗin.
"Shine, wallahi shine Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un wacce kalar rana nake gani ni Roomana? Wanne irin tsuhun abune yake shirin bayyana, Ubangiji ka sanya abinda nake gani a yanzu ya tabbata a zahiri, da Tabbas zanfi kowa farin ciki, zanji daɗi Ubangiji ya amshi addu'a na ya dubi Zaki mai ɗura masa zama Maraya gaba da baya ba, Subuhanallah!"
Sai kuma Numfashinta ya ƙara ɗaukewa ta ƙara sumewa a wajan.
Cikin tashin hankali Arɗo ya miƙe yana jin jiri na kwasarsa ya wani irin jan numfashi mai kama da shiɗewa, cikin wani irin firgitaccen sabon yanayi yace..
"What is this please? Hhh kai ba kai kawai akace kazo a madadin kuɗin fansar matar ka ba? To Meye ne kazo mana da wannan mutanan" cikin ɓacin rai da goshewar hankali Abu Maleek ya nufi wajan Arɗo yana zuwa, ya ɗaga hannu ya shaƙe wuyan Arɗo idanunsa na fitowa yace.
"Ina Matana? Where is she eh? Idan nine ba gani ba? Ka basu ita su tafi can Benin ni kuma gani duk abinda kuke so ya watar dani" ambatar sunan Benin ya sanya Arɗo yaji zuciyarsa ta ƙara bugawa wanda ƙarfin sautin bugun dai da ya sanya ya runtse idanunsa ji kake "Dammmm!!" Sautin da zuciyarsa ke badawa kenan.
Hannu Abu Maleek ya ƙara sanyawa zai shaƙe wuyan Arɗo, wani ƙyakƙyawan mari yaji an sauke masa a saman kamilalliyar fuskarsa mai ɗauke da tsantsar tashin hankali, da wani irin sauri ya sake wuyan Arɗo tare da juyawa domin yaga me marin, Queen Roomana ya gani tsaye Idanunta fal hawaye, bakinsa na rawa ya buɗe zai magana ta ƙara sauke masa wani irin mari ji kake "Tassss" runtse idanunsa Yay sosai, bawai dan yaji zafin marin bane a'a tsantsar mamaki da ta'ajjuji ne yasa yay Hakan, idanunsa ya buɗe wanda tuni suka cika da hawaye yace.
"Mami Matata? What i have done to you matana suka ɗauke wacce take tsananin buƙatar kulawa na, Matata mai ɗauke da gudan jini na Mami"
Cikin ɗaga Murya tace.
"Abeg shut up and leave from here kaji"
Wani irin kallonta yay lokacin da hawaye yake saukar masa cikin zafin da zuciyarsa yake masa yace "na tafi? Na bar matan tawa a nan a wajan Wannan azzalumin duk muguntar da sukai mata na baya bai isa ba sai sun kashe ta? Wallahi if anything happens to my wife uhm!"
Ya jinjina kansa kallonsa Arɗo yay, domin shi yama kasa fahimtar wace matar tasa, domin tunda aka kawo Yarinyar da idanunsa bai ganta ba, haka kuma sosai yay mamakin ganin Abu Maleek acikin Rugar nasu a karo na biyu.
Fuskarsa Queen Roomana a haɗe still hawaye na bin fuskarta tace.
"Akan matarka zaka ɗaga hannu ka daki Mahaifinka? Ka daki mutumin daya salwantar da rayuwarsa akan rayuwarka ta inganta, akan mace zaka manta tsantson daka fito daga jikinsa? Ko da baka sanshi ba jini da ƙwayar halitta za suyi maka jagora zuwa ga mahaifin ka? Jalaluldeen this is your father your real father"
Gaba ɗaya mutanan wajan, Queen Ayoola, Shakiru, Sharefddeen, Junaid, Otun da Agba Akin, suka juya a wani irin razane saboda jin abinda Queen Roomana take faɗi, Mai Babban ɗaki da Hadima Zubaida daman sun san kwanan zan can, kawai suna mamakin Yadda za'ai ace wannan shine Muhammad Jalal? How? Yaya akai hakan ya kasance, mutumin da duniya ta shaida mutuwarsa, mutumin da ko gawarsa ba'a samu ba sai toka, wanne irin curarran al'amari ne wannan? Wata iriyar Mummunar faɗuwar ne ya riski Sharefddeen idan ya kashe Tunde Muhammad Jalal kenan ya kashe mahaifinsa da kansa ba mahaifin Abu Maleek ba? Yaya akai Mahaifinka yake amfani da sunan Muhammad Jalal?
Abu Maleek kasa motsi yay sai jikinsa da ya ɗauki ɓari tashin hankali tsantsa ya bayyana a saman fuskarsa, yama kasa cewa komai sai sulalewa yay a wajan ya zauna idanunsa cike fal da hawaye, kansa gaba ɗaya ya juye baya fahimtar komai, baya gane yaran baki ɗaya, Tayaya Arɗon rugar Mahinjo zai zama mahaifinsa, mene ya sanya babu wanda ya taɓa cewa Daddy ba shine mahaifinsa ba? Kansa ya ɗaure zuciyarsa ta toshe ya zama kamar wani statue mafita kawai yake neman cikin sauke ajjiyar zuciya a can kuma cikin ransa ya shiga faɗin.
_" يامن لا يستحي من مسألته يرجى ولا،العغو إلا من قبلة، أسكوا إليك مالا يخغى عليك، وأيام مالا يعظم عليك، صلى على محمد وآلى محمد"_
Itace addu'ar neman mafita da samu sukuni da Abu Maleek yake ta maimaita wa a zuciyarsa, a hankali kuma ya sauke Ajjiyar zuciya.
Cikin rashin fahimtar zan can Arɗo yace "what the you mean by that, and who are you ban san ki ba, ban san waye ke ba i don't have any son a wannan duniyar sai ɗana Barkido, Barkido come out"
Ya faɗa yana ɗaga murya tare da tafe kansa dake masa bala'in ciwo, da sauri Barkido da Lamiɗo da suke cikin buka suka fito hannunsu ɗauke da wasu manyan bindiga, kallonsu yay sosai yace.
"Ku ɗauko garon nan ku fito dashi ko kame wan shan mutum kafin Oga yazo" da sauri Barkido ya nufi wajan Abu Maleek kullum da baƙin cikin dukan da yay masa yake kwana yake tashi.
Kafin ya ɗauke sa Queen Roomana tayi saurin faɗin.
"Kada ka kuskure kata ɓashi, idan yana son kama shi ya zo ka masa da kanshi yazo ka kashe da kansa, amma babu wani ɗa da kake dashi aduniya face Jalaluldeen da Khaleluddeen"
A wannan karan Arɗo ji yay bazai iya jure wa ba da sauri ya juya ya shige cikin bukkar tare da rufewa.
Queen Ayoola kowa mutuwar tsaye tayi, ta kasa fahimtar komai da ake faɗa.
Barkido kuwa tsayawa yay yana kallon Abu Maleek wanda shima kallonsa yake kafin cikin ɗaga murya yace..
"Hannu Umbani, yadda kazo har Rugar mu ka ɗauke min mata gashi ta dalilinka ta dawo har inda nake, kuma tunda nai sha'awar ta dole burina ya cika akan ta, dalilin rashin auranta da banyi yasa har yanzu na kasa samun sukuni bana Shauƙin ko wacce mace sai ita, kuma ina maka albishirin da cewa sai dai gangara jikinka ta bar nan badai kai ba"
Cikin sauri Abu Maleek ya nufi wajan Barkido kafin ya ƙarasa Barkido ya juya da gudu ya nufi gefen cikin wani daji.
Hakan yasa cikin azama Abu Maleek ya ɗaga ƙafa zai bisa da sauri Sharefddeen ya riƙesa yace.
"Kwantar da hankalinka Abu Maleek mubi waccen hanyar za muje har inda ya ɓoye maka Queen Hawwa'u" yana faɗin haka yay gaba da sauri Abu ya juya zai tafi saukar muryar da yaji ya sashi tsaya.
Yayinda Sharefddeen kuma ya kasa juyawa saboda tashin hankali da kuma ruɗani.
A hankali Bola ke sakkowa daga strains ɗin benen bayanta kuma Adams ne, daman tunda suka zo wajan suna ciki suna jiran lokacin bayyanar su yayi ne,
Murmushi tayi tace.
"Surprised ko? Kana mamaki wacce kasa wuƙa ka kashe da hannunka tana raye ko?"
Kasa motsawa Sharefddeen yay saboda mamaki yana sakkowa hannunta dafe da cikinta tace.
"Ba wannan ne abin mamakin ba, abun mamakin a gareka yadda a kullum kake son nuna cewa na Allah ne kai, Allahamdulillah naji daɗi dama kasance a raye, jin daɗi na Shine bayyana gaskiya da zanyi wacce ta jima a ɓoye, kayi amfani dani ta hanyar da kake so, ka yaudari rayuwarta saboda kawai bani da gata, ina Cikin halin maraici da kuma neman alhalin da zasu maye gurbin iyaye na, amma ne watsi da damata ta hanyar banzar huɗu bar da kake min a kullum" Shiru tayi lokacin da wani hawaye yake sakko mata cikin share yawa tace.
"A yau zan faɗa maku Wacece ni da kuma illar da nayi wa wannan ahlin naku, mummunan Abu Maleek" dafe kai Abu Maleek yay wai akansa duk ake wannan masifar da tashin hankali, akan sarauta? Akan Shegiyar kujerar da bai damu da ita ba sam, wacce kalar rayuwa ce wannan ace wanda ka yarda dashi ka amince masa shine zaici mutumcin ka? Shine zai yaudare ka yaci zarafin ka?? Wai Sharefddeen saya bambanta shi fiye da Adams shine yake shirin tarwatsa farin cikin sa?
Murmushi Bola tayi kafin tane waje ta zauna, yayinda kuma kusan gaba ɗaya Fulanin rugar Mahinjo suka ke waye su Abu Maleek, Junaid daman tunda Barkido ya tafi wajan nan ya mara masa baya da gudu.
Share wani Hawayen tayi tace.
"Kamar yadda kuka sani Sunan Bola,Nima ɗaya ce daga cikin ƙabilar ku, na rasa iyaye na ne ta hanyar tasarin mota, wannan dalilin ya sanya Sharefddeen ya ɗauke ni zuwa Alaafi a zummar Hadima,Wannan lokacin ban san hawaye Jalaluldeen ba, Shakiru kawai nake gani da Adams sai Sharefddeen, wata rana na fito da daddare ana ruwan sama sai kawai naji an riƙe ni tsananin tashin hankali yasa na gasa fahimtar waye? Bana fahimta sai ji nai kawai an cire min kaya a nan wajan aka keta min haddi na, nayi kuka sosai kamar raina zai fita musamman dana tabbatar cewa ba kowa yay min hakan ba sai Sharefddeen, wanda ya taimake ni, bayan sati biyu da hakan at the same time ana saka da ruwan sama na ƙara fitowa cikin dare, na zauna a inda na saba zama, babu jimawa Sharefddeen yazo ya fara kissing ɗina, yana ƙoƙarin kwanciya dani ne yaji sahun tafiya alamar wani zai zo, babu jimawa naga wani matashiyar saurayi mai ƙarancin shekaru,Amma ya girman sosai da sosai, hannunsa dafe da kansa dake zubar da jini, ƙyakƙyawa ne ajin farko ban taɓa ganin Mutum kamarsa ba, da idanunsa ya tsare ni ya kasa tafiya sai yatsuna fuska yake yana lumshe idanunsa, ga wani jini da yake ƙara zubu masa, sosai nai mamakin ganin yana zuwa kai na, gan gane komai ba naji ya shiga jikina, ji nai a lokacin tamkar wani ɗa namiji bai taɓa shiga ta ba, saboda girman halittar Jalaluldeen! Yana kammala abinda yake kuma naji ya fashe da wani irin gigitaccen kuka mai ratsa zuciya kafin a hankali ya miƙe cikin ƙasa da murya yace "Am sorry ki yafe min dan Allah" yana faɗin haka yay gaba abinsa daga wannan ranar kuma ban sake ganinsa ba, sai bayan wasu shekaru naji ance baya ma gari a kuma can inda yake yana fama da zazzaɓi da ciwon kai, bayan shekara guda lokacin Jalaluldeen shekarun 17 da hakan na fahimci ina da ciki sosai na shiga tashin hankali mara misaltuwa kai tsaye na faɗawa Sharefddeen sosai naga yana farin ciki, uhm mamaki tashin hankali da kuma abin al'ajabi gwajin farko da akai min ya tabbatar da cewa ina da cikin kuma bana kowa bane face na..
😂🙆🏾♀️ Jama'a naga tarin comments jiya musamman Nrml grp ɗina, Vip kuna bani dariya tabbas zan sanya ku a waƙar littafin TSINTACCIYA😍
*SARAUTAR MARUBUTA*
*_93-94_*
"Sharefddeen" a wani mugun sauri kiɗima gigita tashin hankali, al'ajabi da Zallar mamaki haɗi da ta'ajjujin Alamarin su duka mutanan wajan suka ɗaga kai suna Kallonta, hatta Abu Maleek sai daya kalleta with much surprise ga wani shock da yaji ya kama shi.
Wani kukan ne ya kuma kwance mata hakan yasa ga shiga rera kayanta ganin kukan ba mai ƙarewa bane yasa, Queen Roomana faɗin "ba lokaci kuka bane wannan, lokacin bayyanar da gaskiya ne komai ɗacin ta muna jinki" hawayen idanunta ta goge kafin tace.
"Sosai Sharefddeen yay farin ciki da samun cikin babu damuwar komai a ransa cikin jin daɗi ya same ni a ɗaki na yace..
"Naji daɗi wannan cikin sosai dear" da mamaki na kallesa nace "cikin shegen kaji daɗin sa? Bayan kasan babu kyau kuma haramun ne? Mene yasa baka samar da cikin ta hanyar halak ba sai ta haramun? Yanzu fa cikin shege ne a jikina" Murmushi Yay a wannan lokacin kafin yace "Eh cikin shege ne,amma yanzu zamu samar masa da nagartaccen uba, kuma halattacce" cikin sakin baki nace "As how?" Miƙewa tsaye yay yace "na daɗe da sanin idan har Jalaluldeen yana raye babu ni babu hawa kujerar mulki, idan har aka bawa Jalaluldeen wannan cikin a zummar ɗan sa tabbas soon or later dole zan zama King of Kanzaf lallai wannan haka yake" miƙewa tsaye nima nayi kafin nace "akan mene zaka ɗura masa abinda baiji ba kuma bai gani ba? Akan mene zance cikin Jalaluldeen ne bayan kasan ba nasa bane?" Murmushi Yay kafin yace "ina mamakin rashin wayonki dear, idan kika haihu ya tabbatar cikin shege ne a jikinki wannan hukuncin Zaman gidan kurkukun Alaafi zama irin na har abada ɗin nan, sannan baki isa kice nawa bane,idan kuma kin amince ni da kaina zan tabbatar cewa kin zama matar Jalaluldeen, kinga nan gama kece Queen of Kanzaf, yayinda ni kuma zan sa duk yadda nayi na kashe Jalaluldeen nasan babu wanda zai gaji Wannan kujerar a lokacin sai abinda zaki haifa, abinda kika haifa kuma mallakin Sharefddeen ne, daga nan sai kiyi idda na aure ki that all" a wannan lokacin fuskar Jalaluldeen kawai nake gani a idanu na, ba tare da wani tunani ba na amince.
Kai tsaye kuma wata rana naje har sashin Mai Babban ɗaki ina kuka kamar raina zai fita, kai tsaye na shaida mata abinda yake faruwa, sosai tai mamaki kafin tace "Ikon Allah kuma cikin bai bayyana ba sai a lokacin?" Da sauri Sharefddeen daya shigo yace "Kafin tazo wajanki sai da nayi mata tambayar nan kuma akaje asibiti likitoci sun tabbatar cikin kwanciya yay sai yanzu ya samu damar tashi" to banyi mamakin yadda Mai Babban ɗaki tai saurin amincewa ba, saboda Sharefdeen ya rufe bakin kowa sai abinda yace, kai tsaye kuma Oumuu-Ayman cikin damuwa da tashin hankali ta kira Salimerh akan ta kira mata Zaki anjima ana kira kafin ya ɗauka, yana ɗagawa Oumuu-Ayman tace "zaki da gaske wani abu ya taɓa haɗaka da Hadima Bola?" Shiru yay cikin halin zazzaɓi da rashin kuzari yace "Eh Oumuu na, I'm sorry" Shiru tayi tana jin wani hawaye na saukar mata kafin tace "To ka kyauta yanzu haka ciki ne da ita kuma cikin ka" buɗe baki yay zai ce wani abu Oumuu ta kashe kira..
A haka Abu Maleek na can Madrid King Tunde Muhammad Jalal ya aura masa ni wanda har kawo yanzu babu abinda ya taɓa shiga tsakani na dashi" Shiru tayi tana sauke ajjiyar zuciya yayinda Abu Maleek kawai yake kallonta yana jin wata sabuwar tsanarta na ƙara shigarsa a hankali tace.
"Daga nan sai wasan ya sauya, domin Sharefddeen ya dawo min ne kullum yana kwanciya dani a haka na samu wani cikin amma yace a zubar, bayan nan ya kawo min fuskar Hadima Zubaida akan yana son na dinga shiga ina jiyo masa komai dake faruwa, a nan naji labarin cewa wai za'a ce Maleek ya mutu saboda masu san ganin bayansa, wanda nima ban san su ba, Ni da kai na na ɗauki waya mai vedio da fuskar Hadima Zubaida sannan na kawo nace gayamin akai, dalilin daya sanya aka kulle Hadima Zubaida kenan, dab da Abu Maleek zai dawo kuma Sharefddeen ya kawo garin meriz yace aiki zai dashi, a cikin Abincin da Hadima Zubaida take kaiwa King Tunde Muhammad Jalal aka zuba Garin meriz ɗin, hakan yasa ya fara jinya sosai, batun auran Zaki da Kubraahh kuma dalilin rashin kasancewa da Abu Maleek ba yayi dani sai ake tunanin idan har aka aura masa mace mai ilimi zata iya janye hankalinsa, hakan yasa aka aura masa Kubraahh without his permission, ban san yaushe ne Abu Maleek ya samu ciwon juyewar tunani ba, amma ina da tabbacin dukan da akai masa aka shine ya jawo faruwar hakan, Soyayyar Abu Maleek ta fara a Zuciyata tun lokacin daya kira Oumuu-Ayman a waya na ɗauka naji muryarsa yadda yake zuba mata shagwaɓa, lokacin Oumuu na wajan Queen Roomana wacce aka bawa wani abu abinci Allah dai ya rufa asiri bata mutu ba, na samu Sharefddeen akan zan faɗi gaskiya saboda yace lokacin yay da zance wannan ɗan bana Abu Maleek bane, dalilin da yasa ya caka min wuƙa kenan"
Wani sabon kuka ne ya kwance mata bayan ta gama bayanin, Shakiru ne ya jinjina kai kafin yace "Ikon Allah! To yaya akai kika kasance a raye?" Kafin tayi magana Adams yace "Akan ido na Sharefddeen ya ɗauke ta zuwa Cikin ƙarshen Alaafi, jinin dana gani kuma ya ɗaga min hankali sosai matuƙa, a hankali a ɓoye nake binsa har ya ajjiye ta, yana barin wajan naje na ɗauke ta na kaita asibiti a nan take zama ana kula da ita kullum kuma ina zuwa wajanta, yau kuma bayan munshirya zamu taho nan naga ya dace azo da ita duk da bata gama warkewa ba"
Shiru kawai wajan ya ɗauka kafin aji kuma Bola ta saki ƙara tare da faɗin "Wayyoooo Abu Maleek bayanka" da wani irin sauri Shakiru ya riƙe hannun Sharefddeen mai ɗauke da wuƙa yana niyyar cakawa Abu Maleek a tsakiyar kansa.
Murɗe hannunsa Shakiru yay nan suka fara kokawa cikin rashin Sa'a kuma wuƙar ta goce tare da shigewa Marar Sharefddeen,wata iriyar Razananiyyar ƙara ya saki yana dafe mara saboda wuƙar akan J ɗinsa ta sauka.
Kuka Queen Ayoola ta sauke tana yadda zani tare da ɗura hannu a ka.
Dai-dai lokacin ne kuma Junaid ya ƙarasu wajan ɗauke ta Julde wacce take a sume