Showing 63001 words to 66000 words out of 161948 words
da zama a wajan wata duguwar kujera ta hutawa,
Jikin kujerar yabi ya ɗan kishin giɗa yana sauke ajjiyar zuciya tare da lumshe idanunsa, a hankali kuma ya zura ƙafafuwansa cikin ƙoramar,
Ya shiga wasa da ƙafafuwansa nasa yana jin daɗin sanyin ruwan nayi masa daɗi,
Wayarsa dake aljihu ce ta fara ƙara yana ji amma bai ko motsa ba, sai da akai wajan 5 miss call kafin ya zaro haɗaɗɗiyar wayar tasa,
Ganin sunan Salimerh yasa yayi answering call tare da sawa a speaker.
Daga can ɓangaren kowa Salimerh ce, zaune a cikin mota Dawowar ta daga makaranta kenan, har zata shiga ciki sai kuma ta tsaya tare da ɗaukan waya ta kira Abu Maleek ajjiyar zuciya ta sauke lokacin da taji ya ɗaga kiran.
Kafin a hankali ciki ƙasa da Murya yadda ba zata damesa ba tace.
"Fatan zaki yana cikin koshin lafiya?"
Ta faɗa tana ƙara gyara zama, sanin ba lallai yayi magana bane yasa ta faɗin.
"Zaki dan Allah dukkan abinda zai fito a hannun Mumy kada kaci, ko ruwa ta baka kada kasha"
Ta faɗa cikin raunin Murya.
Abu Maleek dake sauraranta ya ɗan gyara kwanciyar sa yana ware idanunsa tare saukar da idanunsa a saman nunannun gauva wacce sukai manya gwanin sha'awa,
Kafin ya Fito da tongue ɗinsa ya shiga taune leɓansa tare da sauke ajjiyar zuciya yace.
"Uhm"
Ya faɗa cikin wani Emotional sound domin tun ɗazo ya kejin jikinsa duk yayi weak.
Jin "Uhm" ɗin da yace ne yasa Salimerh fahimtar cewa ƙarin bayani ya keso cikin nutsuwa da kuma dadɗan kalami tace.
"I don't means anything Zaki, kowa da kalar zuciyarsa, Mumy mahaifiyata ce, amma kwanan na fahimci wasu muna nan abu a tare da ita, to dan Allah ka tayani tseratar da rayuwarka, idan kayi hakan zaka taimake ni ƙwarai wajan ganin nayi aikina ba tare da wani matsala ta faru ba, a yanzu hana da shaidar da zan nuna maka amma Tabbas ina zargin mahaifiyata akan abubuwan da suke faruwa a cikin Alaafin, Dan Allah Zaki daga nan har abada kada ka sake bawa Mumy dama a kanka, Kada ka sakar mata fuskar da zata baka wani abu tace kaci"
Ta ƙare maganar Muryarta na rawa kamar zatai kuka,
Tunda ta fara maganar yake sauraranta yake kuma fahimtar kalaman nata, amma tayaya Mumy zata cutar dashi? Baya tana bashi maganin damuwa a lokacin da zuciyarsa take masa ciwo? Wannan maganar ma ta sanya yaji yana ƙaunar zuwa wajan Mumy yaji idan zai samu abinda take basa.
Jin yayi shiru ne Kamar baya fahimta yasa Salimerh faɗin.
"Please Zaki saboda Allah ba danni ba"
Ganin tana shirin sauya masa lissafi yasa a ɗan kasalance ya buɗe baki yace.
"Ok!"
Ya faɗi hakan yana kashe kiran nata,
Kafin a hankali ya miƙe jin ana sallar Asar, ko flat ɗin bai koma ba ya nufi Masjid.
Oumuu-Ayman ce ta kalli Adams tace.
"Me kace?"
Ta faɗa like batai understanding maganar tasa ba, bai damu ba domin shike nema a wajanta dan haka ya gyara zama yace.
"Wacece wannan Julden? Mene haɗin ta da Alaafi??"
Murmushi Oumuu-Ayman tayi tace.
"Ba kowa bace ita ɗin face sabuwar Hadima wacce ake sanya ran zata zama Amintacciyar Hadimar sabon King"
Jinjina kai yayi cike da gamsuwa kafin yace.
"Zan ƴantar da ita, domin naji kamar ina sonta Oumuu-Ayman, kuma zan fita da ita waje domin a gyara mata idanunta"
Kallonsa kawai Oumuu-Ayman tayi tana Miƙewa tsaye tace "To babu matsala za muyi magana da Mai Babban ɗaki, batun ƴantar da ita kuma baka da wannan damar Aremo Adams Tunde Muhammad Jalal"
Ta faɗi hakan tana shigewa bedroom ɗin Julde tana zuwa ta sameta har bacci ya ɗauke ta, Abu Maleek kam bai dawo cikin flat ɗin nasa ba sai bayan sallar Isshā domin daga Lambun nasa gidan gonarsa ya shige.
Yana dawowa wanka yayi ya shirya cikin wasu Maroon ɗin Payjmas masu kyau, kana ya ja sweet ya rungome.
Washe gari
Da yamma a can bayan Masarauta cikin wani ƙaramin ɗaki wanda ciyayi ya lulluɓe, wata mata ce tsaye akan wata wata magidanciyar mace, wacce ta cure Jikinta wace guda, jikin nata sai ɓari yake kafin a hankali ta buɗe baki tace.
"Ban sani ba, ban san inda take ba, bana da Labarin komai akai, ki yarda dani"
Dariya matar dake kanta tayi kafin cikin fusata ta ɗaga hannu ta shararawa mai maganar mari tare dasa ƙafa ta danne mata ciki da ƙarfi kuma tace.
"Ohhh! Ba zaki faɗa ba? Munafuka ƙarya kike, babu wanda King Tunde Muhammad Jalal yake bashi amana yake faɗa masa sirrinsa kamar ke, Tabbas a wannan karan idan kikai gardama ba Iya kan ran King Tunde Muhammad Jalal zan tsaya, zan taɓa abu mafi suyiwa a Ranki, zan nakasta jikinki ko kuma na kawar dashi daga Duniyar baki ɗaya, wallahi billahi idan baki faɗa min inda TASWIRAR Masarautar nan take ba, zaki mamakin abinda zai aikatawa JALALULDEEN TUNDE MUHAMMAD JALAL"
A gigice matar ta riƙe ƙafar mai maganar tana faɗin.
"Duk abinda zaki aikata Kada ki taɓa Zaki, he's innocent Zaki ladama idan kikace a wannan karan zaki ƙara cutar dashi, ki rabu da Zaki ki rabu da King Tunde Muhammad Jalal duk abinda zaki ya tsaya iya kai na"
Ta faɗa tana sakin kuka, tare da ƙara riƙe ƙafar matar,
Wata dariyar matar tayi tana gyara tsawarta kafin tace..
"Au ashe fa maki da labari ko? Yanzu wajan 30days sa rasuwar King Tunde Muhammad Jalal kenan kinga Jalaluldeen kawai ya rage min idan har baki faɗa min inda zan samu taswirar da za'a iya fita da kaya a cikin Alaafi ba tare da kawo ya gani"
Cikin Kaɗuwa da tashin hankali matar tace.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Mijina ya rasu??? Kin kashe min miji....,"
Katseta tayi da faɗin
"Uhm ba kiga komai ki zauna kada ki faɗa min Inda Taswirar take zuwa gobe zaki samu labarin mutuwar ɗakin ki"
A gigice matar ta ɗaga Idanunta kana da ƙarfi tace "Zanan Taswirar yana ƙirjin Jalalu.....
😍👏🏻 Ayi weekend lafiya, mun kusa zuwa wajan daɗin kamar yadda na faɗa ba sauri nake ba, sannu a hankali za kuyi farin ciki...
Abu Maleek isn't free contact to subscribe 08119237616
*_47-48_*
"Ƙirjin Jalaluldeen" wata iriyar juyawa matar tayi tare da sauke idanunta akan wacce take gabanta tace "what!? Zanan Taswirar Alaafi a ƙirjin Abu Maleek? How can that be possible? Lallai Kunyi amfani da iliminku kun nuna min cewa ban iya komai ba, amma a wannan karan zan nuna maku cewa ban fito ba sai dana shirya, Tabbas zaku gane cewa ni murucin kan dutse ce"
Ta ƙare maganar tana sakin wani shu'umin e mai ɗauke da Zallar mugunta haɗi da mugun nufi a hankali kuma taja baya tare da neman wajan zama ta zauna saman kujera cikin nutsuwa da izza tace.
"Lallai kun raina ni, kuna da tabbacin cewa akwai mai farautar zanan Taswira wannan dalilin ya sanya kuka rasa inda zaku zana Taswirar sai jikin Abu Maleek? Well-done, what a great idea? Waye mai wannan tunanin tsakanin ko ukun nan?"
Shiru tayi tana kallon idanun matar dake gabanta wacce har zuwa lokacin bata daina kuka ba, saboda tashin hankali da take ciki, ga mutuwar King Tunde Muhammad Jalal data risketa a yanzu tayi mugun gigita mata lissafi, hakan yasa take kuka bil haƙƙi da dukkan Zuciyarta, tayi baƙi ta rame, saboda rashin saboda da kuma rashin Abinci wanda bata samun ishesshe ta sanya a cikinta.
Miƙewa Matar tayi tana gyara ƙyakkyawar sutturar dake Jikinta, cikin isarta tace.
"Any way kin taimaki rayuwar ɗan ki, da kuma kanki gaba ɗaya kuma idan ina da rai da lafiya wallahi sai naga ƙarshen Abu Maleek na maki wannan Al'ƙawarin"
A gigice Queen Roomana wacce kanta yake a ƙasa ta ɗaga Idanunta cikin sabon tashin hankalin daya shigeta take bin matar da kallo kafin a hankali ta sauke Ajjiyar zuciya cikin ranta take faɗin.
"Uhm Rashin sani yafi dare duhu, ina mai tabbatar maki da cewa duk ranar da kika yi gigin taɓa Zaki da niyyar samun zanan Taswirar nan ina mai tabbatar maki sai dai wata bake ba, duk yadda kike tunanin Alaafi ta huce haka, tsananin tsaro da kuma kariyarta basu taɓa bari ki samu abinda kike so ba, wannan dalilin ya sanya komai na Alaafi a shirye yake, koda kin kashe Abu Maleek kinyi banza domin ba iya jikinsa kaɗai wannan zanan Taswirar take ba"
Da sauri matar ta juya tana kallon Queen Roomana kafin ta nuna ta da hannu tace.
"Magana kikai? Did you just talk back at me Roomana???"
Girgiza kai kawai Queen Roomana tayi tana jin zuciyarta wani irin bugawa, tsoro da fargabar abinda zai samu Abu Maleek ya cika mata zuciya, so take tace ko sauya ɗaya takk ta fita da ita taga Zakinta,Amma ina bata da wannan damar tasan har abada ita da Abu Maleek sai dai a darin Salam, domin zuciyarta ka gab da muguwa Abubuwa sun taro sun yi mata yawa a Zuciya.
Hawayen idanunta ta share ta kifa kanta a saman cinyoyinta a hankali ta shiga sauke ajjiyar zuciya,
Wani killer smile matar tayi kafin a hankali ta juya tare da fita daga cikin ɗan ƙaramin ɗakin.
Mutumin dake gadin wajan ne ya rusuna tare da gaisheta,kai kawai ta ɗaga masa cikin iko haɗi da isa tace.
"Ka haɗa mata fruits ka bata, ka tabbatar tasha domin ina buƙatar ganin a raye saboda yanzu ne wasan zai fara, badai ta rusa min dukkan wani plans ɗina ba, Tabbas ni kuma zan sanya ɗan cikinta wanda take ji dashi ya kasheta da hannunsa Just watch and see"
Tana faɗin hakan tayi gaba Abinta, sa idanu kawai mai gadin ya bita a ransa yana jinjina rashin imani na matar.
A hankali ya fito daga cikin bathroom sanye da wani long white towel wanda ya sauka zuwa west ɗinsa, hannunsa riƙe da wani ƙaramin towel yana tsane ruwan dake zuba daga gashin kansa zuwa farar matar jikinsa.
Lumshe idanunsa yayi a hankali tare da jan wani reaction sound mai bayyana ƴar kasalar dake kwance a jikinsa,
Slowly kuma ya buɗe dugwayen eyes lashes masa wanda sukai wani kyau yalolo ruwa duk ya manne masu.
Stool yaja ya zauna tare da gyara zamansa sosai yay farcing mirror'n dake maƙale a jikin dressing mirror ɗin bedroom ɗinsa,
Cikin nutsuwa ya shiga shafawa jikinsa wani cream mai ƙamshi da laushi, kafin ya ɗauki handrayer ya gyara tsaftacciyyar sumar kansa, kana ya shafa mata Ginger Geminal Oil - hair kana ya ɗauki wani ribbon ya ɗaure sumar kan nasa daga ƙasa.
Body spray ya shafa a jikinsa kana ya nufi wajan wardrobe.
Wasu floral jacquard one button suit ya sanya, wanda suka kasance nevy blue ga wani taushi da suke dashi, sai wani Black Leather shoe daya sanyawa fararan ƙafafuwansa bayan ya sanya wata Black ɗin Safa,
Lumshe idanunsa yayi lokacin daya gama kimtsa kansa cikin tsaftatattun sutturar da sukai mugun mugun yi masa kyau,
Bayan ya kammala ne a kasalance yana cije laɓɓansa ya kwashi wayoyinsa tare da ɗaukan briefcase walking slowly ya fita zuwa babban Parlo.
Tun daga nesa idanunsa ya sauka akan Julde wacce take zaune a saman sofa, hannunta riƙe da Mug sai juya abu take da spoon da alama coffee ne, ya lura kwana biyu babban Parlon shi ne wajan shan iskar ta.
A kallon seconds 10 da yayi mata ya lura da kayan Jikinta taba sanye cikin Emilio pucci Silk kaftan dress, red colour ga wata siririyar necklace dake dugun wuyanta wacce ta ƙara haska farar fatar Jikinta, sai ƙafarta dake cikin Aquaholic Slippers ga gashin kan nan ya fito sosai ya kwanta har saman goshinta so ma sha Allah! Tayi kyau sosai Banda jajayen laɓɓanta babu abinda ke haske a fuskarta skin ɗinta kam sai glowing take.
Gajeren tsaki yana yana ɗauke idanunsa, kafin ya mayar da Kallonsa ga Oumuu-Ayman dake faɗin.
"Tubarkalllah, Ma sha Allah! Zaki yau kuma ina zaka?"
Ya tsuna fuska yayi wanda hakan ya ƙara fito da ƙyallin sajan sa wanda yasha Luxury Beard Oil.
A hankali yaci gaba da tafiya ba tare da yayi magana ba yana zuwa bakin ƙofa kuma ya tsaya tare da kallon Oumuu-Ayman cikin serious tone voice yace.
"Oumuu-Ayman Kada wannan Yarinyar ta ƙara sanya wannan abin aljanun is totally haram"
Ya faɗa yana haɗa fuska domin zahirin abinda yake ransa kenan.
Murmushi kawai Oumuu-Ayman tayi domin tuni zuciyarta ta fara harshashen wani abu dake shirin faruwa soon kuma dalilin hakan komai zai zama dai-dai, numfashi taja kafin ta kalli Julde wacce tayi rau rau da idanu kamar zata saki kuka.
Domin tun fitowar ta taji Zuciyarta ta fara bugawa ga wani fargaba daya risketa, ƙasa kawai tayi da idanunta ba tare da ta faɗi abinda take shirin faɗa ba sai Ajjiyar zuciya kawai da take saukewa.
"Zaka daɗe idan ka fita?"
Shine tambayar da Oumuu-Ayman ta cilla masa ba tare data bi ta kan mitar da yake ba.
Lumshe idanunsa yay
Yana jin zcyarsa na tsananta bugu shiyasa gaba ɗaya kwana biyun nan ya ƙaura cewa zaman babban Parlon nasa.
Ci gaba yayi da tafiya yayinda ya ɗura hannunsa a saman handle ɗin ƙofar yana faɗin.
"Oumuu na, zani sabon company dana buɗe na art mai suna J&J ART SHOE AND JERSEY DESIGNER"
Ya faɗa murya can ƙasa tare kuma da ficewa daga babban Parlon nasa ya nufi waje.
Mamaki ne ya kama Oumuu-Ayman, domin iya saninta bai taɓa ce mata zai buɗe wani company ba, shi dawa ya tsara hakan? Shiru tayi kana kuma ta miƙe tsaye tare da nufar inda Julde take.
Julde kam tunda taji ya buɗe ƙofa ya fita gaba ɗaya ta narke fuska kamar zatai saki kuka, kafin a hankali cikin raunin Murya mai kama dana shagwaɓa tace.
"Oumuu na ya tafi ko? Mene yasa ya bar mu a nan to? Shi baya magana ne?"
Ta jerawa Oumuu-Ayman tambayar lokaci guda, Murmushi kawai Oumuu-Ayman tayi kafin tace.
"A'a ba kiji yace company za shi ba? Yana magana ai ko yanzu yayi kawai bada kowa yake bane"
Ruwan dake cikin idanunta ne ya sauka zuwa saman innocent face ɗinta cikin ƙasa da murya tace.
"Oumuu mene yasa ni ba yayi min magana to? Ko dan na fishi kyau ne?"
Sosai maganar Julde ta bawa Oumuu-Ayman dariya sai ba tayi ba kawai tace.
"A'a Hawwa'u kin san bashi da sabo ne, amma idan kina yawan gai dashi zai saba, kema ai da laifinki tunda baki gaida yayan naki"
Da sauri ta ɗaga Idanunta ta sauke a inda take tunanin shine fuskar Oumuu-Ayman tana sakin Ajjiyar zuciya tace.
"Oumuu ban san mene zance ba ai"
Jinjina kai Oumuu-Ayman tayi cike da gamsuwa kafin ta gyara zama sosai tace.
"Da safe idan Kinji muryarsa kice Good morning Ballowo na, da Yamma idan Kinji muryarsa kice Good Evening, da daddare kuma Kice Good nigh kinji Daughter na"
Shiru Julde tayi tana nazarin abinda Oumuu-Ayman tace kafin cikin Muryar wacce take ɗauke da sautin kuka tace.
"Oumuu bazan iya ba ai, wannan ban san shi ba"
Cikin so da kuma zallar ƙauna Oumuu-Ayman tace.
"Kada ki damu zanta maimaita maki har ki iya, kuma idanunki suna buɗewa zaki shiga makaranta ki fara karatu"
Murmushi Julde ta saki wanda ya sanya gaban Oumuu-Ayman bugawa da sauri ta runtse idanunta a cikin zuciyarta take faɗin.
"Yasubuhanallah, why she look like familiar?? Her smile the way she's talking komai yayi mata kama dana wata amma Wacece? A ina ta taɓa ganin mai wannan kamannin na Julde lallai akwai wani abu dole ta matsantawa zuciyarta tunanin akan wannan abun daya kunnu mata"
Ta ƙare maganar tare da zubawa Julde idanu tana kallon yadda manyan dimples ɗinta suke lomawa.
Abu Maleek na fita fadawa suka fara zubewa suna gaisar dashi, fuskokinsu ɗauke da zallar murmushi domin ganinsa a halin yanzu yasa sunji wani sanyi a ransu sai suke ganinsa kamar late King Tunde Muhammad Jalal,
A hankali yake taka ƙafafuwansa a ƙasan carpet ɗin da aka shimfiɗa masa mai ɗauke da sunansa ɓaro ɓaro ABU MALEEK.
Tun kafin ya iso wani matashin saurayi ya buɗe masa ƙofar baya yana zuwa ya miƙawa matashin saurayin wayoyinsa da kuma briefcase ɗin hannunsa,
Da sauri matashin mai suna Sameer ya nufi mazaunin mai zaman banza suna shiga driver yaja da sauri suka bar cikin Alaafin.
Bayan tafiyarsu ne Adams yaja Ajjiyar zuciya, kafin a hankali yana jikinsa ya koma zuwa flat ɗin sa, a saman kujera ya zauna tare da rufe idanunsa da sauri kuma ya buɗe saboda ƙyakkyawar fuskarta wacce take masa gizo a cikin ƙwayar idanunsa, a kwana biyun nan so da kuma ƙaunar Yarinyar sunyi masa mugun kamo ko cikakken bacci ha yayi, tun yana ɗaukan abun a wasa har yanzu masa a zahiri yanzu kuma yake neman fin ƙarfinsa.
Miƙewa yayi tsaye tare da ɗaukan Wayarsa da key car ɗinsa ya nufi cikin motarsa da sauri ya jata kai tsaye kuma ya nufi Maxiview Eye Clinic.
Yana zuwa ya samu ganin wani babban Dr Jemeal cikin nutsuwa Dr Jemeal yake yiwa Adams bayanin kana kuma cikin harshen turanci kafin ya ɗura da faɗin.
"Makanta kala daban daban ce, Wani a haka ake haifarsa,Wani kuma gado yake ,Wani kuma accident, Akwai:
low vision
•macular degeneration
•glaucoma
•cataracts
•damage to the retina
Total blindness
Congenital blindness
Legally blind
Color blindness, Duk Wanda na faɗa babu Wanda accident yake sawa kai tsaye, Amma misalin accident din da yake saka mkanta •Car Accidents.
•Side Effects from Dangerous Drugs.
•Defective Products.
•Dangerous Toys.
•Chemicals.
•Dog Bites.
•Workplace Accidents.
•Fires and Explosions, Idan duk daya daga ciki ya faru ze iya kashe wani Abu a idoIdan wani abun kuwa ya mutu a ido, to ido ya tafi kenan"
Dr Jemeal ya faɗa yana turawa Adams wani Album na photo nan idanu, jinjina kai kawai Adams yayi kafin yace.
"Ina tunanin kamar haifarta akai dashi, amma I'm not sure gaskiya"
Ya faɗa yana ƙara duba Album ɗin hasalima gaba ɗaya babu idanun da yayi kama dana Julde hakan yasa ya miƙe tsaye, ganin haka yasa Dr Jemeal faɗin.
"Zaka iya kawota a duba ta sosai, idan da yiyuwar ai mata aiki sai ayi mata idan kuma magani ne sai a bata amma dole a duba ta first"
Kai kawai Adams ya ɗaga kafin yace.
"Ok thank you Dr Jemeal"
Murmushi Dr Jemeal Yay kafin yace "It's my pleasure Aremo"
Motarsa ya nufa inda Dr Jemeal Yay masa Rakiya har zuwa jikin motarsa.
Abu Maleek a hankali ya lumshe idanunsa tare yin baya kaɗan ya ƙara yin nutsu cikin lallausan kujerar haɗaɗɗan office ɗin nasa, wasu tagwayen ajjiyar zuciya ya sauke, tunani ne fal ransa amma wannan karan tunanin Hadima Zubaida ne ya faɗo masa, innocent woman like Her da wahala taci amanar Alaafi dole ya nemi ganawa da ita a week