Showing 75001 words to 78000 words out of 161948 words
yana miƙawa Abu Maleek Drugs ɗin, a hankali ya sanya farin hannunsa mai ɗauke da baƙar gargasa ya ɗauki maganin ya shiga dubawa, duk da cewa shima baban likita ne, amma baya da hurumi akan wannan ba ɓangaren sa bane.
Miƙewa cikin tarin nutsuwarsa ba tare daya kalli Dr Jemeal a hankali ya taka inda Julde ke tsaye, kamar mai tsoro haka ya kama tsakiyar tafin hannunta, ajjiyar zuciya ta sauke lokacin da ɗumin hannunsa ya ratsa ta.
Tafiya yake da ita dai da yaje baƙin ƙofa kafin ya tsaya yana ɗan fesar da iska yana shaƙar ƙamshin turaren dake fita daga jikin Julde yace.
"Ka shirya aikin"
Ya faɗin haka ya jata zuwa reception ɗin hospital ɗin da sauri driver ya buɗe masa ƙofa ya tura Julde ciki kafin shima ya shiga.
Around 8:40 ya iso gidan bayan ya tsaya a wani haɗaɗɗan restaurant Julde taci abinci, lokacin daya iso mutanan Alaafi sun kwanta bacci, sai masu tsaron ƙofar ko wanne flat..
Yana shiga Babban Parlo Oumuu-Ayman take zaune ta miƙe, kallon tsaf tai masa ba tare da tace komai ba ta kama hannun Julde zuwa bedroom.
Shima part ɗinsa ya shige ya zame Kayan jikinsa yay wanka, tare da yin alwala kana ya zauna ya fara duba aiki a system ɗinsa, ya nayi yana shan Inibi sweet na manne da jikinsa a haka ya gama ya kwanta.
Washe gari
Ya kama weekend a hankali yake tafiya a cikin Alaafi yana sanye da wasu pink ɗin kayan Yaruba, wanda sukai masa matuƙar kyau, gaba ɗaya traditional dress yay na Yaruba, yana tafe wasu fadawa na manyansa, a hankali ya tsaya tare da juyawa ya cilla musu wani kallo, da sauri sukai baya domin sun san mene yake nufi.
A haka ya isa can prison ɗin dake cikin Alaafin, wacce ake kai masu laifi hadda ɗakin duhu ake kai masu laifi mafi muni, kuma ko ɗan sarki idan yay laifi sai an kaisa.
Tsaye yay bakin wata ƙofa yana nan a tsaye kuma aka fito masa da Hadima Zubaida, tana ganinsa ta saki kuka tare da zubaiwa a ƙasa tana faɗin.
"Wallahi ban aikata komai ba, bani bace har abada bazan taɓa cin Amanar Alaafi ba, Zakina nasan zaka yarda dani ban aikata komai ba wallahi"
Runtse idanunsa Abu Maleek yana jin maganar Hadima Zubaida har tsakiyar ransa, sosai kukanta ke taɓa masa zuciya.
Buɗe idanunsa wanda sukai jaa yay kafin a hankali ya miƙa hannunsa tare da miƙar da Hadima Zubaida, ba tare da tace komai ba yay gaba, tsayawa tayi cak tana kallon bayansa ganin hakan yasa Abu Maleek tsayawa yace.
"Follow me"
Ya faɗa yana juyawa bayansa tabi gaba ɗaya tayi baƙi ta rame.
Tunda suka nufi cikin Family house ɗin Hadima Zubaida taji gabanta na faɗuwa, tsoro da rashin sanin abinda zai faru sukaiwa zuciyarta yawa, kai tsaye sashin Mai Babban ɗaki Abu Maleek ya nufa Yayinda Hadima Zubaida ke bayansa.
Murya can ƙasa yay Sallama Otun da Agba Akin suka amsa masa, suna mai binsa da wani irin kallo.
Can saman kujera kusa da Mai Babban ɗaki ya zauna kafin kuma Hadima Zubaida ta zube a wajan tana gaida Mai Babban ɗaki cikin tsawa Agba Akin ya kalli Hadiman Zubaida yace.
"Ke uban mene ya fito dake? Wane ya baki lasisin fitowa, wanne mara kunyar ne ya isa yaja da umarnin da Alaafi ta zartar a kanki"
Daga bayansa yaji Murya mai cike da nutsuwa da kamala ance.
"Ninee, Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal"
Da sauri Agba Akin ya juya bisa mamakin sa sai yaga ko inda suke Abu Maleek bai kallo hasalima idanunsa a lumshe suke.
Miƙewa tsaye Abu Maleek yay cikin bada umarni da nuna shima ya isa ya faɗa aji a cikin Alaafin yace "na wanke Hadima Zubaida daga zargin da ake mata"
Yana faɗin haka ya nufi waje ganin zai fita ne yasa Mai Babban ɗaki faɗin "Nan da kwana huɗu za'ai naɗin sarauta kafin bikin naɗin ya biyo baya ka shirya"
Gaba yay ba tare daya fahimci komai a zan can Mai Babban ɗaki ba.
Kai tsaye kuma Lambunsa ya nufa, Murmushi kawai Shakiru yay lokacin da Abu Maleek ya shige ta gabansa sam bai ma lura dashi ba, a hankali ya buɗe katafariyar ƙofar Lambun ya shiga yana shiga kuma ya ja ya tsaya saboda sauyin bugun zcyarsa da yaji, a hankali ya lumshe idanunsa ya shiga sauke tagwayen ajjiyar zuciya cikin ransa yake faɗin "Ya rabbi, what's this? Only God knows" ya faɗa yana buɗe idanunsa abinda idanunsa suka gani ne kuma ya haddasa sarawar kansa idanunsa suka fito waje, jikinsa ya hau rawa a hankali ya langwaɓar da kansa gefe kafin ya buɗe baki yace "O'ohhhh" ƙara buɗe idanunsa yay inda ganinsa ya ƙara sauka akan Abu mafi muni daya gani a rayuwarsa Julde ce zaune akan....
*Abu Maleek it's 500 via 08119237616*
*_55-56_*
Akan kujera hannunta riƙe dana Adams yana sakin mata wani murmushi tare da ɓare mata chocolate ya bata a baki,
Ita kuma Julde dai Murmushi take tana ƙara fuskantar derection ɗin inda yake tsaye.
Adams kam wani irin farin cikin da kuma daɗi ne ya mamaye dukkan zuciyarsa,
domin gaba ɗaya ya rasa nutsuwarsa tunda idanunsa suka ɗuro akan Julde ya zauce akan so da kuma ƙaunarta, wannan dalilin ya sanya ko fita bai sosai kullum so yake ya samu damar da zai keɓe da Julde suyi Shira ko zucyarsa ta samu sauƙi daga raɗaɗin da yake masa.
Murmushi Julde tayi har sai da fararan teeths ɗinta suka bayyana kafin cikin ƙaramar muryarta mai sauti da ratsa kunne tace.
"Hamma Adams wannan chocolate ɗin akwai daɗi zaka ƙara min?"
Ajjiyar zuciya Adams ya sauke yana ƙara matse hannunta da suke cikin nasa kafin yace.
"Why not my cute? Komai kike kawai let me know, i mean ki faɗa min"
Tana ƙara buɗe fararan haƙuranta tana faɗin
"to kai amma kana da kyau ko? Oumuu tace Ballowo bashi da kyau na fisa kyau"
Zuciyarsa taji ta buga da ɗan ƙarfi kafin kuma ya ɗan ja numfashi yace. "Uhm, ba kince Ballowo ya kaiki za'a buɗe maki idanu ba, so just wait and see idan idanunki ya buɗe za kiga komai, tunda ni baki son na kaiki"
Taɓe fuska tayi idanunsa sukai rau rau kafin kuma tace
"To bashi ne ya kaini ba, lokacin da kace zaka kaini asibiti to kana fita ya shigo ni kuma na faɗa masa"
Ƙuri yay mata da idanu, wato ita komai aka faɗa mata indai ta samu sake sai ta barbaɗawa Abu Maleek kenan,
Meye matsayinta wajanta, Kallonta yay kafin yace.
"Kawai kina shiru da bakinki kinga naji haushi" da sauri ta zare chocolate ɗin a bakinta kafin tace
"to kayi hqr kaji?"
Yana kallon jajayen laɓɓanta yace
"nayi"
hannunsa ya miƙa da niyar shafa lips ɗinta yaji an wani riƙe hannunsa tare da cilla shi baya.
Da sauri Adams ya juya dan ganin wanene, wani kalar zare idanu yay ganin Abu Maleek tsaye jikinsa sai rawa da ɓari yake, ga yadda idanunsa yay jajir jijiyoyin kansa sun fito sunyi raɗa raɗa sai huci yake fesarwa ya dunƙule hannunsa waje guda, idanunsa akan Julde wacce take zaune ta ɗan yi shiru saboda sauyin bugun zcyarta da taji, kafin kuma a hankali ta ɗura hannunta a saman armchair ɗin ta miƙe tsaye, a hankali Idanun Abu Maleek suka fara yawo akanta frm head to toe, tun daga kan yatsun ƙafarta zuwa leg da laps ɗinta, wanda suke waje saboda 3gauther ne a Jikinta sai wata red ɗin Kinomo.
Cikin wani irin sabon yanayi yaci gaba da bin surar Jikinta da kallo har zuwa saman brest ɗin wanda suke a tsaye har shatin nipples ɗinta kana gani, da sauri ya ɗauke idanunsa saboda kansa da yaji ya sara masa dalilin kallon nipples ɗinta da yay.
Hakan ya sanya yaji wani irin tsuma da kuma kyarma sun ƙara sauka a jikinsa, idanunsa sun ƙara rikiɗe wa gargasar jikinsa sun mimmiƙe hakan yasa yaji kalar wani fitananan abu na ratsa kofofin fatar jikinsa.
A hankali kuma yay sama da idanunsa inda ya sauke Kallonsa a saman lips ɗinta masu matuƙar kyau, sun ƙara yin pink so ma sha Allah! Eyes lashes ɗinta sunyi lub lubbb saman fatar idanunta saboda ƙasa da tayi da idanun nata.
Wata lafiyayyiyar ajjiyar zuciya wacce ta samu gurbin tawowa tun daga ƙasan zuciyarsa har ta bayyana a fili yaja, kafin a hankali kuma yaja ƙafafuwansa walking slowly ya ƙarasa inda take tsaye yana zuwa wajanta, yaja ya tsaya.
Sauke numfashi ya sake yi a hankali yaja fatar idanunsa ya rufe ruff, cikin sauri kuma ya fara jan numfashi saboda wani fitananan ƙamshin turaren ta da yake ratsa masa cikin hancinsa, wanda ya haddasa masa wani irin abu a ƙahon zuciyarsa!.
Ƙara matsawa yay sosai kusa da ita yana sake shaƙar ƙamshin ta mai tafiya da dukkan nutsuwarsa wanda bai san dalili ba, cikin nutsuwa kuma ya sake kusantar Jikinta sosai kafin a hankali kuma ya miƙa hannunsa idanunsa a Lumshe kamar bai bacci, ya ɗura hannunsa saman ququnta masu faɗi wanda suka zauna dasss a saman Jikinta.
Da sauri Julde ta sauke ajjiyar zuciya tare da ɗaga kanta wanda gaba ɗaya a ƙirjinsa ta tsaya, tsoro ya kamata hakan yasa ta fara ƙoƙarin yin baya sai dai chair dake bayanta ta tukareta no way to run, a hankali ya ƙara manna hannunsa a saman ququnta tare da murzawa da ƙarfi hakan yasa Julde saurin faɗin "Auchhhiiii!!!" Ta faɗa saboda wani irin abu daya tsirga mata tun daga babban yatsarta zuwa tsakiyar jijiyar kanta, zame hanunsa yay guda ɗaya tare da kamo hannunta wanda ta ɓoye a bayanta.
Zaro Hannun yay a hankali kuma ya tsorawa chocolate ɗin hannunta idanu, wacce ta kusan shanye park guda, kallan chocolate ɗin yay kafin ya ɗaga idanunsa yaga yadda bakinta motsi idanunta ya cika da hawaye, chocolate ɗin ya zare wanda ya sanya ta da sauri ta saki kuka tana faɗin "Ballowo ka ban chocolate ɗina" ko a jikinsa bai bi takan kukan ba yay cilli da chocolate ɗin can gefe guda.
Adams wanda yake tsaye ya kasa koda mutsi saboda mamaki da kuma tarin al'ajabin abinda Abu Maleek yake, mene haɗin sa da ita? Bayan Oumuu-Ayman tace Hadimar sa ce, Zallar kishin daya hango ƙarara a cikin ƙwayar idanun Abu Maleek shi ne yafi tayar masa da hankali, ganin yadda Julde ke kuka shi kuma ya tsaya kanta yana kallonta yasa Adams nufar wajan da sauri.
Yana zuwa wajan yace "come here my cute" saukar Muryar Adams cikin kukan nan ta yasa ta ƙara sautin kukanta tare ƙoƙarin lalubar hanya domin nufar inda Adams yake, gaba ɗaya ta a firgice take, ganin yadda Abu Maleek ya tsaya a kanta ya wani ɗura hannunsa a ququnsa ya bada faɗi yasa Adams faɗin "ka bata waje tun kafin na nuna maka siffata, Come to me my cute" a wani hargitse Abu Maleek ya juya tare da yin kan Adams yana faɗin.
"A gidan Uban baban wa ta zama your cute ɗin?? Heeeehh??? Tell me? Faɗa min when? How ta zama your cute Adams Tunde Muhammad Jalal??"
Ya faɗa lokacin da idanunsa suka gama rinewa da jaaa, gama ɗaya a wannan lokacin tunaninsa ya riga daya gama juye ya nufi ɗaya duniyar tasa wacce ta jima bai leƙa ba, hakan yasa baya tantance abinda yake faɗa da kuma wanda yake faɗawa,
Wani kallo Adams yaywa Abu Maleek kafin ya ɗaga hannunsa ya sharara mata wani wawan mari wanda yasa Abu Maleek saurin taune leɓansa, cikin ɗaga murya shima Adams yace..
"Wow! Yau akai na zaka sauke haukan naka ko??? Gwamma ka tabbatar da haukan ka ai, to idan hauka kake ji dashi Ni na fika, And ka ɗaure kan ka da kanka wannan abinda kayi yasa saina tuna maka asiri na faɗawa jama'ar Alaafi da Kanzaf cewa kai ka ɗauke mahaifiyar mu akan wani dalili naka, ko kuma saboda kana ƙwaɗayin ka zama King of Kanzaf ko????? Faɗa min mana Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal??? Kana maganar yaushe Julde ta zama my cute, baka so hakan ba ko? Na sota a lokacin da idanuna suka sauka akan ta a part ɗinka daka ɓoye ta ciki, And i love her, bana tsoro ko shakka I'm going to marry her no matter what happen!!!"
Ɗaya daga cikin masu kula da Lambun ne ya juya da sauri ya nufi cikin Family house ɗin, domin ganin abin nasu yana neman rikicewa ya zama babban tashin hankali, abinda ba'a taɓa samu cikin Alaafi ba, sai gashi yau ƴan ɗaki guda, wanda suka fito ciki guda gashi yanzu suna ƙoƙari kaiwa juna duka Dalilin shigowar baƙuwar yarinyar da babu wanda yasan Wacece sai Abu Maleek da Oumuu-Ayman, hakan yasa yana zuwa ya nufi sashin Mai Babban ɗaki yaji Sa'a hadda Oumuu-Ayman a wajan, jikinsa na rawa ta zube a gabanta kallonsa tayi kafin yay mgn Oumuu-Ayman ta miƙe tana faɗin..
"My Jalal!!! Zakina"
Domin daman tun ɗazo gabanta ke faɗuwa wanda bata san dalili ba, cikin sauke numfashi Hadimin yace "Mai Alaafi da Kanzaf baki ɗaya sabon al'amari na shirin faruwa, ga Aremos can Adams da Abu Maleek suna faɗa akan wata budurwar yarinya"
Mai Babban ɗaki sandanta ta ɗauka ta miƙe tsaye tare da faɗin "Zaki?? Adams?? Suna ina?"
Oumuu-Ayman kam tuni tayi waje, Mai Babban ɗaki ma bayanta tabi lokacin da Hadimin yake faɗin "Suna Lambu" suna fitowa sukai karo da Bola wacce take cikin shiga ta alfarma ganin yadda suke a rikice yasa ta mara masu baya.
A karo na biyu Adams ya ƙara kai hannunsa ya ɗauke Abu Maleek da wani gigitaccen mari mai tafiya da numafashin mutum, amma Abu Maleek ko motsi bai ba, sai jikinsa daya tsananta rawa haƙuransa suka shiga ƙara suna haɗe juna tare da bada wani sauti ƙass ƙasss, cikin ɓacin rai Adams yace "Mad!!! I love Julde! I love her with all my heart and auranta zanyi mene haɗin ka da ita? Hadimarka bata da ikon zama Matarka Understand?? Wallahi abin takaici yake bani wai mahaukaci like you shine younger brother ɗina ne, I repeat myself da Capital letter I love Julde do whatever you want to do Mad!!!"
Yana faɗin hakan tare da nufar inda Julde take wacce ta durƙoshe a wajan tare da tura kanta tsakanin cinyoyinta tana kuka, gaba ɗaya sun gigita da hayaniyar su, ya miƙa hannunsa da niyyar taɓa Julde yaji Abu Maleek yay masa wata wawiyar shaƙa tare da ɗaga sa sama kamar wanda zai masa rataya, idanun Adams ne suka fito waje saboda sosai Abu Maleek ya sheƙe sa, wato duk ihun da Yaywa Abu Maleek bai motsa daga taɓa Julde ya ƙara ficewa a tunaninsa Wonderful!!
A dai-dai lokacin ne kuma Oumuu-Ayman da Mai Babban ɗaki da Bola hadda Queen Ayoola wacce labari yakai mata, suka ƙarasu wajan, ganin yadda Abu Maleek yake ƙoƙarin yin kisan kai kuma ɗan uwan yasa a gigice Mai Babban ɗaki faɗin "stop it Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal sake sa" banza yay mata domin baya fahimtar abinda take faɗin, Oumuu-Ayman ce ta nufi wajan Julde tare da miƙar da ita tsaye.
Janta tayi zuwa wajan Abu Maleek cikin yanayin damuwa ta kalli Julde wacce take kuka tana riƙe Oumuu-Ayman tace "Go to him, jeki wajan Ballowo and tell him ya saki Adams kinji Daughter ke ɗaya zaki faɗa a yanzu ya saki Adams, ko kina so Ballowo ɗinki ya kashe Adams shima a kashe sa?"
Da sauri Julde ta girgiza kanta idanunta na zubar da hawaye tace "Oumuu-Ayman tsoro na keji, zai min faɗa zai dake Ni" kanta Oumuu-Ayman ta shafa tace "what faɗa? Ba zaki fahimta but soon or later Zaki gane, Ballowo ɗinki har abada bai dukan ki I'm telling you maza jeki"
Ajjiyar zuciya Julde ta sauke a hankali ta fara miƙa hannunta domin tana gab dashi.
Wani irin faɗuwar gaba ne ya samu Bola, Wacece wannan yarinya? Mene matsayinta wajan Abu Maleek? Queen Ayoola itama zare ido tayi gabanta ya shiga faɗuwa, Mai Babban ɗaki kowa daman Alrdy tasan da zaman Julde.
Hannunta ne ya sauka west ɗinsa da sauri ta faɗa jikinsa tare ƙanƙamesa tana sakin wani kuma bakinta na ɓari tace "Ballowo!!!! Ballowo na!!! Ka saki Hamma Adams dan Allah!!"
Idanunsa yaja ya lumshe lokacin da yaji saukar muryarta cikin kunansa, a hankali kuma gargasar jikinsa ta fara zubewa ƙasa tana sauka, jikinsa ya tsahirta da rawar da yake masa, amma ya gagara sakin Adams ganin hakan yasa Oumuu-Ayman faɗin "repeat again Daughter, ƙara faɗa begen him to stop"
Duk da cewa Julde bata fahimtar abinda Oumuu-Ayman ke faɗa ta gane cewa Abu Maleek bai saki Adams ba, ƙara sautin kukanta tayi tana manna kanta tsakiyar ƙirjinsa tare da zagaye dukkan hannunta a saman ququnsa tace "Zan bar gidan nan, idan baka saki Hamma Adams ba, Ballowo na!!!!! Allah zan daina son......,"
Tun kafin ta ƙarasa faɗa yay cilli da Adams da wani irin sauri ya juya inda take ya ƙura mata idanu sai kuma kawai ya sanya dukkan hannayensa ya ɗauke ta cak yay cikin part ɗinsa da ita.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Shine Abinda Bola ke faɗa, kalmar Julde ta ƙarshe tayi mugun mugun gigita mata lissafi da sauri ta nufi wajan Oumuu-Ayman tare da faɗin "Wacece??? Who is she? Kimin bayani Wacece wanna take tare da mijina har yake sanya hannu ya ɗauke ta abinda bai taɓa yimin ba"
Kallonta Oumuu-Ayman tayi kafin tace "calm down Bola I'll tell you everything amma give me some times" tana faɗin hakan tai part ɗin Abu Maleek zubewa Bola tayi a wajan tana kuka.
Hadima Zubaida dake raɓe can da sauri ta juya tare da rufe bakinta tana sakin wani irin kuka mai raɗaɗi da kuma ɗaci a zuciya, Adams kam har yanzu bai miƙe daga kwancan da yake ba ya riƙe wuyansa da hannunsa yana sakin numfashi ganin haka yasa Mai Babban ɗaki nufar wajansa.
Abu Maleek na shiga flat ɗin sa, kai tsaye part ɗinsa ya nufa da ita, da sauri Oumuu-Ayman ta shiga tana faɗin "Jalaluldeen!!! Jalal!!"
Wanda rabon data kira sunansa a haka harta manta, yana zuwa ya cilla Julde saman bed ɗinsa ƙara ta saki Lokacin da kanta ya bugu da frame ɗin gado, juya yay yana kallon Oumuu-Ayman kawai sai ya faɗa Jikinta ya rungome ta sosai yana sakin wasu wahalallun numafashi, jikinsa duk rawa yake, rungomesa Oumuu-Ayman tayi tana bubbuga bayansa, tana jin yadda zucyarsa ke harbawa da ƙarfi rabon daya rungome ta haka harta manta tun lokacin da aka bashi Bola matsayin mata.
"Calm down Zaki? Don't cry okay?