Showing 30001 words to 33000 words out of 161948 words

Chapter 11 - ABU - MALEEK Book Complete BY SARAUTA.txt

05 Jan 2025

6589

*BY*
*NIMCYLUV*












*23-24*
Fasa wani gigitaccen ihu tare da cusa fuskarta a tsakiyar ƙirjinsa, gaba ɗaya jikinta rawa yake al'amarin daya kusan ɗauke numfashinta kenan,
Gudun ruwan saman da taji mai ɗauke da iska haɗi da tsawa ya haddasa mata tsayawar numfashinta na wani lokaci,
Abu Maleek kam sandarewa yayi waje guda, tare da ko mawa baya ya jingina da jikin bishiyar, gaba ɗaya ta gigita sa ya ɗauka Aljanin gaske ta gani koma wani abu cutarwa,
Sauke numfashi yayi tare da fesar da iska daga cikin bakinsa, daga can ƙasan zuciyarsa kuma wani irin ɗaci da ƙona ya keji,
Ga wani juyawa da kayan cikinsa su kayi sabida wani mugun wari daya shaƙa, ya kuma tabbatar a jikin Julde aka samu warin, tamkar mushe ya mutu.


Gajeren tsaki yaja yana mai cije bakinsa da sauri kuma ya sanya ƙafarsa ya tureta daga jikinsa, a ransa yake faɗin.


"Mayya"
Ya ƙare zan can zucin yana matsawa can gaba, tare da haɗe jikinsa waje guda sai tsuma yake saboda gudun ruwan ya firgita sa ainun,
Ga wani sanyi dake ratsa kofufin jikinsa,
Wanda yake gab da illatasa, da kuma tasu masa da tsuhuwar cutar daya manta da ita.


Da wani irin sauri ya tura kansa tsakanin ta fukan hannayensa, saboda wata gigitacciyyar tsawa da akai,
Wacce ta tawo da wani irin ruwa mai ƙarfin gaske har bai sai lokacin daya buɗe baki cikin Muryar kuka da kuma wanda tsoro ya gama ratsa wa yace.


"Wayyoooo Oumuu na"
Ya faɗa yana shagwaɓe fuska, jin Muryarsa kamar yana shirin sanya kuka ne kuma ya sanya ta tsayar da nata kuka tana mamaki hali irin na Abu Maleek
Domin ta tabbatar shi ɗin babbane irin sosai ɗin nan.
Amma mene ya sanya ya saki wannan ihun, Shiru tayi tana sakin Ajjiyar zuciya kafin taja numfashi tare da ɗan juya juyayyun idanunta,
Cikin siririyar muryarta kuma mai ɗauke da ƙuruciya da kuma zallar shagwaɓa tace.


"Kai ma kana jin tsolo ne?"
Ta ƙare maganar tana mirgina kanta can gefe alamar ita tsoran ta keji,
A karo na farko kuma ya ɗaga idanunsa tare da saukesu a saman innocent face ɗinta,
Kyakkyawa ce sosai, amma yunwa da kuma wahalar rayuwa sun ramar da ita,
Fuskarta firit idanunta ya tsorawa idanu ganin yadda take kallonsa,
Kafin ya taɓe bakinsa kamar bazai magana ba sai kuma ya cije lips ɗinsa yana fidda numfashi,
Can ƙasan maƙoshinsa yace.
"Daina kallo na, ko na tsole idanun, witch"
Ya faɗa yana mai ɗauke idanunta daga gare ta, saboda mugun haushin ta ya keji,
Da ace bata zo inda yake ba ai da shima bai ji tsoran saukan ruwan saman ba,
Turo baki tayi tana marai-raice fuska, ita mugun daɗi ta keji ganin mutum kusa da ita,
Tayi imanin bazai cutar da ita ba,
Gashi ita tana bala'in sunyin magana dashi amma ta fahimci ɗan neman rigima ne, kuma shagwaɓaɓɓe ne shi ɗin daga jin muryarsa,
Matsawa tayi gefe kafin ta haɗe Jikinta waje waje da sauri kuma tace.


"Ayyah! Nifa ban kalle ka ba, babu wanda na taɓa gani a duniya"
Ta faɗa Idanunta na cika da hawaye,
"Ji wani iya shege, duk manyan idanun nan ace bata kansa ba to uban ne take kallo, da wani ɗan ƙaramin baki kamar iloka"
Ya ƙare zan can zucin yana murguɗa mata baki kamar wata mace,
"Me kace?"
Cikin damuwa ya taɓe baki yana shagwaɓe fuska tare da haɗe hannayensa yace.
"Ƙilan aljanu irinki kike gani, Momo"
Washe baki Julde tayi har sai dai dafaffun haƙuronta suka bayyana, da sauri ya sanya hannunsa ya toshe bakinsa sabida wani mugun wari daya kawo masa ziraya daga cikin bakinta zuwa hancinsa,
Juyawa yayi tare da bata baya,
Julde da bata san abinda yake faruwa ba, cikin son yi masa magana da kuma surutun da take da shi tace.
"To aini bana gani, ban taɓa ganin kowa ba, ni Makauniya ce fa, ban taɓa damuwa da sai naga wani ba, amma kai dai ina son ganinka saboda ina son ganin yadda Aljanu suke"
Ta faɗa tana zare idanu alamar ɗan tsoro,
Jin shiru yayi yawa yasa ta ƙara matsawa gaba idan take tunanin yake zaune tace.
"To kaima kana kallo na ko? Kaga askin da akai min? Ko gashi ya fara fesuwa ne?"
Ta faɗa tana shafa kanta jin kan suwait ne babu alamar gashi yasa ta kwaɓe fuska, tare da yin shiru tana sauraran kalar numfashin da Abu Maleek yake fiddawa Murmushi tayi tace.
"Ayyah ashe aljanu ma nayin bacci, nima bari nayi"
Abinda bata sani ba, tunda ta fara magana ya sanya tafukan hannayensa ya toshe kunnuwansa, ya shiga sauke numfashi,
Yana jin yadda cikinsa ke juyawa ga wani yawo da yake tarar masa,
A ransa yake faɗin "zata kashe ni da wari, Uhm datti girl"


Sanyin safiya ne mai ɗauke da daddaɗar iska mai daɗi, ga wani ƙamshi ƙasa dake tashi, domin ruwa akai sosai jejin Mahinjo yayi wani irin daɗin gaske,
Saboda tarin ni'imar dake garin, ga kurayen ciyayi sunyi sharr dasu, bishiyoyi sai Kaɗawa suke.


A hankali ya shiga buɗe gajiyayyun idanunsa, kana kallon yadda ya kwanta kasan ba daɗin baccin yake ji ba, babu wanda zai taɓa cewa Abu Maleek zai iya shiga wannan garin bare har yayi rayuwa cikinta,
Amma Ubangiji shike tsarawa mutum rayuwa yadda kake so sam ba haka kake samu ba,
Kyawawan farar idanunsa ya ware sosai a cikin jejin,
Shi kansa jejin da kuma wether wajan yayi masa bala'in kyau,
Miƙewa yayi tsaye tare da ɗura hannayensa a saman waist ɗinsa ya shiga kallon wajan sosai,
Ajjiyar zuciya ya sauke a hankali kuma ya juya sabida motsin da yaji,
Sweet ya gani a gefensa tana girgiza Jikinta ga wani ƙaton kifi a bakinta sai motsi yake,
Idanunsa ya zare tare taune bakinsa,
Ba tare kuma da yace komai ba,
Ya nufi wajan wani ƙwantaccen ruwa mai kyau wanda ya kwanta a cikin rami, tsugunawa yayi ya shiga ɗaura alwala, kana ya wanke bakinsa tass, gently ya miƙe tsaye ya nemi wani waje mai Tsarki ya gabatar da sallah,
Lumshe shanyayyun idanunsa yayi, sai yaushe zai cimma Birnin Bera ne? How long zai kasance a haka duk wanda ya kansa sai ya ɗauka mahaukaci ne,
Ajjiyar zuciya ya sauke yayi kewar abubuwa da yawa masu muhimmanci ƙwarai da gaske a rayuwarsa amma yaushe ne komai zai dai-dai-ta, wannan dalilin ya sanya baya son zaman 9ja, ba komai brain ɗinsa take ɗauka ba,
A karo na biyu ya ƙara sauke ajjiyar zuciya yana jan numfashi kaɗan, Miƙewa tsaye yayi yana ɗan shaƙar iskar dake Kaɗawa, tunanin abinda zai samu ya sanya a jikinsa yake, gaba ɗaya yunwa ta gaba wahalar dashi, bai da cin abinci amma duk bayan 1hour sai ya sanya wani abu a bakinsa ko Inibi ko Apple,
Walking slowly ya fara yana ƙarewa cikin jejin da kallo.


Ruwan dake ɗiga ɗis ɗis ɗis daga jikin leaf zuwa saman fuskarta, ya sanya ta shiga motsawa a hankali da yin miƙa, tana ware blue ɗin Idanunta,
Shiru tayi kamar bai nazari sai kuma ta kwaɓe fuska tace.
"Ayyyah ya tafi kenan bai tashan ba har gari yayi haske"
Ta ƙare maganar tana Miƙewa tsaye tare da tattare duguwar Jallabiyar data yi mata yawa sosai, a hankali ta fara tafiya tana ɗan mimmiƙa hannunta a haka take samawa kanta hanya,
Harta isa gaɓar kogin daya cika sosai, Kamar zai ambaliyya, sam ta manta da batun ruwan dake cikin jejin.


Abu Maleek ƙara ware gajiyayyun idanunsa yayi a gefen ruwan yana kallon tarin manyan kifin da suka fito daga cikin ruwan, zuwa gefen gaɓar kogin, sanadiyyar ruwan da akai sosai, sweet nacan gefe tana ta kokawa da wani ƙaton kifi, ajjiye kifin tayi ta taho da gudu zuwa inda Abu maleek yake tsugune,
Tana zuwa ta tsaya gabansa tana kaɗa jela, slowly ya ɗaga idanunsa ba tare da yace komai ba,
Ganin kallon da yake mata ne ya sanya ta tafi da gudu a hankali ya shiga Binta da kallo har zuwa inda yaga taja ta tsaya,
Fararan yatsun ta ya zurawa idanu, kamar ka taɓa jini yayi tsartuwa,
Tsaki yaja sai kuma a lokacin ya kula gaba ɗaya tazararta da cikin ruwan bashi da yawa, bawai kuma tsayawa tayi ba ci gaba da tafiya tayi, al'amari daya sanya take ƙara kusantar ruwan kenan,
Gajaran tsaki yaja yana tunanin wannan guntuwar Yarinyar sai ta bashi ciwon kai kafin ya bar wannan garin,
Miƙewa tsaye yayi yana mai harɗe hannayensa,
Tare da ƙare mata kallo, ganin yadda take mimmiƙa hannunta gaba, sai a lokacin ya tuna da maganarta dake cewa, bata gani bata taɓa gani kowa ba,
Da gaske Makauniya ce? Is she a blind? Mamaki ne ya kamasa ga idanunta manya kuma blue kamar nasa amma duk wannan ƙaton idanun ace bata gani,
To mene ya kawo ta cikin wannan jejin mai tarin hatsari? Me take a cikinsa? Shi kaɗai yake wa kansa wannan tambayar ganin ita kaɗai zata bashi amsar tambayar yasa ya yatsunsa fuska yana mai shigar da laɓɓansa cikin bakinsa ya shiga tsotsa.


Julde cikin nutsuwa da kuma ƙarancin kuzari taci gaba da jefa ƙafafuwanta,
A haka ta isa dab da gaɓar kogin, cikin rashin fahimtar inda take sanya ƙafafuwansa ta ɗaga ƙafarta damanta da niyya ci gaba da tafiya,
Babu zato bare tsammani taji.




*DAN ALLAH DAN ANNABI KIJI TSORAN KADA KI KARANTA MIN LITTAFI BA TARE DA KIN SIYA BA, 08119237616*




An sanya ƙafa tare dayin ball da ita gaba ɗaya tayi baya zata faɗi ya sanya ɗaya hannunsa ya daga tsaye ya riƙo gaban rigarta, wahalalliyar ajjiyar zuciya ta sauke tana mai zare manyan Idanunta,
Ta gaba sanya ran cewa taje ƙasa, ƙuri tayiwa wani waje hakan ya sanya Abu Maleek yin tsaki tare da sakinta gaba ɗaya ta faɗa saman,
Jiƙaƙƙen yashin dake wajan, gani yake kamar tana sani take zare masa ido, a fili kuma ya lumshe idanunsa tare da faɗin.


"Kamar wani tafi ido"
Ya faɗa yana mai ɗaukan babban kifi tare da yin gaba Sweet ma kifi ɗaya ta ɗauka ta biyo bayansa.


Dafe kai Julde tayi abinka da kai babu gashi, Idanunta ne ya cika da hawaye sosai taji zafin faɗuwar da tayi ko kuma tace ya yar da ita,
Baki ta murguɗa a fili tace.
"Wayyoooo kai na"
Ta faɗa tana runtse idanunta, ganin zaman sam ba zai mata ba ya sanya ta miƙe tare yin alwala duk ba wani iyawa tayi ba,
Sallah tayi kana ta zauna a wajan tana mai jin yunwa ga kuma ciwon da ƙirjinta yake mata.


Bayan yayi kyasto, ya haɗa dotsen wuta da wani a saman ɗan busassun itacen daya samu, nan da nan wuta ta tashi,
Faɗaɗa fuskarsa yayi da Murmushi yana bala'in son tsuntsaye da kuma irin wannan halittun, kifin daya suke a cikin wani ƙaton sanda ya ɗauko,
Kana ya ɗura saman wutar ya fara gasawa,
Almost 20minutes kafin kifin ya gasu sai tiriri yake yayi jajir dashi, gashi ƙato mai tsuka da yawa,
A saman wani ƙaton ganye ya ajjiye kifin kana ya fara ci cikin nutsuwa, sweet ma baki ta sanya ta fara yagar wanda ya sanya mata,
Sai da yaci sosai yabar raguwa kafin yaje yasha ruwa,
Gyara tsaiwa yayi tare da ɗaukan sweet ya fara duban hanyar da zaibi domin ya isa cikin Rugar Mahinjo a yau ɗin nan,
Motsin da yaji a bayansa ya sanya ya juya da sauri ganin Julde tsaye fuskarta cike da hawaye,
Ya sanya ya ɗauke idanunsa da sauri yana mai taɓe bakinsa,
Julde kowa ƙara banza hanci tayi saboda ƙamshin data ji ya sanya cikin siririyar muryarta tace.


"Zanci kifi, zaka sammin ko?"
Zare ido yayi yana mamakin yadda take iya fahimtar wani abun Kamar ba Makauniya ba, tsaki yaja yana Lumshe idanunsa kafin a ransa yace.
"Witch"
Ya faɗa a taushashe cike kuma da gajiya, ganyen ya ɗauka ta cilla mata saman ƙirjinta, da sauri ta ɗauka tana sauke numfashi da kuma Murmushin jin daɗi,
Zama tayi tare da tanƙwashe ƙafafuwanta, ta fara yagar tsukar kifin tana kaiwa ɗan ƙaramin bakinta,
Janye idanunsa daga kan guntun bakin nata, wata dabara ce ta faɗo masa, a hankali yayi baya yana mai shafa ƙirjinsa magana yake sunyi amma sam ya gaji da surutun wannan mai bakin akun,
Yana lumshe idanunsa tare da motsa bakinsa da ƙyar yace.
"Heyyy blind ina ne Mahinjo!!!?"
Ya faɗa yana mai ɗan ɗaga Murya tare da lumshe idanunsa,
Ambaton sunan Mahinjo da yayi ne ya sanya ta tsaya da cin kifin Jikinta ya ɗan ɗauki rawa,
Sai kuma a lokacin ta tuna da shanun da aka bata kiwo,
Cikin sauri ta miƙe tana jujjuya Idanunta kafin a hankali ta sulale ƙasa cikin Muryar kuka kuma tace.
"Na buni, dan Allah ba kaga shanuwa ba? Wayyoooo Madibbo shikenan zasu kashe ni an kwashe masu shanu"
Da mamaki yake binta da kallo ko kalma guda na maganarta bai fahimta ba,
Tsaki Yana cikin ɗaga murya haɗi da tsayawa ya koma Abu Maleek ɗinsa wanda yake na asali bawai yanzu da aka sanya ya zama mahaukaci ba yace.
"Noi inde wuroman?" (Ya sunan garin ku).
Ya faɗa in a serious tone.
Cikin firgici ta tarin tsoro tace "Rugar Mahinjo"
Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya ya sauke yana mai ɗan jin daɗi dan ko babu komai sai ta rama masa taimakon da yayi mata cikin haɗe fuska kamar tana kallonsa yace.
"Let's go"
Ya faɗa yana yin gaba, dafe ƙirji tayi tana sakin kuka kafin tace.
"Dan Allah ka barni a nan wallahi kashe ni Arɗo zaiyi"
Haɗe fuska ya ƙarayi saboda yarinyar ta fara bashi ciwon kai, haushi da kuma takaicin tsayawa inda take ma yake,
Gyara tsaiwa yay kafin cikin kakai murya yace.
"Su kashe ki mana, ni dai ba ruwana saikin raima min abinda nayi maki dan kiji"
Kuka ta sanya masa shi kam ko a jikinsa juyawa yayi ya ɗauki sweet kana kamar mai raɗa yace.
"Muje"
Bata taɓa tunanin bashi da kirki ba sai yanzu, da alama shima daga rugar yake saboda taji yayi fulatanci,
Kanta ta sunkuyar ƙasa kafin tace "bani da sanda ai, bazan iya tafiya ba"
Ta ƙare maganar Idanunta na zubar da hawaye,
Ba tare daya kalleta ba domin shi ya ƙosama yabar inda mayatacciyar yarinyar take, wata igiya ya ɗauka tare da cilla mata yana ɗan yatsuna fuskarsa yace.
"Tied your hand"
Sharrr hawaye ya ƙara sakko mata ta ɗaure hannu kuma? Dabba ce ita da zata ɗaure hannayenta, ganin tana ɓata masa Lokaci ne yasa ya ɗan ƙara daka mata tsayawa wanda shima da kansa sai daya dafe kansa sabida tsorata da tsawar da yayi,
Da sauri ta riƙe igiyar duk Jikinta rawa yake kana ta naɗa a hannunta idanunta na zubar da waye,
Shima yayi hakan ne sabida bai tsayawa kusa da ita bare har ya yi tunanin riƙe mata hannu,
Tana gama ɗaura igiyar ne shi kuma ya riƙe bakin igiyar tare da fara tafiya da sauri yana janta da sabida igiyar dake ɗaure a hannunta.
A haka suka fara tafiya domine isa Rugar Mahinjo.


A can cikin rugar kowa Arɗo ne da Barkido sai kuma Lamiɗo zaune, suna tattaunawa gyara zama Lamiɗo yayi kafin Yace.
"Na aikata da mutane a sirrince domin su duba min abinda ke faruwa a sakamakonsa harbin da mukaji, sai dai abin mamaki gaba ɗaya Shanuwanmu suna nan amma an nemi Julde an rasa"
Da sauri Barkido ya kalli Lamiɗo tare da faɗin.
"Kamarya an nemeta an rasa? Kana nufin ba'a ganta ba ko mene? Tayaya za'a ga Nagge amma ba'a ga mutum ba"
Kallon Barkido arɗo yayi sabida ya gama fahimtar ɗan nasa cewa ya faɗa tafkin soyayyar Julde, shi kam rashin Julden ba ƙaramin daɗi yayi masa ba,
Rashin nata kuma ya ƙara tabbatar masa da cewa Tabbas burinsa zai cika koma yace ya cika, dan matsalar sa ɗaya Madibbo do ya gama da Yakumbo ya gama da Madibbo mai uwa a gindin murhun ma ya gana da shafin ta,
Gyaran murya yayi kaɗan kafin ya kai dubansa ga Barkido yace.
"Meye damuwarka? Mene tsakaninka da ita, daman ai burinmu ace yau babu ita, domin idan har tana raye Tabbas burinmu bazai taɓa cika ba, kafi kowa sanin yadda muka sha wahala kafin mu kawo iya zo, dan haka ina gargaɗinka idan ma wani abu zuciyarka take kissima ta daina, Aradon Allah ina ci maka mutunci"
Arɗo ya faɗa yana nuna Barkido da hannunsa, kafin kuma ya fuskanci Lamiɗo yace.
"Wane mahaukacin daya Shigo cikin jejin?"
Lamiɗo ya kalli Arɗo kana yace "Barkido babu waje"
Tashi yayi zuciyarsa cike fal da tarin baƙin ciki, tattaunawa sukai kafin ko ya tashi ya nufi makwancinsa sabida dare yayi, gari yayi tsitt.


Ganin duhu yayi sosai ya sanya Julde zamewa a hankali ta kwanta tana sauke numfashin wahala,
Shi kansa Abu Maleek ya gaji tunda suka taho babu abinda yake tsayar da su sai sallah, gashi dare yayi duhu ba zai sanya suci gaba da tafiya ba,
Bisa Dole shima ya nemi waje ya kwanta yana sauke ajjiyar zuciya tare da rufe idanunsa,
Julde numfashi ta ƙara ja da ƙyar tana riƙe da saitin zuciyarta dake wani irin harbawa sabida tsananin ciwon da ƙirjinta yake,
Cikin fidda sauti da kuma da kuma tarin wahala da kuma ciwon dake ƙirjinta ta cije bakinta, tana murje ƙirjinta dake mata wani iri zafi da raɗaɗi,
Zame idanunsa yayi daga kanta yana jan tsaki a ransa yake faɗin.
"Guntuwar Yarinya sai ƙaton nono mtwss!!!"
Ya faɗa yana mai kwanciya a saman wata ciyawa dake jiƙe da ruwa.


Washe gari da sassafe sukaci gaba da tafiya ba tare da sunci komai ba,
Tunda suka tafi babu wanda yace komai, yana janye da ita da igiya wajan sallar Zhur sukaiwa Rugar Mahinjo tsinke,
Lokacin gaba ɗaya kowa yana cikin Rugar ana hutawa tare kuma da tarin Alhinin rashin ganin Julde wanda tsirari daga cikinsu suke.
Cikin rugar Abu Maleek yabi da kallo yana kalla kuma yaji kansa ya sara da ƙarfin gaske, zuciyarsa ta harba da ƙarfi,
Hakan nan ya samu kansa cikin tarin fargaba kasancewar sa ba komai ne kai bayyana a fuskarsa ba ya sanya ko alamun tsoro bai nuna ba,
Fitowar Lamiɗo kenan daga cikin bukka idanunsa ya sauka akan Julde da sauri yace.
"Arɗo!! Arɗo!! War, War Arɗo"
Jin Muryar Lamiɗo ne ya sanya Jikinta ya shiga rawa nan da nan idanunta ya fara zubar da hawaye shkknan yanzu zasu kasheta, abinda take rayawa a zuciyarta kenan,
Yana yana cikin bukka hannunsa riƙe da wata paper wacce babu wanda yasan da ita wajansa, sabida babu wanda ya iya karatu bare rubutu a cikin Rugar.
Yana tsaka da duba paper ne yaji Muryar Lamiɗo yana kwala masa kira da dukkan muryarsa, da sauri ya ɓoye paper kana ya fito,
Abinda idanunsa suka gani ne ya sanya shi zare ido,
Julde a hankali tayi bayan Abu Maleek tana ɓoye fuskarta domin a yanzu shi kawai take tunanin zai taimaka mata,
Gyara Arɗo yayi kafin yace.
"Ardon Allah ƙarya kake, shaiii kaci Ubanka ka biya mu Naggen mu, Lamiɗo kawo mana ita nan ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login