Showing 33001 words to 36000 words out of 161948 words
tara mana jama'ar gari"
Jin haka ya sanya Julde sanya ihu a gigice kuma ta sanya dukkan hannayenta a saman ququn Abu Maleek tare da ɗura fuskarta a tsakiyar bayansa ta ƙanƙamesa, da sauri ya runtse idanunsa sabida sarawar da kansa yayi masa ga wata halbawa da zuciyarsa tayi masa,
Kasa motsawa yayi da sauri kuma yasa hannunsa ya dafe kansa saboda yadda yaji Julde ta ƙara....
*ABU_MALEEK NA KUƊI NE KIJI TSORAN ALLAH KADA KI TAFI LAHIRA DA ABINDA BA NAKI BA, IT'S 500 VIA 0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK 08119237616*
*_Nimcyluv 25-26_*
Manne Jikinta a bayansa, tare da ƙanƙamesa sa sosai, hawaye na zuba daga cikin Idanunta, yayinda dukkan Jikinta ya ɗauki rawa tamkar mazari,
Abu Maleek kam abun ne yazo masa a bazata, jin yadda Julde ta rungomesa tana manna fuskarta a bayansa ne ya sanya shi janye idanunsa a hankali tare da rufe su ruff, ya shiga sauke numfashi a hankali yana mai ɗan taune jajayen laɓɓansa,
Arɗo dake tsaye ya ƙara duban Lamiɗo yace.
"Maza ka ɗauka shi ka kawo min shi nan"
Ya faɗa yana mai kallon Abu Maleek kafin Lamiɗo yayi magana Arɗo ya ƙara cewa.
"Kai mahaukaci mene ya kawo ka rugar Mahinjo, me kazo yi a wannan rugar, ko kuma kasan wannan yaron Julde ne?",
"JULDE!!!?"
Sunan da Abu Maleek ya ƙara maimaita wa a cikin zuciyarsa kenan, to mene ma'anar wani suna Julde ne?
A zahiri kuma raunatattun idanunsa ya buɗe tare da saukesu akan Arɗo, ƙara ware idanunsa ya yi akan Arɗo fari ne tass ɗan shawalwali dashi, baya da wani jikin arziƙi sai dugun wuya,
A ƙallah zai iya kaiwa Shekaru arba'in, janye idanunsa yayi ba tare kuma da yace komai ba, domin shi ba wannan yake buƙata ba,
All abinda yake buƙata shine hanyar da zata sada shi da Birnin Bera wannan shi ne,
Lamiɗo ne kai tsaye ya nufi inda Julde take manne a bayan Abu Maleek tare da rufe fuskarta da tsakiyar bayansa, sai tsuma Jikinta yake,
Yana zuwa ya miƙa hannu zai jawo ta tare da rabata da jikin Abu Maleek ance.
"Wait"
Jin sautin zazzaƙar Muryar mai cike da ilhama da kuma tarin nutsuwa da kamewa ya sanya, Lamiɗo tsayawa cak, sosai Muryar ta dakar masa zuciya ta sanya shi tuna wata makamanciyar Murya data huce a shekarun baya,
Da sauri Lamiɗo na ya ɗaga idanunsa ya kalli Abu Maleek cikin azama kuma ya janye idanunsa dan baya jin zai iya, ci gaba da kallon ƙwayar idanunsa sai zuciyarsa ta buga,
Ya kuma janye idanun ne dalilin wani tarin nutsuwa da kuma kwarjinin daya hango a cikinsu,
Tsoro da fargaba duk ya cika zuciyarsa, saukar Muryar Abu Maleek kuma ya haddasa masa wani irin faɗuwar gaba, sosai Muryar tayi masa kama data wani can a shekarun baya,
Cikin son dakewa da kuma mazewa Arɗo yace.
"Haii yaron arziƙi wasa ina maka, Hai ka fito daga Bayan wannan Mutumin"
Ya faɗa yana sakin Murmushin takaici, domin ba ƙaramin cika masa ido Abu Maleek yayi ba, baya jin zai iya yiwa Julde wani abu akan idanunsa,
Jin abinda Arɗo ya faɗa ya sanya ta sakin ajjiyar zuciya a hankali ta shiga zare Jikinta daga bayan Abu Maleek idanunsa a Lumshe tana shaƙar wani fitananan ƙamshi daya kawowa hancinta ziyara,
Kallon Arɗo Lamiɗo yayi da alamar "ya haka?" Girgiza kai Arɗo yayi kafin ya juya da baya yana faɗin.
"Noi indema?" (Ya sunanka)"
Sarai Abu Maleek ya fahimci maganar kuma ya san dashi ake, sabida yana ɗan jin fulatanci ba tare da kowa ya sani ba ake koya masa,
Na zai manta sanda Hamida Zubaida take koya masa ba, akwai sanda Oumuu-Ayman ta koya masa,
Lamiɗo ne yayi murmushi yana kallon Abu Maleek cike da mamaki gashi dai sak mahaukaci amma sam muryarsa ba tayi kama data mahaukaci ba,
"Muje daga ciki"
Lamiɗo ya faɗa yana mai ɗan dai-dai-ta Hausar sa, yadda Abu Maleek zai fahimta, jinjina kai yayi tare dabin bayan Lamiɗo jin haka ya sanya Julde ɗan miƙa hannu zata riƙesa da sauri yayi gaba yana mai harɗe hannayensa a ƙirjinsa,
Tsaya tayi cak jin ance.
"Ko damata maa?" (Meke damunki?)
Zare idanu tayi waje tana dafe ƙirjinta saboda jin Muryar Barkido,
Murmushi Barkido ya saki yana ƙarewa Julde kallo, yana jin wata zallar soyayyarta a zuciyarsa,
Wanda bai san lokacin daya fara ba haka kuma bai san lokacin da zai goshe ba,
Ja baya tayi tana ɗan girgiza kai ganin tsoransa ta keji ya sanya cikin ƙasa da murya yace.
"Babu abinda zan maki Julde kiyi haƙuri dana baya ma"
Ya faɗa yana juyawa sabida baya sun Arɗo ya fito ya samesa a wajan, shiru tayi ba tare da tace komai ba,
Kamar zai kuka Barkido ya ƙara buɗe baki yace.
"Julde kiyi haƙuri jin? Zaki haƙura ko, bana ƙara yi maki komai"
Ya faɗa idanunsa na ciccikowa da hawayen so da kuma ƙaunar ta, ƙasa tayi da kanta a hankali cikin ƙaramar muryarta tace.
"To na haƙura"
Ajjiyar zuciya ya sauke kafin yace "Nagode, muje ciki na baki kindirmo mai zafi"
Farin ciki ne ya kamata hakan ya sanya ta fara bin sahun tafiyarsa har suka isa wata bukka, ciki ta shiga tana zaune ya je ya kawo mata kindirmo mai yawa a ƙwarya, kana ya sake fita babu jimawa ya dawo hannunsa ɗauke da wasu kayan Fulani masu ɗan haske ya bata tasa.
Arɗo ne a gaba Abu Maleek na bin bayansa a hankali cike da Zallar nutsuwarsa irin ta ƴar ƴan sarakai, wanda jinin sarauta ya gama ratsa su,
Wata bukka mai kyau wacce aka cikata da kayan ado irin nasu na Fulani, Arɗo ya sanya kansa cikin Bukkar, Abu Maleek kam tsayawa yayi cak,yana mamakin ta inda zai shiga bukkar gaba ɗaya bukkar a tsakiyar cikinsa ta tsaya, baya tunanin cikin bukkar ma zai Wada cesa, waro manyan gajiyayyun idanunsa yayi waje ganin yadda Arɗo ya sunkuya sosai kamar zai dafa ƙasa kafin ya samu ya shiga cikin bukkar, cije lips ɗinsa yayi yana fesar da iska daga cikin bakinsa, a hankali cikin kuma ƙasaitacciyar muryarsa mai cike da kamala ya ware softness lips ɗinsa masu taushi da ɗan kauri cikin ƙasa da murya very slow yace.
"Goodness"
Ya faɗa yana janye idanunsa daga kan Bukkar, Arɗo dake ciki ne yaji Shiru baƙon mahaukacin nasu bai shigo ba, ya sanya shi leƙo dakai ganin Abu Maleek yayi a tsaya hakan ya sanya yace.
"Ai shaii ka rarrafa ka shigo"
Arɗo ya faɗa yana mai tsare ƙirjin Abu Maleek da kallo saboda wani baƙin zane daya hango, kwance a saman faffaɗan ƙirjin nasa,
Ganin hakan ya sanya Abu Maleek haɗe rai kafin ya ɗauke idanunsa yana faɗin.
"Wicked and stringy man"
Ya faɗa a fili amma Murya ƙasa, Murmushi kawai Arɗo yayi ba tare da yace komai ba,
A hankali ya sunkuya sosai, cikin rashin Sa'a kansa ya bugu da gefen bukkar, kwaɓe fuska yay sosai kamar zai sanya kuka, a hankali cikin Muryar taɓa ra yace.
"Auchhhiii! Daman salon mugunta akai wannan guntuwar abar, an san ai baƙi zasu iya zuwa, mtwss!"
Ya faɗa yana ƙarasa shiga cikin Bukkar duk ya marai-raice fuska kamar zai kuka, ganin ya shigo yasa Arɗo fita tare da ƙwarya a hanunsa, Not too long ya dawo da ƙwaryar cike da kindirmo mai kyau, wanda yake zalla babu algus,
Kindirmon yabi da kallo kafin a hankali ya haɗe ƙafafuwansa waje guda, bai son Kindirmon sabida sam bai yarda da tsaftar mutanan garin ba,
Amma idan yaƙi sha bai san abinda zai samu nan gaba yaci ba.
Zama Abu Maleek ya gyara tare da ɗaukan ludayin Dumar ya sanya cikin ƙwayar kindirmon da aka kawo masa, ganin yadda Kindirmon yake da haske sosai ga wani irin kyau da yayi masa a idanu, ya sanya a hankali cike da nutsuwa ya ƙara naɗe ƙafarsa kana ya ɗebi Kindirmon yakai bakinsa, da sauri ya ja idanunsa ya rufe saboda wani daɗi da kuma garɗi daya ratsa cikin kunnuwansa, shan Kindirmon kuma ya taso mata da duka yunwar daya keji a haka yaci gaba da sha, sai da yasha fiye da rabi kana ya ajjiye,
Murmushi Arɗo yayi yace.
"Birnin Bera kace ko, haii daga wannan rugar sai Birnin Bera tafiyar kwana guda ce rakk, amma haɗarin tafiyar yafi na shekara guda"
Kallonsa Abu Maleek yayi sai kuma ya ɗan taɓe baki, yana tsotse laɓɓansa wanda har yanzu daɗin Kindirmon yaƙi barin saman harshansa,
Lumshe idanunsa yayi harga Allah matsu ya samu maganin ya koma Benin kana ya ga King Tunde Muhammad Jalal ya samu lafiya daga nan kuma sai koma Madrid baki ɗaya, ya samu ya huce dukkan gajiyarsa a can!.
Kai tsaye waje Arɗo yayi yana zuwa ya nufi wajan Lamiɗo ba tare da yayi magana ba, yaja hannun Lamiɗo zuwa wata bukka,
"Meka fahimta dan gane da wannan baƙon?"
Arɗo ya tambayi Lamiɗo yana share zufar data karyo masa,
Gaba ɗaya Abu Maleek ya gama firgita Arɗo da kwarjininsa, har baya iya tsayawa inda yake saboda tsoro,
Lamiɗo ne yaja numfashi kafin yace.
"Ban fahimci komai ba, amma dai kamar bashi da lafiyar ƙwaƙwalwa, duba da yanayinsa da kuma shigarsa, ga kuma yadda kansa gaba ɗaya yaƙi tsayawa waje guda"
Jinjina kai Arɗo yayi kafin yace.
"Haka ne,amma akwai lauje cikin naɗi, mene ya kawo sa wannan garin? A cewar sa dai wai Birnin Bera zashi, amsar magani kuma babu wani magani da ake bayarwa, uhm! Kasan babu wanda ya taɓa shiga Birnin ya fito da ransa, saboda haɗarin da mutanan garin suke da shi, kasan mutanan tamkar kuraye haka suke, su kuma kalar tasu maitar a fili suke cin shan jinin Mutum, kuma da sun cijeka shikenan kai ma harbo wannan maitar"
Cike da gamsuwa Lamiɗo ya jinjina kansa kafin yace "haka ne, amma wannan mutumin kamar da sammu a jikinsa, ina kallonsa naji hankali na yaƙi kwanciya, ina ganin mu taimaka masa mu faɗa masa gaskiya zaifi"
Murmushi Arɗo yayi domin shi ya gama tsara Abinda zaiyi,
Juyawa yayi tare da nufar bukkar da Julde ke kwance har zai shiga sai kuma ya fasa ya juya yana mai sakin murmushi.
Cikin dare Abu Maleek yana kwance tunani fal ransa, idan ka ganshi zaka ɗauka da gaske bacci yake amma idanunsa biyu,
Ƙara yaji kamar na ringing ɗin waya daga bakin bukkar, mamaki ne ya cika masa zuciya domin yasan babu yadda za'ai a samu waya a wannan garin, garin da ku service bashi dashi, gashi ya lura ko addini basu iya ba,
Ware fararan idanunsa yay yana da ɗan kasa kunne muryar Arɗo yaji yana faɗin.
"Sir trying to remembered it, nayi ƙoƙarin ganin na aikata hakan but it's difficult to me, gaskiya i can't do that I'm sorry!"
Shiru yayi yana mai ƙara juya gudun kada wani yazo ya riskesa a haka, jinjina kai yay kafin yace.
"That's great job, any way duk yadda mukai I'll get back to you"
Ya faɗa yana mai kashe wayar tare zuge ta zugen wandonsa, a cikin aljihun 3gauther ya sanya wayar kana ya shigo cikin bukkar,
Da sauri Abu Maleek yaja idanunsa ya rufe mamaki ya hanasa tunanin komai bare ya fahimta, Tabbas akwai abinda yake faruwa a wannan Rugar mene shi, yaya akai Shugaban Rugar Mahinjo ya iya sarrafa harshe haka? Da wannan tunanin bacci ya ɗauke sa.
Washe gari waje ya samu mai kyau ya ɗan watsa ruwa a tsaye gudun infection,
Bayan ya shirya cikin wasu fararan kayan Fulani masu kyau, ya fito daga cikin Bukkar yana mai ɗan fesar da huci daga cikin bakinsa,
Arɗo dake gefe yace.
"Har ka fito?"
Kallon Mutumin yayi a ransa yace "munafuki"
A zahiri kuma idanunsa kawai ya lumshe tare da buɗe su,
Gyara tsaiwa Arɗo yayi kafin ya kalli Abu Maleek yace.
"Haii ka buɗe kunne da kyau kaji baƙo, babu wani magani da ake bayarwa a Birnin Bera, gaba ɗaya mutanan garin masu shan jini ne, a tarihi ma babu wanda ya taɓa zuwa koda ƙofar garin ne balle ya shiga, duk wanda yace kazo garin to bayanka ya keson gani Aradon Allah"
Kallonsa A.m yake domin yana son ya fahimci asalin Maganar, babu Abinda Ya gani a idanun Arɗo sai zallar tarin gaskiya tsagwaronta,
Juya idanunsa yayi kana ya mirgina kansa gefe yace.
"Are you sure?"
Ya faɗa yana cije bakinsa dan nan da nan yani kansa ya fara sarawa, sosai maganar ta dakesa, mene ya sanya akai hakan? Wane ya sanya Malamin Alaafin ya faɗi haka, lallai Tabbas biri yayi kama da mutum dalilin daya sanya kenan suka hana ya duba King Tunde Muhammad Jalal sabida suna tunanin zai iya fahimtar wani abu, Tabbas dole ya koma Benin ba tare da ɓata wani lokaci ba.
A can Alaafi Kanzaf kowa, tsaro aka ƙara mai tsananin gaske, cikin Alaafin yayi shiru baka ganin komai, ko jin motsin wani face na securities, tsaron da aka ƙara yafi na kullum, babu mai shiga babu mai fita, Al'amarin daya tayarwa da jama'ar Kanzaf hankali kenan,
Kana kuma ya sanya masu tsoro da tarin zullumi a cikin zuƙatansu,
Yau wajan sati guda kenan da tafiyar Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal kenan, tafiyarsa kuma ta haifar da tarin matsaloli wanda ba'a san ta inda suke kunna kai ba.
Salimerh ce zaune a saman bed ɗin ta tana sanye da kayan bacci dark brown panjamas, masu kyau,
Waya ce maƙale a kunanta tana sauraran abinda Junaid yake faɗa mata,
Daga can ɓangaren Junaid gyara kwanciyar sa yayi a hankali cikin ƙasa da murya yace.
"My princess kina son zuciyata ta buga saboda soyayyyar ki da tayi min yawa ko? I can't control my self idan ina wajanki ko su kike ba aikata abinda ba Shikenan ba?"
Ya faɗa yana jan numfashi, girgiza kai Salimerh tayi kafin tace.
"Ba haka bane, ni aure a yanzu ta kurani zai, ina karatu akwai tarin abubuwan da yake gabana masu muhimmanci"
Uhm kawai ya iya cewa kafin yace.
"Kenan baki sona?"
Girgiza kai tayi tace "i love You, ina sonka Junaid but...,"
Ka tseta yayi da "if you really love me, then marry me"
"I'll" da sauri yace "then when? Kinga stop pretending gobe zanwa Otun magana ya nemi Agba Akin (CHIROMA)domin a nema min Auranki, I'm tried My princess ki shirya zama matar Junaid soon"
Bai jira tayi magana ba, ya katse kiran yana mai mamakin yadda sam bata fahimtar son da yake mata,
Ajjiye wayar tayi domin ita sam babu maganar aure a tsarinta yanzu, tana big issues dalilin daya ta zaɓi karanta Law kuma ɓangaren criminology justice.
Washe gari da yamma Adams ya fito daga shashinsa cikin shigarsa ta ƙasaita, yana sanye cikin wani tattausan farin yadi mai manyan zane, anyi masa ɗinkin half body sai shot hand, yayi masu kyau sosai, ya ɗura wata hula mai gashi sai manyan murjani daya sanya a wuyansa,
Yana tafe a hankali a haka ya isa dinning room ɗin, Oumuu-Ayman ce zaune sai Mai Babban ɗaki da kuma Queen Ayoola, kana Bola lunch suke ga Cook yana serving kowa, lafiyayyan Moi-moi ne wanda yaji bushasshen kifi da kwai, kana da curry da kayan magi, ga wani ƙamshi da yake fitarwa musamman da aka samu wanke mai kyau..
Sai vegetable soup wacce tasha carot da beans sai zallar hanta wacce aka yanka manya,
Kujera yaja ya zauna, yana mai ɗan cilla idanunsa ganin babu Shakiru babu SHAREFUDDEEN, motsawa yayi kafin yace.
"Barka da rana Granny Oumuu, Mumy"
Duk suka amsa da "yawwa" a hankali ya fara yin lunch kafin ya kalli Mai Babban ɗaki yace "yau zan tafi Cairo"
Da mamaki ta kallesa kafin tace.
"Daman akwai tafiyar ne ko yanzu ka shirya?"
Kallon Salimerh yayi dake fitowa cikin shirin ta mai ɗaukan hankali, tana riƙe da hand bag sai kuma school bag ɗinta, da sauri ta zauna ta fara luch ɗin,
Ɗauke idanunsa yayi yace.
"Na daɗe shirya tafiyar sai yanzu komai ya dai-dai-ta, zuwa dare jirgin mu zai tashi"
Kallonsa Oumuu-Ayman tayi tana jin sam bata yarda da tafiyar amma bata ce komai ba.
"Da ka haƙura zuwa lokacin da ɗan uwanka zai dawo, muga jikin Mahaifin ku zaifi"
Miƙewa yayi yace "nasu yin hakan, amma tafiyar ta zama dole but ba daɗewa zanyi ba"
Jinjina kai tayi tace "Allah ya bada Sa'a"
Queen Ayoola ma Miƙewa tayi tace "za muyi missed babu kai babu Shakiru balle Sharefddeen, ga kuma tashin hankalin da muke ciki na rashin lafiyar King"
Kallonta kawai yayi ba tare da yace komai ba, tafiya yayi kai tsaye zuwa sashin King Tunde Muhammad Jalal domin dubasa, Salimerh ma makaranta ta nufa.
A daran jirgin Adams ya ɗaga zuwa Cairo.
Washe gari Otun ya samu Agba Akin da maganar Auran Junaid da Salimerh, suna cikin maganar ne kuma saƙo ya riskesu jikin King Tunde Muhammad Jalal ya tashi,
A ranar babu wanda ya runtsa dan yin Bacci fargaba da cika zuciyar kowa,
Banda sunan JALALULDEEN TUNDE MUHAMMAD JALAL babu sunan wanda yake kira sai sunan Little wanda ba'a san ko sunan waye ba, kawai sun ɗauka zafin ciwo ne, a haka gari ya waye masu suna tare da shi sai kumfa yake fitarwa ta cikin bakinsa, ga wani irin zafi da jikinsa ya ɗauka jikin yayi jajurr dashi.
Kimanin kwana uku kenan da zuwan Abu Maleek Rugar Mahinjo, rabonsa da Julde tun ranar da suka shigo garin gaba ɗaya, ya manta da babin rayuwarta, shirin komawa ƙasar sa yake,
Domin kwana biyun nan hankalinsa sam yaƙi kwanciya,
Yanzu ma fitowar sa kenan daga cikin Bukkar da yake kwana, a hankali yaja idanunsa ya rufe yana shaƙar iskar dake Kaɗawa,
Cikin Rugar yayi tsitt duk sun tafi kiwo,
Walking slowly hannayenta a saman ququnsa yake tafiya yana ɗan sauke ajjiyar zuciya,
A haka ya isa can gefen wata bishiryar mango wanda sukai manya sunyi jawurr dasu,
Daga can gefe kowa Labbo ne tsaye a gaban Arɗo yana faɗin "Da gaske ina sonta kuma na shirya auranta" ƙirjin Arɗo ne ya buga da ƙarfi, yana shirin yin magana kenan sai Barkido yace.
"Nima ina son Julde kuma auranta na ke sonyi"
Da wani irin sauri Arɗo ya kalli ɗan nasa yana zufa na yanko masa, Lamiɗo ne yayi murmushi yace.
"Kenan Shaɗi ya wajaba a cikin wannan Rugar ta Mahinjo, ga Labbo ga Barkido mazaje a motsa"
Arɗo kasa magana yayi sosai tashin hankali ya wanzu a saman fuskarsa, Tayaya Barkido zai ce zai auri Julde bayan yasan burinsu? Kuma yana da tabbacin Barkido zai iya shanye dukkan bulalar da Za'ai masa.
Hannunsa ya miƙa ya ciri Mango tare da cillawa sweet ɗinsa, tsalle tayi tare da buɗe baki Mangon ya faɗa bakinta,
Lumshe idanunsa yay a hankali kuma ya ware bakinsa yace "O'ohhhh" yayi hakan ne saboda zuciyarsa da yaji ta tsananta bugu kwanan nan, musamman yanzu da yaji ta wani harba masa, mango ya cira manya guda biyu kana ya ɗauki Sweet domin komawa cikin bukka, a hankali yake tafiya cike da tarin nutsuwa kamar ance ya kalli gefensa da