Showing 138001 words to 141000 words out of 161948 words
tsaro daman? Ace har cikin Airport Kidnappers su shigo su ɗauki mutum amma baku sani ba? Kenan a haka kuka zama securities? U don't even know your job? Damn it" ya faɗa yana share zufar data keto masa, ɗaya daga cikin securities ɗin ne ya kalli Aremo Sharefddeen cike da tsantsar Ladabi yace.
"Forgive us Aremo, an janye tunanin mu ne ta hanyar sanya Tia gas, al'amarin daya sanya muka shiga tashin hankali kenan, kusan gaba ɗaya Securities ɗin muka nufi wajan, yayinda Kidnappers ɗin kuma sukai amfani da waccar ƙofar ta baya wajan fitar da motar su" tsaki Aremo Sharefddeen yay kafin yace "A ina Cc t.v ɗin ku yake, we have to check motar da number ta" gaba ɗaya suka nufi wani babban sashe dake cikin Airport ɗin.
Abu Maleek gudu kawai yake a motar yama kasa tantance inda yake cilla motar, murza string motar kawai yake, yayinda dadɗan sautin Amon muryarta yake ratsa cikin dodon kunansa, ita ɗin kawai yake gani yana kuma tuna tashin hankalin da zata shiga, yayinda kuma zuciyarsa ke tsayawa da aiki ta daina harbawa idan ya tuna cewa zasu iya kashe ta.
Da wani irin sauri ya ƙara danna giyar motar ya kaita number ƙarshe, motar har wani tashi take saboda tsananin gudu, musamman daya kasance duk titin babu jama'a saboda duhun dare daya fara shiga sosai.
_"You're my life,my everything I love you so much my King Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal, I love you!"_ sune dadɗan words ɗin daya dawo cikin dodon kunansa sai ya zama kamar yanzu take faɗa masa, musamman da yaji wani fitinan ƙamshin Jikinta na ratsa masa cikin hancinsa, da wani irin sauri ya juya da nufin ya jawota jikinsa, amma babu ita babu labarin ta, idanunsa ya lumshe cikin wata iriyar Murya yace "Noting will happen to you Queen Hawwa'u, noting idan mijinki na raye" ya faɗi hakan yana sauke wani irin numfashi ƙarar da motar tayi yasa ya buɗe idanunsa kafin yay wani yunƙuri tuni motar yaje ya daki wani dutse babban wannan sabon al'amarin da kuma tashin hankalin da Abu Maleek ya shiga, ya haɗu yaywa zuciyarsa yawa hakan yasa nan take Numfashinsa ya tsaya da aiki!.
A wannan daran aka kulle dukkan wasu tashoshi da suke a garin Benin duk wata ƙofa ta shiga garin Benin da fitar ta Securities ne ta ko ina, wasu securities ɗin ma bana garin bane a daran suka sauka, wasu kuma suka zama private investigator, da kuma masu fararan kaya suna shiga cikin jama'a da gari ya waye, ko ina ya ɗauki labarin Kidnapping ɗin da akai na matar sarkin Yaruba Sarkin Benin wato Sarki Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal.
A can ɓangaren Kidnappers ɗin kuwa, daman a shirye suke a cikin motar su, tun kafin jirgin su Abu Maleek ya sauka a airport ɗin, ana announcement cewa jirgin ya sauka suka shirya, akan idannunsu Abu Maleek ya shiga mota a hankali ita kuma take tafiya tana gab da ƙarasawa motar takalmin ƙafarta ya gurɗe, kasancewar hill ne sosai, ta sunkuya da niyyar gyarawa wata haɗaɗɗiyar mota tazu wajanta kafin tai magana su ɗauke ta cak zuwa cikin motar su, hakan yasa cikin tashin hankali ya buɗe baki ta shiga kwarara wa Abu Maleek kira.
Suna shigar da ita suka danna mata powder wacce take jikin hanky ɗin su, nan take idanunsa suka shiga rufewa wani irin bacci mai kama da suma ya ɗauke ta, kai tsaye sauka sukai daga kan titi suka nausa cikin jeji, tafiya sukai mai tsayi har kusan a suba, kafin su kawo wata gaɓar ruwa, jirgin ruwa ne masu yawa wasu na tafiya wasu kuma suna tsaye, wajan wani ma dai-dai ci wani daga cikin su wanda ya ta rufe fuskarsa ne ya ɗauki Julde ya sanyata cikin ruwan, kana a hankali suka shiga suka wajan su biyar suna shiga jirgin ya fara tafiya, basu isa ƙarshen ruwan ba sai wajan 12 na safiya, suna isa suka samu wasu Fulani wanda suka rufe fuska suma, transfer Julde sukai daga hannunsu zuwa wajan Fulanin su kuma suka juya ta cikin ruwan, a bisa wani amalake suka ɗura Julde kana suka nausa cikin jeji suka fara tafiya babu tsayawa.
Misalin 11: na dare A hankali Abu Maleek yake buɗe gajiyayyun Maraitattun idanunsa wanda suka yi masa nauyi, hasken da yay masa yawa ne kuma yasa a hankali ya maida idanunsa ya rufe yana sauke wani irin numafashi, slowly kuka ya ƙara try na buɗe idon, cikin nutsuwa da kuma tarin gajiya ya buɗe idanunsa da sauri ya gama ware su ganin drip maƙale a hannunsa, with much surprised yake bin igiyar ruwan da kallo tsananin mamaki da ta'ajjuji ya sanya ya rufe idanunsa ya shiga tunanin abinda ya kawo sa Hospital.
Queen Roomana ce ta kallesa cikin tausayawa ɗan nata tace.
"Zaki na"
Ta faɗa a taushashe saukar muryarta yasa ya ɗan ji wani iri domin rabon da yaji Muryar mahaifiyar tasa tun kafin ya dawo daga Madrid, juyawa yay cike da rashin sabon mgnar da ya jima bai da ita ba, idanunsa ya tsorawa mata ganin yadda ta ɗan faɗa ga kuma zallar kamanninta da Adams daya ƙara bayyana, da idanunsa kawai ya bita da kallo ba tare da yace komai ba.
"Sannu yaya jikin naka?"
A hankali ya sauke numfashi yana dafe kansa dake bala'in sara masa, idanunsa ya lumshe yana taune leɓansa cikin dauriya kuma ya buɗe bakinsa mai makon ya amsa mata sai yace..
"Mamina"
Ya faɗa a taushashe cikin ƙasa da Murya very slow wacce tasa Adams ya kallesa a karo na farko a rayuwarsa da yaji yana tausayin ɗan uwan nasa, Murmushi Queen Roomana tayi irin Murmushin nan na gefen baki tace.
"Sannu Jalaluldeen ɗina sannu kaji" ya motsa fuska Yay a hankali ya yunƙura zai tashi yana cije bakinsa, da sauri Adams ya matsa gefen gadon ya riƙe sa, jin hannun mutum ne kuma yasa ya juya a hankali kallon Adams yay da mamaki, bai ce komai ba ya jingina da frame ɗin gadon yana sauke ajjiyar zuciya.
Queen Roomana nace ta kallesa cike da nutsuwa tace "ya kamata ka rama sallolin kanka, sai kasha coffee za kaji ƙarfin ka ya dawo" ba tare daya kuma cewa komai domin har yana mai mamakin abinda ya kawo sa Hospital, cikin tausasa Murya yace.
"Uhm wanne salloli ne?"
Kai tsaye Mami tace "Sallolin sati guda ne kayi missing nasu, kana cikin duguwar suma" da wani sauri Abu Maleek ya kalli mahaifiyar tasa tace.
"What? 1week fa, me nake to?" Ya faɗa yana kallon cikin haɗaɗɗan room ɗin da yake ciki wanda kana ganinsa kasan cewa na musamman ne, ganin babu wacce yake son gani yasa ya juya idanunsa zuwa ga Mami yace "Where is she?" Gaban Queen Roomana ne ya faɗi tama rasa mene za tace sarai tasan halin yaranta, cikin damuwa da son gasgata abinda zuciyarsa take raya masa ya dafe kansa wajan ƙasan wuyansa a ɗan hargitse yace "Mami!!! Ina matata where is my wife Mami? And me nake a hospital har good 7days Mami?" Aremo Adams ne ya ɗan sassauta murya ganin Mami ta kasa magana yace.
"We lose her" wani hantsilawa Abu Maleek yay jikinsa ya ɗauki rawa tashin hankali ya bayyana a saman fuskarsa, wani irin ɓari jikinsa yake cikin tashin hankali yace.
"What? Wa aka rasa ɗin? matar tawa Ko za'a a ɗauke kowa banda Mrs JALALULDEEN TUNDE MUHAMMAD JALAL wallahi sai naga bayan dukkan wanda ya nemi rusawa Queen Hawwa'u Julde rai" sai kuma ya sulale a wajan yana haɗa numfashi yana dafe kansa, cikin sauri Queen Roomana tace "jeka kira Dr Adams" da Sauri Adams yay waje Mami kuma wajan Abu Maleek ta nufa tana zuwa ya miƙe tsaye tare da shigewa Jikinta kafin tai magana ya sanya mata kuka wanda rabon da taji kukansa tun yana yaro, ƙanƙame ta yay yana kuka tare da faɗin.
"Mami! Why me tai masu? Mene yasa suke son kashe Jalaluldeen da ransa ne Eh Mami? My wife is my life Mami, wallahi zan mutu ne idan bata dawo rayuwata ba, i love my wife Mami, i love her, I love her har abada har lokacin da numfashi zai tsaya, Mami ki taimakamin wallahi mutuwa zanyi idan na rasa Naa.. nahhhh" rungomesa tayi a jikinsa tana wani sanyi a ranta, Tabbas rashin Julde ya sanya dole zata bayyana abinda yake ɓoye amma Tayaya ne Abu Maleek zai fahimta? Tayaya zai gane cewa shi ɗin Maraya ne gaba da baya? A hankali ta shiga bubbuga bayansa tama kasa magana, sakin jikinsa yay daga jikinta da sauri yay waje zai fice, yana zuwa bakin ƙofa yaci karo da Adams da Kuma Dr, gefensu yabi zai fita Mami tai saurin cewa "Stop him from living Aremo Adams Tunde Muhammad Jalal" Adams ne ya kalli Abu Maleek shima Abu Maleek Adams ya kalla yana jiran yaga yaya zai ya hanasa fita.
Kasawa yay saboda wani irin masifar kwarjini da Abu Maleek yay a idanun Adams, ƙasa yay da idanunsa yace.
"I can't Mami kilani baya hayyacinsa" da sauri Abu Maleek yace "tunda mahaukaci ne ni ko? Eh? Malam bani hayya" ya faɗa a tsawace cikin ɗaga murya, ganin haka yasa Queen Roomana ƙarasawa wajan Abu Maleek hannu tasa ta riƙesa, amma ga mamakinta sai taga yana neman kwace mata, wato dai babu wanda Abu Maleek ya kejin maganarsa kai tsaye irin Oumuu-Ayman da Julde, cikin sassauta murya yace "Leave me Mami" fuskarta babu wasa tace "Kana hauka ko?" A ɗan hargitse yace "I'm not mad Mami" ƙuri tayi masa da idanu sai kuma tace "A haka Oumuu-Ayman ɗin ta rene ka ta baka tarbiyya ma yarwa da Babba magana, Ni kake faɗawa haka Am Your mother Jalaluldeen" da wani sauri ya rungome ta yace "Am sorry Mom! Am sorry wallahi Oumuu na bata ce min haka ki yafe min Oumuu, Mami zuciyata zata fashe Jidderhh itace rayuwata" zaresa Mami tayi a jikinta kafin a hankali tace "go take a shower" tana faɗin hakan ta nemi waje ta zauna tare da buɗe Azkar ɗin da take taci gaba dayin Azkar ɗin ta.
A sanyaye yana sakin ajjiyar zuciya ya nufi bathroom ɗin kansa ya sakarwa shower, wata kyakkyawar ajjiyar zuciya yake saukewa yana jin zuciyarsa na tafarfasa banda juyawa babu abinda yake, a haka ya kammala, yana ciki yaji ana masa knocking jikinsa sanye da towel ya buɗe ƙofar bathroom ɗin Adams ne tsaye da wata sabuwar Embrodiery Islamic jallabiya Amy color, amsa yay ba tare daya kalli Adams ɗin ba, bayan ya sanya ne ya fito cikin nutsuwa yana ɗan ya motsa fuska, alrdy an shimfiɗa masa prayer mat yana zuwa tayar da sallah kafin ya isar da sallar wajan 1:5 na dare.
Mami dake zaune ta miƙe tsaye tare da ɗaukan basket ɗin dinner ta ƙarasa inda yake, plate ta ɗauka ta haɗa masa Bread sandwich Chicken And Waffles sai coffee mai zafi, ajjiye masa komai tayi tace "eat" girgiza mata kai yay yana lumshe idanunsa yace "i can't eat anything Mami" kallonsa tayi kafin tace "you most ko coffee ne" idanunsa ya buɗe wanda sukai jaa yace "how can i eat Mami? Bayan matata da Unborn ɗina suna cikin tashin hankali" da mamaki Mami take kallon Abu Maleek kafin tace "Ita Hawwa'u ce mai ciki ko me?" Ba tare da wani tunanin komai ba yace "Mami Allah da cikina a jikinta na mata ciki fa" jinjina kai Mami tayi a ranta tace "Ikon Allah" sosai kuma tayi mamakin rashin kunyar Abu Maleek, yana nan da halinsa irin na mahaifina a gaban kowa baya iya ɓoye soyayyyar Matarsa to ga ruwa dai ya biyo jini, a hankali tace "Zaki idan hankali ya ɓace nutsuwa ke samu shi, U Only care about your wife Julde, amma ka manta da cewa Bola ma tana ƙarƙashin kulawar ka ne? Yau kimanin wasu kwanaki masu yawa bamu san inda take ba, guduwa tayi ko kuma sace ta akai kamar yadda aka sace ni no one's know, ka nutsu mu fara barin hospital ɗin nan, kamar yadda baka da lafiya haka Mai Babban ɗaki da Salimerh sun shiga tashin hankali sanadin haka ɗan ƙaramin cikin dake jikin Salimerh ya zube, komai zai dai-dai everything will be okay" wayar Adams ce tayi ƙara a hankali ya kallesu yace "Excuse me Sharefdeen ne ƙilan ko wani impormation ne" jinjina kai Mami tayi da ƙyar ta samu ya sha Coffee ɗin, a wannan daran yace zai tafi gida "Mami i can't sleep ba tare da matata ba" haɗe fuska tayi ganin hakan yasa dole ya kwanta yana ta juyi har Subhi yay.
Yana yin Sallah Dr yazo ɗauke da file kallone Abu Maleek yay kafin ya kalli Mami yace "Congratulations brain ɗin King Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal ya dawo dai-dai cikin hukuncin Ubangiji" da wani irin farin ciki Mami tace "Allahamdulillah! Allah na gode maka" wasu hawaye ne ya sauko mata.
7 dai-dai suka nufi Alaafi yana zuwa part ɗinsa ya shige tare da rufe kai tsaye wajan wata ƙaramar locker yace ya zaro wani haɗaɗɗan box wani ƙyakƙyawan ring ne ya bayyana, a hankali ya dinga murza ring ɗin sai kawai ya cilla shi a cikin aljihu.
Queen Roomana kai tsaye sashin Mai Babban ɗaki ta nufa a nan ta samu Salimerh tana kwace da ƙyar take magana, tana zuwa Hadima Zubaida ta shigo tare da Maleek da kuma Khaleluddeen, idanunta sunyi jajirrr alamar taci kuka ne ga ƙoshi.
Kallonta Queen Roomana tayi kafin tace "Zubaida har yanzu ba zaki daina wannan kukan bane? In sha Allah Ubangiji zai bayyana mana Hawwa'u cikin Aminci da kwanciyar hankali" Murmushi kawai Hadima Zubaida tayi ba tare da tace komai ba ta juya.
Abu Maleek yana gama shirya cikin wata haɗaɗɗiyar Three-piece dinner suit Nevy blue ya ɗauki Wayarsa yana dannawa, ɗaya wayar nasa ne yay ƙara kamar bazai ɗauka ba sai kuma yay picking, wata iriyar sassanyar murya ce ta fara magana cikin ɗan ɗaga Murya, amma kana jin Muryar kasan cewa mallakin ta ya samu cikakken ilimin addini da kuma tarin nutsuwa.
Jikinsa ne ya fara rawa har buɗe baki zai ɗaga Murya sai kuma yace.
"Idan akai na ne kuka ɗauki matata kada kuyi mata komai zan kawo kai na har gabanku amma wallahi idan har wani abu ya samu Queen Hawwa'u uhm!"
Kashe wayar yay da sauri ya ɗauki box ɗin ring ɗin tare da wasu abubuwa, yana dailing wata number yay waje cikin bata umarni yace.
"Ka shirya min private jet yanzun nan on my way" yana faɗin haka yay waje da sauri Queen Roomana tace "Ina zaka?" Ba tare daya kalleta ba yace "Rugar Mahinjo" da sauri yay waje cikin sauri itama ta juya.
Washe gari
Misalin 11:15 na safe Jet ɗin Abu Maleek ya sauka a Rugar Mahinjo a wani babban fili na musamman, kasancewar kuma ba wani babba bane jirgin.
Wani ƙarar saukar jirgin yaji da mamaki shida Sharefdeen da P.a ɗinsa suka ɗaga kansu a hankali jirgin yake sauka, yana gama parking aka buɗe ƙofa, Mai Babban ɗaki ce a farko, sai Queen Roomana, Hadima Zubaida, Queen Ayoola, Shakiru, da Junaid da kuma Otun da Agba Akin.
Sosai Sharefddeen yay mamakin ganinsu, a hankali ya goge zufar dake yanko masa, duk da irin sanyin garin da kuma tarin ni'imar dake ke waye da rugar Mahinjo uwa uba ga babban ruwan wanda yaywa garin ƙawanya.
Gaba ɗaya family Alaafi ne a wajan suna tsaka da kallon juna wata dadɗar Murya mai cike da haiba tace.
"Wow! What a beautiful family, barkanku da zuwa Rugar Mahinjo" da wani irin sauri Mai Babban ɗaki da Queen Roomana suka juya tashin hankali, gigita, mamaki, ta'ajjuji ya saukarwa Queen cikin wani ɗaga murya ta nuna mutumin tare da faɗin....
Allah ya sadamu da alkairan da suke wannan rana ta juma'a😍🤝🏻
Babu Edited am sorry!
*SARAUTAR MARUBUTA*
*_91-92_*
"King Muhammad Jalal" wani Irin Harbawa zuciyar Arɗo tayi, da wani irin sauri ya sanya hannunsa tare da dafe kansa wanda yake sara masa ainun, wanda ya kejin tamkar zai rabe masa gida biyu ya zare daga gangar jikinsa baki ɗaya.
Wani Irin zamewa yay tare da zama akan wani ƙasan bishiya yana sauke numfashi, cikin rashin fahimta da kuma rashin gane kan kalaman da suke fita daga cikin bakin Queen Roomana yake Binta da idanunsa wanda sukai jaa, gashi dai bai san wannan sunan ba ko kaɗan, amma kiran suna ya haifar masa da wani irin tashin hankali har yana jin wani iri acikin zuciyarsa, A hankali yaja idanunsa ya rufe da sauri kuma ya buɗe saboda wani irin Flash back dake gilmawa ta cikin idanunsa ƙwaƙwalwarsa na son tuna masa da wani irin shuɗaɗɗan abu da suka shige daga cikin rawuyarsa..
Tsananin gigita da ganin Arɗo da Queen tayi ya sanya tai wani irin baya ta tafi Luuuu zata kifa, da wani irin sauri Abu Maleek ya zube a ƙasa ta faɗa a jikinsa a sume bata ko numafshi.
Wani irin tashin hankali Abu Maleek ya shiga abubuwan suke neman yi masa yawa, cikin wani irin sabon firgici ya shiga jijjiga Queen Roomana tare da faɗin "Mami! Mami!! Mami na!!" Amma ko motsi Queen Roomana ba tayi wani damuwa da ƙunci ne suka taro suka samu wajan zama a zuciyar Abu Maleek wanda tsananin damuwar da yay masa yawa ne ya sanya Numfashinsa fita da sauri tamkar zai bar gangar jikinsa cikin sauri ya shiga faɗin.
ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺇِﻧِّﻲ ﻋَﺒْﺪُﻙَ، ﺍﺑْﻦُ ﻋَﺒْﺪِﻙَ، ﺍﺑْﻦُ ﺃَﻣَﺘِﻚَ، ﻧَﺎﺻِﻴَﺘِﻲ ﺑِﻴَﺪِﻙَ، ﻣَﺎﺽٍ ﻓِﻲَّ ﺣُﻜْﻤُﻚَ، ﻋَﺪْﻝٌ ﻓِﻲَّ ﻗَﻀَﺎﺅُﻙَ، ﺃَﺳْﺄَﻟُﻚَ ﺑِﻜُﻞِّ ﺍﺳْﻢٍ ﻫُﻮَ ﻟَﻚَ ﺳَﻤَّﻴْﺖَ ﺑِﻪِ ﻧَﻔْﺴَﻚَ، ﺃَﻭْ ﺃَﻧْﺰَﻟْﺘَﻪُ ﻓِﻲ ﻛِﺘَﺎﺑِﻚَ، ﺃَﻭْ ﻋَﻠَّﻤْﺘَﻪُ ﺃَﺣَﺪًﺍ ﻣِﻦْ ﺧَﻠْﻘِﻚَ، ﺃَﻭِ ﺍﺳْﺘَﺄْﺛَﺮْﺕَ ﺑِﻪِ ﻓِﻲ ﻋِﻠْﻢِ ﺍﻟْﻐَﻴْﺐِ ﻋِﻨْﺪَﻙَ، ﺃَﻥْ ﺗَﺠْﻌَﻞَ ﺍﻟْﻘُﺮْﺁﻥَ ﺭَﺑِﻴﻊَ ﻗَﻠْﺒِﻲ، ﻭَﻧُﻮﺭَ ﺻَﺪْﺭِﻱ، ﻭَﺟَﻠَﺎﺀَ ﺣُﺰْﻧِﻲ، ﻭَﺫَﻫَﺎﺏَ ﻫَﻤِّﻲ”*
*_Allahumma inniy ‘Abduka ibn Abdika ibn Amatika, Naasiyatiy biyadika, maadin fiyya hukmuka, ‘adlun fiyya Qadaa’uka, as’aluka bikulli ismin huwa Laka sammaita bihi nafsaka, au anzaltahu fiy kitaabika, au ‘allamtahu ahadan min khalqika, au ista’sarta bihi fiy ilmil gaibi ‘indaka an taj’alal Qur’ana rabiy’a Qalbiy, wa nuura Sadriy wa jala’a huzniy wa zihaaba hammiy_*
Addu'ar yaye damuwa da tafiya da ƙuncin zuciya, addu'ar da dukkan yadda zuciyar mutum yakai da ɗaukan zafi da kuma toshe wa saboda tsananin damuwa ita kaɗai ya wadatar ta tafi maka da dukkan damuwar dake maƙale a cikin zuciyarka.
A hankali ya dinga sauke ajjiyar zuciya yana ƙara girgiza Queen Roomana tare da ɗan bubbuga kumatun ta, ganin hakan ya sanya Sharefddeen da sauri