Showing 6001 words to 9000 words out of 161948 words
kama nata hannun yace.
"Look! My princess love me or hate me is not my problem, amma dan Allah ki aminci da auran mu please dear"
Cikin rashin sanin abinyi kawai da jinjina masa kanta,
Cike da farin ciki ya zame hannunsa a nata yana faɗin.
"Ohh Wow! Junaid you're the best thank you My princess"
Murmushi kawai tayi tana ci gaba da duba courses ɗin da zata karanta onder criminology justice kamar su.
Introduction to Criminology.
Theories of Crime Causation.
Human Behavior and Victimology.
Professional Conduct and Ethical Standards.
Juvenile Delinquency and the Juvenile Justice System.
Dispute Resolution and Incidents Management.
Criminological Research.
*🇪🇸SPAIN/ MADRID*
Only you hotel atocha!
Babban hotel ne, wanda kana ganinsa kan cewa bana ƴan zauni gari banza bane.
Musamman yadda tun farkon titin da zai sadaka da hotel ɗin yake ɗauke da manyan jami'an tsaro (Securitie's).
Haka kuma cikin hotel ɗin tun kafin ka shiga sai na'ura ta cajeka tsaf ta tabbatar babu abin cutarwa jikinka sannan za'a baka damar shiga.
Tun a reception na fara ganin manyan ƴan wasan Madrid sanye da farar riga wacce a gaban rigar aka sanya (Emirates fly).
Kowa na ɗauke da small bag a bayansa sai gorar ruwa mai sanyi.
Sai fitowa suke daga cikin room ɗin su gasu nan irin su ALABA, LUNIN, MARCELO, KROOS, ISCO.
BENZEMA ne ya ɗan ja Sirrin tsaki yana mai juyar da kansa gefe cikin harshen turanci yace.
"What the fuck"
Ya faɗa yana fesar da iska,
Sarai sauran sun fahimci dalilin daya sanya Benzema yace haka, amma no one's talk dole su jira domin umarnin coach.
A can cikin room 212 kowa baka jin komai sai ƙarar gudun A.C da kuma ƙarar gudan ruwan dake zuba daga cikin shower, alamar dai wani ke wanka a ciki.
A hankali ya sauke wata zazzafar iska tare da sanya fararan teeths ɗinsa ya datse jajayen laɓɓansa da haƙoran,
Hakan ya samu asali ne sabida sanyin ruwan showern daya sauka saman ƙwantaccen gashin kansa wanda yake da tsayi sosai ainun domin ya sauka har ƙasan wuyansa,
Gashin baƙi ne siɗik amma daga ƙarshen gashin wanda ya samu nasarar kwanciya a bayan wuyansa ya kasance coffee,
Da sauri da sauri kuma ya shiga sauke ajjiyar zuciya yake ya ɗaga kansa sama ruwan da dukan fuskarsa yana sauke saman faffaɗan ƙirjinsa wanda yake cike da baƙin gashi,
Sun manne da farar fatar sa,
Idanunsa da sukai jajirr kuma yaja ya rufe bayan ruwa ya gama dukansu,
Yana da ƙirar sosai ga tsayi da kuma faɗin ƙirji ƙwayar idanunsa blue ce kana ganinsa zaka tabbatar cewa shi ɗin half-caste ne (ruwa biyu)
Gaba ɗaya jikinsa yana ɗauke da gargasa hakan yasa yake da yawan jin zafi,
Wannan dalilin yasa bai fiya zama da complete dress ba idan yana cikin room ɗin nasa,
A kasalance ya miƙa hannunsa tare da kashe shower,
Kana ya shiga wanke bakinsa da brush da yana gamawa kuma ya ɗauki bathrobe fara tas ya saka cikinsa,
Ya fito daga cikin bathroom ɗin kai tsaye kuma ya tsaya gaban dressing mirror,
Bai wani shafa komai ba sabida weather garin is too high!
Farin wando ya sanya wanda ya kasance 3gauther sai farar singlet,
A hankali ya sanya hannunsa ya ɗauki wani perfume Tom-ford ya fesa a jikinsa a saman singlet ɗin,
Duk wannan abinda yake kansa yaƙi tsayawa waje guda, sabida tsananin zafi da kuma azabar da yake masa,
Ga wani irin nauyi yau da kan yay masa yana jin komai ya tsaya masa sai wani shuuuuuu ya keji a cikin kunnuwansa!
IWC Schaffhausen Rolex ɗin dake tsintsiyar hanunsa ya duba yaga 3:48 gajeran tsaki yaja yana taune leɓansa tare da tsotsar na ƙasa ya shiga ganawa kansa a zaba,
Ƙara sauke numfashi yay yana mai tsitsyaya win a cikin glass cup kana ya kafa a saman bakinsa ya shanye tass,
Idan ta sabon shan win ya riga daya saba domin ya ɗauke ta kamar ruwa ne,
Amma duk da hakan tasbihi baya barin bakinsa yanzu ma cikin ransa yake faɗin.
"Astagafirullah wa'atubu ilaik!"
Ƙara duban agogon yay yaga 3:50 dai-dai kuma 4:00 za'a dake wasa wanda ya kasance wasan cikin gida, ma'ana zasu buga wasa tsakanin Madrid da Chelsea.
Bayan ya gama shan win ɗin ne kuma ya ɗauki farar rigar Madrid ya sanya a jikinsa nan take harafin A.M ya bayyana a bayan rigar,
Da sauri kuma ya ɗauki bag ɗin ɗinsa da lemon power horse energy ya fita zuwa reception ƙafarsa sanye cikin combust.
A can reception kowa gaba ɗaya ƴan wasan sun yi gaba kaɗan ya rage, cikin nutsuwa yake tafiya idanunsa yay jajir jijiyoyin kansa sun fito sunyi raɗa raɗa gaba ɗaya jikinsa tsuma yake,
Shi kaɗai yasan yadda ya keji, sosai naman jikinsa yake rawa kamar zai zame daga jikin ƙashi ya faɗo.
Coach ɗin Madrid mai suna Carlo Ancelotti, yana ganin fitowar sa yay saurin kama hannunsa cikin harshen turanci yace.
"ABU_MALEEK time is not our side, kasancewa kai ne ma dadin Christiano Ronaldo, kawo lokacin da muka rasa Ronaldo matsayin ɗan wasan Madrid muka fara samun matsala, amma daga lokacin daka dawo club ɗin mu komai ya dai-dai-ta, da buga ƙwallonka dana Ronaldo babu bambancin sam, But why are you doing this? Kana behavior like wani mental problem"
Ya ƙare maganar yana jan hannun wanda aka kira da ABU_MALEEK ɗin wanda a taƙaice mutane suke cewa A.M
Abu_maleek sam bai fahimtar zan can Coach ɗin nasu,
Banda duhu babu abinda yake gani dan haka kawai yake biye da Coach ɗin har zuwa cikin wata babbar mota lafiyayyiya,
Kai tsaye kuma suka nufi *Santiago Bernabèu Stadium*
Lokacin tuni ƴan wasan Chelsea sun gama zuwa kowa yana riƙe da hannun yaronsa,
A.M na zuwa Coach ya ɗauki wani yaro sai bawa Abu_maleek da sauri kuma cikin tsananin a zabar daya keji yay gaba abinsa,
Dan a duniya ko kaɗan bai son ganin yaro musamman Namiji, hakan na tayar masa da tsohun tsumin dake zuciyarsa,
Kai tsaye kuma ƴan wasan suna fara shiga cike da ƙwarin qwiwwa musamman yanzu da suka san cewa Abu_maleek yana tare dasu, domin shine hope ɗinsu a wasan.
Yana gab da shiga tsakiyar filin wasanne kuma yaji kansa ya tsara nan take yaga wasu stars a cikin idanunsa a hankali kuma wani majic na shekara da shekaru suka fara gilmawa ta cikin blue eyes ball ɗinsa,
Nan da nan kuma jikinsa ya ɗauki rawa idanunsa suka firfito sosai,
Coach da tsoro ya kamasa zuciyarsa cike da fargaba ya ƙarasa inda Abu_maleek yake cikin rashin sanin abinda ke damun A.M ɗin ne kuma yasa Coach ɗin faɗin.
"Abu_maleek my champion what happened to you?"
Banza Abu_maleek yay masa a zahira ma sam baiji mai yace ba domin yanzu yana ɗaya cikin duniyar tasa ya fita daga asalin
Abu_maleek ɗin da suka sani,
Ganin hakan ne kuma yasa Coach cikin ɗaga Murya yace.
"Abu_maleek It's 4:15 Already an take wasa me kake haka? Meye ya shiga cikin tunaninka ne? Ko kuma wasan ne baka so"
Abu_maeek ya juya da sauri sabida bazai jure ihun da Coach ɗin yake masa ba, yana ɗaga ƙafa da niyyar shiga cikin Stadium ɗin ne kuma yaji gaba ɗaya ya gama shiga ɗaya duniyar tasa a hankali ya ɗan dafe kansa yana taune leɓansa tare da furzar da iska daga cikin bakinsa cikin zafin harshe kuma yace.
"O'ohhhh"
Coach da ransa ya gama ɓaci ya ɗaga hannu zai riƙe A.m da wani irin zafin nama irin na ƴan ball da kuma juyewar tunani Abu_maleek ya sanya hannunsa ya shaƙe wuyan Coach tare da yin sama dashi.
*SHARE FISABILILLAHI SABIDA ALLAH*
_Bana sauri acikin tafiyar rubutun nan nawa, dan haka karatu za kuyi cikin farin ciki da kuma kwanciyar hankali, fatana kuci gaba da bin littafin *ABU_MALEEK* domin tafiya ce mai cike da ƙaddara za kuji sabbin abubuwa wanda dole za kuyi mamakin su amma babu mamaki a ikon Ubangiji, a next page ne kuma za kuji wani sabon part mai tarwatsa zuciya, ku nutsu ko fahimta sosai🥰☺️_
🌈🌈🌈🌈
*ABU_MALEEK*
🌈🌈🌈🌈
NIMCYLUV
BOOK 1
PAGE 7-8
Idanun Coach ɗin ne suka fito waje sabida tsananin azaba haɗi da ficewar hayyaci,
Ba ƙaramin shaƙa Abu_maleek ya yi masa ba,
Sabida ko buɗe idanu ba ya iyawa, A.m kam cikin rashin sanin abinda yake aikatawa yay cilli da Coach ɗin gefe guda,
Yana sakin numfashi tare da fesar da iska, gaba ɗaya blue ɗin ƙwayar idanunsa ta rine tai jajirrr tamkar gauta!
Yana dafe bango cikin zafin nama kuma kamar walƙiya ya ɓace daga wajan ɓat, da idanu kawai Coach yabi bayan A.m a ransa yana mamakin wanne kalar Mutum Allah ya haɗasa da shi,
Gaba ɗaya gane inda Abu_maleek ɗin ya nufa wahala ne, kaifi ɗaya ne shi, idan yace zai yi Tabbas zai yi, duk tsayin lokacin da suka ɗauka da Abu_maleek babu wanda ya taɓa ganinsa ya tsaya da wani yana magana irin mai muhimmanci ɗin nan,
Bare kuma ai tunanin friendships bashi da yarda ko kaɗan, gani yake kowa zai iya cutar da rayuwarsa, da alama akwai abinda ya gana masa a zaba a rayuwarsa wanda har lokacin babu wanda ya san menene shi.
Maza na rungome matayensu amma shi wata ƴar farar magensa wacce yake ce mata SWEET, ita ta maye masa gurbin mata, uwa da uba,
Magen zai sanya gaba yay tai mata surutai kuma abin mamaki sosai take iya fahimtar kurman baƙin nasa,
Abu_maleek bai son ihu yanzu zaka hargitsa masa tunaninsa bare kuma ka sashi gaba kace zakai masa faɗa, yana da wani Ɓoyayyan hali wanda har yanzu babu wanda ya samu nasarar gane wane hali ne Abu_maleek yake ɓoyewa wanda bai son kuma a gani? Yana da saurin ɗaukan zafi da kuma saurin yanke hukunci shiyasa baya shiga sabgar duk da bai shafesa ba.
Ajjiyar zuciya Coach ya sauke tashin hankali kuma tsantsa ya bayyana a saman fuskarsa, yanzu yaya zai yi? Da wanne ido duniya zata kallesa? Musamman yanzu da kowa ya saka wa wannan babban wasan nasu ido, idan ta tabbata Chelsea sun ciye ƙwallayen ina ya dosa to? Abu_maleek shine hope ɗinsa, cikin sauri ya juya tare da shigewa cikin Stadium ɗin idan da yiyuwar ɗaga ball ɗin sai ai masa alfarma amma abu ne mai wahalar gaske.
A hankali yake tafiya yana haɗe hanya kamar ɗan shaye-shaye, daya rufe idanunsa zai fara ganin wani tsuhun tarihi yana gilmawa cikin ƙwayar idanunsa,
wanda tunusa a yanzu dai-dai yake da bugawar zuciyarsa, hannunsa dafe da goshinsa dake tsastsafar da gumin wahala,
Duk mutanan da suke hanya sai sun tsaya sun kallesa cike da mamaki domin sun san ko waye,
Wasu ma waya suke ɗaukowa suna masa vedio da picture, domin babu wanda ya taɓa ganinsa haka without his guards.
Yana tafe a tsakiyar titin yayinda ya kejin gaba ɗaya duniyar na juya masa a wannan karan ko idanunsa baya iya gani, a dai-dai kuma tsakiyar kan titin ne kuma wata mota tazo da mahaukacin gudu gaba ɗaya tayo kansa,
Cikin ikon Allah, motar ta tsaya cak wata ƙyakkyawar Badurwa ce a ciki sanye da ƙanan kaya masu matukar kyau da kuma ɗaukar idanu, idanunta manne cikin wani tafkeken glass,
Ganin Abu_maleek a gaban motar ta yasa ta saki baki With much surprise ta shiga kallon A.m domin kallo ɗaya tai masa ta gane wanene!
Amma mamakin ganinsa ya kasa barinta ta tabbatar ce eh lallai shi ɗin ne da gaske ba wani ba,
Ganin jini na zuba a gefen kansa dalilin buga kansa da yay daga jikin bango yasa tai saurin buɗe ƙofar motar ta fito,
Tana zuwa ta nufi inda yake tare da leƙa farar ƙyakkyawar fuskarsa tace.
"Sir Are You okey? The you need some help?"
Ta jera masa tambayar lokaci ɗaya!
Ganin mutum kusa dashi yasa a hankali cikin rashin sanin mene yake aiwatarwa ya shiga miƙa hanunsa yana ƙoƙarin kama hannun budurwar da niyyar kare kansa daga faɗuwar da yake ƙoƙarin yi,
Ganin haka yasa budurwar saurin matsawa gabansa Musamman da taga few people suna kallon su, ita kam abin farin ciki ne a gareta da kuma ci gaba a ganta da Abu_maleek mutum mai zarrah,
Wanda sai ka shafe shekaru baka gansa ba indai ba'a t.v ba.
Abu_maleek cikin sabuwar duniyar daya shiga ta juyewar tunani da kuma win ɗin data fara aiki a jikinsa yasa gaba ɗaya, jikinsa ya saki yay kan budurwar baki ɗaya tare da kifa kansa a saman wuyanta, tsananin farin ciki yasa budurwar faɗin.
"Supia my name sir, lemme help you"
Ta ƙare maganar tana ɗura hannunta a saman waist ɗinsa wanda yake da faɗi sosai, nan take ta lumshe idanunta sabida wani firgitaccen ƙamshi daya daki hancinsa.
Abu_maleek jinsa a jikin wani abu ya tabbatar masa da cewa ya samu kariya ne, a hankali yaja numfashi mai ƙarfin gaske, tare da sauke wata Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya a hankali kuma ya shiga motsa jajayen laɓɓansa masu kauri da kuma sheƙi, cikin rashin sani ya manna softness lips ɗinsa a kunan Supia kana ya datse bakinsa da wani irin emotional sound ya ware laɓɓansa cikin tsakiyar kunanta yace.
“Sweet, Mami, Secret”
Ya faɗa lokaci ɗaya tare da zare bakinsa yana jin yadda zuciyarsa take masa lugude sosai, har yana jin kamar zata faso ƙirjinsa ta fito.
Da sauri Supia ta sanyashi mota tare da shiga da Wani irin speed taja motar tare da nufar gidanta.
A bakin wani tangamemen gate tai horn cikin sauri security dake gadin gidan yazo da sauri ya buɗe mata gate,
Kai tsaye ta cilla hancin motar cikin katafaran compound ɗin gidan me cike da Flowers.
Da ƙyar ta samu taka A.m cikin gidan sabida nauyin da yay mata ga wasu surutai da yake mata wanda bata san ko mene yake faɗa ba.
Cikin farin ciki Supia ta kwantar da A.m saman makeken royal bed ɗinta wanda yake ɗauke da white bedsheet
Tana kwantar da shi ta nufi cikin bathroom ta sauya kaya wannan lokacin bambamcinta da tsirara babu shi,
Kana ta shiga gyara gashin kanta tana wargatsa shi, wayarta mai ƙirar Iphone 11 max pro ta ɗauka ta nufi cikin bedroom ɗin inda ta kwantar da shi domin tuni bacci yay gaba dashi.
A can Stadium kowa kamar yadda Coach ya yi tunani haka ne ta kasance, domin sam ba'a ɗaga masa ƙafa ba duk da ya shaida masu cewa ɗaya daga cikin masu buga Wasan ne babu lafiya amma sam sukaƙi yadda, haka aka fara wasa tun kafin aje ko ina Chelsea ta lallasa Madrid da ƙwallo biyu da nema.
Supia matsawa tayi sosai jikin A.m bayan tayi nasarar zame rigar jikinsa, ta shiga ɗaukan su selfie, ƙara matsawa tayi dai-dai saman ƙirjinsa ta ɗura bakinta dai-dai saman nasa nan ma ta ɗauki selfie bayan vedio'n da tayi masu yawa!
Sosai take farin cikin kasancewa da sananne wanda duniya ta sani, tana gamawa ta ɗauki bowl da tewel ta haɗa warm water ta shiga goga masa domin shi ɗaya sai zufa yake haɗawa tana gamawa ta miƙe tare da barin bedroom ɗin ta koma Parlo ta fara watching TV tana jiran tashin sa.
A can Cikin University kowa Salimerh ce zaune a cikin hall ɗin da suka gama ɗaukan lectures, ganin ita kaɗai ya rage yasa, ta ɗan taɓe baki tare da fesar da iska cikin nutsuwa ta shiga latsa keyboard ɗin wayarta tana sanya wasu Numbers, tana gamawa
Kuma tai dailing number tare da mannawa a kunanta,
Bisa mamkinta a karo na farko bayan shekara biyu kenan taji number data kira tana ringing.
Cikin Zallar farin ciki tare da nuna jin daɗin ta,
Ta shiga faɗaɗa fuskarta da Murmushi, kira wajan 5 amma babu response dole ta haƙura ta maida wayar jeka,
A hankali kuma wasu siraran hawaye suka shiga fita daga cikin idanunta,
Yaushe zata samu damar da zata fallasa asirin wanda zuciyarta ke zargi ne? Yaushe ne gaskiya zata bayyana a cikin Alaafin, mene yasa gaba ɗaya kowa kansa ya sani?
Abubuwa da yawa suna faru, babban tashin hankalin ta bai wuce rashin ganin Queen Roomana da ba'ai ba, innocent woman like Her ace wani ya cuci rayuwar ta ya sace ta,
Domin har kawo lokacin bata yarda cewa ɓata tayi ba tayi amana da cewa wani ya ɗauke ta sabida wani banzan dalili nashi mara toshe.
Misalin 7 na dare ya shiga buɗe manyan idanunsa wanda sukai masa nauyi, ga wani irin raɗaɗi da suke masa,
Bakinsa ɗauke da addu'a ya fara sauke ganinsa a saman tafkeken photon Supia dake maƙale jikin bangon ɗakin nata,
Da mamaki saman fuskarsa,
Ya shiga ware gajiyayyun idanunsa wanda yake jinsu tamkar an zuba masa yaji sabida zafin da suke masa,
A hankali kuma ya shiga bin bedroom ɗin da kallo kana ya ɗaga hannunsa da ƙyar,
Ya sauke a saman ƙirjinsa nan mamakin sa ya ƙara tsananta sabida ya jisa naked babu kaya,
Jikinsa yabi da kallo yana taune leɓansa tare da runtse idanunsa cikin ƙarfin hali ya buɗe bakinsa tare da faɗin.
“O'ohhhh”
A hankali kuma ya miƙe tsaye tare da ɗaukan kayansa ya sanya a zuciyarsa kuma ya mamakin reason ɗin daya kawo sa cikin wannan banzan gidan,
Yana gama sa kayan Supia na shigowa,
Kallo ɗaya yay mata ya kawar da idanunsa kefe nan take yaji kuma tsanar mace ta ƙara nunkuwa ainun fiye da baya a cikin zuciyarsa,
Ko inda take bai kalla ba kansa a ƙasa idanunsa a lumshe yay waje, da sauri ta mara masa baya tana faɗin.
"Sir! Sir! Sir!"
Amma ina ko tsayawa bai ba da yaga ta fiya binsa sai ya tsaya yana kwaɓe fuska tare da marai-raice fuska ya shiga langwaɓar da kansa gefe kamar ƙaramin yaro murya can ƙasa yace.
"O'ohhhh, stay away for me Ma'ah"
Yana faɗin haka yay waje kai tsaye kuma ya shiga gudu kasancewar sa ɗan ball ya saba da gudu yasa gaba ɗaya baya jin gudun duk da cewa bai daɗin jikinsa ya keji ba,
Babu jimawa ya ƙarasa hotel ɗin,
A reception yaci karo da Coach kallo guda yay masa ya ɗauke kai, zuciyarsa cike da tarin tambaya,
Ko wasan aka fasa yau? Mene yasa ya ganshi a gidan waccen ƴar shilan da baki kamar alawar madara,
A haka dai cike da sassarfa ya shige room ɗinsa,
Coach kawo yazo labarin Abu_maleek ya daina bashi haushi sai tsoro da yake basa,
Cike kuma da tsananin mamakin yadda yaga kamar blood a jikin farin wandonsa ya bisa da kallo!
Yana shiga room ɗin ya nufi bathroom ɗin sa bayan ya sutale kayan jikinsa ya sakarwa kansa shower wata wahalalliyar ajjiyar zuciya ya sauke yana matse jikinsa waje guda,
Sharp-Sharp ya yi wanka ya ɗaura alwala kana ya fito ɗaure da towel ɗin a jikinsa.
Yana fita magensa ta