Showing 54001 words to 57000 words out of 161948 words
sanya kuma har yanzu ya kasa tantance photon Namiji ne ko kuma na mace? A kullum yayi zanan sai yaga kai babu gashi idanu a rufe, kirji kuma fal da brest kamar zasu tsaga ƙirjin su fito,
Ajjiyar zuciya ya sauke yana ƙara ware idanunsa akan laɓɓan wacce ya zana, kawo yanzu ya fara tunanin macace, duba da yadda laɓɓanta suke jajir gwanin sha'awa, amma irin laɓɓan tsiwa ne.
Lumshe idanunsa e a hankali ya ware laɓɓansa tare da cizon lips ɗinsa na ƙasa kamar zai kuka Murya a narke yace.
"Fitananniyyaaaa!!!"
Ya ƙare maganar yana jan harafin Yaaaa!!! Yana nan zaune har aka kira sallar Asar, gaba ɗaya baya jin daɗin fresh milk ɗin babu abinda yake son sha yanzu wanda ya huce Alcohol, Abar da aka sabar masa sa shanta tun yana Ƙarami.
A sanyaye ya miƙe ya koma bedroom ɗinsa yana zuwa ya samu sweet na shan madara kanta ya shafa yana faɗin "Sweet my love, my best friend"
Ya faɗa yana shigewa bathroom ya ɗaura alwala kai tsaye yabi ta ƙofar baya kasancewar yana sahun gaba yasa bai haɗu da ƴan uwansa ba, bayan an idar da sallah kuma zama yayi tare da lumshe idanunsa yana sauraran bugawar zuciyarsa.
Haka sallar magrib da Isshā duk haka yayi bai ƙara haɗuwa da kowa ba,
Ko Abinci bai tsaya ci ba ya shige cikin bedroom ɗinsa tare dayin wanka ya sanya wasu haɗaɗɗun nightwear Panjams masu santsi da taushi ya sanya bayan ya fesa parfume ne ya kwanta tare da jawo sweet ya rungome ya lulluɓe su da duvet mai laushi bayan ya ƙure gudun a.cn bedroom ɗin.
Washe gari
Tun 4:05 ya tashi saboda sautin kiran sallar farko na Subhi da yaji, jiki a sanyaye jike da kasala ya ware duvet ɗin jikinsa kai tsaye bathroom ya nufa,
Yayi wanka ya wanke bakinsa tare da ɗaura alwala,
Shirya kansa yayi cikin wata farar tattausan Male La Doublej Jallabiya mai gajeren Hannu, wata farar hula ya ɗauka wacce ake cewa tashi kafiya naci irinta larabawa, a saman sumar kansa ya sanya hular wacce ta rufe masa sumar kan sauran gashin kansa kuma suka sauka saman wuyansa, kai tsaye masjid ya nufa bai dawo ba sai wajan 7:00
Yana dawowa ya shirya kansa cikin ƙana nan kaya masu kyau, wandon ya tsaya masa iya laps ɗinsa kamar dai kayan spots wear, gorar ruwa ya ɗauka mai sanyi kai tsaye gym part ɗinsa ya nufa, yana zuwa ya fara motsa jikinsa domin idan yace zai zauna haka tabbas damuwa da kuma rashin mahaifinsa sai iya tarwatsa zuciyarsa, haka ya dinga motsa jiki har wajan 10:30 sai zufa ce take karyo masa.
Tura ƙofar side ɗinsa yayi a hankali bakinsa ɗauke da gorar ruwa yana shan yayinda gumi ke yanko masa, ganin Oumuu-Ayman ne yasa ya ɗan ware idanunsa tare da kwaɓe fuska a sanyaye ya ƙarasa saman kujera yana sauke numfashi.
Murmushi Oumuu-Ayman tayi kafin tace.
"Wlcm Zaki"
Jinjina kai Abu Maleek yayi kafin yace.
"Barka da safiya Oumuu na"
Kallonsa tayi sosai ajjiyar zuciya ta sauke ganin babu abinda Abu Maleek ya bari na dan gane da kamannin Murgayi King Tunde Muhammad Jalal.
"Zaki Ya mai jiki?"
Zare idanunsa yayi kafin ya langwaɓar da kansa gefe guda cikin gajiyawa yace.
"Ayyah! Baga irinta ba, wallahi Oumuu na manta da ita tun shekaran jiya"
Murmushi kawai Oumuu-Ayman tayi kafin tace "Ni ina sane da ita, domin duk bayan wasu awanni sai nazu na gyara mata Jikinta na shafa mata mai a kanta, Allahamdulillah naga gashi ya lulluɓe kan nata, gwanin sha'awa wallahi"
Taɓe baki yayi ba tare da yace komai ba, gani yau bai tashi da ƴan son magana da ita bane yasa Oumuu bashi breakfast Pancakes and Syrup sai haɗin salad Wanda yaji da faffan ƙwai, da Tomato's With Onion kana masan Salad da caroot.
Yana gama ci ya shige bedroom ɗinsa, Miƙewa Oumuu tayi ta nufi bedroom ɗin da Julde ke ciki, tana kwance tana sauke numfashi goge mata Jikinta tayi ta bata madara tare da gyara mata sumar kanta daya feso da yawa Lokaci guda.
Kwaɓe fuska Julde tayi a hankali ta shiga motsa bakinta cikin Murya mai rauni tace.
"Ballowo!!"
Shiru Oumuu-Ayman tayi domin ta fahimci Julde Makauniya ce, amma sam bata Fahimci sunan "Ballowo" da take yawan faɗa.
After 7days
Bayan anyi sadakar bakwai ne aka fara shirin yin naɗi, gefen Abu Maleek kowa ya manta da batun Julde rabonsa da ita tun ranar daya bata jininsa tasha wajan kwana shida ko biyar kenan.
Yayinda kullume sai Oumuu ta gyarata kuma sosai Jikinta ya murje saboda zama waje guda, cima mai kyau ga kulawa, har lokacin kuma babu wanda yasan da zamanta a cikin Alaafi!.
4:40 dawowarsa kenan daga masjid yana sanye da wata Blue ɗin Armless mai kyau, wacce ta ɗan kamasa yayinda ya ɗan zuge gaban rigar bayan shigowar sa cikin side ɗin nasa,
Walking slowly yake shigowa cikin side ɗin nasa, yayinda yake tafe yana ɗan sauke ajjiyar zuciya saboda bugawar zuciyarsa take masa, wacce lokaci zuwa lokaci take masa,
Ya iso dab da bedroom ɗin da Julde ke ciki yaji Zuciyarsa ta harba da ƙarfin gaske da sauri ya runtse idanunsa tare da saurin faɗin.
"hasbunallah!"
Ya faɗa yana dafe ƙirjinsa, har ya ɗaga ƙafa sai huce kunnuwansa suka jiyo masa sautin Muryar ta, tare da buge bugen da take,
Golden eyes ɗinsa wanda suke fidda wani ruwa ruwa saboda tsabar farinsu,
Kamar zai tafi sai kuma ya nufi bedroom a ransa yana faɗin "O'ohhhh This Fulani girl..."
Hanunsa ya ɗura saman wajan passward ɗin yana rubutawa ƙofar ta buɗe, a hankali ya sanya ƙafarsa ciki yanayin kusantar ɗakin yanayin ƙaruwar bugun zcyarsa, can ya tsaya lokaci guda kuma yaja baya da sauri yana dafe ƙirjinsa saboda idanunsa da suka sauka akan......
Abu Maleek isn't free contact to subscribe 08119237616
*_41-42_*
Dugwayen ƙafafuwan ta, wanda suke farare tass har wani yellow suke saboda wani fari da tayi fatar ƙafafuwanta sunyi fresh, sunyi ɓulo ɓulo.
Ga wasu gargasa da sukai kwance a saman farar fatar jikin ƙafafuwan nata, sai ƙyalli suke saboda tsanani kulawar da Oumuu-Ayman take bawa Julde,
Sauyawa ta musamman tayi saboda zama waje guda, da kuma kulawar da Oumuu-Ayman take bata akai akai.
Ajjiyar zuciya ya sauke a hankali ya jingina bayansa da jikin door, yana ɗan sauke numfashin tare da jan Maraitattun idanunsa ya rufe su, a hankali yake fidda numfashi kuma yake shaƙa, almost 30seconds kafin cikin nutsuwa ya shiga ɗaga zara-zaran eyes lashes ɗinsa wanda suke kwance saman fatar idanunsa.
Kai tsaye kuma ya sauke idanunsa a saman fararan farcen yatsun ƙafafuwan ta, wanda akaiwa ado da wani red ɗin jan farce, hakan ya ƙara bayyanar da Zallar kyau da kuma tsarin kyawun yatsun nata.
Ƙuri yaywa yatsun ƙafar nata kamar mai Shirin neman wani abu, some seconds kuma ya shiga zame idanunsa yana ɗan taɓe bakinsa kamar wanda yaga kashi,
Teeths ɗinsa yasa ya datse jajayen laɓɓansa tare da fara tauna su, saboda wani irin harbawa da zucyarsa tayi masa da ƙarfi, al'amarin daya haddasa masa saurin runtse idanunsa yana furzar da iska daga cikin bakinsa.
A hankali kuma ya sanya tafin hannunsa da a kullum baya rabuwa da gumi ya manna a saitin wajan da yaji yafi harba masa a cikin ƙirjin nasa, kwaɓe fuska yay tare da langwaɓar da kansa gefe guda,
Cikin wata kasalalliyyar murya mai matuƙar sanyi ya ware laɓɓansa tare da faɗin.
"Uhm! Ya Hakkamu!!!"
Ya faɗa yana ɗan juya da sauri zai bar cikin bedroom, domin ji yake idan yaci gaba da tsaiwa Tabbas zuciyarsa zata iya fitowa saboda a zabar bugawar da take masa.
Kamar daga sama yaji sautin Amon muryarta wacce take fita a hankali, Muryar da Amonta kawai zai sanya ka fahimci rauni da kuma halin buƙatuwa da mai muryar take ciki tana faɗin.
"Ballowo!!"
Shine abinda ta faɗa yayinda sautine Amon muryarta wajan faɗin wo!!!!! Ya ƙare a raunace kamar mai shirin fashewa da kuka.
Julde kam tun kafin ya shigo taji, Zuciyarta tayi sanyi a hankali kuma ta shiga bada sautin dib! dib!! dib!!! Sakamakon kusanta zuciyarta data Abu Maleek, shiru tayi kamar mai nazari a hankali kuma ta tsaya da buge bugen da take, yanayin yadda Jikinta ke ɓari da kuma bugawar zcyarta daya tsananta yasa ta fahimci Kallonta yake.
Ajjiyar zuciya ta sauke, a hankali kuma kunanta yaji sautin mutsawar gangar jikinsa alamar fita zai wannan dalili ya sanya ta kwaɓe fuska a hankali wasu sila sila hawaye suka ganganro daga cikin idanunta zuwa gefen fuskarta, kafin cikin muryarta mai ɗauke da zallar shagwaɓa ta ambaci sunan nasa.
Wannan dalili ya sanya Abu Maleek tsayawa ba tare daya juyawa ba, shi kam shagwaɓe fuska yayi kamar zai kuka,
Jin shiru yasa Julde fara sakin shassheƙar kuka yayinda da Jikinta yaci gaba da bugawa, tana shirin yin magana taji Muryar sa wacce ta sanya tayi saurin yin shiru da bakinta sai Ajjiyar zuciya take saukewa amma still Jikinta bai bar rawa ba.
Walking slowly ya fara taka ƙafafuwan sa a saman lallausan carpet ɗin bedroom ɗin, hannunsa duk biyun zube cikin aljihun wandon sa, cak ya tsaya saman kanta, Jin numfashinta a kusa da ita ne yasa,
Ta ƙara marai-raice fuska ta shiga ƙoƙarin Miƙewa zaune,
Ganin abinda take ne yasa ya ɗaga ƙafarsa guda ɗaya, tare da ɗurawa a saman hannunta ya danne.
Ƴar ƙara ta saki tana turo bakinta gaba kafin tace.
"Bafiiii fa Ballowo"
Juya idanunsa yayi sosai a ransa yake faɗin "wato Yarinyar nan komai nawa take kwaikwayo Uhm, Witch!"
Ya faɗa a ransa yana ƙara danna ƙafarsa dake saman hannunta.
Oumuu-Ayman ce ta turo ƙofar a hankali tare da shigowa bakinta ɗauke da sallama, tun kafin ta shigo ta san cewa yana ciki saboda ƴar danjar dake harbawa a bakin ƙofar alamar an shiga ciki.
Akan wani table ta ajjiye tray ɗin hannunta, tare da juya ta nufi wajan Abu Maleek fuska ɗaure take faɗin.
"A'a ya zaka zaki? Bafa na son cin zaki kaji ko?"
Ta faɗa tana zama gefen bed ɗin tare da sanya hannunta ta ture ƙafarsa amma ko motsi ƙafar ba tai ba,
Kallonsa tayi tace.
"Kaga kowa zan ɓata maka"
Zame ƙafarsa yayi a hankali tana sakin numfashi kana ya ɗan zauna a gefen Oumuu na dama, Murya can dai-dai kunnan Oumuu yadda Julde baza taji abinda yace ba yace.
"Oumuu na, yunwa taimakamin"
Ya faɗa yana narke mata fuska kamar yaron goye, banza tai masa duk tasan cewa lallai yunwar ya keji tunda har ya buɗe bakinsa yayi magana.
Oumuu-Ayman Julde ta kalla a hankali kuma ta sanya hannunta ta shafi lallausar baƙar sumar data yiwa kan Julde ƙawanya har wani tsayi tayi sosai, saboda mayukan da take shafawa kan bana wasa bane dalilin da yasa lokaci guda gashin ya Fito ya cika kan, yanzu kuma tsayi kawai yake.
Cikin kulawa Oumuu-Ayman tace
"Daughter Meke damun ki?"
Jin Muryar matar da kullum take zuwa wajanta ta bata abinci ta gyara mata jiki harda wanka some time, yasa ta ɗan juya fuskarta zuwa derection ɗin inda yake jiyo Muryar Oumuu, cikin Sa'a kowa juyayyun idanunta suka sauka akan Oumuu kafin ta kwaɓe fuska tana shirin yin kuka tace.
"Wala ko Damata'm"
Ma'ana ba abinda yake damuna, jinjina kai Oumuu-Ayman tayi kafin ta sanya hannunta ta ɗaga Julde tare da ɗan Rungome ta, kallon fuskarta tayi, Zallar kyau kawai take gani kyau na a salin gaske, yayinda kuma fuskar take mata kamanceceniya data wata, sai take gani kamar ta taɓa ganin fuskar Julde.
Jinta a jikin Oumuu-Ayman yasa ta lafe tana tura baki gaba tare da sakin Ajjiyar zuciya, Abu Maleek da bai san mene ake ba Wayarsa ya zaro ƙirar Iphone 13pro max ya fara latsawa, kai tsaye kuma team ɗinsu na Hala Madrid ya fara dubawa.
Oumuu-Ayman ce ta kallesa kafin tace.
"Zaki maza ɗauko min tray ɗin lunch ɗin can"
Idanunsa ya ɗaga ya kalli Oumuu-Ayman ganin kallon da take masa ne, ya sanya shi karyar da wuya ba tare da yace komai ba, ya miƙe jiki a sanyaye ya nufi wajan tray ɗin a gefen Oumuu ya ajjiye kana shima ya zauna a gefenta yana mai ajjiye Wayarsa waje guda tare da zuba masu idanu.
A hankali kuma ya fara yawo da idanunsa akan shigar dake jikin Julde wasu, Applique logo detail T-shirt black color ce a Jikinta, wacce ta tsaya mata iya cinyoyinta, wuyan rigar nada faɗi sosai, gashi mai siririyar igiya ce, ga wani shape ɗin Almakashi da wuyan rigar yake dashi, hakan ya sanya farar fatar wuyanta ta bayyana, har ana iya hangen saman tsayayyun brest ɗinta.
Ƙasa yayi da idanunsa a hankali kuma ya sauke ganinsa akan shatin nipples ɗinta Wanda suka bayyana sosai, jin kansa ya sara da ƙarfi ne yasa a hankali ya janye idanunsa yana mai sauke ajjiyar zuciya tare da faɗin.
"Iskanci kawai,uhm!!"
Ya faɗa a cikin ransa, yana mai ɗan lafewa a jikin Oumuu-Ayman hakan yasa fuskarsa tayi farcing data Julde har yana iya shaƙar ƙamshin Jikinta dake fita a hankali yana kawowa hancinta, lumshe idanunsa yay yana ƙara narkewa jikin Oumuu-Ayman kafin a hankali cikin daddaɗar sautin Muryar sa yace.
"Oumuu ki matsar da ita daga jikin ki"
Ya faɗa yana ƙara kulle idanunsa saboda wani mahaukaciya sarawa da kansa yay masa,
Oumuu-Ayman Murmushi tayi kafin tace.
"Matsayinta ɗaya dakai akai, Daughter sunana Oumuu-Ayman, Zaki kuma nace min Oumuu na!!"
Ta faɗa tana sanya spoon a cikin plate ɗin lunch ɗin me ɗauke da Amala and ogbono soup, sai how head Wanda yaji kayan ƙamshi hadda daddawa.
Julde dake shaƙar ƙamshin wani ƙamshin strowbeery dake fita daga cikin bakin Abu Maleek ta kwaɓe fuska tare da faɗin.
"Oumuu na, kin gansa ko?"
Ta faɗa tana ɗaga hannunta tare da saukewa a ƙirjin Oumuu wanda yay dai-dai da kusa da bakin Abu Maleek, Oumuu-Ayman ganin yadda Julde take kwaɓe fuska za tayi kuka tace.
"Me yayi maki?"
Oumuu-Ayman ta faɗa tana ɗebo Amala tare da kaiwa bakin Julde ƙaramin bakinta ta buɗe, wanda laɓɓan sukai jajirr Tamkar wacce ta shafa Lip balm saboda jan da sukai, a hankali ta fara cin abincin tana zare juyayyun idanunta hakan yasa Abu Maleek kwaɓe fuska.
"Oumuu na, kallo na yake fa"
Julde ta ƙara faɗa bayan ta cinye Amalan bakinta, Tuni Abu Maleek ya kulle idanunsa ba tare daya bari Oumuu-Ayman ta gansa ba.
Ganin Ba ita yake kallo ba yasa Oumuu-Ayman ƙara mata Abincin tana faɗin.
"Ba kallonki yake ba Daughter"
Oumuu-Ayman ta faɗa tana ƙara bata Abincin, lumshe idanunta kawai tayi domin a Jikinta ta kejin kallon da yake mata,
A hankali take cikin Abincin harta ƙoshi, koda Oumuu-Ayman ta bata naman kan saa ƙin ci tayi saboda rashin sabo,
Ruwa tasha mai sanyi a hankali ta sauke Ajjiyar zuciya tana ƙara riƙe ƙirjin Oumuu-Ayman kamar wani zai gudu da ita.
Abu Maleek da idanunsa yake a lumshe ya shiga buɗewa a hankali kana ya sauke idanunsa akan ɗan ƙaramin bakinta, wanda suke shanny sun ɗan tattare hakan yasa suka ƙara kyau.
Idanunsa ya janye kafin ya kalli Oumuu-Ayman murya dai-dai kunanta yace.
"Ki daina shafa mata jambaki ba kyau"
Ya faɗa yana Miƙewa daga jikin Oumuu-Ayman tare da ɗauke fresh milk ɗin da Oumuu-Ayman tazo dashi zata bawa Julde.
Da sauri Julde tace.
"Oumuu na ya tafi fa"
Kanta Oumuu ta shafa tace.
"Rabu dashi kinji Daughter na"
Marai-raice fuska Julde tayi tace.
"To ya sunansa shi?"
Jinjina kai Oumuu-Ayman tayi tana girmama Surutun Julde kafin ta bata amsa da.
"Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal, popular name Shine Abu Maleek Amma ke yayanki ne Kinji kina ce masa Yaya Jalal is better"
Shiru kawai Julde tayi, Oumuu kan ƙara gyara mata jiki tayi kana ta fita zuwa sashin ta, domin ta shirya ta amsa kiran Mai Babban ɗaki.
Abu Maleek kai tsaye flat ɗinsa ya nufa, a ƙawataccen parlon nasa ya samu sweet a saman kujera, gana ganinsa ta tashi da gudu ɗaukan ta yayi yana shafa bayanta, sai daya ƙara shan fresh milk ɗin kana ya zube saman kujera yana faɗin.
"Miss You so much sweet, sorry Kinji"
Ya faɗa yana kafawa sweet fresh milk ɗin a baki sai da ta shanye tass Sannan ya cire yana yin baya tara da kwanciya, ba jimawa bacci ya ɗauke sa, kiran Sallar Magrib ne ya tayar dashi, yana tashi kai tsaye cikin bedroom ɗinsa ya nufa yana ajjiye sweet tare da shigewa bathroom.
Yana shiga ya zame kayan jikinsa ya sanya jikin hanger, kansa ya sakarwa shower ruwa ya fara saukar masa, a hankali ya sauke idanunsa akan zanan ƙirjinsa zanan da har yanzu bai fahimci na mene ba, lumshe idanunsa yayi yana mai da idanunsa akan J ɗinsa wacce take kwance ko harbawa ba tayi bare yayi tunanin lafiyarta,
Zuwa yanzu kam baya damuwa yasan Ubangiji ne kaɗai yasan abinda yake ɓoye, idanunsa ya ɗauke kana ya kashe shower, ya fito sanye da bathrobe jikinsa na zubar da ruwa, ko mai bai shafa ba, sai parfume daya fesa kana ya ɗauki wata Muslim thobe jalabiya Maroon color mai kyau ga wani laushi da take dashi, yana sanyawa yasa Mon mule slippers, ta can ƙofar baya yabi zuwa Masjid.
Yana zuwa ana tayar da Sallah hakan yasa ya zamana yana layin baya, bayan an idar ne kuma ya zauna a haka sallar Isshā ta samesa, sai daya gabatar da ita kana ya nufi part ɗinsa.
Yana shiga Bedroom ɗinsa ya samu Wayarsa na haske, ganin mai kiran ne kuma yasa yayi answering tare da manna wayar a kunansa, tare da kwanciya a saman bed ɗin sa.
Shiru yayi yana sauraran abinda mai kiran yake faɗa, "Uhm"
Kawai yace bayan ya gama sauraran komai kana ya kashe wayar, jin baya jin yunwa ne yasa yaci Apple da Inibi, kana ya shiga bathroom ya watsa ruwa.
Wasu fararan Tartan check print pyjama ya sanya kana ya fesa turare tare da cilla strowbeery mouth freshnerh a bakinsa, kai tsaye royal bed ɗin sa ya nufa tare da jawo sweet ya rungome duvet yaja ya rufe masu jiki babu jimawa bacci ya ɗauke sa.
Washe gari
Tun safe da Mai Babban ɗaki ta kira Abu Maleek bai dawo part ɗinsa ba, yana can tare da ita da Oumuu-Ayman da kuma sauran Aremo.
Yanzu ma yana zaune bayan ya dawo daga masjid ya ɗan zauna kusa da Oumuu-Ayman yana jin kansa duk a takure, ga kuma kallon da Bola take masa, ga MALEEK dake jikinsa yasa, hakan yasa duk ya kejinsa a takure sarai Oumuu-Ayman tasan bai san yawan mutane da kallo, hakan yasa tai masa banza tana jin yadda zungurinta tare da riƙe mata hannu, sosai take son ya saba da ƴan uwansa, to mutumin da zai wakilci dubban jama'a ga baki ɗaya kenan.
Mai Babban ɗaki ce ta ɗan sakace bakinta saboda naman da taci tace.
"An zauna da