Showing 147001 words to 150000 words out of 161948 words
wacce kake so, da sauri Julde ta zare rigar jikin Cucuu, cikin sauri Arɗo ya zare rigarsa nan take Zanan Taswirar ya bayyana a ƙirjin ko wannan su, da wani irin sauri Salimerh ta.....
Allah Ubangiji ya nuna mana Monday lafiya😍🤝🏻 idan nai kuskure feel free bawai ka zagen ba dan Allah, ɗan Adam ajizi ne,a kullum muna yiwa Ubangiji laifi bare ɗan Adam😭
*SARAUTAR MARUBUTA*
*_95-96_*
Tai baya luuu zata faɗi Junaid yay saurin tare ta, da wani irin hargitsastsan kallo take bin kirjin ko Wannan su, a hankali kuma cikin ruɗu ta fara bin zanan Taswirar dake ƙirjin ko wannan su,sosai tai mamakin ganin zanan Taswirar yana da bambanci da wacce take jikin Arɗo da kuma wacce take jikin Abu Maleek, Murmushi Muhammad Jalal yay yana wani ɗan lumshe idanunsa kamar yadda Abu Maleek keyi Salimerh ya kalla yace.
"Mamaki ko? Ban san ki ba, i have no idea akan who are you, amma ke har kin samu damar farautar abinda yake ba naki ba? Kin samu damar da zaki kwashe dukiyar da ko mahaifiyar ki bata da iko a kanta balle kuma ke? Uhm kamar nasan da haka, hanyar fitar da kaya ta ƙarƙashin ƙasa a Alaafi guda biyu ce, ko kin samu Taswirar jikine Abu Maleek akwai inda zaki ɓata a hanya, domin an cire zanan ƙofa biyu na ƙarƙashin ƙasa, kina tafiya hanyar zata bauɗe maki, Wow! The you know what? Zaki koma hanyar Zanan Taswirar jikina, ita kuma bakinsa yadda zata fitar dake waje ba, hakan yasa zaki ɓata ɓatt, ki ƙasa dawowa Alaafi kuma ki ƙasa fita wajan gari, hakan na nufin zaki ƙare rayuwarki ne a cikin ƙarƙashin ƙasa" Shiru yay yana sauke numfashi yana jin yadda kansa ke masa ciwo kafin a hankali ya dawo da dubansa ga Malamin Alaafin yace.
"Ka sauya min fuska, kasa anyi min juyan tunanin Mutumin da bashi da imani ko ɗaya a ransa, ko iya haka na Barka Ubangiji zaimin sakayya dakai, na amince maka na yarda da kai na baka dukkan amanata amma kai watsi da hakan ka ruguza farin ciki na, bana ƙaunar fuskar daka sanya aka samin Kamilalliyar fuskata tafi wannan da take jikina, kamar yadda ka sani mu biyu mahaifin mu Jalal ya haifa, da Tunde da kuma ni Muhammad, nine babba amma ko da nayi aure ban samu haihuwa da wuri ba, sai ya zamana Tunde ya rigani haihuwa ya haifi Sharefddeen, Tunde ba yaji he's very stubborn wannan dalilin tun kafin yay aure yabar ƙasar, sai da yay auran muka samu labari, lokacin Mahaifin mu ya rasu, Ni kuma naci gaba za riƙe kujerar sarautar Kanzaf, bisa taimakon Otun da Agba Akin, da Mai Babban ɗaki, sai kuma Ƙwarƙwara ta Roomana" shiru yay yana jin wani hawaye na kawowa fuskarsa cikin dauriya ya kalli Salimerh yace.
"You killed my wife, me tayi maki? Akan kawai biyan buƙatar ki? She's so nice, friendly Educated ina da tabbacin komai kika ce kina so zata baki, kin kashe min matata ba tare da laifin komai ba, ƙilan abinda take gudu kenan shi ne yasa ta maida kanta matsayin ƙwarƙwara, akwai ƙyakkyawar fahimta tsakanin matata da brother na, akwai wasan ƙanin miji yana girmama ta sosai, shiyasa take kula da shi amma kalli yadda kika kasheta,ta hanya mai muni you killed my wife Salimerh" ya faɗa yana zubewa a wajan tare da fashewa da kuka, jikin Abu Maleek ne ya ɗauki rawa ko ina na jikinsa tsuma yake, duk da cewa ya samu lafiyar ƙwaƙwalwarsa amma zafin zuciya ya riga daya samu gurbi a cikin zuciyarsa..
Zame hannunsa yay daga cikin na Julde a hankali yake tafiya zuwa inda Daƙile take wacce ta kasa koda mutsi, yana zuwa ya sanya hannunsa tare da ɗauke ta da wani ba hagon bari, ƙarfin marin yasa tai baya da sauri zata faɗi Junaid ya sake riƙe ta.
Jiki na rawa Abu Maleek ya ƙara ɗaga hannunsa tare da sauke mata wani marin jiki na rawa kuma ya riƙe wuyanta tare da shaƙe ta, wani irin nishi ta fara Idanunta ya shiga fitowa.
Ganin hakan yasa Junaid faɗin "Abu Maleek ka sake ta please na roƙe ka, nasan tayi abinda ya cancanci kisa, amma kayi min alfarma saboda cikin dake jikinta" da sauri Queen Roomana ta kallesa jin Abinda yace a hankali kuma tace..
"Wanne ciki kuma? Cikin daya daɗe da bin rariya lokacin data faɗi tun baya, ka kuma manta lokacin da tayi jinya ko ita tace maka tana da ciki"
Baki ya saki cikin rashin fahimta yace "kamar yaya? Bayan ina da tabbacin akwai ciki a jikinta" Murmushi Queen Roomana tayi kafin tace "to gata nan ai, Jalaluldeen sake ta sai tayi masa bayani" Abu Maleek baya gane zan can, idanuna kawai ƙyakkyawar fuskar Oumuu-Ayman suke hasko masa da wani irin ƙarfi yace.
"Kin cuce ni, you blackmailed me, kin kashe min uwa mahaifiya, sai yanzu na fahimci soyayyar da Maaamahh take min ba iya ta mai raino na bace, Zallar soyayyya ce ta uwa da ɗan ta, sai yanzu na fahimci abinda kalamanta suke nufi na S...J..K tana nufin na kula da macuciya kuma ma yaudariya Salimerh, tana nufin na kula da haƙƙin daya rataya akai na, na zama gata,da farin cikin Matata Julde, tana nufin bayan ni akwai wani tarbiyyar sa na hannun Allah tana hannu na, na kula da maraicin Khaleluddeen, kina tunanin kin rusa farin ciki daman ai ban buɗe ido akan cewa ita ce mahaifiyata ba, look! Kalli can waccan itace mahaifiyar Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal itace uwa ga Abu Maleek, na tsane ki ban sonki Maƙiyi na bayyana kansa ke kuma sai kika zo min a mace, suffar mutanan ƙwarai ki nuna soyayya a gareni ashe ba haka bane,kin ƙara sanya min tsoran mata, matata itace ƙawata, itace Abokina, itace farin ciki na itace sirrina"
Ya faɗa kuka na kwance masa mutuwar Oumuu-Ayman ta dawo masa sabuwa.
A hankali Muhammad Jalal yake kuka zuciyar nayi masa zafi, yana jin zazzafar Kunyar sirikar tasa, Yaywa Julde abubuwa da yawa ya musguna mata, ya batta da yunwa.
A hankali Mai Babban ɗaki ta miƙe tsaye ta nufi wajan Arɗo kuma Muhammad Jalal tana zuwa ya ring mahaifiyarsa yana faɗin.
"Mama" rungomesa Mai Babban ɗaki tayi tana bubbuga bayansa.
A hankali Queen Roomana ta kalli Julde wacce take tsaye Idanunta har yanzu zubar da hawaye yake, cikin dauriya tace "to kika bari dai mijinki yay kisa kema zaki rasa shi" da sauri ta girgiza kanta hawaye na ƙara zubu mata, da sauri tai wajansa, lokacin Salimerh ta fara ficewa daga hayyacinta cikin sanyin murya tace..
"Let her go"
Cak ya tsaya yana maida numfashi yana sakinta kuma ta faɗi a wajan tana mai da numfashi, cikin sauri ya juya ya rungome Julde yana mai ƙara sakin wani kukan..
Shiru tayi domin a lokacin ta fisa dauriya cikin lallashi ta dinga shafa kansa ba tare da tace komai ba..
Junaid ne ya kalli Salimerh yace "kin barni cikin duhu ina cikin dake cikin ki?" Idanunta ta rufe hawaye na zubu mata tace.
"Lokacin da naje duba akwatin dana ɓoye a cikin swwiming pool ɗin Abu Maleek na tarar babu, cikin gigita na dawo side ɗina lokacin baka nan, tashin hankalin da yay min yawa ne yasa nan take jini ya fara zuba a jikina, nasha wahala sosai ina wannan halin ne kuma Hadima Akin ta shigo ita ta saman a lokacin cikin dake jikina tuni yabi jini tunda ba ƙwari yay ba, hakan yasa na buƙaci ta ɓoye suma ban su sukaji ba, dalilin ciwon da nayi har asibiti ne yasa likita ya faɗa masu ɓari nai, nasan Queen Roomana ba zata taɓa cewa komai ba shi yasa ban damu da ita ba, damuwa tai min yawa sosai, hakan yasa na shirya wata akwatin da niyyar idan Abu Maleek ya biyo mu zan masa dole akan ya bani dukkan wasu kadarori daya samu da kuma abubuwan company ɗin sa, da gifts na Daimond, a zurfa daya samu, idan yaban ni kuma zan sake sa, tunda bani da kayan da zan fitar daga cikin Alaafi, banyi tunanin abin zai juye har haka ba,dan Allah ɗan uwana kayi min rai kaimin afuwa ka haife min sharri sheɗan ne" wani mari Julde ta sauke mata tace..
"Sharrin sheɗaniyya dai, bari kiji tun lokacin dana sanya idanuna akanki nasan cewa baki da gaskiya, koda gubar da kika zuba aka kawowa Mijina ita wallahi noting will happen to him saboda ina iya ganewa ina kuma fahimta, bashi da ikon ya yafe maki,domin rai kika kashe kin kashe mana farin cikin mu idan Kinje Court zaki bayani za kuma ki girbe abinda kika shuka stupid"
Tunda ta fara magana Abu Maleek yake kallon ta,yana jin kalar daɗi na ratsa masa dukkan zuciyarsa ga wata nutsuwa ta musamman na sakko masa.
Kuka Queen Ayoola ta saki tace.
"Ban taɓa nufar kowa da sharri ba, sai Adams dana faɗa masa cewa Jalaluldeen ne ya ɗauke Roomana na faɗa ne kuma nima kawai saboda isan inda take amma wallahi babu abinda naiwa kuwa, na haifi yara ban haifi halinsu ba, dukkan abinda akai Maku kune kuka jawa kanku,gwamma Sharefddeen yana da hujjar yi amma ke mene taki hujjar keda mike AGOLA, wacce baki da mara ba sa TSINTACCIYA a gidan"
Shiru ne ya biyo baya Junaid kam kasa cewa komai yay, yana son matarsa sosai, amma yasan dole hukuncin kisa ya hau kan ta.
Bola ce ta gyara zama tace.
"Munji komai amma wanene ya daki Abu Maleek a wannan ranar? Kai kuma Jon wuro mene ya faru a rungar ku bayan barin Zubaida?"
Shakiru ne ya sunkuyar da kansa ƙasa cike da Kunya yace.
"Nine, domin a wannan ranar gaba ɗaya mu ukun muka fito ana tsaka da ruwan sama, Abu Maleek ya fito daga sashin Queen Roomana zuwa sashin Oumuu-Ayman, ni kuma tsananin kishi ne ya sanya na aikata hakan, musamman daya zamana Abu Maleek ya fini kyau ko nace ya fimu komai na rayuwa, a wannan lokacin kishin sane ya cika min zuciya, koda na aikata kuma nai ladama itana astagafirullah a rai na"
Jinjina kai kowa yay kafin Jon wuro yace.
"Bayan komai ya lafa na kisan da akai, wanda sukai saura daga cikin fulanin suka fara firfitowa daga wajan ɓoyewer da sukai, a haka kowa ya haɗu akaita kukan rashin, Muido kam a wannan lokacin daman bai ko motsa ba, haka kuma muka rasa Shatuu (Zubaida) muna zaune da raguwar Naggen da suka rage wanda gaba ɗaya mallakin Muido ne, kamar yadda Modibbo ya shaida min, a wannan ranar ne kuma Modibbo ya fita zuwa samu ruwa. Acikin ruwan ya samu jaririyar ko cibi ba'a yanke mata ba, cikin sauri ya kawota wajan Yakumbo, washegari kuma shirya muka kwashe dukkan kayan mu da bukkokin mu muka kama hanyar barin rugar, muna rafe muna yadda zago muna kuma kula da Hawwa'u Julde, a haka muka ɗauki shekaru masu yawa har Julde tai wayo kafin mu ƙarasu wannan garin muka samu waje gurin nan ya zamana RUGAR MAHINJO, banyi mamakin yadda Arɗo yake baya Julde wahala ba domin bashi da imani ko ɗaya yana son kuɗi musamman daya fahimci duk Naggen da sukai saura nata ne, to Allah sarki ashe shima bayin kansa bane bai san abinda yake aikatawa ba" shiru ne ya biyo baya kowa abinda yake tunani a ransa daban, yayinda kuma rashin Oumuu-Ayman ya dawo sabo a zuciyar ko wannan su.
Lura da halin da Abu Maleek yake ciki ne yasa Julde kama hannunsa a hankali yabi bayanta, Queen Roomana, Adams, Mai Babban ɗaki, Bola, Shakiru, Junaid da sauran su ga a ɗaya miƙewa sukai domin lokacin sallar zhur yayi.
Bayan sun idar da sallar da Muhammad Jalal ya jasu ne suka shiga cikin bukka, Zallar madara aka tasu masu sai hucin zafin take tana ɗumama musu.
A hankali suke tafiya cike da nutsuwa kana kallon su kaga cikakkun masoya masu masifar son junansu.
A baƙin wata gaɓar ruwa suka tsaya a hankali Julde ta matsa kusa dashi ta bayansa, dukkan hannunta ta ɗura saman ququnsa tare da kwantar da kanta a bayansa, a hankali take shafa ƙirjinsa tare da murza ƙwantaccen gashin ƙirjinsa, cikin ƙasa da Murya tace.
"_Love is something beautiful, and a feeling that one will like to carch. Love is the feeling that makes you feel alive_, Ina sonka Ballowo, zuciyata tana maka sahihin so da ƙaunar da ita kanta bata san adadinsa ba, kowa iyaye suna zame masa gurbin farin ciki kuma Garkuwa ga rayuwa duk yaransu, amma ka zame dukkan abinda wata mace take buƙatar samu a rayuwa, So a baki ba shine ba, a daraja kalmar da kuma wanda ake so Shine cikar SO shine aka bawa so dukkan haƙƙinsa, I love you so much Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal ina fatan zuciyarka zata suni kwatankwacin yadda nake _SONKA_"
Wasu hawaye ne suka sakko mata a hankali hawayen kuma ke sauka bayan, lumshe idanunsa yay yana jin zuciyarsa na wani irin fitinannan harbawa.
A hankali ya sauke Ajjiyar zuciya tare da sanya hannunsa ya jawo ta zuwa gabansa, kyawawan idanunsa masu ɗauke da so da ƙaunar ta haɗi da masifaffiyyar sha'awar ta, kasa ce mata komai yay sai zamewa da yayi ya zauna a gaɓar kogin yare da zura ƙafafuwansa a ciki yana Kaɗawa.
Idanunsa ya ɗaga a hankali ya kalleta a taushashe yace "have a set" ya faɗa yana kama hannunta zama tayi kusa dashi tare da ɗura kanta a saman kafaɗarsa cikin sauke ajjiyar ya kama hannunta yana murzawa tsakiyar tafin hannun nata yace.
"Kalli yadda kifi suke wasa a ruwan, kalli how happy da suke ciki uhm" Shiru yay tare da zameta ya ɗura ta akan cinyarsa yana shafa gashinta daya hargitse kafin a taushashe cikin wata kasalalliyyar murya mafi kaushi yace.
"Farin cikin kifayen nan bazai taɓa tabbata ba sai suna cikin wannan ruwan, a duk sanda ɗaya daga cikin su yabar ruwan to tabbas adadin kwanakin rayuwarsa ne ya ƙare" shiru yay a hankali kuma ya tura hannunsu cikin rigarta cikin nutsuwa yake shafa lafaffan cikinta wanda yake a manne da mara, lubb tayi jikinsa tana jin wani irin daɗi da nutsuwa na ratsa mata zuciya.
Cibiyarta ya murza da sauri ta lumshe idanunta tana ƙara narke masa kafin taja wani sauti mai ɗauke da buƙatuwar mijin nata, shiru tayi irin shirun nan na bani da mafita sai abinda akace.
"Uhmm Ɓallo...." Saurin kifa fuskarta tayi a tsakiyar cikinsa lokacin da ya kifa hannunsa a saman brest ɗinta, wata Sassanyar iska ya sauke kafin yace.
"You're my life Naaa... nahhhh, ni kece cikon rayuwarta I hope you understand that I will ove you untill the end, because .you are notjust my girl. But you are also my best friend, akanki nasan cewa nima cikakken namiji ne mai zuciyar soyayya, Abu Maleek da zuciyarsa duk naki i love You too"
Kallonsa tayi hankalin gira ya ɗaka mata yace.
"YES! I know you love me, And i love You more and More Jidderhh, if Anything happens to you wallahi I'll die mutuwa zanyi" wani kalar Murmushi tayi taji duk yunwar da take ji ya kau,a hankali ta gyara zaman ta a cinyarsa fuskarta dai-dai saman nashi tana kallonsa, a hankali yake jifanta da wani irin kallo na so da ƙauna yana yawo da narkakkun idanunsa akan fuskarsa.
Hannunta ta sanya tana shafa sajan fuskarsa a hankali ta ɗura yatsunta akan laɓɓansa tana shafawa tace.
"I love You Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal" a hankali shima ya ɗura hannunsa a saman fuskarta yace.
"I love You Hawwa'u Julde Muido" lumshe idanunta tayi kana ta buɗe tana ƙara shafa masa laɓɓansa tace.
"Ina son ka My heart will forever beat for you My King"
Narke mata fuska yay murya a raunace yace.
"My heart,my soul, my everything will forever beat for only you Naa.. nahhhh Hawwa'u"
Kasa daurewa tayi sharr sharrr hawaye suka shiga bin fuskarta cikin Muryar kuka tace.
"My feeling love you, and my. heart just far you. I will love you forever. I miss you ‘mydear"
Murmushi yay tare da miƙewa tsaye bayan ya zareta a jikinsa, a hankali a sanya hannunsa a cikin aljihun wandonsa wata ƙarar box mai tsananin kyau ya ɗauko.
Zubewa yay a gabanta tare da buɗe box ɗin ya zaro haɗaɗɗan ring ɗin da yake ciki sai sheƙi yake.
Hannunsu ya miƙa ya kama nata yana durƙosa gabanta akan gwiwoyinsa yace.
"You'll be with me forever and ever Naa... nahhhh?" Da sauri ta ɗaga masa kanta tana toshe bakinta saboda kukan da tazo mata, hannunta ya kama kamar a India ya sanya mata ring ɗin idanunsa na zubar da hawaye yace.
"Jalaluldeen Loves you Queen Hawwa'u Julde Muido, I promise to love you, And love you,And too love you regardless of anything and everything Queen Hawwa'u Julde Muido, Jalaluldeen LOVE'S YOU"
Kukan ne ya kwace mata kawai ta faɗa jikinsa ta ƙanƙamesa tana sakin wani irin gigitaccen kuka bayanta kawai ya shiga shafawa.
Kafin gently ya zareta daga jikinsa tare da tallafo fuskarta, slowly ya manna tashi fuskar akan nata yana sauke mata fitinan huci daga bakinsa, red tongue ɗinsa ya fidda tare da manna a saman zara-zaran eyes lashes ɗinta cikin nutsuwa ya shiga shanye hawayenta ta tass yana jin yadda take sauke ajjiyar zuciya, bakinsa ya manna a goshinta ya sauke mata wani sassanyan kiss a wajan, kafin ya zare jikinsa yace.
"Look! I got you something" idanunta ta buɗe wani ƙaton kifi ta gani a hannunsa yana motsi, da sauri ya maƙale sa tace.
"Cucuu tsolo ina" Murmushi Yay mata yana lakace mata hanci yace.
"Eyee! Za kizo kice za kici ne kin manta last time ko lokaci kina ƴar ƙwailar ki" Murmushi tayi masa tana ganin har kifin ya mutu ya haɗa hutu ya gasawa, idanu kawai ta bisa dashi hakan ya tuna mata da farkon haɗuwar su, kallonta yay yace "Ohyyyah come here" wajansa ta ƙarasa yawon ta har tsiyaya yake tana zuwa ya tura mata yace "Eat" kwaɓe fuska tayi tace "kai fa" yana kaɗa mata harshansa yace "You first then me" bata tsaya jiransa ba hannu baka hannu ƙwarya ta fara ci.
Da idanu kawai yake binta yana mamakin yadda ta kecin kifin wanda ko magi babu cikinsa, tana ci kamar wai zai kwace mata sai da ta kaji dan kanta ta cire hannunta tana kallonsa, ganin yadda ya kafeta da narkakkun idanunsa yana sakin wani irin fitinannan Murmushi yasa ta tura baki gaba, shafa sumar kansa yay zuwa sajansa cikin