Showing 57001 words to 60000 words out of 161948 words

Chapter 20 - ABU - MALEEK Book Complete BY SARAUTA.txt

05 Jan 2025

6598

Sarkin Fada, da kuma dukkan wanda suke da ruwa da tsaki a naɗin Sarautar sabon sarki"


A tare Adams da Shakiru haɗi da Otun suka ɗaga idanunsa suka kalli Mai Babban ɗaki, Sharefddeen da Junaid kam kowa Wayarsa yake dannawa, dan wannan shirgin baya gabansu.


Gyara zama Queen Ayoola tayi tana faɗin.
"Ma sha Allah, to wa aka tsayar matsayin wanda zai zama tsarki na huɗu a wannan gari na Benin wanda zai shugaban cin Al'ummar Kanzaf damu baki ɗaya"


Sanin cewa idan Mai Babban ɗaki na magana babu mai tankawa sai an bada damar Magana hakan yasa Kowa yay shiru,
Mai Babban ɗaki dai-dai-ta zamanta tayi cikin halin daddako domin yau bata tashi da rikicin ba cikin kamewa tace.


"Queen Ayoola Femi Zaki iya fita waje"
Mai Babban ɗaki ta faɗa in a don't care manner ɗin nan, ba tare kuma data kalli Queen Ayoola ɗin ba.


Murmushi kawai Queen Ayoola tayi tana mai danne abinda ta keji a ranta kafin ta miƙe tana gyara zaman Alƙyabbar jikinta ta ɗan durƙosa tare da faɗin.


"Allah ya huci zuciyar mai Kanzaf da Alaafi baki ɗaya"
Ta faɗa tare dayin waje, tana fita Mai Babban ɗaki tace.
"Nasan kowa ya matso yaji wanda yake shirin zama King? Akwai meeting da yamma so a nan kowa zaiji komai kowa zai iya tafiya"
Ta faɗa tana ɗaukan Apple ta sanya a bakinta, ɗaya bayan ɗaya suka shiga barin ɗakin.


Da sauri Abu Maleek ya yunƙura zai tashi Oumuu-Ayman tayi saurin riƙe hannunsa, hakan yasa ya ɗan kwaɓe fuska tare da faɗin.


"Oumuu na Please"
Ya faɗa yana karyar da wuya, Mai Babban ɗaki ce ta kallesa tana Murmushin jin daɗi kafin tace.
"Oumuu-Ayman ja yaron ki kuyi gaba kada ya cika min ɗaki da mita, kamar wanda yake zaune da wasu dodona"


Kwaɓe fuska yay tare da kallon Mai Babban ɗaki yace.
"Allah Grandma duk kin cika mutane da surutu,uhm!"
Ya faɗa yana tashi tsaye tare da cire Maleek dake jikinsa.
"Kai ka sani, kaci caka baki yanzu zan ce na sake ka"
Mai Babban ɗaki ta faɗa tana miƙewa tare da shafa kansa tace.


"Allah yayi maka albarka, Ubangiji yayi riƙo da hannayenka Jalaluldeen, Allah ya kare ka daga sharrin mutum da aljan, mugun ji da mugun ya kiyaye ka daga su Zakina"


Kallonta yayi tare da yin gaba, kamar bazai magana ba sai kuma yace.
"Ameen badan halinki ba"
Ya faɗa yana ficewa daga parlon nata, kana ya nufi ficewa daga part gaba ɗaya, ganin haka yasa Maleek binsa da gudu yana faɗin.


"Bàami zan kwana wajanka Please"
Shiru Abu Maleek yayi ba tare da yace komai ba, Bola dake tsaye tai saurin faɗin.


"Abu Maleek"
Cak ya tsaya ba tare daya juya ya kalleta ba, domin tuni ya ɗauki Muryarta, ganin ya tsaya yasa Bola dawowa gabansa ta tsaya, da sauri yayi ƙasa da idanunsa, tare da zubawa yatsun ƙafar Maleek ido, ganin hatta ɗan cindon dake ƙaramin yatsar sa yaron na tashi, mai san mene yasa yake jin faɗuwar gaba da zarar Maleek ya raɓu dashi ba.


"Abu Maleek, sai yaushe zaka fara duba na a matsayin mace, macan ma matarka, ko ka manta da cewa niɗin matar kace?"


Maleek ne ya sanya kuka ganin mahaifiyar tasa tana kuka, ƙara riƙe hannun Abu Maleek yayi yana shigewa tsakanin ƙafafuwansa,
Shi dai shiru yayi still kuma kansa yana ƙasa, yana jin jijiyoyin kansa na Miƙewa.


"Ni fa macace kamar kowa, shin kana tunanin bazan so kasancewa dakai bane Abu Maleek? Ban san me nai maka ba haka kuma bana da laifi wajan kasancewa matarka, ko kuma kai ƙaddarar ce ba zaka iya amsa ba kamar yadda na amsa? Yeah nayi believe kowa akwai nayi destiny ɗin so mu ɗauka dani dakai haka ƙaddarar mu take, kuma ta haka tazo, bana da laifi haka kuma ɗana Maleek bashi da laifi amma mene ya sanya baka son buɗe idanu ka gamu ne? Dan Allah Jalaluldeen accept me as your wife please"


Ta ƙare maganar tana haɗe hannayenta alamar roƙo, kana ta saki kuka tana yowa gabansa a ƙoƙarin ta na son shigewa jikinsa,
Saurin yin baya Abu Maleek yayi Maleek dake ƙafafuwan Abu Maleek ya saki Kuka yana ƙara riƙe Abu Maleek duk ya gigice.


Runtse idanunsa Abu Maleek yayi yana jin wani jiri na ɗibansa, nan da nan numfashinsa ya fara sama, ya shiga fisgarsa da ƙyar, ga wani duhu daya fara gani a cikin idanunsa, da alama ciwon daya jima bai ba shine yake shirin tashi.


Bola da bata fahimci komai ba ta ƙara nufarsa a ɗan gigice ya sanya duk hannayensa a saman shoulder ɗinta tare da matsawa da ƙarfi, wanda ya sanya Bola saurin sakin ƙara kafin tai magana yayi saurin yin gefe da ita tare da yin gaba yana rufe hancinsa, saboda wani hayaƙi daya tawo kai tsaye ya shige hancinsa ba tare kuma da sanin daga inda hayaƙin yake ba.


Ihu Maleek ya sanya yana tafiya wajan Bola rungome sa tayi tana sakin kuka itama.


Abu Maleek a daddafe ya shige babban side ɗin sa wanda yafi na kowa girma kyau da kuma tsaruwa, da ƙyar yake jan ƙafafuwansa yana tafe yana fisgar numfashi, a haka ya buɗe ƙofar shigowa side ɗin kana ya nufi part ɗin da yake rayuwa ciki, yana zuwa parlon Oumuu-Ayman na ajjiye Julde a saman kujera 3seater, wacce ta taimaka mata tai wanka tai sallah tare da sauya kaya zuwa wata silk Falling rose pattern nightdress masu mafifafan kyau, wanda suka tsaya mata iya cinya, ga yadda manya manyan cinyoyinta da suke a waje sai ƙyalli suke saboda gyara, abin mamaki kuma kawo lokacin har yanzu Julde bata fara period ba, sai brest da Allah ya wadata dasu,
Ta ƙara fari tai fresh kamar ƙwayar ƙwai, ga pink ɗinta sunyi kyau tare dayin wani bala'in pink, sai wahala hula mai gashi da Oumuu ta sanya mata tafin ƙafarta sanye cikin Aquaholic Slippers, tai kyau sosai kamar ba Julde ba.


Oumuu na zaunar da ita ta juya da ɗan sauri saboda ƙarar buga ƙofar da taji, gabanta ne ya faɗi saboda ganin Abu Maleek dake shirin faɗuwa dukkan jikinsa rawa yake, idanunsa a Lumshe da sauri tayi wajansa, Julde kam ƙara zama tayi tana tsotsar yatsarta tana jin daɗin fito da ita da Oumuu tayi.


"Innalillahi wa'inna ilaihir Zaki na, mene ya sameka Sabunallahu! Zaki what happened to


you kai da waye? Waye ta tare ka? Me akace maka? Ina ke maka ciwo? Ko wani ya baka wani abu kaci ne???"
Ta ƙare tarin tambayoyin nata murya a raunace, hanunsa ta riƙe cikin fusgar Numfashin ya fara kokawa da laɓɓansa kafin ya samu zarafin furta.
"Asthma,, Inhaler!!!!! Oumuu!!!!!!"
Ya faɗa yana yin baya kai tsaye ya faɗa saman kujerar da Julde take kai, kansa ya sauka a ƙirjinta saboda tsayin da yayi mata, da wani irin sauri Oumuu tayi waje.
Wani irin galabaitaccen numfashi Abu Maleek yaja tare da juyar da kansa inda yake jiyo wani sihirtaccen ƙamshi da ɗumi na dukan fuskarsa, da wani irin sauri ya cusa fuskarsa a cikin ƙir.......






Abu Maleek isn't free contact to subscribe 08119237616


If you read for free🤷🏾‍♀️🤷🏾‍♀️🤷🏾‍♀️🤷🏾‍♀️🤷🏾‍♀️🤷🏾‍♀️🤷🏾‍♀️












*_43-44_*
Ƙirjinta inda yake jiyo wani ƙamshi da kuma ɗumi na fitowa ta ciki, wani irin wahalallan numfashi ya ja da ƙarfi, yayinda jikinsa ya tsananta ɓari, idanunsa sun jajir.


Tsananin a zaba da kuma fitar hayyaci da suka ratsa gangar jikinsa ya haddasa masa wani irin matsanancin ciwon kai, nan da nan kuma jijiyoyin kansa suka fito tare dayin raɗa raɗa a saman goshinsa.


Kawo lokacin tuni ya fara ficewa daga hayyacinsa, saboda sosai ya shaƙi hayaƙin da bai san daga inda ya fito ba, hakan ya haddasa wa Numfashinsa cushewa tare da dunƙulewa waje guda.


Jikinsa na rawa kamar mazari ya ƙara manna fuskarsa a tsakiyar ƙirjinta inda yake jin wani mugun daɗi idan yayi hakan, a hankali kuma ya miƙa hannunsa tare da kama na Julde wacce take zaune.


Tun lokacin da taji kansa a saman ƙirjinta taji zuciyarta ta buga da ƙarfi, yayinda taji wani abu mai kama da fargaba na saukar mata a Zuciyarta, tsoro da zullumin rashin abinda yake faruwa ya wanzu a saman fuskarta, kallo guda zakai mata kasan tayi matuƙar razana.


Ga wani a zabban hucin Numfashinsa wanda yake fita da ƙyar yake sauka sauka a saman ƙirjinta zuwa fuskarta,
Ajiyar zuciya duk su biyun suka sauke lokacin da Abu Maleek ya manna tafin hannunsa a saman tsakiyar lallausan hannunta wanda ya sha ado da wani red ɗin lallai da Oumuu-Ayman ta ɗaura mata a ƴan yatsun.


Kasa magana tayi itama ta shiga fidda numfashi saboda ba ƙaramin nauyi yayi mata a Jikinta ba,
Musamman ƙirjinta da take jin kamar zai rabe gida biyu, saboda yadda ya sanya kansa da kuma tulin gashin kansa ya danne mata ƙirjinta,
Hakan ya haifar da ɗan tsayawar nata numfashi itama ta shiga fidda dashi a hankali.


Shiru tayi tare da sauke ajjiyar zuciya yana ƙara sauraran yadda bugun Zuciyarsu ke bugawa a tare dib! dib!! dib!! Haka zuciyarsu ke buga in one time kuma very fast, yadda numfashin nasu ke fita a tare kuma yake haɗewa waje guda,
Zaka fahimci Tabbas su ɗin abu guda ne, amma rashin sani kowa yaƙi amsar ƙaddarar da tazo masa.


Matse tafin hannunta dake cikin nasa yayi dalilin tsayawar da yaji numfashin sa yayi, kafin ya zagayar da ɗaya Hannun nasa zuwa bayan ququnta ya ƙanƙame shi da ƙarfi kana yaja wani irin wahalallan numfashin daya sanya Julde sakin kuka tare kifa fuskarta a saman tashi ba tare data sani ba.


Abu Maleek kama duk yadda kake tunanin halin da yake ciki ɓata baki ne, dan ma yana trying control ɗin kansa ne, bakinsa ya buɗe zai magana amma ya kasa domin, he can't say what was in his heart ba,
he can't explain how pain he feel in his heart, and it's difficult Mutum ya fahimci halin da yake ciki sai shi kaɗai da mahalicci, the pain is unexplainable.


Shiru kawai yayi bayan ya ƙara manna innocent face ɗinsa a cikin ƙirjinta by mistake kuma laɓɓansa suka sauka a gefen nippy ɗinta da suke cikin rigar baccin.


Da sauri Julde ta matse idanunta saboda jin yadda tsigar jikinta take mimmiƙewa, hakan yasa taji kamar wani abu ke mata yawo a jiki like kiyashi, All her life bata taɓa jin irin abun nan a Jikinta ba, hakan yasa ta ƙara sakin kuka.


A hankali kuma hawayenta ke sauka a saman fuskarsa hakan yasa ya fara fidda wani gigitaccen numfashi, cikin fitar hayyaci ya ware laɓɓansa da sauri cikin wata kalar Muryar wacce take nuna ciwon daya keji yayi worse da yawa yace.


"Ya Jabbaruuu!!"
Ya faɗa yana taune lips ɗinsa tare da ƙanƙame Julde sosai a jikinsa yana jin kamar ya shige Jikinta ya wuta.


Cikin tashin hankali Oumuu-Ayman ta fita daga cikin Sashin na Abu Maleek, kai tsaye kuma ta nufi nata sashin tana zuwa ta shige bedroom, tare da nufar wata ƙaramar box ta sanya hannunta a jikin box ɗin ta kawo wuta, tana sanya yatsarta jikin tampering ɗin box ɗin ta buɗe, cikin sauri ta fara duba Drugs ɗin ciki, cikin Sa'a ta samu Inhaler nasa.


Gaba ɗaya a gigice take hakan yasa ko tsayawa rufe box ɗin ba tai ba, ta fice daga cikin bedroom ɗin, kai tsaye wajan flat ɗin nata tayi, tana jin yadda Hadimarta take mata magana, amma ina hankalin ta na can kan Abu Maleek.


Wanda suran ciwon nasa ya ɗimauta ta, da sassarfa ta nufi Abu Maleek flat, a hanya taci karo da Adams, wanda yake tafe yana latsa Wayarsa da alama yana wani abu mai muhimmanci ne.


Kallon Oumuu-Ayman yayi yaga ba yadda ya saba ganinta ba, duk da cewa baya sakin jikin yin magana da ita sai ta kama Amma ya danne zuciyarsa,
Tare da zame wayar kunansa ya nufi wajan Oumuu cikin tafiyar ƙasaita yana zuwa ya kalli hannun Oumuu-Ayman zaro ido, saboda kaɗuwa da yayi sakamakon ganin Inhaler Abu Maleek a hannunta, sai kuma yayi saurin ɗauke tunanin da yake a ransa yace.


"Oumuu-Ayman lafiya dai ko?"
Kallonsa tayi cikin damuwa kamar zatai kuka tace "Adams jikin ɗan uwanka ya tashi"
"Ikon Allah" Shine kawai abinda Adams ya faɗa kafin yace.
"Tunda ya dawo yayi ne??"
Kai ta girgiza masa Idanunta na kawo hawaye, kowa da rauninsa amma ita Abu Maleek shi ne nata raunin kafin tace.


"A'a wallahi, ko ciwon kai bai ba, kawai yanzu ina parlonsa naga ya Shigo riƙe da ƙirjinsa ya rufe fuskarsa da tafin hannunsa, hakan yasa na fahimci halin da yake ciki, Adams ina jin tsoro ban sani ba ko har a Madrid yana tasar masa ko kuma yanzu ne, ɗan uwanka yana buƙatar ka Adams"


Ta faɗa hawayen idanunta na zuba, sosai Adams yayi mamaki, domin rabon da yaga Oumuu na kuka ya manta, har rasuwar King Tunde Muhammad Jalal babu wanda zai ce yaga zubar hawayenta, amma yanzu dalilin Abu Maleek tana sakin Kuka.


Kai kawai ya jinjina yabi bayan Oumuu da kallo, kamar zai huce sai kuma yabi bayan Oumuu-Ayman ɗin just to see yadda jikin Abu Maleek ɗin yake.


Kasancewar ƙofar shiga babban Parlon abuɗe take yasa Oumuu-Ayman kai tsaye ta shige ciki, tana shiga ta nufi inda suke sai a lokacin ta tuna da Julde, wacce ta zaunar da ita a wajan,
Kallon yadda Julde take kuka wiwi tayi,
duk Jikinta rawa yake, yayinda shi kuma yake riƙe da ita zuwa lokacin, ko ido baya iyawa buɗewa,
sai amon sautin Muryar kukanta kawai da yake jiyowa,
sai kuma wani duhu da yake gani a cikin ƙwayar idanunsa.


Oumuu-Ayman na zuwa ta zauna gefensu,
tare da ɓalle Murfin Inhaler,
har zata sanya ta ɗauke Abu Maleek daga jikin Abu Maleek,
sai kuma ta sauke ajjiyar tare da kallon Julde a hankali tace.


"Dai na kuka Daughter maza sanya masa wanann a baki, bari na ɗura yatsarki a inda zaki dinga dannawa"
Ta faɗa tana ɗurawa Julde Inhaler a tafin hannunta kafin ta ɗura hannunta a saman bakin Abu Maleek tare da saita bakin Inhaler a cikin bakinsa, sai da ta tabbatar komai ya dai-dai-ta sannan tace.


"Stop cry My Daughter, idan kina kuka zuciyarsa zafi take, maza fesa masa Inhaler he will be fine in sha Allah"


Ta ƙare maganar tana shafa kan Abu Maleek tare tsorawa fuskarsa idanu,
Julde da har yanzu bata san meke damunsa ba, haka kuma bata san matsayinta a wajansa ba, yasa tana jan ajjiyar zuciya Jikinta na ɗan rawa ta danna yatsarta a inda Oumuu-Ayman ta ɗura mata,
Wata ƙaƙƙarfar ajjiyar zuciya Abu Maleek ya sauke lokacin da Inhaler ta ratsa cikin bakinsa,
da sauri kuma ya zame hannunsa da ququnta ya ɗura saman hannunta dake bakinta,
kafin ya saita hannunsa a wajan na Julde ya shiga danna Inhaler da sauri da sauri.


Turo baki Julde tayi tana kwaɓe fuska kamar zata ƙara sakin wani kukan tace.
"Oumuu bana iya ba? To mene yasa yake yi da kansa? Ko baya son nawa ne"
Girgiza kai Oumuu-Ayman tayi tana faɗin.
"Is not like that Daughter, yafi yi da sauri saboda ya samu sassauci daga ciwon da yake ciki, kiyi masa addu'a Kinji"


Adams dake tsaye bakin ƙofa ya kasa koda mutsi ne, saboda mamakin da yayi masa yawa, tun shigowar sa idanunsa ya sauka akan ƙyakkyawar Yarinyar,
Wacce kallo yayi mata yasan shekarunta basu huce 17yrs ba, gefe guda kuma tunda Idanun zuciyarsa suka kalli Julde yanayin bugawar zuciyarsa tasa ya sauya, daga wani abu na daban zuwa wani abu wanda yake jinsa kamar so!


A hankali ya ƙarasa shiga Parlon kafin yace.
"Yaya jikin nasa?"
Ya tambaya yana ƙara ware idanunsa akan Julde, wacce kyahun da tayi a cikin idanunsa ɓata baki,
Wacece ita? Mene ya kawota cikin Alaafi? Har Kuma cikin sashin na Abu Maleek sashin da ko shi bai fiya shigarsa ba, saboda matakan tsaron da suke jikin ko wacce ƙofa, something is feshin,
Oumuu-Ayman da tayi shiru tana kallon yadda Abu Maleek yake sauke numfashi a hankali, da alama ya fara jin sassauci daga ciwon da yake ciki,
Idanunta ta ɗaga ta kalli Adams ganin Gaba ɗaya idanunsa ba akanta yake ba yasa ta juya, sai a lokacin data tuna da Julde na wajan, a ranta tace.


"Shikenan batun ɓoyewa ya ƙare"
Mema ya sanya ta fito da ita ne, yanzu bata da wata mafita wacce zata kare kanta da kuma ƙaryar da zata shimfiɗa akan Julde, cikin basarwa tace.


"Allahamdulillah, naga ciwon ya fara sauka, taimakamin na kaisa Bedroom"
A hankali ya zame idanunsa yana mai dashi akan Abu Maleek, wanda gumi ya shiga feso masa jikinsa kuma duk ya saki,
Shikam tunda ya fara shaƙar Inhaler yaji numfashin nasa ya fara sauka a cikin huhunsa, hakan yasa ya ƙara narkewa jikin Julde yana shaƙar Inhaler yana shaƙar ƙamshin dake fita a ƙirjinta, yayinda har kawo lokacin hawayenta bai tsaya ba.


Miƙewa Oumuu-Ayman tayi tare da ƙoƙarin janye kan Abu Maleek dake ƙirjin Julde, da sauri Julde ta kwaɓe fuska hawaye na sakko mata tace.


"Oumuu zai gudu fa, kice kada ya sauka Kinji"
Ta ƙare maganar tana ƙaryar da wuya like yadda Abu Maleek ɗin keyi,
Ganin haka yasa Oumuu-Ayman faɗin.
"A'a Daughter, ɗaki zan kaisa fa, naga bacci zaiyi"
Girgiza kai Julde tayi tace.
"A'a Oumuu ni kibarsa ba kinci bashi da Lafiya ba?"


Adams dake Kallonta yace
"to ba kya jin nauyi ne? Kalleki ba kuma ki kallesa"
Shiru tayi Saboda jin baƙuwar Murya da tayi sai kuma tace
"waye wannan ɗin? Shima ɗan ki ne?"
Oumuu-Ayman dake janye Abu Maleek tana miƙar dashi zaune tace.
"Eh, yayan Ballowo ki ne"
Washe baki tayi haƙuranta da sukai fari yanzu suka bayyana kafin tace.
"To amma dai kana magana ko? Ba Irin Ballowo ne ba kai? Nama san zakai magana ai ina jin hakan a jikina"


Shiru yayi mata sai fuskarta daya tsorawa idanu, kafin a hankali ya sauke idanunsa zuwa cikin idanunsa da yake masa tsananin kama da dana Abu Maleek har blue ɗin ciki iri guda ne, bambancin kawai nata a ɗan juye suke, sosai surutun ya birge Adams.


Abu Maleek kam cikin dauriya ya ɗan aro jarumta ya sanyawa kansa, duk da cewa har kawo lokacin bai ji dai-dai ba, amma ya ɗan samu relief daga azabar ciwon da yake ciki, bisa taimakon Oumuu-Ayman ya miƙe tsaye gaba ɗaya kuma ya narke a jikin nata, ita dai Oumuu-Ayman bata tsaya biyewa Adams ba taja Abu Maleek zuwa can part ɗin da yake amfani dashi a cikin flat nasa.


Bayan shigewar su ne, kuma Adams ya gyara tsaiwarsa cikin son jin sautin zazzaƙar Muryarta yace.
"Ke kuma magana kike so? Cai cai cai haka?"
Ya faɗa yana kalon tsarin surarta, jerarrun teeths ɗinta ta buɗe tace.
"To ai kurma ne kawai yake shiru da bakinsa ko? To kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login