Showing 69001 words to 72000 words out of 161948 words
kuyi kuka da kanku"
Zubewa sukai suna mata kirki tare da al'ƙawarin babu abinda zai faru, gaba tayi ta barsu a nan.
4:14
Agogon Nigeria ya buga, wanda yay dai-dai da fara kiran sallan farko da Subhi, a hankali ya juya daga rufda cikin da yay, tun kafin ya buɗe idanunsa yaji gaba ɗaya kwanciyar ba tayi masa daɗi ba.
Ga yadda wuyansa ya ƙage, ya motsa fuska Yay bakinsa ɗauke da addu'a ya shiga ware gajiyayyun idanunsa wanda suka janye kawo lokacin kuma gaba ɗaya jan da sukai ya ye.
A mamagance ya shiga ware gajiyayyun idanunsa saboda ganinsa da yayi a parlo ya matuƙar bashi mamaki, a hankali ya furta "Astagafirullah!!" Domin sai a lokacin ya tuna da abinda ya faru, bai san mene ya sanya har yanzu ya kasa daina shan Alcohol ba, yasan is totally haram in Islam, amma what should i do? Ya tambayi kansa, ya buɗe idanu da Alcohol wanda tun yana ɗan shekara 5 ya fara shanta musamman idan yana jin zucyarsa babu daɗi, runtse idanunsa Yay sosai yana jin wani irin abu mai ɗaci nayi masa yawo a cikin maƙoshinsa.
A hankali ya fesar da iska daga cikin bakinsa kafin gently ya miƙe tare da zuba hannayensa a cikin aljanu ya nufi part ɗinsa, yana shiga ya hangi sweet akan bed ta naɗe Jikinta da duvet, kansa kawai ya girgiza yana mai kwaɓe fuska.
Yana shiga ya sakarwa kansa shower wanka yay sosai, kafin ya wanke bakinsa da sumar kansa, tun a bathroom ya busar da sumar kansa.
Yana fitowa ya shiga shirya kansa bayan ya shafa lallausan cream ɗinsa ne, ya shafa man gashinsa dana gemu ya fesa body spray.
Wata lallausar Embrodiery islam jallabiya ash color ya sanya mai ƙaramin hannu, prayer mat ya ɗauka ya tayar da sallar raka'atul fijir, zama yayi ya fara addu'a da neman yafiyar Ubangiji, miƙewa yayi tare da sanya Scuff faux-shearling slippers kai tsaye ya nufi Masjid yana fidda wani ƙamshi mai daɗi.
Bai dawo gida ba sai wajan 7:15 yana dawowa ya shirya kansa cikin three-piece dinner suit, wacce take dark Maroon, Wayarsa ya ɗauka da briefcase ɗin sa, sosai yay masifar kyau shi kansa yasan kyansa daban yake dana sauran mutane, a haka kai tsaye ya nufi babban Parlo yana zuwa ya samu Oumuu-Ayman da Julde a zaune wacce take sanye cikin Halter top bayan t.shirt ɗin Jikinta, sai black trouser mai kyau, an sanya mata hula mai butterfly, a cikin seconds yay mata kallon siririn tsaki yaja tare da neman wajan zama a gefen Oumuu yace.
"Mrng Oumuu"
Ya faɗa yana lumshe idanunsa wanda sukai masa ɗan nauyi domin har yanzu bacci bai sake sa ba, wani Murmushin jin daɗi Oumuu-Ayman tayi ganin yadda Abu Maleek ya fara sanya kansa busy wannan lokacin tunanin da zaman kaɗai cin duk babu, cike da kulawa tace.
"Mrng, how was your night Zaki?"
"Allahamdulillah" Shine abinda ya faɗa yana ɗan taune leɓansa tare da ƙara Lumshe idanunsa.
Julde dake zaune tun fitowar sa tasan cewa shi ne, saboda yanayin yadda bugawar zcyarta ya sauya, haɗe Jikinta tayi waje guda ta kasa ci gaba da shan tea ɗin dake hannunta, a hankali ta shiga motsa jajayen laɓɓanta Wanda suka ƙara wani irin jaa kamar ana shafa masu jambaki, bakinta na rawa tana ƙara riƙe rigar jikinta da ƙarfi cikin runtsewar idanun cikin wata raunatacciyar murya tace.
"Goo... Good morning Ballowo"
Ta faɗa lokacin da hawaye yake ciki idanunta, sosai yaji saukar sautin Muryarta a cikin kunansa amma ko motsawa bai ba, bare a sanya ran zai amsa, jin Shiru ne ya sanya Julde sakin Kuka tare da kwaɓe fuska kamar Yarinyar tace.
"Oumuu kinga bazai amsa ba ko? daman nace baki ni baya so na, Nima zan daina son shi Allah"
Ta faɗa tana ƙara sakin kukan shagwaɓa wanda kana ganin kukan kasan cewa Zallar taɓa ra ke damunta, Cikin lallashi Oumuu-Ayman tace "A'a ya amsa ba kiji bane Daughter"
Oumuu-Ayman ta faɗa tana share mata hawaye cikin rashin yadda tace "Allah Oumuu bai amsa ba"
Ta faɗa lokacin da take sakin wani sabon kukan, juyawa Oumuu tayi da nufin cewa Abu Maleek ya amsa amma ko inuwarsa bata gani ba, tuni ta fice daga cikin parlon kamar walƙiya.
Abu Maleek kam tun lokacin da yaji saukar Muryarta ya miƙe cike da nutsuwa da kamala haɗi da kamewarsa cike da kwarjini da haiba yay waje, kai tsaye kuma sashin Mai Babban ɗaki ya nufa.
Masu tsaron ƙofar na ganinsa suka shiga yi masa kirari, ko takan su bai bi, kai tsaye ya shiga Parlo Mai Babban ɗaki a can saman wata haɗaɗɗiyar ladduma ya sameta.
Amintacciyar Hadimar ta wato Hadima Akin ta shirya mata breakfast, zamewa yay tare da zama a gefen ta, kafin ya ɗan narke fuska ba tare da yace mata ya sanya hannunsa a saman plate ɗin dake shaƙe da kayan marmari ya ɗauki Apple wacce aka yayyanka.
Cikin nutsuwa ya sanya yankakkiyar Apple ɗin a bakinsa, zaki da kuma sanyin Apple ɗin ya haddasa lumshewar idanunsa ba tare daya shirya ba, Murmushi Mai Babban ɗaki tayi kafin tace.
"Yau Mijina na gaban goshi ya tuna dani kenan, anya wannan auran zai yiwu kowa Zaki?"
Ta faɗa tana ƙara tura masa plate ɗin fruits ɗin, idanunsa a lumshe cikin nutsuwa kuma yake tauna Apple ɗin sa, kafin ya ware idanuna a kanta cikin kamala da kamewa yace.
"Barka da safiya Granny"
Ya faɗa lokacin da yake kai ɓararan tanjirin bakinsa, Mai Babban ɗaki da farin ciki ya cika mata zuciya tace.
"Sai naji abin farin ciki wajan Oumuu-Ayman, tace ka buɗe Company ko? Toh toh ma sha Allah, Allah ya taimaka ya shige maka gaba"
Idanuna a Lumshe yana shafa cikinsa da yaji yayi ɗan nauyin kafin a hankali ya kama lip's ɗinsa ya shiga taunawa kamar bazai magana ba sai kuma yace.
"Ameen Granny, uhm Ina son ganin Hadima Zubaida"
Shiru tayi tana kallonsa kafin ta ɗan jinjina kai tace "You have to do that kana da ikon yin haka baka da shamaki"
Sauke numfashi yay tare da ƙara gyara zama cikin ƙasa da murya ya buɗe baki zai magana yaji saukar muryarta, da sauri ya haɗe fuska tare da juyawa ya fuskanci Granny ɗinsa, Maleek dake Hannun Bola ya zame da sauri tare da nufar wajan Abu Maleek cikin farin ciki yake faɗin.
"Bàami! Bàami!! Bàami na"
Ya faɗa lokacin da yake faɗawa kan Abu Maleek da sauri Abu Maleek ya runtse idanunsa saboda wani kalar bugawa da zuciyarsa tayi masa.
A sanyaye Bola ta shigo ciki tana ɗan sauke wata Ɓoyayyiyar ajjiyar, ganin Abu Maleek a yanzu ba ƙaramin sanya mata nutsuwa da farin ciki yay ba,daman tazo da niyyar gaishe da Mai Babban ɗaki ne.
Zama tayi kanta a ƙasa tana ɗan satar kallon dugun wuyansa wanda gashi ya kwanta a kai, ba ƙaramin kyau yay mata duk da cewa bata kalli fuskarsa ba, cikin ƙasa da Murya tace.
"Barka da safiya Mai Babban ɗaki"
Jinjina kai Mai Babban ɗaki tayi kafin tace "Ya Maleek ya kwana da jiki?" Cikin damuwa tace "Allahamdulillah, amma zazzaɓin ya takurasa jiya kwana yay yana kiran Bàami da ƙyar yay bacci"
A hankali Abu Maleek yakai dubansa zuwa ga Maleek wanda yake kwance a jikinsa, sai a lokacin ya lura da ramewar da yaron yay ga wani hucin zafi da yake fitarwa, a hankali cike da tsoro kamar mai shirin taɓa wuta ya shafa wuyan Maleek, zafin da yaji ne ya sanya shi lumshe idanunsa lokaci guda kuma tausayin ɗan nasa ya ratsa masa zuciya, a hankali ya shafa kansa ba tare da yace komai ba.
Ba jimawa kuma ya miƙe yana jin lokacin da Bola tace "Mrng Abu Maleek ya jiki?"
Banza yay mata a hankali yaci gaba da tafiya da sauri Maleek ya riƙe hannunsa yana faɗin.
"Bàami zan bika"
Narkakkun idanunsa ya zubawa yaron wanda yake tsananin kama dashi, domin kamannin sa da Maleek har makaki yake basa, ba tare daya hana Maleek ba sanya hannunsa tare da ɗaukan sa cak ya rungome sa, kana ya juya cike da nutsuwa yabar flat ɗin.
Yana fita ya haɗu da Salimerh da Sharefddeen, Murmushi Sharefddeen yay yace "A'a yau kai da Maleek, like father like son"
Salimerh dake tsaye cikin shirin makaranta tace "Zaki Allah komai naka my son ya kwashe ina ga saura kaɗan ya fara buga ball a gidan nan"
Ta faɗa tana kama hannun Maleek da sauri ya kasance hannunsa yana Rungome Mahaifin sa da kyau, saboda gani yake yana sauka zai gudu ya barsa.
A sanyaye Abu Maleek ya sauke numfashi tare ware idanunsa cikin kasala ya kalli Sharefddeen yace "Bro" ya faɗa a hankali Sharefddeen yace "Munji abin Alkairi Allah ya sanya alkairi Congratulations once again Bro"
Salimerh dake yiwu Abu Maleek da Maleek photo a iphone ɗin ta tace "wlh I'm so much happy Zaki, ba kaji daɗin da naji ba, sai nazo siyan Shoes da jersey masu kyau na Companyn J&J ART SHOE AND JERSEY DESIGNER.
Wani sangartaccen Murmushi gefen baki Abu Maleek yayi wanda kai tsaye ba zaka kirasa da Murmushi ba, saboda rashin sabo dayin Murmushi kafin ya ɗanyi gaba yana faɗin.
"Thank you Bro/Sis"
Ya faɗa yana yin Gaba yana jin yadda Maleek yake sauke numfashi mai zafi alamar tuni bacci ya ɗauke sa, kai tsaye mota ya nufa inda ya samu p.a Sameer na jiransa, karɓar kayan hannunsa yay shi kuma ya shiga mota yana ɗauke da Maleek.
Kamar kullum sai bayan sallar Isshā ya dawo gidan saboda aikin da yayi masa yawa, ganin dare yayi ne ya sanya ya nufi sashinsa da Maleek a nan ya barsa ya kwanta shi kuma ya shiga wani bedroom ɗin ya kwanta Shida sweet.
Washe gari
Wajan 11 na safe Oumuu-Ayman ta shigo sashin na Abu Maleek yau gaba ɗaya makara tayi, kai tsaye bedroom ɗin Julde ta nufa tana zuwa taga babu kowa ciki, da mamaki ta shiga Bathroom tasan cewa ballai tana ciki ba,ga tunaninta kowa bata ciki, da sauri ta nufi part ɗin Abu Maleek tana zuwa ta samu Maleek zaune da Sweet suna wasan ball, tashin hankali ya bayyana a fuskar Oumuu-Ayman, ina Julde zata da wanne idon zata fita? Babu inda bata shiga a cikin flat ɗin Abu Maleek ba amma babu ita, cikin kiɗima da kuma tashin hankali ta shiga kiran Number Abu Maleek sai da tayi kira wajan uku kafin ya ɗaga, lokacin yana tsaka da drawing na wata sabuwar jersey a hankali ya sauke numfashi tare dayin baya yana ɗan tsotsar laɓɓansa cikin wata husky voice yace.
"Oumuu!!"
Jin Muryar Abu Maleek yasa Oumuu faɗin "Zaki Banga Julde ba"
Cikin rashin fahimta ya ɗan saki laɓɓansa kafin yace "wace haka?" Wani haushi ne ya kama Oumuu-Ayman cikin ɗan faɗa tace.
"Ohh! Saboda ina rabuwa dakai ko? Matarka ce baka sani ba? To ka sani duk abinda ya sameta wallahi laifin ka ne"
Taɓe baki yay kafin cikin nutsuwa yace "to ban gan ta ba" ya faɗi hakan ya kashe kira a hankali kuma cikin wani irin sabon yanayi juyar da kansa tare da sauke ganinsa akan Jul....
Abu Maleek na kuɗi ne, kiji tsoran Allah ki daina karanta abinda ba naki ba, ko banyi Allah ya isa ba nasan Ubangiji zai isar min domin baya barin haƙƙin wani akan wani ki biya 500 ki karanta cikin nutsuwa 0116886423 sulaiman Naima s union bank 08119237616
*_51-52_*
Julde wacce take kwance saman sofar office ɗinsa tana bacci, sai sauke Ajjiyar zuciya take saboda kukan da tayi.
Domin har ya janyeta daga cikin Bedroom ɗin ta ya kawota office ɗinsa bata san ko wanene ba, hakan yasa ta tsorata, tsoron da yayi mata yawa ne kuma yasa gaba ɗaya ta kasa fahimtar yanayin sauyin bugawar zcyarta.
A hankali ya zame idanunsa daga kanta, tare da maida kallonsa ga zanan da yake, cikin nutsuwa yaci gaba da zana sabbin Desgner na jersey masu kyau da tsari.
Yana nan zaune har lokacin sallar zhur tayi, A hankali ya miƙe yana tattare hannun rigarsa, cikin nutsuwa ya nufi bathroom ɗinsa, alwala ya ɗaura, bayan ya fito kai tsaye ya bar office ɗin ya nufi Masjid ɗin dake cikin babban Company nasa.
A hankali Julde ta shiga motsawa tare daya motsa fuskarta, har lokacin kuma ajjiyar zuciya take saukewa, domin duk a firgice take, kwaɓe fuska tayi tana cinno bakinta gaba kamar ƙaramar kafin a hankali cikin ƙunƙuni tace.
"Uhm, ko waye ya satoni ma ohhhu, Allah sai na faɗawa Ballowo na, dan anga bana gani ko?"
Ta faɗa tana narke fuska, kafin a hankali ta miƙe tana mimmiƙa hannunta gaba domin samawa kanta hanya.
Slowly ta Fara tafiya tana bin bango, tana a haka ne kuma cikin rashin sani goshinta ya daki bango, wata gigitacciyyar ƙara ta saki tare da zubewa a wajan tana yarfe hannu nan da nan kuma wajan ya kumbura jini ya taro cikinsa.
Wata a zaba ce ta shiga ratsa dukkan jijiyoyin jikinta, yayinda Jikinta ya ɗauki rawa da kyarma, gaba ɗaya ta firgice ta shiga rera kuka tana yarfe hannunta.
Abu Maleek dake tsaye shida P.a yana sauraran abinda p.a yake faɗa masa, a hankali ya sauke numfashi tana ɗan Lumshe idanunsa kafin ya ware idanunsa da suke ɗauke da gajiya akan P.c cikin ƙasa da murya yace.
"Wane date aka sanya?"
Rusunawa p.a yay cikin girmamawa yace.
"Sir, till now ba'a sanya date na ƙaddamar da sabbin kayan namu ba, amma mun gama komai kai kawai muke jira, domin a lokacin za'a haɗa da bikin buɗe Company baki ɗaya ne, to the choice is yours"
Hannayensa duk biyun ya zuba a wandon suit ɗin jikinsa, kafin ya ɗan taune leɓansa yana furzar da iska daga cikin bakinsa kana a hankali kamar mai raɗa yace.
"Kayi komai p.a"
Ya faɗa a taƙaice tare da juyawa ya fara tafiya, da idanu p.a ya bisa, sosai yake mamakin Abu Maleek gashi dai company nasa ne, amma yana abu like an masa dole, ɗauke wannan tunanin yayi a ransa kafin yace.
"Sirr!"
Cak Abu Maleek ya tsaya a hankali ya juya ya kalli p.a da wannan narkakkun idanunsa masu ɗauke da wasu ninadari mai karyar da zuciyar mai kallonsa, ware idanunta yay sosai, hakan yasa P.a fahimtar yanayin kafin yace.
"Sir wasu sun buƙaci ganinka, saboda suna buƙatar kayan wannan company, nace zan shirya masu appointment dakai, hakan yasa nake gaya maka Yanzu domin naji wacce rana kake free sai nayi masu magana ta Gmail ɗinsu"
P.a ya faɗa yana yin ƙasa da kansa domin sam bazai jure ganin ƙwayar idanun Abu Maleek ba, Abu Maleek kam ƙuri yaywa P.a da gajiyayyun idanunsa kafin a hankali ya janye idanunsa ba tare da yace komai ba, domin baya jin zai iya magana a wannan lokacin.
Juyawa yay yaci gaba da tafiya yana shirin ɗura hannunsa a saman handle ɗin ƙofar p.a ya ƙara faɗin.
"Sirr"
Da wani sauri ya juya ya kalli P.a cikin yanayin damuwa da kuma zafin zuciya ya buɗe baki da niyyar yin magana, sai ya fasa saboda wani gigitaccen ihu daya jiyo daga cikin office ɗin sa, da sauri ya juya yana mamakin ihun mene haka??? Domin serious yana manta da batun Julde, yana ƙoƙarin juyawa ga P.a ya ƙara jin ihun a karo na biyu, da sauri ya murɗa handle ɗin tare da ɗan tura kansa ciki.
Idanunsa ya shiga rarraba wa, sosai ihunta ya sanya kansa sarawa, a hankali ya ƙara tura kansa ciki can ya hangeta ta durƙoshe sai kuka take tana yarfe hannu, idanunsa ya ƙura mata, ganin yadda take acting like baby girl, gaba ɗaya kuma ƴar duguwar rigar Jikinta ta tattare daga ƙasa fara manyan cinyoyinta sun bayyana sai glowing suke.
P.a dake bayan Abu Maleek wanda shima ya kasa tafiya saboda ihun da yaji, da ɗan sauri cikin yanayi na kulawa yace.
"Sir what happened?"
P.a ya tambaya yana ƙoƙarin tura kansa cikin office domin ganin abinda yake faruwa, ganin hakan ne kuma yasa Abu Maleek haɗe fuska yana ƙara bada faɗi cikin wata dakakkiyar murya ta bada umarni yace.
"P.a leave from here"
Ya faɗa a kaushahe da ɗan hanzari kuma ya shige cikin office ɗin yana rufe ƙofar da ɗan ƙarfi tare da murza key,
Da idanu kawai p.a ya bisa sosai yake mamakin Uban gidan nasa juyawa yay jiki a sanyaye ya nufi office.
A hankali Abu Maleek ya jingina jikinsa da jikin door ɗin shigowa office ɗin nasa,
kafin cikin wani irin yanayi da mutum bazai iya fasaltashi ba, rikitattun idanunsa masu kama dana mai jin bacci ya ƙara mannawa a kanta,
Harga Allah ya manta da ita, mene ya sanya ma ya tawo da ita ne? Shifa bai san wannan yawan kukan nata kamar ƴar yaya ne.
Ƙara ware idanunsa yay sosai a kanta,
ganin yadda take ta yarfe hannu ga yadda goshinta ya kumbura ne ya sanya a hankali ya shiga takawa cikin Zallar nutsuwarsa da kuma tarin haibarsa,
tsaye yayi a kanta tare da lumshe idanunsa saboda yadda yaji Zuciyarsa tana harbawa sauyin bugawar ta ya sauya daga yadda take masa.
Tsananin zafin da yayiwa Julde yawa ne ya sanya ta ƙara sakin kuka domin burgewa da tayi ya haddasa ɗan langwashewar yatsarta wacce ta kejin har wani ƙara tayi,
hakan ya sanya Julde ƙara sautin kukanta, idanunta yayi jajirrr ga wata zufa da take karyo mata.
A hankali ya ƙara jan ƙafafuwansa zuwa inda take durƙoshe,
duk sumar kanta wacce zuwa yanzu ta fara tsayi sosai ta ɗan ya mutse, fuskarta tayi jaa lokacin guda.
A karo na barkatai ya ƙara runtse idanunsa, gaba ɗaya ya kasa ƙarasawa inda take durƙoshe,
bawai kuma shakkar ta yake ba, a'a kawai tsoro da kuma fargaba sune sukaiwa zucyarsa yawa,
bai taɓa tunkarar wata mace da niyyar bata kulawa ko ya rarrasheta ba,
Hasalima baya kallon Julde a matsayin mata kamar yadda su Arɗo suke faɗa masa,
kawo yanzu kawai kallon sister yake mata,
kamar yadda yake ganin Salimerh matsayin ƙanwarsa haka itama Julde kallon da yake mata kenan.
Amma yanayin da yake samun kansa idan yana tare da Salimerh daban da yadda yanayin da yake samun kansa idan yana tare da Julde,
wani kalar abu ya keji wanda a all his life yayi ƙarya yace ya san kalar wannan yanayin.
A duk sanda zuƙatansu sukai kusanci dana juna yana jin wata kalar bugawa da zuciyarsa take masa,
wacce take shirin tafiya da dukkan nutsuwarsa harta kai wani lokacin sai ya dafe saitin zcyarsa zucyarsa da dukkan hannayensa,
time to time kuma ya kanji wani abu mai kama da sanyi na sauka a cikin zuciyarsa.
Ƙarar data kuma saki ne yasa shi dawowa da duniyar tunanin daya shiga,
a ɗan tsorace yana kwaɓe