Showing 48001 words to 51000 words out of 161948 words
wanda ya keji sai Abu Maleek, wani Daimond ring King Tunde Muhammad Jalal ya bawa Abu Maleek kafin yace.
"Duk yarinyar daka sanyawa wannan ring ɗin yayi mata dai-dai to itace farin cikin ka, itace mahaɗin rayuwarka kada ka sake ka wulaƙanta ta"
Tsayawa yay da maganar da ƙarfi kuma yace "La'ilahaillahu Muhammadur Rasulullah S.A.W"
Cak Numfashinsa ya tsaya, haka ma bugun zcyarsa ya tsaya da aiki, yayinda jikinsa gaba ɗaya ya saki a jikin Abu Maleek, Salati Gaba ɗaya suka sanya, Kafin wasu daga ciki suka sanya kuka,
Shikenan lokaci yayi tashin hankali sun gashi, gaba ɗaya Alaafi ta hargitse banda ihu da yarda zani babu abinda mutane suke, Garin Benin ya ɗauki sautin tamburan gidan sarautar wanda yake shaidawa mutane Tabbas Sarki kuma Mai Martaba, King Tunde Muhammad Jalal ya rasu!
Nan da nan aka shiga sanarwar gidan t.v da kuma Redio kafin Yamma tuni Garin Benin ya ɗauki tururuwar jama'a, Sarkin Kano, sarkin Katsina, manyan sarakuna shugaban ƙasa, da gwamnoni suka dira A Benin.
Yayinda kusan a tare jirgin Adams dana Shakiru, Sharefddeen sukai saukar ungulo,
Jalaluldeen kam yanayin daya shiga ba'a magana gaba ɗaya ya gigice bai taɓa ganin mutuwa haka ba, yau gashi mahaifin nasa ne ya rasu a saman cinyoyinsa, banda sakin ajjiyar zuciya babu abinda yake.
Sai washe gari da safe akai jana'izar King Tunde Muhammad Jalal jana'izar data tara mayan mutane ƙososhin ƙasa, da manyan malamai.
Abu Maleek na kwance a saman Royal bed ɗin sa sai Ajjiyar zuciya yake saukewa, tun jiya daya sanya mahaifinsa a gidansa na ƙarshe ya dawo part ɗinsa bai ƙara fitowa ba, ko ruwa bai sanyawa cikinsa, yana tunani abubuwa da yawa Mahaifinsa ya tafi ya bar shi da nauyi masu yawa nauyin da baya jin zai iya saukewa, baya jin zai iya zama Sarkin Benin ba zai iya da wannan tashin hankalin ba sam.
Juyawa yayi gaba ɗaya baya jin daɗi duniyar, sosai yake neman mai rashinsa, da sauri kuma ya buɗe idanunsa saboda da tunawa da Julde yayi.
"You see ba?? Abinda nake gudu kenan yanzu idan ta mutu sai a ɗura laifin a kai na"
Ya ƙare maganar kallon sweet kafin ya miƙe tsaye kai tsaye kuma prvt bedroom ɗin daya sanyata ciki ya nufa, passward ɗin jikin ƙofar ya saka, kafin a hankali ya shiga yana rufe ƙofar, yana shiga ya fara jin ƙarar buge bugen da take a hankali ya buɗe sanyayyun gajiyayyun idanunsa kafin ya sauke a kanta, tana kwance saman lallausan carpet sai bige bige take saboda azabar data keji ga kuma maitar daya tasu mata.
Lumshe idanunsa yayi yace.
"Ya Allah!"
Ya faɗa yana sauke wata wahalalliyar ajjiyar zuciya ganin zata jima kanta ciwo ne ya sanya ya nufi inda take tare da durƙosa wa dai-dai inda take ya sanya tattausan hannunsa ya ɗaga ta cak ya dire saman bed ɗin, kafin ya zauna a gefen ta, cikin rashin Sa'a kuma ɗaurin dake bakinta ya zame,
Da wani irin sauri ta hantsila saman cinyar Abu Maleek kai tsaye kuma bakinta ya sauka a saman ƙirjin ta, da sauri ta buɗe bakinta zata sakar masa cizo wata tsawa Abu Maleek ya sakar mata wacce ta amsa duk sashin nasa, ba ita ba hatta shima sai daya tsorata da tsawar daya fito daga cikin bakinsa, wata zabura Julde tayi sosai tsawarta gigita mata lissafi, hakan ya sanya gaba ɗaya tayi baya zata faɗa ƙasa cikin zafin nama irin na ɗan Ball yasa ƙafa ya tarota tare cilli da ita zuwa baya kai tsaye ta dawo jikinsa, wani gigitaccen ihu Julde ta sanya ihun daya sanya cikin sauri Abu Maleek ya haɗe hannayensa tare da run.....
ABU MALEEK IS NOT FREE CONTACT TO SUBSCRIBE 08119237616
*_37-38_*
Rungome nata hannayen, ya zamana ya sanyata a tsakiyar jikinsa ba tare daya rungome ta ko kuma ya riƙe Jikinta ba.
Sassanyar Ajjiyar zuciya ya sauke, yana wani irin masifafan harbawa da zucyarsa yake masa,
Tsananin bugun da take masa ne yasa har yake ɗan sauke ajjiyar zuciya da sauri da sauri.
A hankali yasa tongue ɗinsa tare datse laɓɓanta ya shiga taunawa, tare da gana masu azaba, a hankali ya fesar da wani zazzafan huci daga cikin bakinsa zuwa saman fuskarta wacce take dab da nasa fuskarsa, kasantuwar kusanci da suka samu da juna.
Narkakkun gajiyayyun idanunsa da suke a lumshe ya ɗan buɗe yana mai ya motsa fuska saboda kansa daya sara masa,
Ga bugawar zuciyarsa data ƙaro fiye da baya, ba tare kuma daya san dalilin hakan ba.
Idanunsa ya sauke a saman fuskarta wacce take ɗauke da ruwan hawaye har lokacin kuma shassheƙar kuka take,
Tsawar da yayi mata ne kuma ya sanya ta firgita, wanda ya haddasa mata tsoransa Sosai.
Sosai take jin azaba a jikin a zaba a Jikinta, amma bata da ikon faɗa ko kuma samun abinda ta keso, ta san tayi kaɗan ya bata abinda take so ɗin a yanzu dole ne taja bakin tai Shiru tare da maida ƙwala marta.
A hankali ya shiga zareta daga jikinsa, jin hakan ne kuma yasa gaba ɗaya ta kwaɓe fuska ta fara buɗe baki zata sakar masa kuka.
Fuska ya ɗan ya motse alamar gajiyawa, tare da ɗura yatsarsa guda a baki yace.
"Shittt!!"
Luff tayi a saman bed ɗin yayinda ta buɗe bakinta ta shiga taunar lallausan bedsheet ɗin dake saman bed ɗin
Abu Maleek a hankali ya ƙara sauke ajjiyar zuciya cikin nutsuwa kuma ya fara taka ƙafafuwan sa a saman lallausan carpet ɗin dake kwance a tsakar bedroom ɗin.
Cikin takunsa na ƙasaita da kuma zallar izza ya nufi waje hannunsa duk biyun zube cikin aljihun wandonsa na long white jeans wanda ya ɗan tattare da can bakin wandon wajan sanya ƙafa.
A hankali kuma ya sanya hannunsa tare da ɗura shi saman handle ɗin ƙofar yaja a hankali yadda sautinsa bazai dame sa ba, shi kansa yanzu duk a razane yake, baya son wata ƙara ko ihu a saman kansa,
Walking slowly ya nufi ɗan ƙaramin part dake cikin side ɗin nasa, a hankali ya sanya kansa ciki, wani ƙawataccen Pharmacy ne wanda babu abinda babu a cikinsa, har wani ɗan ƙaramin gado na marasa lafiya.
Kayan da zai buƙata ya ɗauka kana ya fito daga cikin Pharmacy ɗin ya koma can side ɗin da take ciki.
A hankali ya tura ƙofar yana jin bugawar zuciyarsa na tsananta kamar zata tsaga ƙirjinsa ta fito haka ya kejin zuciyarsa, sam baya jin daɗin duniyar nan a dai-dai irin wannan lokaci, komai yayi masa zafi, da ace za'a amince kuma a lamunsa masa Tabbas da ana yin 40days na rasuwar Mahaifin su zaibi jirgi ya koma inda ya fito.
Tura ƙofar yayi a hankali kana ya zura kansa, tana jin motsin shigowar sa ta ɗan zabura, tare da cure Jikinta waje guda, cikin nutsuwa kuma ta sanya yatsarta a baki ta fara tsotsa tamkar ta samu lolipop.
Jingina bayansa yayi da jikin door ɗin a hankali ya ware Manya kuma gajiyayyun Maraitattun idanunsa,
Wanda suka ɗan janye kaɗan, saboda tension ɗin da yake ciki ga kuma rashin bacci,
Uwa uba wata azababbiyar yunwa dake zaƙulan cikinsa, baya jin kuma zai iya kai wani abun bakinsa.
A hankali ya sauke wani sound tare da janye idanunsa daga kallon saman bedroom ɗin da yake ya rufe su ruff,
Tamkar wanda yake Shirin yin Bacci sosai ya kejin wani irin acikin jikinsa yanayi mai wahalar fassaruwa,
Yanayin da bakinsa yayi kaɗan wajan furta sa.
Ji yake wani nauyi na musamman wanda baya jin zai iya sauke sa ya hau kansa, sosai yake jin kansa Tamkar wanda aka sanya igiya aka ɗaure masa jikinsa,
Ga wani nauyi da kansa yay masa, nauyin kuma daya sauka a ƙasan jikinsa.
A hankali take tsotsar yatsarta wanda sautin tsotsar Derect yake tafiya cikin kunan Abu Maleek, al'amarin daya sanya tsigar jikinsa tashi kenan ta wani mimmiƙe,
A hankali kuma wani sihirtaccen sanyi ya fara kawowa fatar jikinsa farmaki kasantuwar buɗewar kofufin jikinsa.
A sanyaye cikin gajiyawa kuma ya ƙara buɗe luntsumammun idanunsa wanda suka ƙara janyewa, kai tsaye kuma ba tare da wani shamaki ba ya sauke idanunsa a kanta.
Tana kwance luff saman bed ɗin dai tsotsar yatsarta take tana sakin Ajjiyar zuciya, ga yadda Jikinta yake ɗan rawa,
Alamar wahalar da take sha ya tsananta, a ko wanne lokaci tana iya samun kanta cikin wani hali nada ban.
A karo na barkatai ya ƙara sauke ajjiyar zuciya tare da jan numfashi mai wahala, Cikin nutsuwa haɗi da kamewa ya fara taka Fararan sahunsa a saman lallausan carpet ɗin dake malale saman tayals ɗin bedroom ɗin.
A haka yana tafe yana sauke ajjiyar zuciya akai akai ya ƙarasa inda take kwance,
Wata ƙaƙƙarfar ajjiyar zuciya Julde ta sanya tana mai ƙara kulle idanunta, yayinda zuciyarta take wani irin harbawa tare dayin wani tsalle tsalle kamar zata faso tsakiyar ƙirjinta ta fito,
Tsoransa ya bayyana ƙarara a saman fuskarta yayinda kuma a hankali take jin sanyi da kuma tarin nutsuwa na saukar mata a can ƙasan zuciyarta.
Abu Maleek shiru yayi a hankali yake yatsar da take tsotsa da idanu, ganin yadda yayi jaa, ya tattare waje guda, ga wani ɗan janyewa da yayi, Amma a hakan ta dake sai tsotsa take ko mene ta keji a jikinsa ohhhu!!????
Ya tambaya a cikin ransa yana mai ɗan taɓe bakinsa.
Jin shiru kamar babu kowa cikin bedroom ɗin ne ya sanya Julde, kwaɓe fuska idanunta ya cika taff da hawaye, hawayen da suke nuna zallar buƙatar abinda take so ɗin,
Tayi ƙarya ta kwana da yunwa idan tace dai a yanzu abinda zuciya da kuma gangar Jikinta take buƙata zata samu,
Numfashi mai zafi taja saboda zazzafan zazzaɓi dake ƙoƙarin mamaye ilahirin gangar Jikinta, domin har wani ƙara taji ƙashi da ɓargwan Jikinta nayi,
A zabar datai mata yawa ne ya sanya a hankali hawayen dake cikin idanunta silaluwa zuwan gefen fuskarta, kafin a hankali ta shiga motsa bakinta dake rawa yana ɓari kamar laɓɓanta zasu fita, cikin tear out taja wahalallan numfashi tace.
"Ballowo!!!!!!!!!"
Ta faɗi sunan a sanyaye tana mai jan harafin O!!!! Ɗin saboda raunin da zuciyarta yayi, so take tace ya riƙeta a jikinsa ko ta samu sauƙi na azabar da take sha, amma ta kasan saboda tsoran abinda zai faɗa mata, ita gaba ɗaya Matsayin Madibbo ɗinta take jinsa, kawo Yanzu ma bata san cewa ita ɗin mata ce a garesa ba, to mutumin ba bata taɓa ganin ba, ko da ace ta kansa ba zata taɓa sanyawa ranta cewa zai so ta ba, bare harya aureta ya zauna da ita matsayin mata wacce take ƙarƙashin kulawar sa, it's difficult!!!.
Abu Maleek dake zaune kamar statue yana kallon yadda hawaye ke tsiyaya daga cikin idanunsa yaja numfashi ta ɗan ƙarfi tare da haɗiye wani Salivas ɗin cikin bakinsa, daga cikin zuciyarsa wani sound ne ke tashi dib dibb dibbb dibbbb!!!! Saboda kukanta har tsakiyan kansa ya kejinsa, ganin bata niyyar kuka ne yasa a hankali ya furzar da iska daga cikin bakinsa kafin cikin husky voice ɗin nan nashi mai sanyaya zuciyar mace ya ɗura yatsarsa a baki yace.
"Heyyyyyyhh!! Fulani girl be quite!!"
Ya faɗa ba taushashe cikin dakakkiyar muryarsa wacce take nuna cewa Tabbas ya dawo Abu Maleek ɗinsa ba wanda ta sani na cikin jeji ba,
Juyawa yayi gaba ɗaya da raguwar ƙarfin daya rage masa, ya ware wani ƙaramin drip daya ɗauko tare da saƙale sa a jikin wani ƙarfe,
ganin yadda take a kwancan ne yasa hannunsa guda biyun ya riƙe kafaɗun ta ya jata zuwa can sama,
Kana ya zauna a gefe shi kansa yasan cewa tana shan azaba haka kuma akwai abinda take buƙata,
yadai shareta ne saboda haushin auran da aka liƙa masa yake, he's not interested at all!.
Wrist ɗinta ya kama tare da zuba masa,
da sauri ya ɗauki wata siririyar igiya fara,
ya ɗaure wrist ɗin da kyau, nan take jijiyoyin hannunta suka firfito, Wata allura ya ɗauka tare da fara gogawa a inda yake tunanin itace jijiyar ruwa.
Tsinin allura data jini ya sanya ta kwaɓe fuska tana ƙara narke masa, cikin siririyar muryarta mai Amo!!! Da amsa kowa a cikin kunan nan Abu Maleek tace.
"Mene zakai min Ballowo???"
Ta ƙare maganar hawaye na sauka idanunta duk da cewa bata gani
Amma ta Fahimci abinda yake shirin yi mata,
banza yay mata sai ma saurin nutsa allurar da yayi wacce ta lume cikin Jikinta, wani irin raunataccen kuka Julde ta sanya,
tare da sanya bakinta a dai-dai saitin lap ɗinsa ta sakar masa cizo!
Da sauri ya runtse idanunsa tana taune leɓansa tare da faɗin.
"Auchhhiii hyyyyyyyh!!"
Ya faɗa yana tsotsar laɓɓansa,
nan take gumi ya shiga tsastsafo wa daga saman goshinsa,
a hankali ya buɗe idanunsa tare da saukewa a saman fuskarta ƙuri tai masa da idanu a tunaninta wajan data ke kalla daban yake,
nan kowa Kallonta babu inda ya tsaya sai tsakiyar idanun Abu Maleek.
Ɗauke idanunsa yayi tare da taɓe idanunsa a cikin ransa yace..
"Munafuka, ji idanu kamar idanun babyn rubber!!"
Ya ƙare maganar zucin yana juya idanunsa kafin ya gama ɗaura mata drip ɗin,
Wata duguwar siririyar farar robber ya ɗauka, wacce Jikinta yake ɗauke da allura, can ƙasa kuma wani baki ne, a hankali yaja jikinsa kusa da ita tare ɗaga kanta wanda ya fara duhun tsastsafuwar gashi, ya ɗura saman pillow kafin kuma ya tsorawa ɗan mililin bakin nata idanu, ya tsuna fuska yayi domin duk ya gaji banda ceton rai da gudun faɗawar jahannama mene yayi masa zafi da wannan yarinyar, tattausan hannunsa yakai zuwa bakinta Ajjiyar zuciya ta sauke tana mai ɗan ƙara lafewa saman lallausan bedsheet ɗin dake saman bed ɗin, yatsarsa guda biyu ya sanya ɗaya a ƙasa ɗaya a sama ya buɗe bakinta, kana cikin sauri ya tura mata robber cikin bakinta, kakarin Amai ta fara hakan yasa bada tunanin komai ba ya mai da hannunsa ɗaya saman ƙirjinta ya shiga dannawa yana ƙara tura robbern cikin bakinta, yayinda idanunsa suke manne cikin wata na'ura har sai da robber ta shiga cikinta, kana ya tsaya.
A lokacin kam tuni Julde idanunta yana ɗan yooo waje saboda azaba, sai ruwan hawaye dake zuwa daga cikin idanunta.
Abu Maleek allurar ya ɗauka a hankali ya fara saitawa da jijiyar hannunsa kana ya zura can ciki nan take jini ya fara fita daga jikinsa zuwa cikin Julde, domin sosai wannan mutumin ya shanye mata jinin Jikinta, kuma duk wannan fisge fisgen da take yasan cewa abinda take buƙata kenan wanda ko ita kanta bata san menene shi ba.
Wata ƙaƙƙarfar ajjiyar zuciya Julde ta shiga saukewa, yayinda tayi tsitt sai motsi take ta yatsun hannunta, wani daɗi da farin ciki ya lulluɓe mata zuciya, cikin Lokaci kaɗan kuma idanunta ya fara Lumshe wa saboda baccin daya kawowa idanunta ziyara!
Sauke numfashi Abu Maleek yayi yana mai jingina jikinsa da frame ɗin gadon, Shiru yay yana sauraran sautin bugawar zuciyarsa ga kuma jinin jikinsa dake fita da gudu yana shiga Jikinta.
Almost 30minutes
Yana zaune idanunsa a lumshe tunani ne fal ransa a yanzu kuma tunanin ball ɗinsa ce ta faɗu masa, idanunsa ya buɗe a hankali tare da kai dubansa zuwa gare ta, tuni bacci ya ɗauke ta sai Ajjiyar zuciya take saukewa, hannunsa ya sanya ya zare allurar daga jikin hannunsa, yabar iya carnonar, kana ya miƙe tsaye.
Da sauri ya dafe bango saboda wani jiri daya ɗebe sa tamkar zai yarda shi, dai-dai-ta gudun drip ɗin yayi kafin cikin nutsuwa da haibarsa haɗi da zallar izzar sa ya fara tafiya.
Ya fita ya maida ƙofar ya rufe tare da ƙara sanya mata passward, kai tsaye shashinsa ya koma idanunsa ya sauka akan sweet, wani sassanyar murmushi ya sauke yana shafa ƙwantaccen gashin ƙirjinsa, ciki lafiyayyiyar muryarsa mai daɗi.
"Wake up sweet!!"
Ya faɗa yana jan ƙafafuwanta, ƙara curewa waje guda tayi bisa dole ya barta domin ya fahimci itama ta gaji sosai, cije lips ɗinsa kawai yayi kana ya huce bathroom ɗinsa.
Wanka yayi sosai domin har lokacin jikinsa bai masa daɗi, duk wannan baƙin fenti sai daya fita, kafin yaji daɗi Fatar jikinsa har wani jaaa take, brush yayi sosai kana ya ɗauki handrayer ya gyara kansa...
Nan da nan ya fara wani sheƙi da ƙyalli kafin ya ɗauki wani siririn ribbon ya ɗaure gashin dashi, jelar ta ɗan sauka a bayan wasu kuma suka kwanta gaban goshinsa.
Fitowa yay daga cikin bathroom ɗin ya nufi gaban dressing mirror a sanyaye ya fara shirya kansa nan da nan ƙamshi turarensa ta cika cikin bedroom ɗin nasa.
Wasu Olivia von Halle silk robe ya sanya dark masu taushi da laushi, yana gamawa ya sanya wani Vally Slippers na maza masu gashi gashi, jikinsa na fidda wani dadɗan ƙamshi ya nufi parlonsa,
Yana zuwa Oumuu-Ayman na shigowa hannunta riƙe da tray, fuskarta ɗauke da Murmushi ganin Abu Maleek ya sauya ya ɗan kimtsa kansa,
Zama tayi gefensa tana faɗin.
"Zakina!!!"
Kwaɓe fuska yay yana langwaɓar da kansa gefe guda tare da narke mata cikin shagwaɓaɓɓiyar Murya yace.
"Oumuu na!!"
Ya ƙare maganar yana mannewa jikin lallausan kujerar da yake kai, yana ɗan sauke numfashin gajiya da kuma yunwar dake damunsa,
Kallonsa Oumuu-Ayman tayi kafin tace.
"Kayi breakfast?"
Ƙara narkewa yayi a jikin kujerar yana ɗan lumshe idanunsa tare da sauke nauyayyiyar ajjiyar zuciya kafin yace.
"Ba'a bani baaa"
Kallonsa tayi cike da tausayinsa wato bazai taɓa cewa a bashi abinci ba, indai ba mutum ne yayi niyya ya basa da kansa ba,
Sandwich da Bacon Egg and chee Read ta shiga buɗe masa, sai lafiyayyan kunun gyaɗa wanda yaji gyaɗa sai ƙamshi yake, mug ta ɗauka ta zuba masa kunan Gyaɗar tare da miƙa masa tace.
"Shanye wannan yanzu"
Marai-raice mata yayi yana sauke wani fitinan nan numfashi fuska a narke yace.
"Oumuu kiban, jikina babu ƙauri fa"
Ya faɗa yana buɗe idanunsa da suke a Lumshe, girgiza kai kawai Oumuu tayi mai hali baya fasawa, Kunun gyaɗar ta shiga bashi yana sha yayinda yake ɗan jan numfashi tare da Lumshe idanunsa saboda garɗin gyaɗar da yayi masa daɗi a baki sosai, kafin ya shanye gumi ya gama yanko masa.
Bakinsa ya janye yana faɗin "Allahamdulillah! Allahamdulillah biii Ni'imatikaaaa Ya Arhaman rahimin"
Ya ƙare addu'ar yana kallon Oumuu-Ayman wacce take faɗin.
"Da saura ai"
Narkewa yay kamar zai kuka yana shafa cikinsa yace
"Allah Oumuu I'm full kuma sai nai tusbi na kasa buga ball"
"Anzo wajan"
Oumuu ta faɗa a ranta dan bata tunanin zai ƙara buga wata ball ya barta kenan duk da cewa itace mafarkinsa amma dole zai barta.
Tissue ta bashi ya goge bakinsa kafin ta miƙo maza zuma da bakilawa dasu Alkaki, babu abinda yaci sai Inibi ɗaya daya cira ya sanya a bakinsa, sanyin