Showing 9001 words to 12000 words out of 161948 words

Chapter 4 - ABU - MALEEK Book Complete BY SARAUTA.txt

05 Jan 2025

6583

taho da gudu ta haye jikinsa tana sakin ƙara wacce take nuna alamar cewa taji daɗin ganinsa kuma tai kewarsa.
Rungome ta yay sosai yana shagwaɓe mata fuska tare da motsa bakinsa yace.


"O'ohhhh my sweet i miss You"
Ya faɗa yana ɗurata saman wuyansa tare da ɗaukan wata farar Jallabiya ya sanya a jikinsa.
Tana gefensa ya gabatar da sallah, yana idarsa ta haye cinyarsa tana kallon fuskarsa,
Ƙuri yay mata da idanu sai kuma ya langwaɓar da kansa gefe guda cikin nutsuwa haɗi da kamewa da kuma zallar jarumta ya shafi kan magen yace.


"Sweet i need my mother, i need a shoulder to cry sweet, why dukkan mutane mugwaye ne, the you know what sweet?"


Kamar mai fahimtar zan cansa magen ta girgiza kanta tana buɗe baki, shafa kanta yay yace.
"O'ohhhh sweet na hannu da fitinanniyar yarinya,
Mai ido a tsakiyar kai, look! Duk girman jikina bata ji tsoro na ba, nikam I'm scared sweet idan naga mace zuciyata bugawa take"


Ya ƙare maganar yana sauke numfashi tare da janye idanunsa ya lumshe, zame jikinta tayi daga nasa da sauri kuma ta nufi deep frizer ɗin bedroom ɗin,
Da ƙafarta ta jawo wani basket ta shiga zaƙolo fruits irin su Apple, Inibi, strowbeery , hadda tomato's da gauva,
Da ƙafarta ta shiga jan basket ɗin zuwa gabansa,
A karon farko ya sakar mata lallausan murmushi wanda ya haddasa lomawar dimples ɗinsa tare da bayyanar teeths gave ɗinsa wacce take siririya,
A hankali yay kissing kanta tare da ɗaukan Apple guda ɗaya ya sanya bakinsa, tsananin sanyi da kuma zaƙin da yaji ya tilasta masa lumshe idanunsa har ya manta how long ya kasance babu abinci.


Jin ƙarar abu ne kuma yasa ya juya a hankali, ganinta yay tana ƙoƙarin jawo masa win hakan yasa ya taɓe bakinsa tare da taune leɓansa cikin ƙasa da Murya yace.


"It's okay! Sweet, stop hurting yourself”
Apple da Inibi ta sha sosai kafin yaja sweet su kwanta saman bed ɗin sa bayan ya sauka kayan bacci zuwa Panjams, ya rungome ta sosai nan take bacci ya ɗauke sa.


Masarautar Kanzaf
Sosai tsaron da ake baya Alaafi ya tsananta matuƙa,
Tashin hankalin su ya ƙaro amma har kawo lokacin babu wanda yasan cewa King Tunde bashi da Lafiya,
Haka kuma babu wani labari game da ɓatan Queen Roomana,
Adams ya fice a hayyacinsa, ya rasa maka ma da kuma abinyie,
Rashin uwa ba ƙaramin giɓi bane a Rayuwar yara,
Hadima Zubaida kowa taci gaba da rike sirrin da aka bata, duk da cewa tana samun matsala amma Allahamdulillah babu wanda ya takura mata da son jin yadda King Tunde yake,
Zuwa yanzu kuma Sharefddeen ne yake zama a fada mutanan da suke zuwa kawo gaisuwa daga Kanzaf,
Ake faɗa masu King Tunde yana shirin bikin ODUN EGUN kowa ya shirya wannan ranar akwai biki wanda ba'a taɓa yinsa ba a jahar Benin ɗin.
Duk da a gefe guda jikin King Tunde ya rikice babu wanda yake fargabar bari a wannan duniya face mutum biyu, Jalaluldeen sai kuma wani giɓi na rayuwar tasa!




*GUINEA*
Tarihi Fulani makiyaya sun yi kiwo a cikin filayen da ke kewayen yankunan Sahel na Yammacin Afirka, wani bangare saboda yanayin muhalli da ke iyakance yawan filaye don dalilan noma, wanda ke haifar da gaba mai tsanani a fili tsakanin manoma da makiyaya.
bayan yawan fari a yankuna masu bushewar Sahel, Fulani makiyaya a hankali sun koma kudu zuwa Guinea savanna da yan kunan daji na wurare masu zafi, wanda hakan ya haifar da gaba kan hanyoyin kiwo tare da manoma.
Manoma sun koma arewa tare da karuwar yawan mutane.


RUGAR MAHINJO
saukar su kenan wani yanki dake ƙasar Guinea a ƙallah sun ɗauki Shekaru masu tsayi a hanya kafin su iso wannan waje mai tarin Ni'ima,
Domin waje ne mai cije da bishiyoyi da kuma ƙurama,
Gaba ɗaya dai dajin ruwa ne ya kewaye shi, shiyasa yake ɗauke da wani kalan ni'im taccen sanyi da kuma yashi mai ɗauke da ruwa.
Babu jimawa Fulanin wanda suka kasance Fulani makiyaya suka shiga haɗa Bukkoki, da kuma wani gini da ake kira da “Suudu hudo”
Sunyi Bukkokin da ciyayi ne, tun lokacin rani shiyasa duk inda zasu suke tafiya da ita domin samun sauƙin kafawa!


Gaba ɗaya shanun wajan da kuma raƙumi da sauran dabbobi akai masu wani ƙaton waje wanda ya cinye kusan rabin filin sabida yawan dabbobin.


Sanyin safiya ne gaba ɗaya fulanin Rugar Mahinjo sun tafi kiwo, hakan yasa Rugar tai shiru sai sanyi dake Kaɗawa.
Daga can cikin wata bukka wata tsuhu ce kwance tana numfashi da ƙyar ko Idanunta bata iya buɗewa sabida tsananin yunwar data keji.
Idanunta a rufe ta miƙa hannunta tare da shafa kan yarinyar dake kusa da ita wacce ta sunkuyar da kanta ƙasa.
Gaba ɗaya yarinya ba zata wuce Shekara 17 ba, kayan jikinta fare wanda suka kasance na Fulani sunyi baƙiƙƙirin sabida dauɗa.
Tulin sumar kanta kuma an naɗeta da wani baƙin zare, duk da hakan gashin rawa yake ita kanta yay mata yawa.


Cikin kulawa Yakumbo tace.
"Ko damata maa?" (Meke damunki?)
A hankali ta shiga jan numfashi a wannan lokacin bata damu da nata cikin ba, burinta kawai ta samu abinda zata bawa Yakumbo taci,
Domin Yakumbo itace rayuwarta itace wacce take gani taji daɗi a duk faɗin wannan rugar,
Buɗe idanu Yakumbo tayi ita kanta ta san abu nai mai wahala ta wuce yau ba tare da aljalinta ya risketa ba, cikin tausasa murya Yakumbo tace.


"Kayi haƙuri yarona JULDE komai yau tsanani akwai sauƙi cikinsa kaji ko?"
Ta faɗa tana shafa kan wacce ta jira da sunan JULDE ɗin,
shirun da Julde taji ne yasa ta ɗago fuskarta wacce ta ɓaci da hawaye,
Yasubuhanallah! Ubangiji yay halittar kyau a nan, fara ce tass kamar jini zai tsar tuwa a Jikinta, madadin ƙwayar idanunta ya kasance baƙi kamar na kowa sai akai dace ƙwayar Idanunta ya kasance blue amma a juye suke, tana da dugwan hanci, ga lip's ɗinta so pink.
A rikice ta shiga lalubar inda Yakumbo, cikin Muryar kuka Julde tace.


"Har ki mutu ki barni a Wanga duniya Yakumbo, kai ne komai nawa, kada ka barni a cikin wannan azzaluman Yakumbo"
Ganin da gaske Yakumbo bata motsi yasa da sauri ta lalubi inda sandar ta take,
Cikin fahimtar hanya da kuma baiwar da Allah yay mata na cikin ƙwayar Idanunta, duk da kasancewar ta Makauniya amma tana iya fahimtar inda zata nufa.


Fitowa tayi daga cikin Bukkar tana bin hanyar da sandan ta ke mata jagora hannunta riƙe da wata ƙaramar ƙwarya,
Akwai tarin dukiya a Rugar amma ita da Yakumbo ɗinta sam dukiyat batai masu wani amfani ba,
Sai su wuni su kwana da yunwa ko madarar shanu ba za'a basu su gasa cikin su ba.
Ganin yanzu Lokaci fita kiwo ne yasa kai tsaye ta nufi ke wayan shanun, domin tasan dole za'a bar wasu musamman masu ciki.
Idanunta na zubar da ƙwalla, ga yadda kayan jikinta suka yage har suna shirin fito da ƙyakkyawar surar da Allah ya bata, musamman ƙirjinta a zahiri ko ruwa mutum bazai iya sha a inda Julde take ba sabida wani irin warin ƙazanta da take.
Haka take tafiya babu ko takalmi dan ma garin akwai Ni'ima.
A haka ta isa garken shanun kai tsaya inda taji kukan wata Nagge (shanuwa) tana zuwa fuskarta ɗauke da Murmushi sabida jin daɗi da tayi zata samu madarar da zata bawa Yakumbo ɗinta tasha.
Bayan ta tatsi nonon ne kuma ta ɗauki hanyar komawa, tana tsaka da tafiya taji an rafka salati tare da faɗin.


"Shai gyan yaro mai satar madara, woooo! Su Julde anji kunya jama'a ga ɓaro mun kama"
Nan da nan aka tarawa Julde mutane sabida tsananin tsoro da firgici tuni tai cilli da ƙwarya hannunta,
Gaba ɗaya suka ɗauke ta zuwa wajan ARƊO cikin tsana da kuma Allah wadai da hali irin na Julde yace.
"Walle ka bani kunya yaro ashe duk madarar da muke rasawa kai kake sacewa kai da uwarka"
Cikin tashin hankali Julde ta shiga girgiza kanta, sosai take son magana amma bakinta ya gaza furta komai.
Babban tashin hankalin yadda bata jin maganar Modibbo, ga babu idanun gani bare taje wajansa neman taimako, wani daga cikinsu mai suna Labbo yace.
"Ai jiyama shi ne yaje har garke ya tatsi nono ƙwarya biyu"
Zaro ido ARƊO yayi yace.
"Wallai dole ai maka hukunci dai-dai da abinda ka shuka"
Ya faɗa yana kallon wani Mutum yace.
"Maza ɗauko Aska"
Jin an ambaci Aska yasa Julde zubewa a wajan ta shiga rufe sumar kanta, tuni wanda akace ya ɗauko Aska yaje ya ɗauko ya dawo,
Yana zuwa wajan ARƊO yace.
"Maza aske min gashin kansa, cire sumar kai masa ƙwalƙwal"


Kasancewar Fulani mace ita suke bawa kalmar Namiji hakama namiji su bashi kalmar mace,
Ihu Julde ta sanya ta shiga kiran sunan Yakumbo da kuma Madibbo, Lamiɗo tuni ya sanya hannunsa ya cafki sumar kanta tare da cire ɗaurin nan take gashinta ya sauka har wajan waist ɗinta,
ARƊO ya ƙara cewa "maza cire gashin kada abar masa komai kai masa irin na jariri arado"
Cikin rashin imani da tsoran Allah Lamiɗo ya ɗaga Askar tare da....




SALON NA MUSAMMAN NE🥰💃🏻 KADA A BARKA ABAYA.




*ABU_MALEEK NA KUƊI NE, IT'S 500 VIA 0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK EVEDANCE OF PAYMENT 08119237616 GA ƳAN UWA ƳAN NIGER KUMA SUYIWA NANA AI'CHA MAGANA AKAN WANNAN NUMBER 84506476*


KASAN MUTUM NA FARKO WAJAN BIYA DOMIN SAMUN DAMAR SHIGA VIP✍🏽




KUYI SHARE FISABILILLAHI SABIDA ALLAH👏🏻








🌈🌈🌈🌈
*ABU_MALEEK*
🌈🌈🌈🌈


NIMCYLUV




BOOK 1
PAGE 9-10






Cafkar gashin kanta, sabida tsananin zafin daya ratsa jijiyoyin kan Julde ya sanya bata san lokacin data saki wani gigitaccen ihu tare da fasa ƙara da dukkan ƙarfinta,
Wanda hakan ya ƙara haddasa juyewar blue ɗin Idanunta wanda suka gama rinewa da jaaa sabida azabar da tayi mata yawa.
Baya Arɗo yayi cikin matuƙar jin daɗi da kuma farin cikin yau ya kama ɓarauniyar da take shiga cikin garken shanun har take samun damar tatse masa madarar shanunsa,
Zabura yay cikin son dukiyarsa da kuma son bawa dukiyar tasa kariya yace.
"Billahi Yaron nan ya kashe mu, madarar shanu ƙwarya biyu, dole ai masa hukuncin da yafi wannan, dole sai kayi mana kiwon shanu na mako biyu"
Da Zallar mamaki Lamiɗo ya tari numfashin Arɗo yace.
"Tayaya ne wannan ƙaramin yaron zai iya kiwon Nagge wajan guda 100?"
Murmushi Arɗo yayi yana mai jinjina kansa domin shi kaɗai yasan dalilin daya sanya yace haka,
Ba tare daya bada waccen amsar ba cikin bada umarni ya ƙara cewa.
"Cire sumar nan yanzu wannan kuma shi ne hukumcin ɓarawon madarar shanu, barin irin wannan a Rugar Mahinjo babban hatsari ne, domin cigaban faruwar hakan zai iya kawo daƙoshewar tattalin arziƙin Fulani makiyaya, kunfi kowa sanin cewa wannan shanun sune arziƙin dukkan wani ɗan Rugar Mahinjo,
Da kuma madarar shanun muke samun kuɗaɗan kula da wasu dukkan Nagge da suke ƙarƙashin kulawar mu"


Cike da fahimta kowa na wajan yay na'am da maganar Arɗo, domin yay amfani da abu mafi suyiwa a zuciyar fulanin wato shanunsu,
Babu wani abu dake baƙanta ran Fulani makiyaya irin nakastuwar shanunsu.


Lamiɗo ya jinjina kai tare da murmusawa, shi kaɗai shima yasan dalilin daya sanya Arɗo faɗin hakan,
Da ƙarfi kuma ya ƙara jan sumar kan Julde wacce har yanzu ya kasa kama ƙarshen sumar sabida tsayin da gashin yake dashi,
Ganin yadda Julde take ihu tare da ƙoƙarin fisgewa zata gudu yasa Arɗon Rugar Mahinjo faɗin.


"Ɗaure shi, maza kawo igiya a ɗaure wannan mugun irin"
Julde numfashinta ne ya kusa ɗaukewa sabida sabon tashin hankali,
Ita burinta a yanzu ta koma wajan Yakumbonta bata san halin da yunwa ta sanya ta a halin yanzu ba,
Da rarrafe taja Jikinta ta shiga lalubar inda take jiyo muryar Arɗo, duk da cewa bata gani amma tana iya bin sautin Muryar mutum ta isa inda yake.


Tana zuwa wajan Arɗo ta rirriƙesa tare rushewar da wani irin raunataccen kuka mai tarwatsa zuciyar dukkan wani mai imani da kuma tausayi,
Kuka take wanda yake nuni da irin hali ƙunci da kuma takurar da take ciki,
Kuka take da dukkan ƙarfinta zuciyarta, kuka ne wanda yake nunawa duk wani Mutumin dake wajan irin halin yunwa da kuma ƙishin da suke ciki ita da Yakumbo,
Kuka ne wanda yake nuni da halin ƙazantar da suke ciki domin rabonta da wanka a rayuwa harta manta,
Balle ai maganar gyaran jiki duk da cewa da fulanin daji irin su ba'a san so da haka ba.
Cikin muryar da kuka ya gama cin ƙarfinta tace.


"Kayi mini rai Arɗo, ka taimaki rayuka biyun da basu da wani mataimaki sai Allah, dan Allah kada ki cire min sumar kai ma, za'a min dariya kuma zan zama abin kallo da ƙyamata wajan mutanan Mahinjo,
Kaimin dukkan wani hukunci amma ka janye maganar cire min sumar kai, Ni macace ne, kada kuyi abinda zaku mai dani ta namiji,
Ban taɓa sata ba, yanzu halin yunwar da muke ciki ne yasa Ni fitowa neman abinda zan bawa Yakumbo,
Dan Allah Arɗo ki taimaka kada yunwa ta kashe shi, kada yunwa ya kashe Yakumbo, ka bani madarar ko kaɗan ne na bashi yasha"


Zame ƙafafuwansa Arɗo yayi yana ƙara kallon ƙyakkyawar fuskar Julde wacce take masa kama da wata halitta,
Kallon JULDEN kuma na ƙara ta fasa zuciyarsa, yana san yashi tuno da wani shuɗɗaɗan tarihi wanda tuno sa a yanzu dai-dai yake da bugawa zuciyarsa,
Cikin ɓacin rai yasa ƙafa tare da hankaɗe Julde wacce ta kasance bera a Rugar Mahinjo bata da kowa sai Yakumbo da Madibbo,
Da sauri kuma Lamiɗo yazo ya fisgi gashin kanta ya fara janta jikin wata bukka,
Gaba ɗaya mutanan Mahinjo suka mara masa baya domin suma a lokacin cike zuciyoyinsu suke da tsanar Julde wacce take shirin ganin bayan tattalin arziƙin su,.
Wani tsuhu kowa tuni ya koma gefe ya kuka wiwi, sabida a jikin shanuwarsa Julde ta tatsi nono, gashin Naggen tana da ɗauke da tsohun ciki wannan dalili ya ƙara tayarwa da tsohun hankali a tunaninsa shike nan Julde ta kashe masa abinda yake cikin shanuwarsa.


Cikin rashin Imani haɗi da rashin tausayi, Lamiɗo ya fara zubawa Julde ruwa mai sanyin a tsakiyar kanta tare da ɗaukan wani abu mai kama da sabulu ya shiga goga mata akai,
Cikin rashin Sa'a sabulun ya fara shiga cikin nakasassun Idanunta,
Wani kalar ihu da kurnani Julde ta fara wanda sabida tsabar kuka ko muryarta ba'a ji.
Wata duguwar aska Lamiɗo ya ɗauka sabu tass da ita sai sheƙi take, ya kafa askar a gaban ƙwantaccen sumar dake gaban goshinta, tunda ya ɗura askar bai dire ba sai daya zabtare gaba ɗaya rabin sumar kan.





*ABU_MALEEK IS NOT FREE BOOK, IT'S 500 VIA 0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK EVEDANCE OF PAYMENT 08119237616, ƳAN NIGER SUYI MAGANA TA WANNAN NUMBER 84506476*


A can cikin Bukkar su Julde kowa, Yakumbo wani kalar numfashi take,
Gaba ɗaya ta galabaita takai munzalin da idan Numfashin ya fita baya dawowa, a hankali ta buɗe bakinta ta shiga kiran sunan Julde tana faɗin.


"Hai kizo nan, kizo na faɗa maki wata magana kafin Ubangiji ya ɗauki raina, Julde!! Julde!! Julde!!!...." Kafin ta ƙara cewa komai numfashinta ya fara fisga ta shiga miƙewa domin babu komai Cikinta rabon da suci abinci ita da Julde har sun manta sabida zafin talaucin da suke ciki.


Shin su ba ƴan garin bane? Ko kuma dai basu da kiwo ko guda ɗaya ne wanda za suyi taƙama dashi suma a matsayin su na Fulani makiyaya?
Ko kuma dai akwai wani dalili daya sanya su cikin wannan halin?
Tabbas ruwa baya tsami banza..


Salati Yakumbo ta fara kumfa na fita ta cikin bakinta hannunta riƙe da wani abu wanda take sakinsa, a dai-dai lokacin da Lamiɗo ya gama yiwa Julde aski tass ya zamana ko jaririn da aka haifa yau ya fita sumar kai nesa ba kusa ba,
A kuma dai-dai lokacin ne Ubangiji ya amshi ran Yakumbon Julde, wanda ta tafi lahira ne cike da burin faɗawa Julde wata muhimmiyar magana Amma Ubangiji ya fita sanin komai dake cikin wannan duniyar mai cike da ruɗani da kuma tashin hankali,
A kuma wannan lokacin ne Madibbo yake can cikin daji yana haƙa rami da kuma ɓoye wani muhimmin abu, hakan ta sanya bai san abinda yake faruwa cikin Rugar Mahinjo ba.


A can Madrid kowa yau ya kasance weekend, wato ranar daya kasance hutu ga dukkan wasu ma'aikatan gwamnati,
11 dai-dai na safiyar lahadi wato Sunday, A.m ya shiga buɗe nauyayyen idanunsa wanda suke cike da tarin bacci da kuma gajiya,
Tunda ya buɗe idanunsa yaga duhu daga cikin bedroom ɗin sabida kashe hasken ɗakin da yay ya maida idanunsa ya rufe,
A hankali kuma cike da tarin gajiya da kuma ciwon da kansa yake masa a ƴan kwanakin nan,
Ya sanya hannunsa tare da ɗurawa a tsakiyar goshinsa yana murzawa a hankali sabida zufar da yaji tana tsastsafo masa,
A wannan lokacin tunani ne yake ta ziyartar ƙwaƙwalwarsa,
Wanda Yawan tunanin yake ƙara haddasa juyewar tunaninsa a koda yaushe,
Abunka da mara cikakken lafiya, wanda hankali irin na sauran mutana ne bai gama ratsa shi ba.


Tunanin Mami, da kuma kuma matar data zame masa tamkar uwa yake a wannan lokacin yake, yaya suke? Meke faruwa dasu babu abinda ya sani,
Sosai yake son zuwa gare su koda ace bazai zauna tare dasu ba,
Wata lafiyayyiyar ajjiyar zuciya ya sauke yana mai ganganro da hannunsa zuwa tsakiyar ƙirjinsa wanda yake ɗauke da kwantacciyar suma,
Mai kyau da tsari,
Fuskarsa, bugawar zuciyarsa ce ta tsananta da sauri ya sanya hannunsa a saitin ƙirjinsa yan kwaɓe fuska tare da marai-raice wa, kamar ƙaramin yaro,
Cike da tsoro ya ƙara buɗe idanunsa ya shiga rarraba su a cikin tafkeken bedroom ɗin nasa,
A sanyaye ya buɗe ƙyakƙyawan laɓɓansa wanda suke fresh so pink damn cute and softness, cikin can ƙasan maƙoshinsa yace.
"Ya Rabbi! How can that be possible?,
Mene yasa ya kejin tsoro da kuma fargaba ne?"
Ya shiga yiwa kansa tambayar can kuma yasa hannu ya ɗan matse kansa a fili cikin slow voice ɗin nan nasa mai narkar da zuciya cike da tarin shagwaɓa yace.


"You're mad Abu_maleek" zare ido yay sosai tare da pouting kansa da finger yace.
"What? Mad me? No!!! No!!! I'm not ni ba mahaukaci ba and never na zama mahaukaci"
Ya ƙare magana tana tsotsar laɓɓansa,
Ɗan juyawa yay kaɗan yana lumshe idanunsa sabida motsin da yaji a gefensa ana yaye duvet ɗin jikinsa, Sweet ce take yaye masa duvet ɗin, farar mage ƙyakƙyawa gata ƙatuwar gaske rainon madara,
Ganinta yasa ya ɗan yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login