Showing 102001 words to 105000 words out of 161948 words

Chapter 35 - ABU - MALEEK Book Complete BY SARAUTA.txt

05 Jan 2025

6623

dry matar tayi kafin tace.
"Uhm! Tunaninki ya huce duk inda kike tunani, ban fara ba sai dana shirya, ba wannan ya kawo Ni ba, nazo faɗa maki yau zaki bar cikin nan wajan ki koma Alaafin, amma wallahi wallahi wallahi Allah, kika sake kika faɗi ko Wacece ni? Uhm wallahi ba Jalaluldeen ba hatta Adams sai kin rasa shi, zaki ce na faɗa maki, maganar kujera bani kaɗai nake farautar ba, Ni abin guda nafi so shi ne Taswira kuma ina gab da samunta"
Murmushin baƙin ciki Queen Roomana tayi kafin ta miƙe bayan an kunce mata sarƙar jikinta tace.
"Ba Taswira kika kisa samu ba, rayuwarki kika kusa rasawa baki ɗaya, idan tunaninki na baki cewa zaki ga jikin Zakina, har ki samu Taswirar Tabbas Kinyi ƙarya neman taswirar nan dai-dai yake da barinki duniya"


Rugar Mahinjo
Arɗo ne da Barkido tsaye sai kuma Lamiɗo ko wannan su ɗauke da bindiga, kafin a hankali wayar hannunsa ta fara ƙara da sauri ya ɗauka tare faɗin.
"Something news??"
Arɗo ya faɗa fuska ɗaure domin tuntuni zuciyarsa ta jimawa da bushewa,
Daga can ɓangaren Mutumin yace.
"Mun sauya tsarin aikin, ku tsahirta zuwa lokacin da zan ƙara kiranku"
Yana faɗin hakan ya kashe wayar, shine Arɗo kashe wayar yay tare da juyawa ya mayar da bindigar hannunsa.


Abu Maleek ne tafe da sauri hannunsa riƙe da wata jakar fetur da kuma abin kunna wuta,
Yayinda Julde da kuma Mai Babban ɗaki da Salimerh suke bin bayansa da sauri,
Da wani sauri Julde ta ƙara sa inda yake kafin tai ƙoƙarin kamasa tuni ya shige cikin Eso (Fada) yana zuwa ya shiga tuttulawa kujerar sarautar fetur ɗin tare kunna wuta kafin ya cilla wutar tuni Julde tai fatali da hannunsa wutar tai gefe guda,
Wani kallo yay mata kafin ya sanya hannunsa ya riƙe ta yace.
"Ki barni Jidderhh, wannan kujerar bata min adalci ba a rayuwa, My Dad is late, Maaamahh left me, even My Mother bata tare dani kin san Dalili?? Just because of wannan gantalalliyar kujerar, ban so Jidderh zan ƙunata kowa ya wuta, bana da kowa Na.. nahhhh Hawwa'u!"
Da sauri tace masa "kana dani Cucuu, gani a kusa da kai"
Da sauri shima ya riƙe hannunta yace "If you really love me come with me Jidderh kizo mubar wannan ƙasar Bana sonta na tsaneta, i lost everything, kizo gareni"
Kai ta girgiza masa Idanunta na zubar da hawaye yayinda ta rungomesa gaba ɗaya a jikinta cikin fulatanci tace.
"Ko juti ful ɓe ragere, Wala mo buri huddirore, Jomirawo on mo bauɗe koɗume"
Cikin ɗubin mamaki da tarin Al'ajabi Julde taji Abu Maleek yace.
"NONNON, ina son Mi seini maa Jidderh"
Kallonsa tayi tace.
"Idan sa gaske kana son sani farin ciki ka zauna tare dani acikin Alaafin"
Da sauri Hadima Zubaida ta juya idanunta na kawo ruwa jikinta yay wani bala'in sanyi, girgiza kai Abu Maleek yay yace.
"I am all alone in this world I don't have anybody Na.. nahhhh come to me dan Allah, i promise to be Everything to you! I'll take care of you, I'll stand by you a ko'ina na faɗin duniyar nan,ki amince ki yarda ki maye bin gurbin Oumuu na"
Kuka ta sanya tana jin kamar ta aikata abinda ya keso,amma barin su Alaafi kamar wata ƙofa suka bawa magauta ne, wanda ita kuma bata son haka, ta ɗauki ɗamarar toshe ko wacce ƙofa, wasu zafaffun hawayene suka zubuwa Abu Maleek daga cikin idanunsa domin amsar Julde kawai yake jira, tana cewa eh idan ya goyata bayansa sai airport daga nan sai Russia, a hankali ta sulale a gabansa tana sakin wani gigitaccen kuka Jikinta duk rawa yake, durƙosawa yay dai-dai kanta Muryarsa na rawa yace.
"Come with me? Ko ƙarya kike baki so na, ok I'll leave here biyoni yana nufin kina so na aduk halin da nake, zamanki cikin Alaafin yana nufin soyayyar ƙarya ce"
Yana faɗin hakan ya miƙe tsaye tare da juyawa wani kuka ne ya kwacewa Salimerh tace "Granny stop him from living, Innalillahi Granny zai tafi"
Idanun Mai Babban ɗaki ne yay jaa domin tasan Tabbas Abu Maleek a yanzu babu wanda ya isa ya faɗa masa yaji, sama Queen Roomana tana nan ne, Adams kam murmushi kawai yay, Amma Tabbas duk inda yaje ya dawo kujera na nan tana jiransa a hannun matarsa Julde, kuka Julde take tana kiran sunansa "Ballowo!!! Ballowo kada kabarni dan Allah" tsayawa yay a bakin ƙofa kafin yace "don't forget you're my wife, ko ina nan ko bana nan ke Matana ne" yana kaiwa nan yay tafi da sauri yabi ta hanyar baya domin bar Alaafin a dai-dai lokacin ne kuma.....




Team Abu Maleek
Team Julde waye mai Gsky??????










*_71-72_*
Queen Roomana ta ƙarasu cikin Fadar a wahalarce, sai sauke Ajjiyar zuciya take saukewa, ganin mutane a tsaye ga kuma wata a durƙoshe yasa tayi wajan Mai Babban ɗaki tare da faɗin.
"Mai Babban ɗaki" sai kuma ta faɗa Jikinta tana sakin kuka yayinda Jikinta ya ɗauki rawa,
Ganin haka yasa Mai Babban ɗaki bubbuga bayanta alamar rarrashe kafin a hankali tace.
"Stop cry, komai yay farko zai ƙarshe hakan kuma alamun sanyi,sa kuma sauƙi haɗi da haske na gab da mamaye Alaafin in sha Allah, mungode ALLAH daya sanya kika dawo cikin aminci"
Ajjiyar zuciya Queen Roomana ta sauke kafin tace.
"Ban san su waye suka ɗauke ni ba, haka kuma ban san su waye suka dawo dani ba, kuma basu nemi komai a waje ba, na rasa dalilin su na ɗauke ni,sai gashi kuma yanzu sun dawo dani a lokacin da hankalin kowa baya kansa, Ummi Zaki da gaske ya tafi ya barni shima?"
Sai kuma ta sanya kuka, Queen Ayoola kam tun shigowar Queen Roomana hankalinta ya ƙara tashi sai harara take zabga mata, ganin haka yasa Sarkin fada faɗin.
"Dole sai an nemi wanda za'a bawa riƙon ƙwarya kafin dawowar Jalaluldeen"
Jin haka yasa Shakiru da Otun saurin kallan Sarkin fada, suna jiran suji wa za'a sanya kuma?
Gyara tsaiwa Mai Babban ɗaki tayi tana faɗin "wa kake tunanin za'a sanya?"
Da sauri Shakiru yace "babu wanda ya dace da wannan kujerar saini"
Julde dake tsugune ta miƙe tsaye a hankali tana sauke ajjiyar zuciya, tana jin gaba ɗaya duniyar nayi mata zafi bata jin daɗin komai,
Tafiyar Abu Maleek ba ƙaramin girgizata yay ba,
Yayinda ta kejin kamar sa zuciyarta ne ya tafi, hannu tasa ta goge hawayenta tass kafin ta ɗan gyara Murya, cikin wata dakakkiyar murya wacce bata taɓa tunanin tana da ita ba tace.
"Tafiyar mijina ba yana nufin babu shi bane, abinda miji kuma zai ina da tabbacin mata zata iya, dan haka ashirye nake domin amsar kujerar mijina har zuwa lokacin da zai dawo gareni, domin tabbas idan kunga ya dawo to soyayyata ce ta dawo dashi bawai dan kujerar ba,
Ni kuma zan sanya masu so da kuma ƙaunar kujerar a zuciyarsa"
Ta faɗa cikin tattausa Murya tana kallon kowa cike da nutsuwa,
Ƙuri Queen Roomana tai mata da idanu yayinda Hadima Zubaida ba take Kallonta,
Wani so da kuma tarin ƙaunarta suna ratsa cikin zuciyoyinsu, Bola dake tsaye tace.
"Mata??? To ke a suwa? Da har zaki zama matar Abu Maleek, mace ɗaya Abu Maleek da ita wannan kuma matar ba kowa bace face Ni"
Murmushi Julde tayi tana mai ɗan Lumshe idanunta a hankali kuma ta cije lips ɗinta kamar yadda Abu Maleek yake,
Kana cikin gajiyawa da magana ta langwaɓar da kanta gefe tace.
"O'ohhhh! Da alama kece uwar Maleek ko? To bana da damuwa dake, maganar kai na nake, idan kin sani to, idan baki sani ba Nima mata nake wajan Mijin naki"
A gigice Bola tace "wallahi ƙarya kike, keda akace Kece Amintacciyar Hadimar sa? Har kina da bakin cewa ke matar Abu Maleek ce? Middle class like you"
Taɓe baki Julde tayi duk tarin fargabar dake ranta amma sai ta dake tace.
"Hadimarsa ce mana, tunda zanyi masa bauta irinta aure, kuma dai a hakan ya haɗa jiki da Hadimar tasa yabar matar tana gantali"
Tana faɗin hakan ta juya ga Sarkin fada tace.
"Shin zan iya amsar kujerar mijina Jalaluldeen??"
Ta tamabaya hankali kwance, wani baƙin ciki da kuma tsoro ne suka mamaye zuciyar Bola wato munafurtar ta akai da akace Hadimar Abu Maleek ce??
Murmushi Sarkin fada yay kafin yace.
"Sosai zaki iya, an gama mai Alaafi da Kanzaf baki ɗaya, Allah ya ƙarawa Queen Hawwa'u lafiya"
Da idanunta kawai ta kallesa kafin a hankali ta taka zuwa inda kujerar take ta zauna, da sauri Sarkin fada ya zube tare da miƙa mata crown da gashin hannu,
Lumshe idanunta tayi a hankali wasu hawaye Masu zafi suka sakko mata, tana jin kamar tayi shisshigi ta amshi abinda ba nata ba, amma hakan da tayi shine dai-dai, shine kuma matar taba da ƙima na masarautar,
Kowa zai san ko babu Abu Maleek akwai mai iya riƙe matsayinsa, haka kuma duk masu ƙwaɗayin mulkin zasu tsahirta tasan duk abinda za suyi a yanzu sai dai suyi mata, idan ita kuma za suyiwa sunyi a banza babu abinda ya isa ya sameta, sai abinda Ubangiji ya ƙaddara,
Shakiru ne ya miƙe tare da faɗin.
"Wannan sam ba dai-dai bane, tayaya za'a bawa mace damar zama Sarauniyar Kanzaf? Wannan ai sai ya jawo raini da kuma tarin naƙasu acikin Alaafi, gaskiya ba zai taɓa yiwuwa ba, kuma macan ma wacce ba'a san ko Wacece ita ba"
A sanyaye Julde ta ɗaga kanta, tare da kallon Shakiru da sauri ya janye idanunsa saboda wasu abubuwa da yanke hangowa a cikin idanunta masu kaifi, ga kuma wata haiba da kwarjini da tayi masa,
Murmushi Julde tayi kafin ta kalli Sarkin Fada tace.
"Meye hukuncin wanda yay kasalandan a maganar Oba?"
Ƙasa Sarkin Fada yay da kansa kafin yace "Anawa Mutum bulala ashirin ne" jinjina kai Julde tayi kafin tace "Tunda yasan doka kuma ya ƙarya babu laifi aje dashi ai masa bulala hamsin saboda gaba" tana faɗin haka ta miƙe tsaye kana a ƙasa take tafiya kafin tace "a tara kowa akwai zama mai muhimmanci" kana a hankali a nutse kuma ta nufi inda Queen Roomana take tana zuwa ta sakar mata Murmushi kafin ta durƙosa tace "Barka da dawowa Mami" lumshe idanu Queen Roomana tayi kafin a hankali ta kama Julde ta rungome hawaye na zubu mata tace.
"Allahamdulillah,sannu sannu Kinji, Allah yay maki albarka ya baki hqrin zama da mijinki ya kuma dawo da hankalinsa zuwa gareki"


Abu Maleek har ya nufi ƙofar fita, sai kuma ya juya da sauri ya nufi cikin flat ɗinsa, a.t.ms ɗinsa ya ɗauka, da phones with system, kafin ya ɗauki car key ɗinsa,
Da sauri idanunsa a rufe ya nufi wajan motarsa ya shiga ya jata da mugun ƙarfi, yana fita kuma Julde da Queen Roomana suna shigowa flat ɗin.
Bayan sallah Isshā a hankali Julde ta Fito daga cikin bathroom jikinta na zubar da ruwa tana sanye da towel, a hankali taja jikinta zuwa gaban dressing mirror ɗin Abu Maleek, tana mai ƙarewa kayan shafarsa kallo, a sanyaye ta zauna saman stool kafin ta fara shirya kanta cikin wasu falling rose pattern nightdress masu masifafan kyau, kafin ta fesawa jikinta parfume ɗinsa, a hankali kuma ta kwanta saman bed ɗin sa tare da rungome pillow, wani kuka ne ya kwace mata ta shiga rera wa ita ɗaya.
A cikin kunan nata ne kuma bacci yay gaba da ita sai ajjiyar take saukewa.
Washe gari
A nutse ta fito daga cikin part ɗin Abu Maleek, tana sanye cikin wata milk ɗin a voyal mai sky blue ɗin Flowers, anyi masa ɗinkin buba, mai ɗan faɗin wuya, ga wata siririyar necklace mai kyau data sanya a da dugun wuyanta, sai ƙafarta dake cikin flat shoe.
Idanunta a ɗan sanyaye ta ƙarasa shigowa cikin parlon, ajjiyar zuciya ta sauke lokacin data tuna Oumuu-Ayman, da tuni a parlo zata sameta ta shirya masu breakfast,
Murmushi ta ɗan yi ganin Queen Roomana zaune cikin shiga ta alfarma, amma har Yanzu jikinta babu wani ƙwari,
Cike da ladabi ta ƙarasa gabanta tare da zubewa tace.
"Barka da safiya Mami"
Murmushi mai taushi Mami tayi, tare da ƙurawa Julde idanu, kafin a sanyaye ta ɗura hannunta a saman kanta cikin sanyin murya tace.
"My dear ya ƙarin hqr?"
Ƙasa Julde tayi da kanta a hankali kuma tace.
"Allahamdulillah, Mami ya jikin naki?"
Juya idanu Queen Roomana tayi tare da ɗan ɗauke kai, domin ita macace mai tsananin kunya, ba tare data amsa waccan Maganar ba tace.
"Ga breakfast"
Ta faɗa tana miƙewa tsaye, a hankali kuma ta nufi wani part dake cikin flat ɗin Abu Maleek not too long ta dawo hannunta riƙe da wata ƙaramar box,
A hankali ta zauna ta ɗan satar kallon Julde dake ɗan sakalar abinci kafin kuma tace..
"So U still thinking about him? He's very stubborn idan Zaki ne, don mind yourself, zai dawo komai jimawa"
Kunya ce ta kama Julde ba tare da tace komai ba ta ajjiye spoon ɗin tare da ɗaukan coffee tasha,
Ganin ta kama yangar cin abincin ne yasa Queen Roomana ɗan miƙewa domin itama magana bata fiye damunta ba,
Inda Julde take ta ƙarasa tana ɗan ɗauke kai kafin tace.
"Get up, zonan"
Ta faɗa tana buɗe box ɗin, miƙewa tsaye Julde tayi still kanta yana ƙasa, wata haɗaɗɗiyar necklace ta Daimond ta zaro daga cikin box ɗin, tare sanya hannu ta zare ta wuyan Julde, kana ta sanya mata ta Daimond ɗin, a hankali taja Julde zuwa Jikinta ta rungome ta, tare da faɗin "wlcm to the family Hawwa'u, you're no longer my in-law, ke ɗiyata ce kamar Zaki na"
Wasu hawayen daɗi suka sauka a fuskar Julde kafin a hankali ta shiga rera kuka, ganin haka yasa Queen Roomana ƙara rungome ta sosai, kafin tace.
"Kada kisa damuwa, nasan kina son mijinki"
Kai Julde ta ɗaga kafin tace "Mami baya sona" juya idanu Mami tayi tare da yiwa Julde kallon ikon Allah kafin a sanyaye tace.
"Who told you that?" Daga bayansu su kaji ance.
"Mami yana sonta ne? Idan kana son mutum ai zaka zauna dashi, look what he did to her? Ba wani maganar so a nan"
Juyawa Queen Roomana tayi ta kalli Adams tare dayi masa nuni da hannu yazo.
Wajanta ya ƙarasa yana zuwa tasa hannu ta murɗe masa kunne ƙara yasa yace "Auchhhiiii, Mami zaki ciran"
Murɗe kunan tayi sosai tace "stop interrupt Adams"
Kallon Julde yay yace "to Mami ya saketa mana ai akwai masu sonta" haɗe fuska Mami tayi tace "fita a idanu Adams, bana son wannan shirman wallahi ranka zai ɓaci, ya sota or not is doesn't matter for you"
Ta faɗa fuska ba walwala domin Queen Roomana bata ɗaukan shirme irin haka, amma she's Educated gata friendly wa yaranta, ɗauke ido Adams yay kafin yace "Kiyi hqr Mami" banza tai masa kafin tace "get out kowa ma ya kiraka ohhhu" da sauri ya fita domin yaji faɗan har ransa, yana fita ta juya ta kalli Julde tace.
"Babu zaman fada ne hajiya sarauniyar Kanzaf" ta faɗa tana juya tabi can ƙofar baya, Murmushi Julde tayi kafin ta juya zuwa part ɗin Abu Maleek, tana shiga ta kwanta saman bed tare da ɗaukan pillow ta rungome ba hankali kuma ta saki kuka tare da faɗin "Mene yasa Cucuu?? Ko kuma da gaske baka sona ne? Dan Allah ka dawo gareni zuciyata zata buga" ta ƙare maganar tana sakin kuka.
Queen Roomana tana zuwa baƙin ƙofa, da buɗe Hadima Zubaida ta gani tsaye ɗauke da Khaleluddeen, da sauri ta sanya hannu ta amshesa, tare da rungomesa tana sakin wani ajjiyar zuciya, shima yaron ajjiyar zuciya ya sauke a hankali hawaye ya sakko mata, tare da faɗin "I'm sorry, I'm so sorry My Luluuna" ta faɗa tana ƙara rungome Khaleluddeen a jikinta, shi kuwa ƙuri yay mata da idanu yana sauke ajjiyar zuciya, kallon Hadima Zubaida tayi kafin tace.
"Shigo mana Zubaida"
Girgiza kai Hadima Zubaida tayi tare da faɗin "a'a basai na shigo, zuwa anjima na dawo na amshesa"
Murmushi Queen Roomana tayi kafin tace.
"A'a zan kwana tare da shi"
Da mamaki Hadima Zubaida tace "kina ganin babu matsala" still ƙara girgiza kai Queen Roomana tayi kafin tace "Babu in sha Allah, Ngd sosai Allah ya saka da alkairi ya biyaki da abinda kikai min"
Juyawa Hadima Zubaida tayi a ranta tana faɗin "aini ya jima da biyana"


*Russia/Norway*
A hankali ya fito daga cikin wata sabuwar motarsa jeep, yana sanye da wasu haɗaɗɗun Suit mai tsananin kyau, kafin ya maida ƙofar ya rufe, sannu a hankali yake tafiya yayinda gefensa kuma Saif ne wanda suka haɗu dashi ɗazo, domin yazo kallon ball ɗin da za'a buga tsakanin Madrid da Rosenborg club, cikin takunsa na ƙasaita da zallar nutsuwa haɗi da tarin Ilhama, ga wani kamilallan kwarjinin a saman fuskarsa,
Hannunsa sanye cikin aljihun wandonsa yayinda ɗaya hannun yake kaɗa key ka ɗinsa,
A haka suka nufi cikin Oslo Norway park, wani haɗaɗɗan waje mafi ƙawatuwa a wajan suka ƙarasa ruwa na gudana, kujera yaja ya zauna kafin Saif ya zauna,
Kallonsa Saif yay kafin yace "a wannan karan abinda yake zuciyarka bai isa ya ɓoye a saman fuskarka ba Abu Maleek, Meke damunka"
A sanyaye Abu Maleek ya zare Glass ɗin dake idanunsa tare da sauke kallonsa akan Saif, ba tare kuma da yace komai ba, yaja idanunsa ya rufe, dai-dai lokacin da Waiter ta kawo masu meno akan duba abinda suke so, Abu Maleek da idanunsa suke a rufe ya buɗe tare da ɗan ya motsa fuska cikin damuwa yace "Black tea" ya faɗa yana sauke ajjiyar zuciya, Saif cewa yay "Chips with chicken soup" Waiter na jin haka ta juya, kafin a hankali kuma Saif ya gyara zama yace..
"Why are you hurting yourself? Tun kallon farko da nayi maka kaida yarinya nasan akwai Ɓoyayyan abu tsakaninka da ita, nai maganar ina sonta domin naji abinda za kace, sai ka nuna min irin sister naka ɗin nan ce, gani ɗan iska ko? Eh? Saboda ban san ƴan gidan naku ba, look Jalaluldeen a wannan gaɓar ba'a yiwa zuciya taurin kai idan har maganar soyayya ta shigo, dan haka tun kafin lokaci ya ƙure maka go to her wallahi"
Wani kasalallan tsaki Abu Maleek yaja ba tare da yace komai ba, Waiter ce ta ajjiye masa Black tea ɗin kana ta ajjiye Saif nasa, a hankali ya ɗauki cup ɗin tare da matse lemon ciki, kafin ya ɗauka ya manna a bakinsa,
Saif kam kallon Abu Maleek ɗin yake cikin tausayawa, ya rame baya cin abinci, sai fari daya ƙara ƙirjinsa ya ƙara faɗi,
Ƙara gyara zama Saif yay yace.
"So a haka kake tunanin zaka iya wasan? Kullum kana winning ball amma a wannan karan banyi maka hangen nasara ba" abinda Saif ɗin ya faɗa ne yasa Abu Maleek ɗaga kansa kafin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login