Showing 51001 words to 54000 words out of 161948 words
inibin da kuma ɗanɗanonsa suka game bakin Abu Maleek.
Ganin kallon da Oumuu take masa yasa shi tura bakinsa gaba kafin yace.
"What again Oumuu!! Allah ni kibar kallo na ina tsarguwa and kinfi kowa sanin bana son kallo ko?"
Jinjina kai tayi Alamar fahimta kafin taja numfashi tace.
"Who is she??"
Juya idanunsa yayi kafin ya zame gaba ɗaya ya kwanta saman kujerar tare da sanya kansa saman ciyar Oumuu wacce yayi missed nata sosai, domin ita ta sabar masa da hakan tun yana Ƙarami.
Yana rufe idanunsa yace.
"Wa????"
Hannu Oumuu ta sanya taja kunnansa da sauri ya riƙe yana faɗin.
"Auchhhiii Oumuu bafiiii fa"
Murmushi tayi masa kafin tace.
"I knew!, I'm talking about yarinyar da kazo da ita Zaki, who is she???"
Taɓe bakinsa yayi yana tsotsar laɓɓansa kafin ya lumshe idanunsa yace.
"I don't even know her Oumuu believe kinji???"
Kallon Mamaki tayi masa kafin tace.
"Stop laying Zaki Allah last question Wacece ita And mene ya sanya bakinta yake rufe??"
Ƙara gyara kwanciyar sa yayi a cinyar Oumuu, yana jin bacci na ɗaukarsa kafin yace.
"Oumuu ban ƙara fa, Allah ban san wannan Fulanin girl ɗin ba, Ahhhaaa ina Rugar Mahinjo da aka faɗa to a nan take then...."
Ya kwashe labarin komai ya faɗawa Oumuu ya ƙare maganar yana faɗin "Jikina ciwo har yanzu why za'a min bulala akan wannan Yarinyar Allah I'll never ever loving her, kai ni sweet ta fimin ita bana sonta Oumuu to me nayi masu ma??? Bulala talatin fa, Uhmmm ai kam hamsin nayiwa ɗayan I'm telling you na girma ina da ƙarfi ai"
Murmushi Oumuu-Ayman tayi mamaki da ta'ajjuji ya hana tayi magana, yayinda zuciyarta take raya mata wasu abubuwa da yawan gaske, Ajjiyar zuciya ta sauke kafin tace "Allahamdulillah!!"
Sai kuma tace.
"I see ka girma tunda kayi faɗa akan mace, ina tafan kuma farkon nasarar Zakina Jalaluldeen ce"
Turo baki yayi gaba yana kwaɓe fuska kafin yaja numfashi mai ɗan ƙarfi murya can ƙasa yace.
"Allah Oumuu bana sonta sai da ta zama Hadi.....
Abu Maleek isn't free contact to subscribe 08119237616
*_39-40_*
"Hadimata" ya faɗa yana mai ƙara gyara kwanciyar sa, a saman cinyar Oumuu-Ayman, a hankali kuma ya sauke tagwayen ajjiyar zuciya yana zuciyarsa na ɗan yin sanyi Saboda raɓuwa da jikin Oumuu-Ayman da yayi.
Murmushi kawai Oumuu-Ayman tayi tana jin wani irin abu nayi mata yawo a cikin zuciyarta, wani abu wanda bata taɓa jin irinsa ba.
Tsananin farin ciki da jin daɗin da yayi mata yawa ne ya sanya ta ɗura hannunta saman sumar kan Abu Maleek tana faɗin.
"Zaki, tayaya matarka zata zama Hadimar ka? Ko baka mayar da ita Hadimar ka ba, daman ai haƙƙin ta ne ta kula da kai, duk mene kake so zaka samu, for now Daman ya kamata ace kana da iyali wacce zaka kasance da ita, wacce zaka gaya mata damuwarka, wacce idan ka raɓeta zaka samu farin ciki, rayuwarka a yanzu tana buƙatar mace Jalaluldeen, me mata sukai maka ne da har baka son a haɗaka dasu? Koda ace sunyi maka abu mai dace ka ɗauki hukuncin yake mu'amala da su ba, rayuwa tana da sauƙi Zaki Yadda ka ɗauke ta a haka nan zata zo maka, why are publishing yourself? Mace na sanya nutsuwa a zuciyar na miji, mace kuma tana taka rawar akan DAI-DAI-TO-WAR halayyar namiji, Allah I'm telling the truth ya kamata ka nutsu ka san mene kake, accept your wife I'm sure wata rana zakai mamaki"
Idanunsa a lumshe yake yayinda yake sauraran dukkan abinda take faɗa masa, mai kama da tatsuniya, she never understand his fellings, ballai tasan abinda yake ransa kuma yake damunsa ba.
Shi kansa baya jin cewa akwai wata rana daza tazo ya amince da mace, komai na rayuwarsa yana tafiya ne bisa umarnin zuciyarsa, bai taɓa yin abu ance ba dai-dai bane, hakan yasa baya gane dai-dai da kuma ba dai-dai ba,
Rayuwa yake ta kaɗai ce wacce kuma yake jin daɗin ta a yadda yake!
Ajjiyar zuciya ya sauke yana mai ɗan Lumshe idanunsa dan baya jin zai amsa maganar ta Oumuu-Ayman dan bata da wani muhimmanci a garesa, rayuwarsa shi kaɗai mugun daɗi take masa.
Kallon yadda ya rufe idanunsa tayi a hankali kuma numfashin sa ya fara sauka,
wanda yake fita da wani irin zafi,
Gane cewa ballai yayi magana ba domin duk abinda bashi da muhimmanci a garesa baya damun kansa dashi.
A hankali ta shafa lallausar sumar kansa tana jin so da kuma ƙaunar Jalaluldeen na ratsa zuciyarta,
yayinda tausayin rayuwarsa ya mamaye dukkan Zuciyarta,
lumshe idanunta tayi a hankali ta sauke ajjiyar zuciya yayinda wani kalar rauni ya cika mata zuciya, cikin tausasa murya mai ɗauke da su da kuma kewa yace.
"Ya Allah! Ka bawanka ka kula dashi, ka sanya albarka a cikin rayuwarsa, Ya Rabbi ka kare rayuwarsa daga magauta, Allah ka sanya masa tawakkali a cikin zuciyarsa, Ubangiji ka sanya kada rauninsa ya bayyana ga maƙiyansa, Allah ka karesa daga cikin kariyarka, Allah ka bashi lafiya ka cire masa tsoron da mata suka dasawa zuciyarsa, Ya Allah ga bawanka Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal ka kula dashiiiii"
Ta ƙare maganar a raunace yayinda idanunta ya cika da hawaye, bata san mene zai je ya dawo ba, amma Tabbas Zuciyarta ta fara samun nutsuwa da kuma gamsu wa wacce bata san dalilin faruwar hakan ba.
Yadda Numfashinsa ke fita a hankali ne ya ɗan cure waje guda, tare da narke jikinsa a jikin Oumuu-Ayman yasa Oumuu fahimtar kewa da kuma ɗumin jikin uwa da yayi, Tabbas Abu Maleek yana buƙatar kulawa yana son kasancewa da Uwa mahaifiya wacce bai daɗe a wajanta.
Hannunta tasa a hankali ta shiga shafa sumar sa yayinda bakinta ke motsawa tana yin addu'a tare da tofa masa a tsakiyar kansa.
Duk da cewa bacci yake amma sosai yake jin daɗi da kuma sanyi a ransa sanadiyar addu'a da Oumuu take masa, wani irin kuzari da kuma ƙarfi ne suka sauka a saman gangar jikinsa, a haka yaci gaba da baccin daya daɗe bai ba, sai Ajjiyar zuciya yake saukewa akai akai!
Ganin yadda yake jin daɗin baccin ne yasa Oumuu gyara masa kwanciya tare da riƙe tafukan hannayensa, a haka suka kasance tare Abu Maleek sai sharar bacci yake.
Adams ne yake tafiya a hankali kansa a ƙasa, cikin nutsuwa da kamala kai tsaye sashin Mai Babban ɗaki ya nufa, bai shiga ba sai da Mai Babban ɗaki ta bada umarnin ya shiga.
Bakinsa ɗauke da sallama ya shiga yana ɗan cilla idanunsa, a can ya hangota saman Ladduma hannunta riƙe da casbawa tana jaa.
Kallonsa tayi kafin tace.
"Lale! Da zuwa mijin tun shekaran jiya ban sanyaka a idanuna ba, lafiya dai?"
Kwallon e kawai yayi ba tare da yace koma ya nemi waje kusa da Mai Babban ɗaki ya zauna, kafin a hankali ya dumeta da kyau yace.
"Matar irin wannan kyau haka, ko ni akaiwa??"
Ya faɗa yana sanya hannunsa tare da ɗaukan Apple ɗin dake gabanta a saman plate ɗin dake ɗauke da nau'in kayan lambu kala-kala.
A hankali yasa Apple ɗin a bakinsa tare da gutsira kafin yace.
"Nikam Ina Oumuu ne?? 2days ban ganta ba"
Ya faɗa yana ƙara gutsirar Apple ɗin.
Jinjina kai Mai Babban ɗaki tayi kafin tace.
"Kasan shalelenta ya dawo, tana can wajanta hala shine ya tsare ta ta son jikin nan nasa, kamar wannan magen tasa wacce yana nan tare da ita rai da rai kamar wata uwarsa"
Shiru Adams yayi bai ƙara magana ba, sai Apple ɗin da yake sha, ganin hakan yasa Mai Babban ɗaki sanya hannunta ta ajjiye plate ɗin fruits ɗin tana faɗin.
"A'a ya haka kuma?? Wannan sata ne ko kuma fashi?"
Kallonta yayi ya ɗan sakin murmushi kafin yace.
"Da bindiga kika ganni hala? Sata kuma ai ba sata nayi ba, Allah ki ban ko naje na kwashe waccar zumar da kike masifar so"
Zare ido Mai Babban ɗaki tayi kafin tace.
"Yau na kejin sabuwar masifa? A'a wallahi babu ruwan maza fice min, kada na sake ganin shuɗaɗɗiyar ƙafar nan taka"
Miƙewa tsaye Adams yayi kafin ya faki idanunta ya kwashe Apple ɗin gaba ɗaya na plate ɗin.
Yana ɗauka Otun na shigowa ganin haka yasa Mai Babban ɗaki sakin kuka tare da faɗin.
" Yawwa Otun tunda kai Ubansa ne ƙilan yaji maganarka, wallahi ko dai ya biyani ko kuma na kira masa Police, dan Allah wannan ba fashi bane, yanzu kai magana ace rikicin tsufa bane, gaba ɗaya kuɗaɗe ba shine yake kwashe su, to Fisabilillahi wannan ba sata bace? A'a wallahi bazan iya zama da ɓaruwa ba"
Ta ƙare maganar tana sakin kuka tare da ɗaukan wayarta tace.
"Wallahi babu ruwana da cewa kai jikana ne, yanzu zan sa akai ka bayan kanta"
Ta ƙare maganar tana danna wayarta, Otun dake tsaye ya nemi waje ya zauna kafin ya kalli Adams dake tsaye yana ɗan sakin murmushi yace.
"Aremo mai kai mata ne? Matar da ba lafiya ba....."
Da sauri Mai Babban ɗaki ta katse Otun da faɗin.
"Muhammadur Rasulullah S.a.w na shiga Aljanna naƙi fitowa masifar da kake jawo min kenan? To wallahi sai dai kaga Junaidu a gadon Asibiti ba dai ni ba"
Ta ƙare maganar tana sakin kuka, Murmushi kawai Otun yayi domin ya fahimci tun lokacin rasuwar late King Tunde Muhammad Jalal Mai Babban ɗaki ta ƙara riki cewa, ga kuma shekaru dake a kanta kullum,
Gyara zama yayi yana faɗin.
"Kai Adams mene kayi mata ne har haka? Ko kuma kana son kwanan kanta ne?"
Ka faɗa Adams ya ɗaga tare da watsar da hannu alamar "Ohhhhoo!!"
Kafin ya juya cikin izza yabar musu wajan yana sakin Murmushi.
Bayan fitarsa ne kuma Otun ya gyara zama sosai, cikin nutsuwa tare dayin ƙasa da murya yadda Mai Babban y zata fahimci abinda zai faɗa yace.
"Mai Babban ɗaki daman magana nazo muyi ne, naga kuma dake kaɗai ya dace nayi maganar shine ya sanya nace bari nazo wajanki"
Kallonsa Mai Babban ɗaki tayi, kafin ta ɗauke idanunta tana ɗan jan casbahar hannunta, gane cewa ba zatai magana bane yasa Otun ƙara yin ƙasa da murya yace.
"Kin san cewa sarauta bata jira..."
Da sauri ta katse sa da faɗin "Ai haba dai, bani da labari ai"
Ta faɗa tana ɗan yi masa kallon gefe, jinjina kai kawai Otun yayi yana danne abinda yake ransa kafin ya ɗura da faɗin.
"Eh! Haka ne, Sarauta bata jira, koda ba za'a naɗa wani ba, ya dace a bawa wani riƙon ƙwarya domin hakan zai sanya Mutunan Kanzaf suji daɗi a ransu su gane cewa ko babu King Tunde Muhammad Jalal akwai wanda zai iya mulkarsu kuma yayi mulki irin na Murgayi"
Jinjina kai Mai Babban ɗaki tayi tare da ɗaukan glass ɗin ta, ta sanya kamar ba zatai magana ba sai kuma tace.
"Au too! Yanzu na gane yanzu mene kake so ayi sarautar za'a naɗa ko kuma riƙon ƙwaryar??"
Ta faɗa tana ɗaukan sandar ta, tare da Miƙewa tsaye hakan ya sanya Otun sauke numfashi kana cikin jin daɗin fahimtar maganarsa da Mai Babban ɗaki tayi yace.
"A'a ko riƙon ƙwaryar ne sai a fara, kafin a duba wanda ya dace ya hau kan wannan kujerar, daman ko Agba Akin ko kuma ni naga duk mu manya ne zamu iya komai"
A hankali Mai Babban ɗaki ta fara tafiya zuwa cikin bathroom ɗin wanda aka ƙawata da kayan mure rayuwa, sai da taje bakin ƙofar shiga bedroom ɗin ta tsaya tace.
"Babu maganar riƙon ƙwarya, Sarauta za'a naɗa ana yin 40days ba kowa bane kuma King ɗin sai Zakina Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal, idan ka fita ka jamin ƙofar"
Tana faɗin hakan tayi cikin ɗaki tana surutu ƙasa ƙasa,
Wata harbawa zuciyar Otun tayi yana jin wani irin mai kama da damuwa ko kuma baƙin ciki yana mamaye dukkan kofufin zuciyarsa,
Cikin rashin kuzari da kuma juyawar da kansa yake ya miƙe tsaye tare da ficewa daga cikin sashin na Mai Babban ɗaki.
Mai Babban ɗaki kowa na shiga Bedroom ladduma ta sanya tare da tayar da sallar zhur saboda jin masallacin Alaafi na tayar da sallah.
A hankali Abu Maleek yake taka ƙafafuwansa, fitowar sa kenan daga cikin Masjid, idanunsa ya lumshe yana sauraran abinda da Shakiru yake faɗa,
Kasancewar duk tare suka fito daga cikin Masjid ɗin, Yana tsakiya Yayinda Shakiru ke gefensa sai kuma Sharefddeen dake gaba yayinda Adams yake baya.
Shakiru ne ya ƙara duban Adams dake baya yace
"Big bro Company's takalan man nan yana buƙatar sabbin ma'aikata, kuma ƙwararro duba da yadda muka samu sabbin disygner masu kyau da kuma ƙayatarwa"
Jinjina kai Adams yayi kafin yace.
"Kuyi magana da P.a mana Shakiru ka faɗa masa abinda ake buƙata, and why kake tambaya ma? Bayan kai ne Manager na Companyn"
Ya faɗa yana gyarawa zaman agogon hannunsa , Murmushi Shakiru yay kafin yace.
"Haka ne big bro daman na faɗa maka gane kada kazo kaga baƙin fuskoki a companyn, amma zanyi komai dani da P.a"
Ya faɗa yana duban Abu Maleek dake tafe a hankali yana sauraran dukkan abinda suke faɗa, bai san komai na daga kasuwanni ba, shiyasa bai fiya gane dukkan zan can da suke faɗa ba, ƙara Lumshe idanunsa yayi yana taune leɓansa saboda bugawar da zuciyarsa tayi,
Wani Murmushi Shakiru ya yi kafin ya dubi Adams yace.
"Ga Abu Maleek ko za'a fara ta kansa ne, domin ya rage zaman gidan hakan zai sa ya daina zama cikin kaɗai ci da kuma samu kansa cikin damuwa"
Ya faɗa yana kallon Abu Maleek Sharefddeen dake gaba juyawa yayi ya kalli Jalaluldeen ganin yadda ya marai-raice fuska ne kuma tare da taɓe baki yasa kawai ya ɗauke kansa tare da shigewa cikin sashinsa, domin tuni sun Shigo cikin Makaken babban side ɗin Family na Alaafin.
Adams ya ɗaga kansa a hankali kuma ya sauke idanunsa akan bayan Abu Maleek dake tafiya kamar bai so, tafiya kuma mai cike da nutsuwa da kamala, sosai Abu Maleek ya kere su a girman jiki tsayi faɗi, uwa ba tarin haiba da kwarjini ga wani sahihin kyau mai ɗaukan hankali,babu abinda yafi ɗaukan hankali a jikin Abu Maleek sai jajayen laɓɓansa da kuma blue eyes ball ɗinsa, sai kuma ƙwantaccen gashin bayansa Wanda yake ɗaure da ribbon.
Ɗauke idanunsa yay ba tare daya ƙara kallon Abu Maleek ba ya dubi Shakiru da yake ƙare masu kallo yana son ya fahimci wani abu yaji Adams yace.
"Shakiru kayi abinda yake gabanka kawai, duk abinda kukai da P.a let me know!"
Ya faɗa yana ɗan tsayawa ganin hakan yasa Shakiru tsayawa yace.
"In sha Allah big bro komai zai tafi cikin tsari"
Yana faɗin haka ya dubi Abu Maleek daya ɗan tsaya shima yana kallon sararin samaniya a hankali kuma yake tsotsar laɓɓansa da suke ɗauke da danshin ruwa yace.
"Our footballer ko magana babu yau?"
Abu Maleek yi yayi kamar baiji abinda Shakiru ya faɗa, yayi hakan ne e saboda baya son takura ko kaɗan, wajansa Shakiru ya ƙarasa yana faɗin.
"Ina fatan gwarzon mu yana lafiya, ya kuma ƙarin haƙurin mu?"
Gently Abu Maleek ya juyo tare da sauke tsumammun idanunsa akan Shakiru kafin ya ɗan sauke ajjiyar zuciya yana dai-dai-ta tsaiwarsa, bakinsa ya shiga motsawa yana son dai-dai-ta kalaman da zai faɗawa Shakiru can kuma ya numfasa yace.
"Allahamdulillah bro"
Ya faɗa yana Lumshe idanunsa wanda suke nuna gajiyawa da maganar da yayi ga kuma tarin baccin dake idanunsa, domin har yanzu gajiya bata gama sakinsa, uwa ba kewa da rashin Dad ɗinsa dake damun zuciyarsa.
Murmushin Shakiru yay yana yin gaba tare da faɗin.
"Allah ya ƙara mana haƙuri da juriya"
Ya ƙare zan can yana shigewa cikin sashinsa shima, wajan ya rage daga Adams sai Jalaluldeen, cikin nutsuwa Abu Maleek ya ɗaga idanunsa tare da sauke kallonsa akan Yayan nasa, wanda ganinsa yake haifar masa da nutsuwa yake jin kamar Maminsa ya gani,
Shima Adams ɗin kallonsa yayi sosai, kallon da yake nuna zallar tsana da kuma ƙyamata,
Zuciyar Abu Maleek tayi rauni sosai a hankali ya langwaɓar da kansa gefe guda cikin nutsuwa kuma ya nufi wajan Adams yana zuwa ya faɗa jikinsa tare da ruggumesa yana sakin ajjiyar zuciya mai nauyi yayinda farin ciki ya lulluɓe zuciyarsa, muryarsa na rawa yace.
"I miss You so much Lovely bro"
Ya faɗa yana sakin tagwayen ajjiyar zuciya mai ɗan ƙarfi, Rungumesa Adams yayi kafin ya ɗura bakinsa akan kunnan Abu Maleek yace.
"Uhm ya tabbata kai ne ka sace Mami, duba da yadda baka damuwa da rashinta, na tsaneka Jalaluldeen tsana mai yawa, tsanar da ban taɓa yiwa wani ɗan adam ba, wallahi muddin baka dawo min da mahaifiya ta ba, uhm!!!!"
Ya ƙare maganar yana janye jikinsa daga jikin Abu Maleek kai tsaye shima ya nufi sashinsa
Runtse idanunsa Abu Maleek yayi yana jin tsallan da zuciyarsa tayi sosai kalaman Adams suka tsaya masa tashin hankali, tsoro da fargaba suka ratsa masa zuciya, lumshe idanunsa ya ƙarayi yana shaƙar iskar dake Kaɗawa a wajan, kafin yaja ƙafafuwansa ya nufi sashinsa, yana shiga kai tsaye bedroom ɗin sa ya shiga tare da murza key yama mance da batun wata Julde.
Kai tsaye Art room ɗinsa ya shiga ya ɗauki pencil da colours masu yawa, wani madaidaicin ɗaki ne, mai masifar kyau, wanda yake ɗauke da wasu ƙawatattun kujeru masu kyau wanda suka kasance na ƙarfe, sai wasu Flowers masu kyau wanda suke fidda wani dadɗan ƙamshi mai sanya nutsuwa da kasala a jiki.
Sai wata A.c mai bala'in bada sanyi a wajan, ka wani lallausan green ɗin carpet dake shimfiɗe a ƙaramin parlon dake cikin bedroom art ɗin, ga deep freezer dake gefe guda, sai ƙaramar plasma, ga wata ƙatuwar kwalba wanda aka cikata da kifaye masu kyau wanda kai tsaye ruwa yake saukar masu daga lambu.
Wani table ya jawo ya zuba pencil da colours ɗin a ciki, kafin a hankali ya nufi wata loker ya zaro wata farar carbon paper a ciki, yana ɗaukowa ya mannata a jikin wani ƙarfe da yake zanan jiki, kafin ya nufi deep freezer ɗin ya ɗauki fresh milk da lemon power horse energy masu sanyi ya ajjiye saman table ɗin, wata ƙaramar kujera ya ɗauko tare da zama kai ya ɗauki pencil ɗin bayan ya ɓalle murfin fresh milk ɗin ne ya ɗan kafa a bakinsa, saboda sanyin daya jine yasa ya lumshe idanunsa a hankali kuma ya manne hannunsa a saman paper ya fara zanan idanunsa a lumshe.
Wajan 20 minutes ya ɗauka yana zaman still kuma idanunsa suna rufe, sanssanyar ajjiyar zuciya ya sauke bayan ya furzar da iska daga cikin bakinsa, slowly ya buɗe idanunsa tare da saukewa akan art ɗin da yayi,
Da sauri yaja idanunsa ya Lumshe saboda zanan da yayi arba dashi, cije lips ɗinsa yay zuciyarsa cike da mamaki why kullum idan yayi zanan idanunta a rufe? Mene ya