Showing 99001 words to 102000 words out of 161948 words

Chapter 34 - ABU - MALEEK Book Complete BY SARAUTA.txt

05 Jan 2025

6605

kuma ya tabbatar da Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal Abu Maleek ya gama zama sarki, Hamdala da Mai Babban ɗaki da Julde suka saki hadda Salimerh.


Gama naɗin kuma yay dai-dai da shigowar wata Hadima jikinta na bala'in rawa ta zubewa a wajan, ganin hakan yasa Otun yace.
"Ke Lafiya??"
Domin shi duk baƙin ciki ya gama isar ya tura da mutane su shiga su ƙone flat y Abu Maleek, amma gashi he's still alive.


Jikin Hadimar na rawa tace.
"Oumuu!!! Oumuu-Ayman"
Da wani mugun sauri Abu Maleek ya miƙe tsaye jikinsa na rawa yace.
"What happened to her?? What happened to my mother??eh??"
Hadimar idanunta na zubar da hawaye tace.
"Ta..taci guba"
Bai tsaya jin mene za tace ba ya kwasa da gudu ya nufi Sashin Oumuu, hakan yasa Julde ta marasa baya kana Salimerh da Mai Babban ɗaki.


Shiru Otun yay, tabbas bayan shi akwai wani daya fisa son wannan sarauta, da alama kuma ya fisa iya shiri amma waye wannan? Duk yadda akai ya shirya kashe Abu Maleek sai kuma abun ya ƙare akan Oumuu-Ayman.


Abu Maleek na shiga ya hangi Oumuu-Ayman kwance bakinta na zubar da kumfa ga plate ɗin abinci a kusa da ita, da wani sauri ya ƙarasa gareta tare da jawota jikinsa yace.
"No!!! Open your eyes Oumuu, don't do this to me, Kada ki barni a lokacin da nafi buƙatar ki, Open your eyes Oumuu"
Ya faɗa yana Rungome Oumuu-Ayman, wani irin firgita Oumuu tayi, tana ƙara riƙe hannu Abu Maleek, numafshinta na wani irin sama yana barin ƙirjinta alama rai gab yake da barin gangar Jikinta, cikin wani jan numfashi tace "S...J...K" sai kuma ta ƙasa faɗin abinda ya keson faɗa a hankali kuma tai wata miƙa tare da faɗin "La'ilahaillahu Muhammadur Rasulullah s.a.w" kafin kuma taj wani numfashi dai-dai lokacin da......




🥲😭








*_69-70_*


Take ƙara riƙe hannun Abu Maleek da ƙarfi, saboda wani irin fitinannan abu ɗaya ratsa daga tsakiyar ƙirjinta zuwa ƙahon zuciyarta,
Yayinda ƙirjinta yake wani masifaffan ɗagawa, tana shiga fidda number da wani mugun sauri,
A hankali wata kuma kumfa ta shiga ratsu cikin bakinta tana fitowa kamar dafara,
Irin Mutum yazo gab da mutuwa ɗin nan.
A gigice Abu Maleek ya ƙara rungome ta a jikinsa yayinda dukkan jikinsa yake wani irin rawa
Tare da ɓari
Julde kam cak ta tsaya ta zama kamar statue sai bin Oumuu-Ayman take da kallo a hankali kuma ta ɗaga Idanunta, ta sauke akan Queen Ayoola, kana ta mayar da Idanunta kan Bola a sanyaye kuma ta kalli Adams,
Suna haɗa idanu ya janye idanunsa a gigice ta kalli Salimerh sai kawai ta nufi wajan ta tare da faɗawa jikinta ta saki wani raunataccen kuka,
Rungome ta Salimerh tayi itama ta saki nata kuka, domin ita ko Oumuu-Ayman ta kasa kallo saboda tsananin tausayin ta,
Musamman da akace goba aka sanya mata, Allah kaɗai yasan kallan gobar da aka mata, domin da garin meriz ne da a hankali zaici jikinta kamar yadda yaywa
King Tunde Muhammad Jalal.


Ajjiyar zuciya Abu Maleek ya sauke numfashi cikin wani irin kiɗima da fitar nutsuwa yace.
"Please Oumuu na, dan Allah kada ki barni, kiga abinda nake gudu ko?
Kinga abinda yasa na gujewa zaman Benin ko?
No one's love me, ke ɗaya nake da ita a yanzu, dan Allah Oumuu.....nahhhh!!! Open your eyes Zakin ke magana, Your professional footballer Oumuu, wallahi billahi i promise to you zanyi komai da kikeso,
Amma stay with me Oumuu dan Allah kada ki barni a wannan duniyar da kuma wannan gidan mai cike da rikici, tell them bana son sarautar nan,
Dan Allah Oumuu ki tashi i love You so much I'm nothing without you Maaamahh"
Ya faɗa lokacin da idanunsa sukai wani mugun jaa suka sauya kala, jijiyoyin kansa sukai bala'in tashi tsaye, yayinda ya kejin shima tamkar numafashi ne yake tafiya, a yanzu ya tabbatar tsananin son da ya kewa Oumuu-Ayman yafi ƙarfin tunaninsa,
Yana mata son da ko Maminsa baya yiwa wannan son,
Sone tsaftatacce mara algus,
Tun yana Ƙarami Oumuu-Ayman ce take masa komai, a wajanta yake kwana yake tashi, a jikinta yake kwanciya, shoulder ɗinta itace gurbin zubar Hawayen sa,
Gashi yanzu wata sabuwar ƙaddarar na son rabasu, wani sabon shafi na sabuwar ƙaddarar rayuwarsa zai buɗe.
A hankali ya kifa kansa a tsakanin shoulder ɗinta, a wannan lokacin ko hawaye ya kasa domin rabon da hawaye ya zuba daga cikin idanunsa ya manta, sai ajjiyar zuciya da yake saukewa kawai,
Wata ƙyakƙyawan miƙa Oumuu tayi kafin a hankali ta samu zarafi buɗe bakinta dai-dai kunansa, a gigice ya buɗe idanunsa jin abinda tace, a hankali kuma ta ƙara ƙasa da muryarta tace.
"Jalaluldeen, Zaki na, Cucuu na! Ka nutsu kasan abinda kake, rayuwa bata Tabbas nasha faɗa mak....,"
Saurin yin shiru tayi Saboda wani irin fisga da numafshinta yay, kafin wata kumfa ta fito daga cikin bakinta,
Ƙara riƙeta yay a jikinsa sosai kafin jin yadda Jikinta ya saki baki ɗaya,
Cikin dauriya tace.
"Cucuu na, Amanar Hawwa'u a hannunka, ka zama mai Hqr ko zaka share kowa Banda haƙƙin matar daya rataya a wuyanka Cucuu, I'm going to my home now, zan tafi inda mahaifinka ya tafi kafin Lokacin ku yayi,
Bana baƙin cikin mutuwa ta, sai farin ciki domin zan mutu ne dalilin kare taka rayuwar, Nagode Allah da nayi hanzarin kawo maka naka Abincin, kafin na dawo an sauya min Abincin ta hanyar da bazan gane ba, komai na Amincin iri ɗaya ne babu bambanci, shiyasa ban fahimta ba,
Anyi tunanin naka Abincin ne wannan dalilin aka sanya goba ciki, i love so much Cucuu na,
Nai farin ciki domin Ubangijin bai ɗauki raina ba sai da ka tabbata a matsayin OBA! Allah ya tayaka riƙo.."
Runtse idanunta tayi saboda a yanzu number ta gaba ɗaya iya wuya ne, idan kuma ya tafi baya dawowa,
Idanunta ta buɗe tare da ɗaga hannunta, da sauri Julde ta ƙarasu kusa da ita tace.
"Ba haka mukai dake ba, Oumuu-Ayman ba cemin kikai zaki tafi ki barmu baki ɗaya, kada ki karya wannan Al'ƙawarin Oumuu, kefa jaruma ce, to dan Allah ki tausayawa maraicin mu ki zauna tare damu,
Oumuu mene yasa zaki tafi ki barni da nauyi mai girma akai na?? Mene ya sanya? Eh"
Ta ƙare maganar cikin ɗacin rai tare da sanya hannunta ta shiga dukan Oumuu da alama tuni ta fice daga hayyacinta ganin haka yasa Oumuu-Ayman sakin wani amintaccen Murmushi, wani zallar annuri na fita daga fuskarta, a hankali ta kalli Abu Maleek,
A wannan lokacin ba zata iya magana ba, sai hannunsa data mana akan na Julde tare da haɗe kawo nan su waje guda,
Wani haske take hangowa a goshin ko wanansu,
Yalwataccen Murmushi ta sauke kafin a hankali tace.
"Allahamdulillah"
A hankali kuma idanunta suka fara yin sama, bai san ya mutuwa take ɗauke Mutum ba, amma daga kan mahaifinsa ya fahimci mutuwa yadda take, bai ji zafi da kuma raɗaɗi a lokacin da Tunde ya rasu ba,
Saboda a wannan lokacin akwai Oumuu-Ayman, ganin Oumuu-Ayman kusa dashi kuma ya kure dukkan wata damuwar dake ransa,
A wannan lokacin kuma zafi da kuma raɗaɗi sun samu wani irin halattaccen gurbi a zuciyarsa,
Yayinda Oumuu-Ayman kuma ta tafi cikin farin ciki da salama da wani annuri saboda ta tafi tabar Jalaluldeen a hannun Julde hannun da bazai taɓa cutar da wani Mutum ba,
Bare kuma Abu Maleek,
Ita daman rayuwar haka take baki ɗaya, dukkan zuciyar da take cike da imani da kuma tausayi da rikon amana, haɗi da riƙo da addini, ranta bazai taɓa muzanta wajan ɗauke sa ba, samaniya da mutanan cikinta a kullum mara ba, suke da irin ran Oumuu-Ayman!
(Nima Na'ima sulaiman Sarauta) Ubangiji ka amshi raina cikin kwanciyar hankali, da nutsuwa da kuma salama da kuma Dukkan musulmi.


"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" shine abinda mutanan wajan kawai suke faɗa, babu wanda baiji mutuwar Oumuu-Ayman ba, sai wanda yake da sanya hannu a rasuwar nata, mutuwar data girgiza dukkan al'umar dake cikin Alaafin, Barori, Hadimai, Fadawa, Hadima Zubaida kam ko motsi ta kasa, abubuwan masu yawan gaske sunyi mata ca!!! Akanta, hatta Sarkin Kilisa yaji mutuwar Oumuu-Ayman har hawaye ya zubar, kasantuwar duk wanda ya rasu a nan cikin Alaafin ake binnesa yasa nan da nan Alaafi ta cika.
Abu Maleek, da Julde tun lokacin da Oumuu-Ayman ranta ya gama barin gangar Jikinta suma jinsu da ganinsu yabar gangar jikinsu,
A gigice Bola tayi kan Abu Maleek ita da Salimerh yayinda kuma Adams ya nufi kan Julde, hannunsa ya sanya da niyyar ɗauke ta, amma bisa mamakinsa hannunta sarƙe yake cikin na Abu Maleek, yin duniya ya kasa bisa dole gaba ɗayansu aka nufi sashin Abu Maleek dasu, ana kaisu kuma,
Salimerh ta kira Dr dukkan su Drip aka sanya masu tare da wata injection na tsayin 48hours,
Suna kwance kusa da juna kamar gawarwaki.
Daga nan kuma guards ɗin Abu Maleek suka sanya tsaro mai ƙarfin gaske a sashin Abu Maleek babu mai shiga da fita sai Dr da kuma Mai Babban ɗaki.


After 2days
Misalin 4:20 na yammacin juma'a, rana mafi farin ciki ga dukkan Musulmi yayinda ranar ta zama ranar tarihi ga Hawwa'u Julde!
A hankali ta shiga buɗe idanunta wanda sukai mata nauyin gaske, cikin nutsuwa kuma ta gama buɗe idanunta,
Kafin ta ɗaga hannunta da sauri ta juya saboda jin hannunta a cikin na mutum,
Da sauri ta sauke ajjiyar zuciya, tare ƙara juyawa sosai, sai a lokacin ta ɗan fahimci drip ne a hannunta, idanunta ta sauke akan hannunsa dake cikin nata,
Wasu kyawawan gashi ne masu kyau a kwance saman fatar hannunsa sai ƙyalli suke,
Ƙuri taiwa hannun kafin a hankali ta kalli nata, dashi da ita ta rasa gane wanda yafi wani haske, ita hasken ta har wani yellow yake,
Yayinda nasa kuma har wani jaa yake, kurayan jijiyoyin hannunsa ana ganinsu sosai kamar ka taɓa jini ya zuba,
Sai wani zufa dake tsastsafo wa a tsakiyar tafin hannunsa,tana ratsa cikin hannunta,
A hankali ta fara sama da idanunta domin sam ta kasa tuna lokacin da suka kasance a ɗaki guda, kan gado ɗaya, hannunsu sarƙe dana juna.
Ƙyakkyawar fuskarsa mai cike da ilhama ta tsurawa idanu, ya wani mugun faɗawa sai wani masifaffan kyau daya ƙara, a hankali ta miƙa hannunta cikin nutsuwa kuma ta kifa hannunta a saman fuskarsa,
Ajjiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke saboda sanyin tafin hannunta daya ratsa masa fatar fuskarsa,
Yarr-yarr kuma haka tsigar jikinsa suka zubewa tare mimmiƙe, kallonsa tayi cike da so da kuma ƙauna, kafin a hankali ta sanya yatsarta a saman sajansa ta shiga shafawa, tana ɗan murzawa, tun ba yanzue ba sajan nata yake bala'in birge ta,
Ƙaramin yatsarta ta ɗan manna saman jajayen laɓɓansa masu kauri sai sheƙi suke, idanunta ta lumshe tana jin wani irin kasalallan yanayi mai wahalar fassaruwa a cikin zuciyarta yana ratsa dukkan gaɓoɓin jikinta,
A hankali ta ɗan shafa laɓɓansa dai-dai lokacin daya ƙara sakin ajjiyar kafin kuma ya buɗe bakinsa a hankali cikin magagin bacci yace.
"Come back! Come to me Maaamahh!!, Kada ki barni Oumuu na"
Dummm! Haka zuciyarta ta buga da ƙarfin gaske, kafin jikinta ya shiga rawa bakin na ɓari tace.
"Oumuu"
Sai kuma ta toshe bakinta jin wani kuka na shirin zubu mata, kafin ta matsa kusa dashi sosai tana matse idanunta tare da mayar da kukan da yazo mata,
Cikin tausayin halin da zasu kasance ita da Ballowo ɗinta ta rankwafa dai-dai kansa cikin wata raunatacciyar murya mafi raunin gaske tace.
"Munyi rashi Ballowo, amma wannan rashin ni nayi sa, na maka al'ƙawarin zan maye maka gurbin Oumuu, zan zama fiye da Oumuu-Ayman a rayuwar ka, Ina sonka Cucuu"
Ta faɗa tana kwantar da kanta a faffaɗan ƙirjinsa,
A hankali ta ƙara manna kanta a ƙirjinsa tana sauraran bugun zcyarsa dake fita dai-dai da nata,
Yayinda wani irin rauni da kuma zafi hadi da raɗaɗi ke ratsa mata dukkan wata ƙofa ta cikin Zuciyarta,
Mafi yawancin raunin kuma akan Ballowo ɗinta ne.
A hankali Abu Maleek ya sauke numfashi tare da fesar da iska, gently kuma ya buɗe idanunsa da sukai masa nauyi, gaba ɗaya jijiyoyin kansa sun fito sunyi raɗa raɗa,
Ga wani azababban huci da kansa ke fitarwa,
Idanunsa ya sauke akan drip ɗin, yana mamakin dalilin daya sanya aka sa masa wani drip,
Ƙamshin haɗaɗɗan turaranta ne ya kawowa hancinsa ziraya, da wani kasala ya lumshe idanunsa tare da yunƙura wa, zai miƙe tsaye cikin sauri ta ɗaga kanta daga jikinsa dai-dai lokacin da yake jingina da jikin frame ɗin gadon,
Fitanannu jajayen idanunsa ya narke a kanta yana kallon idanunta da sukai jaa ga wasu sabbin Hawayen da suke cikinsu, idanunsa ya fara yawo dashi a Jikinta har ya kawo kan ƙirjinta wanda duk rabi ƙirjin ya fito, ƙarara shatin nipples ɗinta suna waje,
Shiru yay yana kallon tsarin Halittar ƙirjinta, brest ɗinta rin wanda akewa laƙabi da mai kan tasa ɗin nan, wanda abu ne mai wahalar gaske kaga sun zube,
Jin zucyarsa na ƙoƙarin rinjayar gangar jikinsa ne ya sa shi janye idanunsa tare da mayar da shi saman fuskarta, a hankali kuma ya sauke wani lamintaccen numafashi yana mai juya idanunsa, so yake ya tambaye ta mene yasa yake nan? Mene ya samesa.
Ganin kallon da yake mata ne yasa a hankali ta ƙoƙarin zamewa tare ƙoƙarin sauka da kan bed ɗin,
Hannunsa ya miƙa tare da riƙe wrist ɗinta, da sauri tai ƙasa da kanta saboda wani abu daya shiga yi mata yawo,
Abu Maleek kam halin da yake ciki ya huce bayani sai da a aikace, idanunsa ya lumshe kana ya buɗe su agajiye kafin ya buɗe bakinsa cikin wata irin kamilalliyar Muryarsa mai daɗi, mai kuma tarin nauyi yace.
"Jidderhh!!"
Saukar Muryarsa haddasa lumshewar idanunta ba tare data shirya hakan ba, rufe idanunta kuma ya bawa hawayen da suke cikin idanun damar sakkowa, kasa amsa masa tayi sai Ajjiyar zuciya da take saukewa, ganin hakan yasa ya ɗan zame hannunsa dake kan nata, a hankali ya zare drip ɗin hannunsa, tare da tattaro raguwar ƙarfinsa ya matsa kusa da ita,
Lallausan hannunsa ya sanya a saman fuskarta tare da ranƙwafawa dai-dai fuskarta, har numafashin su na haɗewa waje guda, kafin kuma ya ɗan ƙara matsota kusa dashi sosai, tare da sanya hannunsa a ƙuncin ta ya shafi hawayen idanunta cikin wata irin murya mafi kaushi a tattare da shi yace..
"How long you have been crying?? And where is your glass?"
Ya faɗa a taushashe kuma a nutse yayinda yake wasa da yatsarsa a saman fuskarta da zummar goge mata Hawayen,
Bisa tarin mamakinsa mai makon Hawayen ya tsaya sai kawai yaga ta fashe da kuka tare da faɗawa jikinsa ta riƙesa sosai,
Lafiyayyiyar ajjiyar zuciya Cucuu ya sauke lokacin daya jita a jikinsa ganin yadda kuma take kukan sosai ne yashi ɗan haɗe hannayensa a gadon bayanta duk da tsananin azabar daya keji a jikinsa bai hana ya ɗanyi control na kansa ba,
Ya tattara dukkan hannunsa ya rungome sosai a saman faffaɗan ƙirjinsa mai yalwataccen gashi, tare da sanya hannu ya fara shafa kanta zuwa bayanta,
Dai-dai kunanta ya ɗura bakinsa a hankali cikin wani gigitaccen salo ya fara sakar mata hucin dake fita daga cikin bakinsa, kafin a hankali ya ɗanyi ƙasa da hannunsa zuwa ass ɗinta ya zura hannunsa ta ƙasan rigarta,
Wani irin raunataccen numafashi suka sauke a tare, lokacin da tafin hannunsa ya taɓa asalin fatar jikinta,
Kafin ya ɗan buɗe bakinsa kaɗan yace.
"Uhm!" kafin ya ɗan ƙara matseta a jikinsa yana ƙara dai-dai-ta zamansa, cikin lallashi yake ɗan buga bayanta kafin cikin wata lallausar Muryar mai cike da tausayin abinda ya sanyata kuka yace.
"Cry Na.. nahhhh!! Cry as so much as you can, I got you Okey.... Cry on my shoulder yi kuka Kuluuu!!.."
Shiru yay yana sauke numfashi kafin ya ƙara manna bakinsa a kunanta yana wura mata dadɗar iskar bakinsa yana ɗan lasar fatar kunanta cikin sigar rarrashi ya ƙara manneta da jikinsa yace..
"You'll not die Hawwa'u!!!.. and nothing will happen to you okey Na...nahhhh"
Ya faɗa lokacin daya miƙar da yatsarsa na tsakiya ya shiga yi mata yawo dashi a tsakiyar bayanta,
Kuka take har wani shuɗewa take kamar zata mutu, kukan da gaba ɗaya tana yinsa ne dalilin Cucuu, bata san yadda zata masa bayanin Oumuu ta barsu ba, bata san kuka yadda zai fahimta ba,
He could feel yadda hawayenta suke jiƙa masa jiki ba, ga wani cizo da dake sakar masa na ɗimauta.
Sun ɗauki wajan 30seconds a haka kafin kukan ya sake ta a hankali ta zame jikinta daga nasa tana ƙoƙarin sauka saurin riƙeta yay kafin ya tsura mata idanunsa masu kaifi, hannunta ya riƙe kafin da ƙarfi ya matse hannunta da sauri tace.
"Ballowo"
Ta faɗa tana kwaɓe fuska tare tura bakinta gama, laɓɓanta ya kalla da sauri ya janye idanunsa kafin ya manna hannunsa a saman fuskarta a hankali kuma ya ɗura hannunta a ƙirjinsa dake harbawa da ƙarfi yace.
"Kina son kashe Ni ko???"
Da sauri ta kallesa kafin tace "Ballowo kisa kuma? Ni a'a na zauna dawa"
Ta faɗa tana tura bakinta gaba, lumshe idanunsa yay kana ya jingina da jikin bango yana furzar da iska yace.
"To why are you crying?? Kamar dai wani ya mutu"
Innalillahi da sauri Zuciyarta ta buga tare da kallonsa tama rasa mene zata ce masa, yayinda wani Hawayen ke ƙara sakkowa daga cikin idanunta,
Ganin haka yasa ya ɗan miƙa mata hannunsa yace.
"Come here"
Ya faɗa yana ƙara jawota jikinsa cikin rashin sanin taƙamai mai abinda yake damun duk zuciyoyinsu ya shafa kanta, domin shima ji yake kamar zai saki ihu...
Ajjiyar zuciya ya sauke kafin ya haɗa fuskarsu waje guda bakinsa dai-dai nata kafin kuka ya buɗe baki yace.
"Gayawa Ballowo ɗinki mene? Shiru stop cry ok"
Ya faɗa yana manna bakinsa saman nata, da sauri ta runtse idanunta tana jin tsigar jikinta na tashi yayinda Jikinta kuma yay sanyi gaba ɗaya, a hankali ya fidda red tongue ɗinsa tare da zurawa cikin bakinta gam gam ta rufe bakinta taƙi bashi damar abinda yake son yi, ganin haka ya sanya ya buɗe idanunsa tare da kallonta muryarsa na rawa alamar kamar zai kuka yace..
"Na... nahhhh"
Zuciyarta ce ta harba domin bata saba ba sam, wannan very close ɗin da sukai da juna ji take kamar numafshinta zai fita, kallonta yay domin tuni zuciya ta ɗebe sa, sakinta yay tare da sauka daga kan bed ɗin ya nufi babban Parlo yana dafe kansa tare da faɗin.
"Oumuu!! Oumuu where are you Maaamahh!!"
Da wani irin sauri Julde tabi bayansa tare da faɗin.
"Ba Oumuu"
Da wani mugun sauri ya juya ya kalleta kafin a hankali ya sulale ya zauna saman kujera..


Queen Roomana ce zaune tana kuka a hankali tare da faɗin.
"Mene ya sanya hakan??? Akan kawai Taswira? Ko kujerar sarautar? Ba Noor ba Oumuu-Ayman? Yanzu kuma rayuwar Jalaluldeen kika tisa gaba akan mene?"
Ta ƙare maganar tana kallon matar gabanta,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login