Showing 24001 words to 27000 words out of 150413 words
Chapter 9 - Kwarya Tabi Kwarya Book Complet by Binta Umar Abbale .txt
'kasan gurin, ajiyar zuciya na sauke cikin raina nace"Abin yazo kenan kallon k'asa kamar makaho." Mun kai minti biyar nida shi a tsaye a kafin naji yace." Ni Bana abun alkairi domin a gode min, ba ni na bawa babanki Lafiya ba Allah ne dan haka shi zaiyi wa godiya ba niba." Yana k'are maganarsa ya bugo min kof'a.
Na jima a tsaye a gurin ina kallon kofar kafin na sauke ajiyar zuciya a sanyaye na sau'ko 'kasa na sameshi a zaune a inda yake.
Cikin taushin murya na sheda masa abinda yace....bai nuna komai ba yace."To babu komai Sumayya dama mafi akasari masu taimako basa so a damesu da godiya tabbas hakane Allah ne ya bani lafiya amma kuma shine ya zama sanadi dan haka zan cigaba dayi masa addua har karshen rayuwata."
A sanyaye nace"Hakane baba Allah ne abin godiya a garemu addua kuma ba zamu daina yi masa ba tunda shi ya zama sanadi.'' To Har muka isa gurin mu muna tattauna maganar a tsakanin mu...........
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 8:19 AM - ???: *'KWARYA TABI 'KWARYA*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE�_ *bintaumarabbale@gmail.com*
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊�*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
_________________________
*Littafin na kudi ne....!*
_#300.....0542382124...Binta Umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin.......... Ga masu bukatar VIP Group 600 ne_
_Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d'aya 90899076_88137740_
*SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
33&34
Kwana biyu kyara da hantara ne a Tsakanina dashi komai nayi masa ba nayi masa gwaninta, magana kuwa sai nayi sau biyar bai bani amsa d'aya ba, haka dai na cigaba da hakuri da halinsa ina kokarin ganin na sauke nauyinsa dake kaina, a tsakanin kwanaki biyu zuwa hud'u duk abinda zan girka masa naci ko sha baya ko kallon daning din ballanatana ya zauna yaci, yanda na ajiye haka zan zo na dauke, ganin kamar 'barnar tayi yawa yasa na yanke shawarar samun sa muyi magana idan baya bukata sai na daina wahalar da kaina da asarar abinci........ samun sa nayi gurin da yake hutawa na tsuguna gwiwa a 'kasa kamar koda yaushe nace" Ranka ya dade Barka da yamma." Kamar da dutse nake magana, kallonsa nayi ina jin wani kunci a cikin zuciyata, a gaskiya na fara gajiya da wannan wulakancin, hankalinsa na kan wayarsa yana latse latse a kai......'bacin ran dake taso min na danne Nace"Dama inaso muyi magana da kai ta fahimta ne." Ta 'kasan ido naga yayi min wani kallo, na cigaba da cewa"Naga kamar baka 'bukatar abincin da nake hidimar girka maka safe da rana da dare me zai hana a daina a sarar abinci idan baka bukata sai na bari akan a dinga zubarwa."
Zamansa ya gyara yayi wani irin zama irin nasu na saurata hannunsa dake d'auke da zobunan azurfa ya d'ora saman gwiwarsa ya tsira min idanunsa.
Kasa kallonsa nayi a yanayin dan ganin yanda ya 'kara wani kwarjini da cika ido gashi zaman da yayi yay masa kyau ha'kika ya dace a kirashi da *Sarki!* ba Yarima ba dan komai nashi cikin mulki da muskilanci yake yi.
"Kece kika ajiye abincin gidan da kike wannan maganar."? Maganarsa ta bani mamaki sosai nace" A'a bani bace ba, ni a nufina 'barnar abincin da ake tayi yawa sabida na safe haka yake tarar dana rana sannan na dare ya tarar dana rana, wani zubin lalacewa yake sai dai na bawa dabbobi ko na zubar."
"Ki cigaba da aikin ki bana bukatar ki huta." Yafad'a tare da tsira mun ido gami da san ya tabbatar min da maganarsa, "Inaso ka fad'a min dalilin ka na yanke wannan hukuncin ya za'ayi kai ba cin abinci kake ba amma kasa a girka a zubar wannan ai izgilanci ne." Gaura min mari yay yana huci yace."Koda yaushe kina yawan fad'ar wannan maganar akai na sabida kin raina ni ko."? yana nuna ni da hannunsa yake maganar, d'auke kaina nayi daka fuskarsa nayi kasa dashi hannuna dafe da kuncina....."Wallahi duk sanda na sake jin kin jefe ni da kalmar izgilanci sai na baki mamaki na lura dake kwata-kwata bakya shakka fad'a min kowace kalma kodan kinga na nuna ina sha'awarki ne kike tunanin wani abu.'"
D'agowa nayi raina a 'bace Nace"Allah ya baka hakuri idan furucina ya 'bata maka rai ni inaso na tunasar da kai abinda ka sani ka manta ko kuma nace kake takewa saboda giyar mulki ranka ya dad'e kai mutum ne mai girman kai gami da Izigilanci a kan komai alhalin kai d'in ba komai bane a gurin Allah inaso na tunasar da kai cewa wannan d'abi'un da kake yi zasu nesan taka da rahamar Allah." Hawayen da nake maqalewa ne suka zubo.
"Tashi ki bani guri."! Kalmar da ya fad'a kenan cikin 'bacin rai! Mikewa nayi na sunkuya cikin tausasawa nace" A gafarce ni idan maganar da nayi ta 'bata maka rai." Ba tare da yace min komai ba ya sunkuyar da Kansa k'asa.
Gurin na bari da sauri na nufi sashen Mahaifiyarsa wato Fulani zuwa zanyi na sheda mata dukkanin abinda ke faruwa, domin kamar ita ta dauke ni aiki ta bani amana yana da kyau duk abinda ke faruwa tasa ni saboda kada wani mummunan abu makamancin wanda ya faru a baya ya faru a tuhume ni da wani abu, a tsakanin kwanaki biyar din da suka gabata bani da masaniyyar inda yake cin abinci na safe rana da dare idan ma a gurinta yake ci to yana da kyau na sani ko hankalina ya kwanta.
Ina gurfane a gabanta na sheda mata dukkanin abinda ke faruwa......a da tana kishingid'e a lokacin da nake maganar sai naga tayi saurin mi'kewa zaune gabad'aya ta mayar da hankalinta kaina tace"Sumayya kika ce yau kwana biyar babana baya cin abincin da kika girka."? Nace"K'warai kuwa ranki ya d'ade ganin kwanakin suna yawa ne yasa na yanke shawarar zuwa na sheda miki."
"A'ina babana yake cin abinci."? Tafad'a tana kallona, Nace" Ranki ya d'ad'e nima wallahi ban sani ba." Ajiyar zuciya ta sauke da sauri tace"Miko min wayata gata nan." Da sauri na dauka na mika mata.
Number shi ta kira inaji yana gaisheta bata amsa ba tace"Maza kazo sashena ina nemanka."
Kashe wayar tayi ta kalleni da fad'in "Sumayya kije ki cigaba da aikin ki kada ki fasa yi masa abinci a duk sanda kika kammala kika sheda masa idan bai ci ba kizo ki sheda min."
Nace"To insha Allah ranki ya dade zanbi umarninki."Tace."Tashi kije Allah yayi miki albarka." Cikin farin ciki na amsa da "ameen Ranki ya dade ina godiya."
Raina fari tas na bar sashen gurinmu na nufa domin nayi shirye shiryen shiga gurun karatu......Tsaf na fito cikin hijabi fari tas da jakar littafai a hannuna Babana na kwance a katifa bacci naso ya daukeshi nace"Baba kayi bacci ne."? Mi'kewa zaune yay yace." Yana dai so ya dauke ni dama ke nake jira ki shirya mu fita tare yau inaso na shiga gurin Dawakai na dubasu.''
Nace"Baba ka zauna ka sake samun 'kwari jikin ka dawakai na nan kalau babu abinda ya samesu." Yace."Sumayya zaman nan ya isheni wace lafiya kuma akeso na samu bayan wannan inaso na koma bakin aiki."Nace"To shikkenan baba nida naso ka k'ara watsakewa sosai kafin nan."
Mi'kewa yay yana dariya yace."Sumayya zaman gida sai mata idan kinga namiji ya zauna a gida to dole ce kamar dai ni da rashin lafiya ya hanani gudanar da harkokina." Murmushi nayi nace "Hakane baba, to tunda Tambaya na gurin aikinsu sai mu sawa kofar 'kwad'o." Yace."Eh hakane yi maza ki d'auko kwad'on insha Allahu kafin ta dawo nima na dawo."
'Kwadon (key) na dauko muka fito tare muna hira na kulle gidan na bashi key din yasa a aljihun rigar jikinsa, muka fara tafiya.......Daf da zamu rabu kowa yay inda ya nufa Lantana ta tari gabanmu, a duk sanda zanga Lantana sai gabana ya fad'i saboda duk sa'kon da zata fad'a bana alkairi bane.
"Sumayya kije can 'bangaran Maigirma Ciroma Gimbiya Lawisa ke san ganinki." Na kalleta da fad'in "Lantana kin dai ga shirin da nayi ko zan shiga gurin karatu ne sai dai idan na fito."
"Kinga Sumayya bani zaki fad'awa hakaba ita wacce ta aiko ni ita zaki fad'awa ni dai na cika umarnina idan kin'ki zuwa zan tabbatar mata da cewa na sheda miki sa'konta."
Zanyi magana babana ya katseni Ya kalli Lantana a nutse yace."Kije kice gatanan zuwa." Lantana ta bar gurin da sauri.......Cikin kulawa ya kalleni yace."Sumayya duk wani uziri naki to yabi bayan na masarauta, kiran da Gimbiya Lawisa tayi miki yafi uzirinki wanda zaki gabatar a yanzu, nasha fad'a miki cewar baki da wani gata da abinda zakiyi tun'kaho dashi sai wannan masarautar domin a cikinta aka haifi iyayena da kakanni na gabad'ayan mu tasowa mukayi muka ganmu a cikinta tsohuwar marasauta ce mai d'umbin tarihi, iyayenmu sunbi umarnin masarauta har suka koma ga Allah, Ina fatan ni dake da mahaifiyarki muma mu kamanta abinda magabatan mu sukayi dan haka kibi umarnin masarauta kije kiji kiran da akeyi miki.
Ajiyar zuciya na sauke ina kallonsa a sanyaye nace"Baba naji kana maganar nabi umarni inaso nayi maka wata tambaya." Yace."Ina sauraranki."" Nace"Baba idan ya kasance wani umarnin ya sa'bawa dokokin Ubangiji ba shin har dashi zan bi."? Girgiza kansa yay yace."A'a Sumayya ban umarce ki akan sa'bawa Allah ba, duk abinda ya zama na sa'bawa mahallici ne to kiyi kokarin nesanta kanki dashi.
Nace."Alhamdullihi baba bari nayi sauri naje domin naji kiran da ake min." Cikin kauna gami da tausayi irin na iyaye yace."To d'iyar kirki Allah yay miki albarka." Ameen nace cikin sauri na bar gurin....Lawi bai bar gurin ba har sai da ya daina hango 'yar tashi.
Lantana ce tayi min jagora har Lambun da take hutawa, tare da hadimanta na sameta. takalmana na cire a nutse nasa gwiwowina a k'asan gurin nace"Barka da hutawa ranki ya dade." Shuru tayi min bata amsa ba. gurin ya dauki shuru na kusan minti uku kafin ta dago kanta cikin shan qamshi ta kalli hadimanta dake gefe da gefanta tace"Ku tashi kuje zanyi sirri da Sumayya."
Jiki na rawa suka miqe suna godiya.
Gurin ya sake daukar shuru na 'yan mintina kafin naga ta gyara zamanta cikin kasaita ta kalleni da fad'in "Zauna sosai muyi magana aini daga yau kin zama qawata aminiyata." Cike da mamaki nake kallonta ina mamakin furucinta. zamana na gyara sosai a gabanta nace"Ranki ya dade ina sauraranki.
Ajiyar zuciya ta sauke kafin naji ta kira sunana. a nutse na amsa ina kallonta, Tace"Inaso na saki wani aiki ta 'bangaran Yarima Ali ina nufin magajin Sarki, tunda ya kasance kin zama mai kula dashi ta fannin abincinsa da abin shansa to zanyi amfani dake gurin ganin bukata ta biya a kansa.
Nasan kin san da maganar auran dake tsakanina dashi ko."? Kallonta nayi ina mamakin maganarta aure a tsakaninta da Yarima gaskiya ban san da maganar ba.
Girgiza kaina nayi nace"A'a ranki ya dade ban san da maganar ba." Tace"To yau na sanar dake cewa Iyayanmu zasu daure aurena dashi farkon watan gobe, a zahiri nike sonsa koda yana sona bai kai wanda nake masa ba, wannan dalilin yasa nake so nabi matakan da zasu janyo hankalinsa kaina, inaso kafin zuwan ranar daurin aurena dashi na mallake shi da zuciyarsa gabad'aya."
Da sauri na kalleta, sai naga tayi murmushi tana d'aga min gira 'kasa nayi da kaina tare da cigaba da sauraranta.
"A kwai wasu sinadarai da zan baki wanda zaki dinga zuba masa a cikin abincinsa da abin shan sa ya zama na dai duk wani abu da zai ci ko ya sha kina sa masa sinadaran dana baki.'' ajiyar zuciya na sauke tare dago kaina na kalleta bayan gama maganarta ta Nace.......
*BINTA UMAR ABBALE*
*Please kuyi sharing��*
2/11/21, 8:19 AM - ???: *'KWARYA TABI 'KWARYA*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE�_ *bintaumarabbale@gmail.com*
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊�*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
_________________________
*Littafin na kudi ne....!*
_#300.....0542382124...Binta Umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin.......... Ga masu bukatar VIP Group 600 ne_
_Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d'aya 90899076_88137740_
*Sannu da kokari mai babban suna*
*DR MUHAMMAD MK*
Ina mutukar godiya da alkairin ka, na baka kyautar wannan pege d'in🥰
*SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
35&36
"Ranki ya dad'e wane irin sinadarai ne kike magana akansu inso kiyi min bayani yanda zan fahimci inda maganar ki ta dosa." Duk da na gane abinda take nufi sai kawai na tsinci kaina dayi mata wannan maganar.
Murmushi tayi tace"Haba Sumayya kamar ba mace ba zaki ce baki fahimci inda na dosa ba, to shikkenan tunda baki gane ba bari na fahimatar dake, Takanas! Mamana ta tura aka kar'bo mata Taimako daga gurun malamanta duk domin na samu nasarar mallakar zuciyarsa kin san hausawa nacewa ko kana da kyau ka qara da wanka to ballanatana ni da ban zauna daram a cikin zuciyarsa ba, kinga kuwa dole na tashi tsaye naga na r'ikeshi a tafin hannuna kafin zuwan ranar daurin auran namu."
Wani irin kallo nake mata na mara hankali Nace"Ranki ya dade ki gafarce koda maganata zata 'bata miki rai ni ina ganin wannan sinadaran babu wani abu da zasuyi miki me zai hana ki nemi soyayyarsa ta hanyar Allah duk ga hanyoyi nan a saukake hanyoyin da zaki bi ki mallakeshi da zuciyar sa, a ganina idan kika ce ta wannan hanyar zaki mallake shi to zakiyi ta wahalar da kanki a banza da wof........."Ke! rufe min shegan bakin ki a nan gurin." A fusace ta katse min magana.
Tsira mata ido nayi kallona take tana huci tace"Ba shawara na nema a gurinki ba umarni na baki zaki aikata abinda na saki ko ba zaki aikata ba.
Har na bude baki zanyi magana sai kuma nayi shuru ina nazari, kai tsaye idan na'ki aminta da umarninta zata bi wata hanyar ne ta cimma k'udirinta, tabbas asiri zaiyi gaggawar tasiri a jikinsa tunda na lura bai wani damu da addini ba wannan tunanin da nayi yasa nayi saurin neman afuwarta nace"Insha Allahu zan zartar da umarnin zaki bani." Gyara kishingid'ar tayi tana saukar da numfashi, shuru gurin yay kimanin minti goma kafin naji tace"Kalleni nan." Na dago kaina na zuba mata ido.
Wata leda viva ta miko min da fadin"Bud'e ki fito da kayan dake ciki." Da sauri nayi abinda tace, magunguna ne a 'kulle a wani 'bakin yanki mai ratsin ja da fari dauri uku tace."Ki duba a tsanake zanyi miki baya ni kada kije kiyiwa mutane baragada."
Nace"Ina dubawa ranki ya dade."
"Wannan wanda yake da ratsin baki da fari na abinci ne kina jina ko."? nace" Eh ina jinki." Ta cigaba da cewa"Duk wani abinda zaici ya kasance sai kin barbad'e shi da wannan maganin sannan ki bashi." Nace" na fahimta ranki ya dade." Ajiyar zuciya ta sauke tace"Shi kuma wannan mai ratsin ja da fari din na lemo ne kina jina ko."? Nace"Eh." ta cigaba da cewa"lemo ko wane iri ne kafin yasha ki bude ki barbad'a maganin a ciki." Nace"To ranki ya dad'e na fahimta insha Allah zanyi miki kokari nima inaso ki mallaki zuciyarsa."
Dariya tasa tana kallona jin furucin da nayi....tsaki naja cikin zuciyata nace"Dubi shashashar banza." "Zaki iya tashi ki tafi inaso yau ki fara gudanar da aikin ki idan naga al'amura na tafiya kamar yanda nake so nayi miki alkawarin kyauta mai tsoka." 'ka'kalo murmishi nayi na yunkura domin mikewa nace"Godiya nake." Hannu ta daga alamun ta amsa.
Takalma na zura hannuna ri'ke da ledar maganin nace"A tashi lafiya." Hanya ta nuna min alamar na tafi. da sauri na bar gurin zuciyata cike da takaici.
Ina tafiya ina mamakin al'amarin gaskiya na raina wayon ta ashe duk 'kasaitarta ta banza ce tunda gashi ta kasa janyo hankalin namiji sai ta had'a da asiri! a zahiri gimbiya Lawisa nada kyau da kyawun jiki babu namijin da ba zaiyi sha'awar ta zama mallakinsa ba, gaskiya nayi mamaki da ba tayi wa Yarima Ali ba wato yanda na fahimce shi kyau ko yawancin wasu abubuwa basa burgeshi yafi duba nagartar mutum. ajiyar zuciya na sauke tsigar jikina na tashi dana tuna irin masifaffan kallon da yake min a duk lokacin da muka had'u....... cikin ramin bulo nasa ledar magungunan na dauki wani dutse na rufe gurin da sauri na bar gurin kai tsaye gurin karatu na nufa karatu sosai akayi an gabatar da wasu darrusan bana nan haka nayi hakuri na zauna na samu abinda na samu.
'Karfe d'aya da rabi mun fito kowa sai shiga gurinsu yake ni kuwa Lahira na bawa jakar littatafai na nace ta'aje min a gurinta, kai tsaye sashensa na nufa domin gabatar da aikina.
Samun sa nayi a falo yana d'acin rai! dan tunda na kalli fuskarsa jikina yay sanyi, gaishe shi nayi ya watsar da gaisuwa cikin 'bacin rai yace."Wato maganar da nayi miki bata gamsar dake ba sai da kikaje kika had'a ni da mahaifiyata ko."?
Da sauri na sunkuyar da kaina nace"Ban fad'awa mahaifiyarka maganar da wata manufa sai dan ganin yana da kyau ta san lamarin domin ta binkici a'ina kake cin abinci."
"Ni yaro k'arami ne da zakiyi min wannan maganar."? girgiza kaina nayi, 'kwafa yay da fad'in " Tun ranar da kikayi min wannan 'bakin abun nake 'kyank'yamin ki da dukkanin abinda zai fito daga hannunki, kece wahalalliya kiyi ta girki kina zubarwa ba zanci ba kuma wallahi kika kuskura kika sake zuwa kika fad'a mahaifiyata wata magana sai nayi miki mugun abu.''
Na jima ina kallonsa kallon da banta'ba yi masa ba, gabad'aya mamakinsa ne ya rufe ni ashe abin arziki yana zama tsiya to wane mugun