Showing 75001 words to 78000 words out of 150413 words

Chapter 26 - Kwarya Tabi Kwarya Book Complet by Binta Umar Abbale .txt

motar, suna daf da fita Mika'il ya shigo da mota, ganin dandazon jamaa harda 'yan jarida da motar 'yan sanda yasa Mika'il gabansa ya tsananta faduwa, da sauri yayi parking ya fito yana tambayar abinda ke faruwa, wanda ya fara ganin abun ne yayi masa bayani, Mika'il a gigice! ya nufi inda yaga mutane na fitowa, tun daga nesa ya hango abunda ke faruwa, yana karasawa ya zube gaban gawarwarkin da'aka gama dauresu, ihu! yake kurmawa yana dukan kansa Wani bawan Allah ya dafa kafad'unsa yana rarrashinsa yace."Ba ihu za kayi ba innalilihi wa'ina ilaihi raji'un zaka dinga fad'a." Mika'il ya dinga fad'in Kalmar innalilihi wa'ina ilahi raji'una da karfin gaske!






Cikin tsantsar tashin hankali Shatima ya shiga masarautar kai tsaye sashen Fulani ya nufa ganinta cikin nutsuwa yasa ya fahimci bata san abinda ke faruwa ba, gaisawa sukayi tana nazarinsa tace"Shatima ina fata dai lafiya dan ba haka na saba ganinka a hargitse ba." ajiyar zuciya ya sauke yace."Mamma lafiya inaso naga Maimartaba ne." Tace."Yau ba anan yake ba yana gurin uwargida." sallama yayi mata ya nufi gurin uwargidan


Tun kafin ya k'arasa ya hangosu a tsaye koda ya karasa gurun samun fuskokinsu yayi cikin yanayi na alhini da damuwa Mussaman shi maimartaban ya hango tsantsar tashin hankali a cikin kwayoyin idanunsa.........Cikin yanayi na damuwa yace."Allah ya baka yawan rai al'amarin nan fa da yake ta faruwa wallahi ko shakka ba nayi dasa hannun masarauta a ciki wa'inda baka ta'ba tsammanin zasu aikata wannan mummunan aikin ba zakayi mamaki idan binkice ya nuna maka su......Ciroma da Galadima jikinsu yayi sanyi suka maida hankalinsu kansa da fadin"Kai a iya bunciken ka wa kake tunanin zai aikatawa Yarima wannan mummunan aikin kada fa ka manta dukkaninmu cibiyarmu d'aya ya za'ayi wasu daga cikinmu su zama bara gurbi."


Shatima yace."Ni dai na fad'i abinda nake hasashe nasan kuma tabbas idan an tsananta binkice akan al'amarin a samu wa'inda suke da hannu a cikin al'amarin."
Ciroma cikin dakiya da nuna shi mai gaskiya ne yace."Shatima kayi gaskiya da wannan maganar insha Allahu zamu tsananta binkice domin gano wa'inda suke kokarin su kawo mana rud'ani a cikin wannan masarautar mai albarka."


Waziri ya sauke ajiyar Zuciya cikin sanyi yace."Yana da kyau muje mu zauna mu jirayi dawowar Yariman amma a gaskiya wannan al'amarin yayi tsanani duk wanda yake shirya wannan abu to babu shakka rayuwar Aliyu yake nema saboda haka yana da kyau dukkaninmu mu zauna domin mu kawo karshen wannan matsala."


Maimartaba ya sauke zazzafar ajiyar zuciya a nutse yace."Ku muje fada mu zauna mu tattauna domin mu samu mafita." Gabad'aya suka nufi fada kowa na sa'ke-sa'ke a zuciyarsa.




"Wayyo Allah na shiga uku na lalace Wayyo! Allahna."!!! Muryar Laure mahaifiyar Haruna mukaji ta shigo tana kurma ihu! had'e da fad'in ta shiga uku ta lalace.!!! da sauri mukayo waje muna rarraba ido! Laure ta shigo a jigace! tayi kozai kozai da ita sai ihu! take tana fadin ta shiga uku! gabadaya rikicewa nayi na nufe ta ina kokarin rik'eta kawai naji saukar mari a kumatuna, kafin ta cukume ni tana fad'in " Sumayya kece kika kashe min d'ana ni dake zanyi kuka ba da kowa ba Haruna yaron arziki ya mutu ya barni a duniya na shiga uku na lalace."!!!!! tana gunjin kuka takarashe maganar, kallonta na dinga yi bakina na rawa nace" ki fad'a min abinda ke fa...ruwa." wuya na ta ri'ke tamau! ta matseni a bango (garu) tace" Ni zaki mayar shashasha ko ? kina nufin bakin san abinda ke faruwa."? Hawaye ne suka kwace min nace"Wallahi tallahi bansan abinda ke faruwa ba dan Allah kiyi min bayani amma kada kice min Masoyina ya mutu."


Wani gigitaccan marin ta dauke ni dashi jikinta na rawa tace"Haruna ba masoyinki bane makiyin ki ne tunda har kika iya bashi guba yaci ya mutu to Haruna bashi da babbar abin 'ki kamar ke."
Kallonta nakeyi inaso nayi magana bakina yayi nauyi jiri ne ya shiga d'iba na ina jin sautin muryarta a kunnena silalewa nayi na fad'i a gurin, sama-sama naji salatin Tambaya a kaina..............Idona na bude a hankali ina kalle kalle Tambaya na gani a gurfane a gabana tana kuka tare da shafa min ruwa a fuskata, a furgice na mike zaune ta rike ni "Sumayya kwanta ki huta kada ki tashi." Girgiza kaina nayi cikin nauyin baki nace."Ina Laure take."? Tace."Me zakiyi mata."? kai tsaye nace."Inaso ta tabbatar min da gaskiyar mafarkina." Hawaye ta share tace"Sumayya ki shiga hankalinki ki samu nutsuwa ki kad'aita Allah ki sani Allah shike rayawa kuma shi ke kashewa babu mahalukin da ya isa yayi wannan al'amarin idan ba Ubangiji ba kawai kiyi wa Haruna kyakkyawar addua da samun rahamar Allah."




Wasu zafafan hawaye ne suka 'kwace min nace"Da gaske ne ashe."? kanta ta daga min....Rungumeta nayi tare da fashe da kuka "Wayyo Allah na shiga ukun...bakina ta rufe min kafin karasa, naji tana nanata kalmar innalillahi da sauri nima na kar'ba na dinga yi da karfi ina wani irin kuka mai tsuma zuciya, Yarima bukatarsa ta biya ya kashe Haruna yaji dadi dama yace." yana da hanyoyin da zai iya ruguza mana farin cikin mu tabbas dana san da gaske yake zai kashe min masoyi to dana bashi abinda yake bukata! da karfi nace"Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un wannan masarauta akwai azzalimai a cikinta."!!! Da sauri ta rufe min baki ta dago ni tana kallona tace"Sumayya wace irin magana ce wannan? ashe kina so ki janyo mana masifa."? Ina kuka nace"Shine ya kashe shi wallahi shine dama yace sai yaga karshen soyayyarmu bukatarsa ta biya ya kashe shi ya huta."






*Na kudi ne...!*
Kada ki karanta min littafi idan baki biya ba ke kuma da kika futa da book din keda Allah! idan kina bukatar biyan kudin ga yanda abin yake...Vip gruop#600 normal gruop#300 account... 0542382124..Binta umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:26 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA*
*SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
79
Wani irin kallon mamaki Tambaya keyi min, ina gunjin kuka nace"Da gaske ne shine ya kashe shi dama yace yana da hanyoyi da yawa da zai iya raba tsakanina dashi domin ya samu nasarar aurena."!
Tambaya kafad'una ta ri'ke tana jijjigani tace."Sumayya ki shiga nutsuwarki dan Allah ki daina sambatu sai surutai kikeyi marasa kan gado da ma'ana shin waye wannan da kike magana akansa."?.


Hanci na sha'ka na kalleta har yanzu na kasa tsayar da ruwan hawayen dake zuba nace"Tambaya Yarima yayi al'kawarin sai ya aureni ko ta halin 'ka'ka bayan mahaifinsa ya gargadeshi akan ya janye maganar aurena sai ya 'kudiri mummunar aniya a kanmu nida Haruna ya tabbatar min da cewa duk rintsi sai ya san yanda yayi ya aureni domin biyan bukatarsa."


Kallona ta dinga yi tana girgiza kanta gabadaya yanayin ta ya nuna alamun tsoro da tashin hankali......Ganin kawai ta kura min ido tana kallo yasa nayi yun'kurin mikewa, tayi saurin rike hannuna na zauna jiki a sanyaye tace"Sumayya da gaske kike Yarima ne silar mutuwar Haruna." Murya a dashe nace."Tabbas ko shakka ba nayi shine ya kashe s......! saurin rufe min baki tayi kafin na karasa maganar dukkaninmu muka kalli bakin kofa saboda sawun tafiyar mutane da mukaji......Murya na rawa tace"Sumayya ki bar wannan maganar a cikin ki duk rintsi kada ki fito da i ta, idan kin fad'a Yarima yayi silar mutuwar Haruna babu shakka zamu shiga tashin hankali a masarautar n........Katse maganarta tayi dalilin shigowar babana da wasu 'yan sanda guda biyu mace da namiji. cikin tashin hankali muka
Mi'ke tsaye. "Malam wannan ce Sumayyan ko."? A sanyaye Lawi ya daga kansa. ya kalli 'yar uwarsa da fad'in ''Merry je kiyi aikin ki." Gani nayi ta nufo inda nake da ankwa a hannunta, bakina ya dinga motsi jikina ya dinga karkarwa a lokacin gabadaya kwakwalwata toshewa tayi na dinga tunanin adduar da zanyi, Tambaya kuwa kuka ta fashe ta durkushe a gurin tana rirrik'e kafar ma'aikaciyyar a lokacin da take kokarin daure min hannu.


Kallonta tayi cikin yanayin hausarta tace."Kiyi hakuri ba zamuyi mata komai ba mutukar bata wahalar damu ba." Tambaya ta kalli namijin tana kuka tace"Dan darajar Allah da annabi kada ku tafi da ita wallahi bata da laifi akan faruwar wannan al'amari." Yace."baba dole ne ayi binkice akan 'yarki domin itace ta girka abincin dake dauke da guba a ciki idan ba tayi mana gardama ba to zata samu sassauci idan kuwa ta tsaya gardama za tasha wuya a gurinmu." Tambaya kallona tayi tana marairaicewa! naji wani irin tausayinsu ya rufe ni, babana tsabar tashin hankali duk kammaninsa sun sauya ya kasa magana kawai ya jingina jikin bango (garu) sai kallonmu yake.


Cikin kokarin danne tashin hankalina nace"Tambaya ki daina kuka dan Allah kiyi min addua insha Allahu mai gaskiya baya ta'bewa Allah zai kub'tar dani daga dukkanin wata musiba."


Mi'kewa tsaye tayi tana kokarin magana suka tasa 'keya ta, Lawi da saurin gaske ya shiga daki yana share hawaye ita kuwa Tambaya bayanmu ta biyo tana kuka had'e da ri'ke min hannun riga sai hakuri take bawa jami'an tsaron.........Dandazon mutanan dake gurin yasa nayi saurin sunkuyar da kaina kasa na dinga tafiya kaina a sunkuye ina kiran sunan Allah a zuciyata, motarsu suka saka ni, na dukufar da kaina k'asa band'ago kaina ba har sai dana muka fita daga gidan.




Suna zaune suna tattanawa dangane da faruwar al'amarin sa'kon mai girma governor ya iso, mai girma governor yayi umarni da cewa lallai a rufe asibitin *ZINARIYA HOSPITAL* sai gwamnati ta gama binkice akan mutuwar da mutane keyi a cikin asibitin." Maimartaba beji ciwo akan umarnin governor ba koda bai bada umarin rufe asibitin ba dama ya yanke shawarar rufe shi..........Galadima da Ciroma cike da tsantsar farin ciki suka bar fada, suka had'u a gurin guda suna ta 'bab'baka dariya bukatarsu ta fara biya gwamnati ta shigo cikin al'amarin zasu san yanda zasuyi su had'a kai da gwamnatin domin su ruguza asibitin.




Ta jima kanta a kasa tana kaiwa Allah kukanta kafin ta d'ago kanta tana zubar da hawaye ta daga hannuwanta sama ta dinga addua tana 'kas'kantar da kanta a gurin mahallicinta, Mamma Fulani ta dade hannunta a sama tana neman sasaauci gurin Ubangiji kafin ta shafa a fuskarta a nutse ta juyo tana kallon mijin nata dake zaune akan kujera, tace"Ranka ya dad'e Har yanzu bai dawo ba kenan."? Maimartaba ya sauke ajiyar zuciya cikin sanyin murya yace."Bai shigo ba har yanzu gabad'ayan mu mun gaji da zaman fada kowa ya shige gurinsa.'' Kanta ta d'aga ta kalli agogon dake kafe a falon tara na dare, a sanyaye tace."Inasha Allahu, Allah zai dawo mana dashi lafiya." Maimartaba ya amsa da ameeen tare da mikewa tsaye! sallama yayi mata ya nufi gurin Uwargida Huwaila.......Tana zaune a bakin gado kunnanta makale da waya sai 'ba'bbaka dariya takeyi da alama tana cikin nishad'i, Tace."Ai al'amura gabad'aya sun dagule wannan karon mun samu nasara akansa dan har yanzu yana hannun 'yan sanda kuma gwamnati ta shigo cikin al'amarin asibitin da yake tutiya dashi gwamnati ta rufe shi, wannan dalilin yasa duk na kira wayarku na sheda muku cewa yau kuyi bacci harda munshari dan bukatarmu daf take da ta biya." Daga daya b'angaran aunty Safiyya ta dinga k'yakyata dariyar farin ciki tace"A gaskiya naji dadin wannan abu Wai!! ya muka ga idon mutsiyaci a cell a gwara yasha duka dan ya bamu wuya." Uwar gida tace"Ai be zama lallai su doke shi ba yanzu abinda nake so daku shine gobe da sassafe ku shigo cikin nuna alhini da damuwarku bana so ko kad'an a gane akwai sa hannunmu a cikin al'amarin." Aunt Safiyya tace."Kada ki damu Mama zamu shigo da wuri kuma ba zamu nuna farin cikin mu ba zamu nuna tsantsar damuwar mu dangane da faruwar al'amarin." Uwar gida tace"To shikkenan sai kun......shigowar Maimartaba dakin yasa ta kasa karasa maganar kashe wayar tayi ta ajiye kusa da ita tana masa barka da shigowa.


Guri ya samu ya zauna a nutse yace."Dawa kike waya da daddare haka."? Tace."Wallahi Safiyya ce ta kira ni yanzu take sheda min cewa na nema mata alfarma a gurinka wai tana so ta 'kara jari akan wanda take juyawa gashi tana jin kunyar Tambayarka kudi."


Murmushi yayi yace."Da alama basu san abinda yake faruwa ba a masarauta ba." Da sauri tace."Me yake faruwa ranka ya dad'e."? yanda ta nuna damuwarta sai ka rantse da Allah bata san komai ba.


Maimartaba cikin nutsuwa ya sheda mata dukkanin abinda yake faruwa, fashewa tayi da kuka ta ri'ke kanta tana fad'in "Innalillahi wa'ina ilaihi raji'una! wannan yaro yana ganin tashin hankali wai shin me Aliyu yayi wa mutane ne suke nema suga bayansa."


Maimartaba tace."Wallahi ni kaina na rasa abinda yasa mutane suke nuna masa 'kiyayya al'amarin yana bani mamaki mutuka! ada ina zargin daga waje al'amarin ya fito sai da na zauna nayi tunani sosai na gane cewa a kwai saka hannun wasu daga cikin masaurata.".




Tana kuka da fyatar majina tace"Allah ya taimake ka shin kai wa kake zargi da aikata wannan aikin dukkaninku cibiyarku d'aya ashe akwai wanda zai iya neman ran d'an uwansa."


Maimartaba yayi murmushi mai ciwo yace."Hulaiwa baki san mulki ba har yanzu mutane na iya aikata komai akan mulki na lura da tun sanda na fara kiransa da Magajin sarki fuskokin wasu daga cikin makusanta na ya nuna b'acin rai ni ban kira Aliyu da Magajina ba wai dan ya gaji kujerata Ali sunan surikina ne wato mahaifin Fulani ke kin sani itama ta sani wannan dalilin yasa nake kiransa da wannan suna na Magajin sarki."!


Uwar gida girgiza kanta ta shagayi kafin ta sauke ajiyar zuciya tace"Babu shakka mutum daya ne zai iya aikata wannan rashin imanin ba kowa bane sai Waziri shine makusancin ka wanda kafi aminta dashi shine kuma zai cutar da kai da zuriar ka Waziri bai ta'ba haihuwa ba tsayin shekarunsa wannan dalilin zai sa ya aikata mugun abu akan 'ya'yan 'yan uwansa sabida yana ba'kin cikin shi Allah be bashi haihuwa ba......


Cikin wani irin yanayi Maimartaba yake kallonta yana mamakin maganarta akan d'an uwansa mafi kusanci dashi wato Waziri." Ganin ya nuna alamun alhini yasa tace"Nasan dole za kayi mamakin maganata ranka ya dade kada kayi mamaki halin dan adam wallahi ko shakka ba nayi Waziri zai iya kashe Yarima saboda wannan dalilin dana fad'a maka.".


Maimartaba girgiza kansa yayi cikin yanayi na damuwa yace."Huwaila kada ki sake wannan maganar zargi bashi da kyau Waziri yana da kyawun zuciya na yarda ba zai cutar dani da zuria ta ba idan da wa'inda ya kamata a d'ora zargi a kansu to Ciroma da Galadima ne domin sune suka fito da hassadar su a kaina kada fa ki manta gwagwarmayar da nasha dasu a lokacin da Allah ya bani mulki nasha wahalarsu kafin su rabu dani nayi mulki cikin nutsuwa, Waziri kuwa tunda muke dashi bai ta'ba nuna min hassadar sa ba yana kaunata yana kuma kaunar zuria ta wannan al'amarin da ya faru yafi kowa damuwa bana zargin akwai saka hannun Waziri dangane da faruwar al'marin."


Huwaila shuru tayi bata sake tofawa ba, ta dauka mijin nata zai dauki maganarta babban burinta ta raba zumuncin dake tsakaninsa da dan uwansa Waziri saboda ta fahimci cewa Wazirin kamar shi yake hana Maimartaba ya kula da 'ya'yansa tunda ta lura da irin kaunar da yake wa Magajin sarki gabadaya taji ta tsane shi dan ita duk wanda zai kaunaci Fulani da d'anta to bata kaunarsa.




Magajin Sarki tare da Acp Mahmud a station, cikin nutsuwa suka gaisa da juna Acp yace.''Ranka ya dade ya kuma ji da faruwar wannan al'amari."? Ajiyar zuciya ya sauke yace.'' Sai godiyar Allah.'' Acp yace."Ranka ya dad'e wannan al'amari daya faru yayi mutukar girgiza mu mun shiga alhini da damuwa dangane da faruwar al'amarin dalili kuwa shine wannan asibitin naka asibiti ne mai mutukar muhimmanci a gurin al'ummar dake cikin wannan jaha mai albarka duka-duka asibitin bai kai rabin shekara da kafuwa ba amma ya kawo mana cigaban da bamu ta'ba tsammani ba, sai dai mace-macen da ake samu a asibitin yasa dukkaninmu jikin mu yayi sanyi dayawa daga cikin mutanan dake kwad'ayin zuwa asibitin domin a duba lafiyarsu tabbas nasan zasu tsorata su janye jikinsu domin tsira da ransu, ranka ya dad'e muna so kayi mana cikakken bayani akan dalilin daya sa ake samun wannan matsala a cikin asibitin ka." Acp ya 'kare maganarsa yana kallonsa.


Dago kanshi yayi da niyyar magana, dan jaridar dake tsaye ya matsa kusa dashi yana gyara masa abin magana, shi kuma Acp ya gyara biron hannunsa....Yana fara maganar ya fara rubutawa a jikin takardar dake gabanshi............A nuste yace."Acp Mahmud wannan al'amarin da yake ta faruwa sai nace maka family issue ina nufin abinda ya shafi cikin gidanmu . wannan al'amarin tunda na diro duniya yake faruwa dani bazan 'boye maka ba kuma bazan 'boyewa media ba al'amarin nan daga cikin gidanmu na sarauta yake fitowa, Acp a rayuwa ta banta'ba nufin wani da sharri ba amma ni kullum cikin 'kokarin so a ga bayana ake abin na damuna mutuka gaya."


Acp ya girgiza kanshi a nutse yace."Ranka ya dad'e Allah ya kare ka daga sharrin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login