Showing 123001 words to 126000 words out of 150413 words

Chapter 42 - Kwarya Tabi Kwarya Book Complet by Binta Umar Abbale .txt

zan wanke."




Cike da mamaki take kallonsa kafin tace"Aa babana ka bari dai a bawa hadimai su wanke ina kai ina wanki." dariya yay yace."Mamma menene ai ni ne na 'bata."


Murmushi tayi tana girgiza kanta, tace"Bari na dubata." kokarin mikewa take ya dakatar da ita ta hanyar fadin"Bari na dubata Mamma." Mikewa yay ya nufi toilet din.




Ina cikin cud'a jikina ya shigo, da sauri na sunkuyar da kaina na fara kokarin tsugunawa, a nutse ya karaso kusa dani! na jingina da bango ( garu) gabana na fad'uwa matsoni yayi sosai ya kar'bi sosan hannuna ya cigaba da cud'a min jiki.....a sanyaye nace"Dan Allah ka bari ka fita kada ka 'bata jikinka." girgiza min kai yayi yace."Gimbiya ai yau ranar kice ki bari kawai nayi miki hidima." shuru nai masa ya cigaba da goga soso a jikina yana watsa ruwa, ajiyar zuciya na sauke nace"to nagode sai ka bari nayi wankan tsarki ko." Ido jawur ya matsa gefe jikinsa dik ya 'baci da kumfar sabulu, yace."Kiyi maza kiyi ina jiranki."


Nasan halin nacin sa shiyasa banyi wata maganar ba na fara wankar tsarki kamar yanda addinin musulunci ya tanada.......Babban towel ya miko min. na kar'ba a nutse na daure jikina, ya miko min hijabina nasa, hannuna ya rike muka fito daga toilet din a tare, dakin babu kowa na kalleshi ya kalleni, a sanyaye nace"Ina Mamma."? Yana dan mirmushi yace."Ta fita da bedshirt dinki wai sai ta nunawa mutane kema cikakkiya ce." Kunya ce ta rufe ni nace"Wallahi banji dadin kiranta da kayi ba." Yace."My love kece kika tsaya gardama shiyasa na kirata ta taimaka miki." ajiyar zuciya na sauke na zauna gefan gado.....Vasillin ya dauko ya zauna kasan kafet a nutse ya fara shafa min, kallonsa kawai nake ina mamaki! wai yau shine ke shafa min mai! mikewa yayi ya bude wardrobe doguwar rigar shadda ya dauko min da pant da breziyya, yace."Kar'ba kisa ko na k'arasa ladana." Kar'ba nayi da sauri! ya juya ya sake nufar wardrb din kayansa ya dauko yana canzawa, damar dana samu kenan nayi saurin kimtsa jikina na zauna.........Yana gyara necktie d'in wuyansa yace." Zan dan shiga asibiti amma ba zan dad'e ba zan dawo ki kula da kanki kinji ko." Kaina na d'aga masa, yace." Wad'ancan magungunan nakan mirror ki daure kisha idan kinyi breakfast zasu taimaka miki." Nace"To nagode kai ba zaka tsaya kayi break din ba."


Agogon hannunsa ya duba yace."Babu lokaci sumayya akwai marasa lafiya sosai da nayi al'kawarin ganinsu a yau yanzu nasan idan naje zan samesu suna zaman jirana so kada ki damu zan samu coffee nasha a ofis."


Nace"To ko dai a kawo maka abinci." ? Girgiza kansa yayi yace." Nace miki zan dawo da wuri okey." binsa nai da kallo yace."Sai nadawo."' a sanyaye nace "Allah ya bada sa'a." da sauri ya bude kofa ya fita.........Na jima a dakin kafin na fita falo, suna zaune ganin fitowa ta suka mike tsaye gaisawa mukayi a hankali na zauna akan kujera, Mariya tace"Ranki ya dade a kawo miki kayan karin nan."? ina kokarin magana Jakadiyar Mamma ta shigo hannunta rike da wani madaidaicin kwando...........






*Na kudi ne*
Koda zaki ganshi a gruops na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abin yake vip gruop#600 normal gruop#300...account... 0542382124....Binta umar gtbank....idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:28 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
100
Koda ya fito daga toilet din kasa kallonsa nayi kaina a kasa har ya gama abinda yake yazo yana kokarin zama kusa dani nai saurin tashi da kokarin dauke bedshirt din da ya 'bata, ba tare da yace wani abu ba ya mike na janye bedshirt din na nufi toilet dashi raina duk a 'bace! koda na fito daga toilet din samunsa nayi har ya kwanta da alama ma bacci ya daukeshi, kayan bacci nasa na kwanta kan kujera tare da rufe jikina da hijabina! da kyar na samu bacci ya d'auke ni............Sai misalin shida shaura muka tashi dan nida shi bacci mukayi sosai sai dana bari tukkuna ya gama uzirinsa sannan na shiga toilet din a gurguje nai wanka na dauro alwala na fito na same shi yana kimtsawa, kauda kaina nayi daga kansa naje ina kokarin fito da kayana........."Sumayya." naji ya kira sunana, juyowa nai ina kallonsa, yace."Me yake damunki ne naga kin tashi cikin rashin walwala ko bakya jin dadi ne."? A nutse nace"Lafiyata lau kawai yanayin rayuwa ne." karasowa yayi inda nake tsaye ya rike kuguna tare da dora kansa a kafadata yace."My love ban yarda ba akwai abinda ke damunki please kada kisa na fita cikin damuwa." Dan tureshi nayi na bar gurin........Kallon mamaki! ya bita dashi kafin ya girgiza kansa, cigaba yayi da shirye-shiryensa ba tare daya sake kulata ba......Kimtsa jikina nayi nasa hijabi na tayar da sallah, ina kokarin sallama ya fice daga dakin, ajiyar zuciya na sauke ina bin kofar da kallo, abin ne yake bani mamaki da haushi! da gaske dai mutumin nan baya son haihuwa tunda gashi nan duk wasu matakan hana haihuwar ya dauka wato idan shi bukatarsa zata biya gurin sex bashi da damuwa wannan al'amarin akwai cutarwa a ciki (Tsarin iyali ne na musulunci wanda Annabi Muhammad SAW ya koyar amma kuma yin hakan baya hana haihuwa idan rabo ya rantse komai tsantsenin mutum sai ciki ya shiga....Sannan kuma ta wani 'bangaran hakan na ragewa ma'aurata jin dadinsu misali idan namiji yazo zaiyi release dole zai fita daga cikin ramin hakan zai rage masa jin dadin ta 'bangaran mace kuwa idan baki da saurin kawowa namiji na samun satisfied zai barki da wahala wani namijin idan ya kawo sau daya shikkenan ya gama duk abinda zakiyi masa ba zai sake tashi ba, kamar dai Yarima yana da kar'fin sha'awa amma kuma baya dogon zango yake gamsuwa kuma idan yayi sau d'aya baya 'karawa! ita kuma Sumayya tana da nisa sosai tana bukatar dogon zango kafin ta gamsu gashi an samu matsala ta 'bagaransa a lokacin da take kan ganiyar jin dadinta a lokacin shi kuma yake gamsuwa kuma saboda gudun haihuwa ya cire jikinsa ya barta da wahala, duk da bata san kan al'amarin sosai ba ta tabbatar da cewa akwai cutuwa a ciki dole ne ta nemawa kanta mafita tun kafin tafiya tai nisa.................Ta jima tana tunane-tunane kafin ta mike jiki a sanyaye ta fita falo ba tare data cire hijabin jikinta ba.




To koda ya dawo da daddare ma sabgar gabansa yayi ya fita ba tare da ya tanka mata ba ta lura yaji haushin abinda tayi masa d'azu shine dalilin da yasa yayi watsi da ita da al'amarinta......Sai da tayi bacci ya shigo dan yana can tare da Shatima suna hira, wanka yayi yasa kananun kaya na bacci ya kwanta kusa da ita.




Kwanciyarsa a kusa dani yasa na bud'e idona jikina na janye ina addua akan Allah yasa kada ya nemi wani abu, kafin ma na gama tunani naji shi a jikina yana shafa wuyana shiru nai masa ina ji yana kesses din baya yana sake matseni a jikinsa, na dinga jin wani irin yanayi a jikina, janyewa nayi, ya mike zaune rai a b'ace! yace."Wai meye hakane? kina abu sai kace 'Yar kauye."




Shuru nayi yace."Kin san duk fushin da kike ba zai hanani biyan bukatata ba me nayi miki tun safe kike fushi na tambayeki dalili kince babu komai."




Uffan bance masa ba, ya koma ya kwanta tare da birkitoni kansa, ringume ni yayi tsam! yana kokarin sa bakinsa a nawa, yanda yake min yasa gabadaya sha'awata ta tashi, jikina ya mutu na kyaleshi yana ta juya ni yanda ransa keso.




Banji zafi sosai ba kasancewar ina da bukatar al'amarin yasa na sakar masa jikina gabad'aya muka fita cikin hayyacinmu yauma kamar jiya yana jin zaiyi release yayi yunkurin cirewa hanashi nai na rikeshi jikina sai rawa yake ni kadai nasan irin halin da nake ciki! da karfi ya fizge jikinsa kan cinyata ya zubar da sperm din. Ya wani kwanta a kaina yana sakin nishi! takaici yasa wasu zafafan hawaye suka kwaranyo min, hannu nasa da sauri na goge na shiga turesa daga jikina.




Ba tare da wata damuwa ba ya mike ya nufi toilet, mikewa zaune nai ina duba jikina da duk ya 'bata min wannan wace irin rayuwa ce sai kace wanda yake auratayya da karuwa! karuwai ne ba'a san haihuwa dasu ake zuba musu sperm a jiki amma matar sinna a dinga yin wata irin mu'amula da ita irin ta yahudawa." Kuka ne yake kokarin kufce mata tana kokarin danneshi...........Yana fitowa daga toilet din ya kimtsa jikinsa yazo yana kokarin kwanciya bedshirt din yake turewa dan a tunaninsa shima ya 'baci! Mikewa nai na bar masa gurin, wanka nayi na fito na kimtsa jikina kujera na nema na kwanta zuciyata na wani irin zafi!




"Sumayya."! naji ya kira sunana murya a sama! shuru nai masa.


Yace." Wane irin abune wannan kika tsiro dashi zaki bar gado kije kujera ki kwanta.'' ? kamar da dutse yake magana, A fusace! ya mike zaune tare da kunna bedlamp yana kallon inda take kwance.


"Bakya ji ne ina miki magana."? murya a cunkushe nace" Ina ji.'' yace."Okey to ki dawo ki kwanta kusa dani." da sauri nace"Dan Allah ka rabu dani nai kwanciyata anan dan banga amfanin kwanciya a kusa da kai ba.''




Shuru yayi na mintu biyu kafin ya d'aga kafad'a alamun rashin damuwa bedlamp din ya kashe ya koma ya kwanta tare da rufe jikinsa da bargo, bacci mai nauyi ne ya daukeshi ni kam sai can dare na samu da kyar bacci ya dauke ni.


Kasancewar na jima banyi bacci ba yasa yau ma na makara, lokacin dana tashi har ya gama shirinsa yana zaune gefan gado yana gyara igiyar takalminsa kallonsa nai ina mamakin dalilin daya sa bai tasheni nayi sallah akan lokaci ba, yanayin fuskarsa yasa na gane akwai matsala.
Ba tare da nace masa komai na na mike a sanyaye na shiga band'aki......koda na fito samun dakin nai babu shi ya fita ba tare da ya tsaya mun gaisa ba dama baya wani damuwa dayin break haka yake ficewarsa sai yaje ofis din yake kiran mahaifiyarsa ta tura masa da abinci.....a rabar yini nayi cikin tsananin damuwa da tashin hankali na dinga tunanin hanyar da zanbi na warware wannan gagarimar matsalar da nake fuskanta.............Har dare ya shigo gari yay shuru idona biyu ina tsammanin sa bai shigo bai kuma kira waya ba, da dai na gaji shirin kwanciya nai na rufe kofa na kwanta da wayata a hannuna, karfe goma da rabi na dare na nemo number sa.....Lokacin yana kokarin shiga gurin Lawisa yaga kiran wayarta, dauka yayi babu yabo babu fallasa ya amsa gaisuwarta.




Ajiyar zuciya na sauke nace"Baka dawo bane.''? kai tsaye yace."Yanzu na shigo yau aiki ya ri'ke ni ina fatan kin wuni lafiya." nace"Lafiya lau.'' yace."To masha Allah sai da safe." kafin nace wani abu ya kashe wayarsa.


A sanyaye na kashe wayar tare da ajiyeta a kan bedside naja bargo na rufe jikina ina addua a cikin zuciyata.




Gajiya da wahala basa hanashi fitina koda yaci abinci ya gama komai na rayuwarsa zuwa yayi ya zauna kusa da ita....Lawisa ta mike zaune tana kallonsa, babu fara'a a fuskarsa ya mi'ka mata magani da goran ruwa. a sanyaye ta kar'ba ta watsa a bakinta ta kora da ruwa.




Goran ruwan ya kar'ba ya ajiye ya hau gadon sosai janyota yayi jikinsa yana sa hannunsa a cikin rigarta Lawisa ajiyar zuciya ta sauke ta sakar masa jikinta sosai suka shiga biyawa junansu bukata.




Washe gari da safe ita dashi cikin walwala suka rabu yana jin dadin mu'amula da ita saboda tabi ra'ayinsa da dokokinsa shiyasa yake jimawa akanta yana dogon zango kuma baya fargabar zubar da sperm dinsa a jikinta domin yana da tabbacin ba zata dauki ciki ba, sa'banin Sumayya da idan yana sex da ita yake fargaba sam baya sakin jikinsa saboda gudun abinda ka iya zuwa ya dawo yana jin zai kawo yake gaggawar cire jikinsa.....Ya fahimci cewa hakan na 'bata mata rai! ita da kanta ta nemi hakan tunda babu yanda baiyi da ita ba akan tabi ra'ayinsa taqi dama sai da ya gargadeta kacewar duk abinda ya biyo baya kada tayi kuka dashi tai kuka da kanta.




Cikin rashin walwala ya shiga gurinta, ko zama bai ba yana tsaye suka gaisa ya juya ya fita ba tare da ya nuna mata wata cikakkiyar kulawa ba.


Kuka sosai tayi a ranar kafin ta yanke shawarar tunkararsa da maganar gwara suyi wacce zasuyi ta gaji da irin wannan zaman da suke mara dadi da ma'ana.




Koda ya dawo guri nata kunya da nauyi yasa ta kasa tunkararsa da maganar duk dare haka zai danneta ya biya bukatarsa ba tare da ya damu da tata bukatar ba.






*******
*BAYAN WATA BIYAR*
Rayuwar dai da suke sai kara tsanani take Sumayya ta shiga cikin wani irin hali na damuwa da bukatuwa yayinda ta 'bangaransa yake gudanar da harkokinsa na yau da gobe ba tare da ya bawa damuwarta mahimanci ba, duk da yasan abinda ke damunta yana saka ta kuka a koda yaushe hakan bai sa ya sauka daga kan ra'ayinsa ba koda yaushe idan bukatarsa tazo zaije gurinta ya biya bukatarsa ya barta cikin matsananciyar sha'awa, lokaci guda ta shiga rama yayinda Lawisa ke 'kara cika tana bunkasa da wata irin 'kiba mara kyau! hakan bai dameshi ba saboda yasan magungunan da take shane suka hura ta yanzu zaman lafiya suke sosai a tsakaninsu ya daina yi mata wulakanci kamar lokotan baya.






Cikin shirin fita ya shiga ya sameni a kwance a gado kwana biyu duk na rasa gane abinda ke damuna kullum da zazzabi nake kwana ga yawan fitsari da nake, shigowarsa tasa na mike zaune.


Nace"Ka zauna mana mu gaisa." girgiza kansa yayi yana duba agogon hannunsa yace."Babu lokacin zama ina fata kin tashi lafiya.''?




'Dan ya mutsa fuska nayi nace"Lafiya lau zazzabi ne dai yake damuna kwana biyu kullum dashi nake kwana."




Tsira mata ido yayi na tsayin minti uku! da sauri yace."Dago ki kalleni." da sauri na kalleshi jin yanda ya fadi maganar! 'Kwayoyin idona ya tsirawa ido kafin ya wani murtuke fuska yace"Bude min tafin hannuwanki." Bud'e masa nayi ya shiga dubawa......."Sumayya watan ki nawa rabonki da al'ada."? gabana ne ya fad'i nace"Wata biyu da kwanaki."


Cikin tsawa! yace."Kin san da haka me yasa baki min magana tun wuri ba." nace"Wai duk me ya jawo wannan hayaniyar ne ciki ne dani ai kai baka isa ka hana Allah ikonsa ba duk dubarar ka kuwa."


Mari ya kwad'a min a zafafe! yace." Ni kike fad'awa wannan maganar." mikewa nai hannuna dafe da kuncina nace" Gaskiya d'aci gareta kai kuma baka so a fada maka dan ka mareni ba zan damu ba kuma insha Allahu komai abinka sai na haife cikin nan."




Zuciyarsa ta dinga tafarfasa yana ji kamar ya zare blet yayi mata dukan tsiya ashe dai yarinyar nan da gaske so take ta rugaza masa tsari! 'kwafa yayi ya kwashi wayoyinsa a fusace! yace."Mutukar kina bukatar zaman lafiya dani sai kin yarda da umarnina idan ba hakaba sai na wulakantaki."


Cikin dauriya nace"Duk abinda za kayi min a shirye nake dama ai na saba da wulakancinka ni ba zaka had'a kai dani gurin sa'bon Allah ba."


Kansa ya girgiza ba tare da ya sake magana ba ya fita daga dakin kamar zai tashi sama.


Tunda daga ranar ya dauke min wuta ya daina shiga sabgata koda a gurina yake baya ta'ba yarda muyi mu'amular arziki fuskarsa kullum a daure idan na gaishe ya amsa a dakile abincina kuwa inda na ajiye anan zan dauki abuna, gabad'aya ma ya daina kusantata yayi tsayin sati hud'u muna cikin wannan hali gashi kullum cikin ciwo nake babu ruwansa dani da lafiyata, ina kuka na sameshi yana shirin fita nace"Wai kai dan Allah baka da imani ne? me nayi maka kake azabtar dani haka? cikin nan fa bani na bawa kaina ba Allah ne ya bani me yasa kake gudun rahamar Allah? dubbanin mutane nacan na nema kai Allah ya za'be ka a cikinsu ya baka kana nema ka butulce masa kaji tsoron Ubangiji ka kar'bi kyautar daya baka watakilama shi kadai zaka haifa a duniya."


Hannu ya daga min ya juyo cikin shan toka yace."Sumayya ke kika zalinci kanki ciki kuma na bar miki kije ki haihu amma babu ruwana dashi."


Nace"Bangane babu ruwanka dashi kayi cikin kace ka bar min wannan wace irin magana ce." !?


Cikin wani irin yanayi yace."Sanin kanki ne bana zubar da k'wayoyin haihuwata a mahaifarki wannan dalilin yasa nace miki kije duk inda zaki da cikin ki."


Cikin fitar hayyaci nace"Aikuwa zani duk inda zani dashi zanje na shedawa Mammah duk halin da ake ciki nasan ita din cikakkiyar musulma ce ba zata yarda da wannan yahudancin ba."


Cikin tsantsar 'bacin rai yace."Sumayya kada ki fasa zuwa gurin Mamma da maganar nan wallahi kikaje kika tayar mata da hankali

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login