Showing 108001 words to 111000 words out of 150413 words

Chapter 37 - Kwarya Tabi Kwarya Book Complet by Binta Umar Abbale .txt

na munafukai ne."
Murmushi yayi yace."Shiyasa ai nake kallonta ita da yaran nata nasan dukkaninsu ba kaunata suke ba kome suke na ganin idone idan babu idona a gurin Allah ne kadai yasan sharrin da suke shirya mun."


Shatima yace."Addua zaka dage dayi ka kuma dinga azkar safe da dare insha Allah duk wanda ya nufe ka da sharri zai koma kansa." A hankali yace."Ina godiya dan uwa insha Allahu zan kula da shawarwarin ka."


Kai tsaye sashen mahaifiyarsa suka nufa, suka sameta ita da Maimartaba a falon suna tattauna abinda ya shafe su, cikin girmamawa suka gaishe su Maimartaba ya dinga kallonsu yana jin dadi da farin ciki a zuciyarsa, addua mai kyau yayi musu ya kuma yi musu nasiha mai ratsa jiki itama Fulani ta d'ora ta tace"Dukkaninku yanzu wani nauyi na mussaman ya hau kanku mussaman kai Babana ka kula sosai kayi adalci a tsakanin matanka Allah yayi muku albarka ya sanya alkairi a cikin zamantakewar auranku." Gabad'aya suka amsa da "ameeen." suna kokarin mikewa tace"Babana na manta ban fada maka ba Sumayya na can gurin iyayenta na tura ta suyi sallama da juna watakila ma a can zata kwana."
Jim yayi kafin yace."to shikkenan Mamma babu damuwa ai." Maimartaba yace."Gobe da safe sai kaje ku gaisa da iyayen nata daga nan sai ku tawo da ita." Yace."To ranka ya dad'e Allah ya kaimu lafiya." suka amsa da ameeen.'' sallama sukayi musu suka fita koda suka fita din basu jima a a tare ba sukayi sallama da junansu kowanne ya nufi sashensa, Magajin sarki zama yayi a falonsa yana jin takaicin abinda Sumayya ke masa tunda suka samu sa'bani kwanakin da suka gabata ya dauki fushi da ita bata ta'ba bashi hakuri ba, idan ta gaishe shi shikkenan sai ta fita sabgarsa ko kiransa a waya ba tayi kawai sabgar gabanta takeyi tana nuna tamkar bata damu dashi ba! abin yana bashi mamaki mutuka a ganinsa shine yake sama da ita koda shine bashi da gaskiya tunda itace a kasa dashi ita zata bashi hakuri amma saboda ta dauki kanta wata mai matsayi ta'ki kallonsa da mutunci dole ya nuna mata shi ba tsaranta bane tunda dai an riga an daura aure zata gane bata da wayo tsarinsa kuwa dole tabi ko tana so ko bata so.
Wanka yayi yasa kananun kaya ya sauko kasa da wayarsa a hannunsa Lawisa ya kira domin tazo ta d'ebe masa kewa aikuwa ko minti ashirin ba'ayi ba ta shigo cikin ado har yafi na dazu! kusa dashi ta zauna tana kwarkwasa kamshin turaranta ya kashe masa jiki hannunta ya rike yana mata wani irin kallo yace."Muje sama ko."? kanta ta daga masa ya mike tare da ita, kugunta ya rike ta sosai tare da manneta jikinsa suka nufi saman rungume da juna.


Bangaran Sumayya kuwa tana cikin farin ciki da annushuwa tana tare da iyayenta sai walwala sukeyi sai dai a duk sanda ta tuna da mutumin nata gabanta sai ya fadi! tana tunanin irin bahaguwar rayuwar da zasuyi ita dashi tunda dai ita tayi rantsuwa akan cewar ba zata amince da tsarinsa ba shi kuma ya tabbatar mata da cewa dole tana karkashinsa tayi masa biyayya mutukar tana bukatar zaman lafiya dashi inda ita kuma take ganin babu yanda za'ayi ya sata ta kauce hanya ba za tayi tsarin iyali ba sai dai shi yaje yayi tsarin iyalin amma ita ba zata cutar da kanta ba......Wannan dalilin yasa gabadaya ta kasa sakin jikinta dashi domun tana so ta nuna masa cewar har yanzu fa tana nan akan ra'ayin ta babu gudu babu ja da baya idan Lawisa tana iya yi taje tayi amma itakam bata da ra'ayi.




Magajin sarki da Lawisa soyayya sukayi sosai kafin kuma ya rabata da budurcinta sai da ya bata kwayoyi tasha tukkuna suka cigaba da gudanar da abinda suke a daran ya kar'bi sadakinsa alhamdullh kwalliya tabiya kudin sabulu dan yaji dadin kasancewarsa da ita bukatarsa ta biya ya dinga alfahari da ita shine yayi mata wanka ya gasa mata jikinta tsaf suka fito daga toilet din a tare, kayanta ta mayar a sanyaye take kallonsa yace."Kada ki damu nasan abinda kike tunani! sunkuyar da kanta tayi yace." Kinzo dakin ki kenan ba zaki koma ba kuma inaso na sheda miki cewa na sameki cikakkiyar mace ina alfahari dake." ajiyar zuciya ta sauke tana kallon bedshirt din daya 'baci da jini! tace."Wannan zanin gadon zaka sa a leda nasan da safe Hajiya zata aiko a kar'ba.'' yace."Lawisa wannan tsohuwar al'adace bana san tonan asiri wallahi." cikin alfahari tace"Ni dai gwara kowa ya gani ya sheda na kawo mutuncina." yace."To babu damuwa." bedshirt din ya cire yace'' kar'bi abinki kisa a leda ki daure." da sauri ta kar'ba! wardrobe dinsa ya nufa can kasa ya dauko sabon zanin gado ya fara kokarin shimfidawa, karba tayi suka shimfida a tare, kwanciya yayi yana kallonta gaskiya yaji dadinta sosai gata da ni'ima ta kowanne fanni tayi ta burgshi lumshe ido yayi yana tunanin irin ni'imar da zai kwasa gurin Sumayya.






Hajiya Karima sashe sashe ta dinga bi tana nuna zanin gadon amarcin Lawisa Jakadiyarta sai rangwada buda take tana fadin"Yarinyar arziki ta cika mace ta kai mutuncinta dakin mijinta! Hajiya Karima ta kalli Fulani cikin farin ciki tace"Fulani inaso ki ajiye wannan zanin gadon idan Maimartaba ya shigo sai ki nuna masa." Fulani na kokarin magana na shigo tare da sallama! gabadaya suka amsa min Hajiya Karima ta wani dauke kanta tana girgiza kafa, a nutse na zauna kusa da ita nace"Mamma barka da asubah." tace"Barka dai Sumayya ya kika baro iyayen naki."? nace"Suna nan lafiya lau sunce suna gaisheki da kyau." tana murmushi ta amsa, ta cigaba da cewa"Tare kuke da babana ne."? girgiza kaina nayi alamun A'a, tana kokarin magana Hajiya Karima ta katseta da fadin" In banda abinki Fulani ina za'a ga Magajin sarki yana can tare da yarinyar arziki aini nayi alfahari da faruwar wannan abu.''


Fulani rai a 'bace! tace"Hajiya Karima maganar nan ta isa haka na sheda na tabbatar Lawisa takai matuncinta dakin mijinta amma banga ammafanin nunawa Maimartaba zanin gado ba ki tafi dashi gurunki.".
Hajiya Karima tace"Aikuwa dole a nuna masa ya sani yarinyarsa yar arziki ce idan ke ba zaki nuna masa ba zan kaiwa Huwaila ta nuna masa." Tana gama maganarta ta mike a fusace! Jakadiyarta tabi bayanta tana rangwad'a bud'a!
Jikina ne yayi sanyi na riga na fahimci abinda keda akwai har yaushe Lawisa ta tare a d'akinta wata Mu'amular aure ta shiga tsakaninsu! wani irin kishi mai zafi ya tokare min kirjina! Muryata ce ta dawo dani nutsuwata. shuru nayi dan banda abinda zance akan al'amarin, ta cigaba da cewa"Kiyi hakuri da duk abinda zaki gani kinji ko ki zauna lafiya da Lawisa kada ki dauketa a matsayin kishiyarki 'yar uwarki ce duk sharrin da za tayi miki ke kiyi mata alkairi Allah zai kare ki daga sharrinta! a sanyaye nace"Insha Allah Mamma." Tana kokarin magana suka shigo a tare, Sunyi ado na sarauta ita dashi sunyi kyau sosai! Mamma sakin fuskarta tayi tana amsa sallamarsu, ni kam gabana ne ya dinga faduwa ina mamakin sharrin d'a namiji har yaushe suka shirya suka daina fad'a da juna! shakuwar su ta bani tsoro tamkar masoyan da suka shekara dubu suna soyayya, gabadaya ji nayi na tsargi kaina, na kasa dago kaina na kallesu ina ji suna magana da Mamma amma fargabar kallonsu nake sabida bana son yayi min kallon wulakancin daya saba." Sai kawai na yanke shawarar barin gurin domin ina ganin kamar hakan shine ya dacewa dani.


"A'a Sumayya ya zaki tashi kuma ana hira ni banga ma kun gaisa da junanku ba."! Dauriya na aro nace" Mamma zanje na kwanta ne wallahi duk na gaji." Lawisar na kalla nace"Ranki ya dade barka da safiya." a takaici ta amsa da "barka dai." na kalleshi tare da daure fuskata nace"Ranka ya dade barka asuba." Da d'an murmushi a fuskarsa ya amsa da "Barka dai gimbiya." kallonsa nayi ina mamakin murmushinsa A gaskiya mutumin nan shu'umi ne baka ta'ba gane inda ya dosa wai harda kirana gimbiya. gurin na bari ina mamakin sauyawarsa....








*Na kudi ne*
Kada ki karanta min littafi baki biya ba, keda kika futa da littafin keda Allah! idan kina so ki biya ga yanda abin yake....Vip gruop#600 normal gruop#300....account... 0542382124...Binta umar gtbank....idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:28 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
93
Koda na shiga dakin kasa aikata komai nayi nai zaune a gefan gado tare zabga tagumi ina mamakin abubuwan da suke faruwa, al'amarin Magajin sarki da Lawisa ya tsaya min a raina mutuka na dinga mamakin sanda suka shirya tsakaninsu, dan ganinsu a yanzu yasa na fahimci a kwai k'auna a tsa'kaninsu, " Watakila ita din ta amince da tsarinsa shine dalilin da yasa kika ga sun hade kansu." zuciyata ce ke fada min haka..... gaskiya kam da akwai alamar haka dan da bata amince da bukatarsa to da ba zasu samu jituwa irin haka ba girgixa kaina nayi ina mamakin wauta da rashin dubara irin nata gaskiya idan da gaske ha sashena ya tabbata gaskiya ne to gaskiya tayi wauta! a maimakon ta bari taga ta haihu kafin ta amince masa kawai saboda tana jin tsoron 'bacin ransa ta cutar da kanta('Kalubale ga matan dake yin tsarin iyali bai tare da sun tabbatar suna haihuwa ko basa haihuwa ba kawai kiga mace saboda rashin wayo ta biyewa miji saboda so yayi ta dibga mata kwayoyi daga karshe ciwo ya hanaki haihuwa shi kuma yaje ya auro wata babu abinda ya dame shi mata muyi hattara) ajiyar zuciya na sauke ina sake mamakin al'amarin, ni kam duk rintsi ba zan amince da wannan tsarin ba...........Shigowarsa dakin ce tasa na saurin kallon bakin kofa, ya mayar da kofar ya rufe dakin, a nutse ya karaso inda nake, tsayuwa yayi a kaina yayi min rumfa, na dago kaina ina kallonsa sai naga fuskarsa a sake sa'banin kwanaki........"Ka zauna mana." nafada ina nuna masa gefena." murmushi yayi yace."Kin bani ikon zama kenan."? shuru nayi masa, ya zauna inda na nuna masa, zamana na gyara ina kallonsa. ya kai hannu zai tsokane min ido nayi gaggawar dauke fuskata , yace."Tun a falo kike kallona ko na sanja miki ne."? girgiza kaina nayi nace"A'a ina mamakin halinka ne." Dan bata fuska yayi yace."Wane irin hali ne dani."? shuru nai, ya kamo hannuna na dama yana duba lallen da'a ka zana min." a baki yasa yana tsotsa! tsigar jikina ce ta tashi da sauri na janye yatsuna ina kallon gefe guda
Matsoni yayi sosai cikin taushin murya yace."Kin samu Labarin tarewar,Lawisa ko." shuru nayi gabana na bugawa kusancina dashi yasa naji wani irin bakon yanayi yana ziyartata! wuyana ya sumbata "Mylov."


A sanyaye na kalleshi dan gabadaya jikina ya mutu saboda abubuwan da yake min.
'Kan'kance ido yayi yace."Yaushe ne zaki tare a naki dakin." ? dan janye jikina nayi nace" Nima ban sani ba." shuru yayi yana cigaba da ya mutsa min jiki. "Dan Allah ka bari." nafad'i maganar can kasan makoshi! Yace."Wannan kamshin dake jikinki nake so." Fuskarsa na ture na mike daga gurin, jikin mudubi na jingina ina kallonsa gabadaya sha'awa nake ji a jikina duk na rasa yanda zanyi ban'taba riskar kaina cikin irin wannan yanayin ba sai a wannan lokacin. daf dani ya tsaya hucin numfashinsa na sauke a fuskata, kauda kaina nayi cikin damuwa nace"Dan Allah ka fita." fuskata ya tallafo da hannayensa yace."Ba zan fita ba sai nasha bakinki." da sauri na kalleshi gira ya daga min yana kokarin kamo bakina da nasa, yun'kurin barin gurin nayi ya matseni jikin mirror kayan shafar dake jere a kai suka zubo kasa, bakina yasa a nasa ya shiga tsotsa yana shashshafa jikina, kasa hanashi nayi kawai na tsinci kaina da lumshe ido sosai nake jin dadin abinda ke faruwa a tsakaninmu......Ido jawur ya kalleni yace."Da dadi ko."? gurin na bari da sauri ya biyo ni ya zauna kusa dani, hannuna ya rike ya kira Sunana, kallonsa nayi ina kokarin daidaita nutsuwata yace."Ina fatan kin shirya zama dani da ra'ayina." gabana ya fadi nace"Ban fahimci maganarka ba." yanayinsa ya gyara babu wasa a tare dashi yace." Kin manta maganar mu ta kwanaki kenan."! ta'be bakina nayi nace"Gaskiya na manta."


Ya shiga girgiza kai yana kallon kasan kafet, yace." Nasan kawai kin fadi hakane ba wai dan kin manta da maganata ba to inaso na kara tuna miki cewa "Ni Ali ina nan kan ra'ayina koda zaku haihu ba yanzu ba tukkuna sai na gama morewa."




Kai tsaye nace"Idan Allah ya kawo haihuwar kuma ya zakayi."? "Allah ba zai kawo ba insha Allahu ina da matakan Kariya." mirmushin takaici nayi nace"Kada kayi mamaki da hukuncin ubangiji duk dabarunka idan ya zartar da ikonsa babu yanda za kayi.''


Hannu ya daga min yana kallona da wata irin fuska. dauke kaina nayi daga barin kallonsa, rai a bace ya mike ya fita, tsaki naja a fili nace"Wallahi ba zan yarda da wannan yahudancin ba sai dai duk abinda za'ayi ayi.




A daran ranar Mamma ta shiryani sosai kana ta kama hannuna ta kaini har dakina kafin kuma tayi min sallama sai da ta jima sosai dani tana min nasiha kuka sosai nayi da kyar! na bari ta tafi yanda na lura itama tana alhinin rabuwa dani daurewa kawai takeyi.......haka na kasance tsayin dare ni kadai a daki ba tare da ya shigo gurina ba har garin Allah ya waye! sosai nayi mamakin lamarin wato fushi yake akan abinda ya faru tsakanina dashi, idan kuwa hakane zai dade yana fushi dani sai dai idan ya gaji ya daina dan bazan yarda ya cutar dani ba.


Wanka nayi tsaf na shirya jikina na fito falo nan na samu sabbin hadimai suna ta goge goge zubewa sukayi suna gaishe ni, na amsa cikin sakin fuska, zama nayi kan kujera duk suka tsuguna a gabana nace"Ya sunanku.'"?


"Ni sunana Mariya"
"Sunana Sakina"
"Ni kuma Sunana Sadiya."


Nace"To ina so ku zauna dani tsakani da Allah dan Allah ku rike amana da gaskiya kuma kada ku bari a cutar da wani ta hanyarku''


Suka ce "Insha Allahu zamu kula." Mariya tace"Ko a kawo miki abin karin kummalo nan."? girgiza kaina nayi nace"Barshi zan karasa dainng din.'' godiya sukayi nace"Kuje ku cigaba da aikin ku." Gabad'aya suka mi'ke da sauri suka bar gurin, waya ta nake dubawa text dinsa ya shigo, da sauri na duba.


_"Ina fata kin tashi lafiya."?_


Abinda ya rubuta kenan, kamar na bashi amsa sai kuma na kyaleshi idan so yake ya tabbatar da lafiya ta ai yasan inda nake, mikewa nayi da wayar a hannuna na nufi gurin cin abincin.






'Bangaran Yarima kuwa yana can gurin Lawisa yana cin amarcinsa so yake ya nuna wa Sumayya kuranta a ganinsa wannan halin ko'in kular da yake nuna mata zai sanya tayi laushi tabi ra'ayinsa, gabadaya ya manta da cewar Sumayya mai taurin kai ce akan Gaskiya ba kuma ta munafurci shi ya kamata ya fad'awa kowa halinta amma ya manta halinta yake tunkarar ta da abinda shi kansa yasan ba mai kyau bane.


Ina kokarin barin daining ya shigo cikin jallabiya milk kallo daya nayi masa na kauda kaina, cigaba nayi da duba wayar hannuna, tsayuwa yayi a kaina yana fadin"Salamu alaikum." a nutse na dago kaina na amsa da "Wa'alaikassalam." Dan ta'be baki yayi yace."Ya kike."? share shi nayi dan naji ciwon abin.'"


"Sumayya." dagowa nayi muka hada ido. yace."Kina ji ina gaisheki kinyi shuru."


"Wace irin gaisuwa ce.'' nafada da rashin walwala." Mirmushi yayi yaja kujera yana kallona, nace"Barka da asubah.'' hankalinsa kan tea din dake gabana ya amsa, cup din tea din ya dauka yana sha, nace"Ka bari na hada maka wani mana." girgiza min kai yayi sunkuyar da kaina nayi ina dube dube a waya.


"Sumayya." dagowa nai ina kallonsa da mamakin yanda yake kiran sunana kamar shi ya rad'a min."


"Na'am." na amsa cikin rashin walwala, yace." Ba kiga text dina ba." shuru nayi yace."Ko bakya ji ne."?


"Na ganshi." nafada kaina a kasa..."Okey kin gani me ya hanaki bani amsa ko ban isa ba."?


Girgiza kaina nayi nace"Ka isa har kayi yawa kawai ban samu lokacin baka amsa ba ne."


Tsira min ido yayi yana kallona, yace."Baki da lokacin kirana a waya sannan baki da lokacin amsa min text ko."? mirmushin takaici nayi nace"Wai baka san inda nake ba meye na damuwa yanzu gashi ai kazo ka duba ni."


Shuru yayi ya cigaba da kur'bar tea d'in, mikewa nake kokarin yi yace."Kada ki tashi ina da magana dake." gabana ne ya fadi na koma na zauna.
Cup din ya ajiye ya tsira min ido.....ni kam wannan jarababban kallon nasa na damuna, nace."Ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login