Showing 15001 words to 18000 words out of 150413 words

Chapter 6 - Kwarya Tabi Kwarya Book Complet by Binta Umar Abbale .txt

ki da cewar kiyi biyayya kamar yanda kika ga munayi a matsayin mu na iyayenki."


Muryata na rawa nace"Baba dan Allah ka daina maganar mutuwa insha Allahu zaka tashi ka cigaba da sabgogin ka cuta ba mutuwa bace." Murmushi yay yace."Sumayya kenan to ina rokon ubangiji Allah ya tashi kafad'una na cigaba da rayuwa a tare daku.'"
murya na rawa nace"ameen baba Allah ya baka lafiya." amsawa sukayi da "ameen" na mike na fita domin wanke hannuna.


Lokacin dana shiga dakin Tambaya na kokarin mikar dashi zaune domin ta d'aura masa alwala taimaka mata nayi mukayi masa alwalar ta gyara shi sosai yanda zaiji dadin sallah ya tayar da iqama a nutse! kallona tayi tace"Kiyi maza ka tafi mana." Sai Naji zuciyata ta karye tunda na taso ban ta'ba zuwa ko'ina na kwana ba kullum ina tare da iyayena
A sanyaye na juya ina goge hawaye da hannuna nace"Na tafi." Itama tambayan cikin alhini tace"Sai da safe." Jin kuka naso ya kufce min yasa nayi gaggawar fita daga dakin, takalmana dake bakin kofar dakin na zura na fita daga gidan.




Haruna da su Isa na samu a falon suna aikace aikace, gaisawa mukayi na nemi kan kujera na zauna ina rarraba idona a katafaran falon nashi daya gaji da had'uwa, ko wace kusurwa hotonshi ne a manne wani da manyan kaya na sarauta wani kuma da 'kananun kaya cikin hotonan nasa babu wanda yayi dariya a ciki fuska a murtuke tamkar wanda akayiwa dole gurin daukar hoton, muryar Haruna ce ta katse min tunanin da nake, na kalleshi inaso ya sake maimaita min abinda yake fad'a, Yace."Sumayya ba zama zakiyi ba zaki hau sama ne ki bubbuga idan ya bude sai ki sheda masa isowarki idan da akwai abinda yake bukata kiyi masa sai kiyi mu dai mun gama aikin mu zamuje mu huta sai ya b'ukace mu.'' Na kalleshi da fadin"Ina ne d'akin nasa."
Wata matattakalar bene ya nuna min da fadin''Kina kaiwa karshen benan za kiga wata kofa mai biyu nan ne d'akinsa sai ki danna wani abu a jikin kofar zai yi magana.


Nayi shuru ina sa'ke-sa'ke mi'kewa nayi na kama hanyar benan, da k'yar nake hawa benan sabida santsin ties d'in ina hawa ina ri'ke sandar benan gabana na fad'uwa! ajiyar zuciya na ajiye bayan na gani a kofar dakin
Sai da na daidaita nutsuwa ta tukkuna na danna abinda zai isar masa da isowata. shuru ba'ayi magana ba, nasa hannu akan abun na latsa da kar'fi! Naji muryarsa yana fad'in "Wanene." "Nice Sumayya.'' Murya a hard'e na fadi maganar. shuru har tsayin mintina goma bai bude ba jikina yayi sanyi kamar nayi tafiya ta sai dai na daure na cigaba da tsayuwa, motsin bude kofar naji nayi saurin ja gefe tare dayin kasa da kaina, koda ya bude kofar ban kalleshi ba nace" Barka da dare ranka ya dade."


"Barka dai shigo ciki." Yafada tare da juyawa cikin dakin. Dago kaina nayi da sauri na mayar dashi qasa sakamakon ganinsa da nayi d'aure da towel gabana ya dinga bugawa kasa shiga dakin nai nayi tsaye a bakin kofar ina tararrabi."


Zama yay gefan bed dinshi yana kallon bakin kofar, "Ke! ki shigo nace dake."! A tsawace ya fad'i maganar, shahada nayi na shiga yace." Kulle kofar." hannu nasa na tura kofar dakin ta rufe, tsayuwa nayi jikin kofar kaina a qasa nace"Ranka ya dade gani nazo." Shareni yayi ya cigaba da murza vasilin a jikinsa, duk da kaina a qasa yake sai da naga cinyoyinsa d'an towel din ya dinga turewa daga jikinsa yana shafa vasilin din, ganin kamar yana so yayi tsirara yasa na juya masa baya.


"Ke! dodo ne ni da zaki juya min ba okey zan saki yanzu ki shafa min vasillin din tunda abin hakane." Ji nayi yawun bakina ya bushe, nace"Dan Allah kasa kayanka baligin mutum kamar ka bai kamata ana ganin tsaraicinsa ba.


"Wa'azi za kiyi min kome."? Shuru nayi masa, yace." Malama Zo nan ki shafa min vasilin din a bayana." Kasa juyawa nayi ballantana naje nabi umarninsa. "Ko bakya ji ne." Hanci na shaqa kunyar duniya ta isheni nace"Dan Allah kayi hakuri ba zan iya ba." Tsaki naji yaja daga hakan be sake cewa komai ba ya cigaba da shafa mai a jikinsa.


"To na gama sai ki juyo.'' A hankali na juya kaina a 'kasa ban yarda na kalleshi ba, yace" Zo ki kar'bi maganin nasa Haruna yaje gurin seda magani ya siyo zo in nuna miki yanda zaku dinga bashi.
Zuwa nayi na durkusa gabansa a nutse ya fito da magungunan daga ciki leda ya shiga nuna min yanda qa'idarsu take, muryata na rawa nace"Allah ya saka da alkairi mungode." Yace."Ki koma yanzu ki bashi maganin kamar yanda nace amma ki tabbatar kafin ki bashi yaci abinci ya koshi." Ina kokarin miqewa tsaye nace"Insha Allahu yanda kace haka za'ayi." da ledar maganin a hannuna na kama hanyar fita daga dakin.
Ka shingid'a yayi tare da bin bayanta da shu'umin kallo, sajensa ya shafa yana lumshe idonsa gabad'aya yarinyar ta rikitashi duk wani abu da yake daurewa yake yi amma yana bukatar wacce zata d'ebe masa kewa.


Sai da na tabbatar da yaci ya k'oshi tukkuna na bashi maganin kamar yanda ya umarce ni, mahaifiyata na kalla dake kokarin gyara masa shimfida nace"koda da safe ban shigo da wuri ba ai kinga yanda na bashi maganin ko."? Tace"Eh na gani insha Allahu zan kwatanta." Miqewa nayi na sakeyi mata sallama a karo na biyu, tace"To Allah ya tashemu lafiya." da ''ameen na amsa cikin sauri na fita daga dakin.




Yana kishingid'e kasan kafet din dake 'kasan bed dinshi na same shi da romot a hannunsa yana kallon wa'ko'kin turawan america, kauda kaina nayi daga kan tv dan ganin yanda turawa ke bad'ala sai rungume rungume suke suna tsotsar bakin junansu.


A sar'ke nace"Ranka ya dade na dawo na bashi maganin kamar yanda kace idan da akwai abinda kake bukata kayi magana sai nayi maka."


Uffan bece min ba hankalinsa na kan tv yana kallon raye rayen turawa.
Na sunkuyar da kaina k'asa, hakika raina yana 'baci idan yana min wannan wulakacin a rayuwata na tsani nayi magana a watsar dani.




Sai da ya mula tukkuna ya kalleni tare da fad'in "Ina bukatar kiyi min matsar jiki kwana biyu sabida rashin motsa jikina da banyi ba yana min ciwo insha Allah gobe zan fita da doki cikin gari na wasa jinina."


Duk da na fahimci abinda yake nufi sai nace"Ban gane abinda kake nufi ba." Gyara zamansa yayi yana fuskantata yace"Ina bukatar tausa shine abinda nake nufi."


Jarumta na aro nace"Amma ina ganin kamar hakan be dace ba idan tausa kake bukata maza 'yan uwanka su yafi cancanta suyi maka bani ba da nake a matsayin mace ba."


Gani nayi ya sha kunu! kaina na sunkuyar gabana na faduwa..."Kina a matsayin mace sai akayi yaya."? shuru nayi bance komai ba, ya cigaba da cewa''Na fahimci kina da taurin kai babu abinda za'a umarce ki dashi kiyi kai tsaye sai kinyi musu, kada ki manta fa kina karkashin masarauta duk abinda aka umarce ki dashi naki to ne."


Hanci na shaqa na sake risinar da kaina qasa nace"A gafarce ni ranka ya dad'e ba wai ina jayayya da umarninka bane A'a inaso na nuna maka illar abinda kake so na aikata bai kamata na ra'bi jikinka ba a matsayinka na baligi nima haka."


D'akin ne yayi shuru bayan gama maganata, dago kaina nayi na kalleshi naga ya tsirawa tv ido fuskar nan kamar wanda aka aikowa da sak'on mutuwa.


Tv din na d'an kalla a sace naga abinda ake aikatawa ya zarce tunani na, mace da namiji ne tsirara sun dage suna sex sai nishi sukeyi......gabana ya dinga bugawa da sauri na miqe na kama hanya zan fita.
"Kada ki kuskura ki fita a d'akin nan." Ja nayi na tsaya ba tare dana juyowa ba gabana na faduwa still ina jiyo nishin 'yan iskan."
*BINTA UMAR ABBALE*


Shearing����


Dan Allah idan ba siyan book din nan zakiyi ba kada ki kira waya ta, masu flashing kuyi wa Allah da Annabi ku bari bana jin dadin abinda kukeyi🤨
2/11/21, 8:19 AM - ???: *'KWARYA TABI 'KWARYA*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE�_ *bintaumarabbale@gmail.com*




*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊�*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
_________________________
*Littafin na kudi ne....!*
_#300.....0542382124...Binta Umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin.......... Ga masu bukatar VIP Group 600 ne_
_Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d'aya 90899076_88137740_
[12/29, 12:33 PM] 💜: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
23&24
"Ki dawo kiyi aikin dana saki." Maganarsa ce ta doki dodon kunnena, juyowa nayi fuskata a had'e nace"Allah ya kiyashe ni aikata haramci Ranka ya dade bana jin zan iya bin umarnin ka tunda ya sa'bawa addinin musulunci." Ina gama maganata na kama handle domin bude kofa na fita muryar mahaifina naji a kunnena lokacin da yake min gargadin akan bin umarnin masarauta, hawaye ne ya ciko a idona ina jin tsoro kada garin bin umarni wani mummunan abu ya faru a tsakani na dashi tunda Annabi S.a.w yace." Duk inda mace da namiji suka had'u to na ukun su shed'an ne babban tashin hankalin kuma shine ya kunna iskanci a d'akin shiyasa gabad'aya na kasa samun nustuwa.......Saukar hannunsa naji akan nawa dake jin kofar dakin, na dinga jin hucin numfashinsa na sauka a daidai wuyana, cikin faduwar gaba na juyo sai na ganshi dab dani saura kadan kirjinsa ya gogi nawa, saurin jingina nayi a jikin bango(garu) numfashina na fita da sauri da sauri, sunkuyar da kaina kasa nayi bakina na rawa magana nake so nayi amma tsabar fargaba da tashin hankali ya hanani cewa komai.
"Ba zakiyi min ba ko." cikin wata 'yar iskar murya ya fadi maganar, cike da jarumta na kalleshi nace"Kaji tsoron Allah a duk inda kake nasan kasan kallon tsaraici haramun ne yanzu dan Allah meye amfanin kallon blue film da kake yi kuma menene na cewa lallai sai nayi maka tausa idan baka da wata manufa akaina."


Shuru yayi bece min komai ba kuma be daina kallona ba, hannunsa dake dogare a jikin kofar na ture ina kokarin fita daga tsakaninsa ya mayar dani jikin bangon ya matse da kirjinsa, kafin nayi aune naji saukar hannunsa akan mazaunai na yana shafa su, karfi ne yazo min da wani tunkude shi ina haki! na nuna shi da hannu da fad'in "Kada ka sake yunkurin kai hannunka jikina ni ba 'yar iska bace irin wanda ka saba nema a turai, yanzu na gane munufar ka a kaina dama badan nayi maka aiki ka bukaci zamana a sashenka ba na gane sabida ka cimma wata munufa ne to ta Allah zai kare ni daga sharrin ka."
Cikin tsanani 'bacin rai na kare maganar a fusace na bude kofa zan fita ya finciko ni kafin nayi wani yunkuri naji saukar mari a kumatuna, ido na tsirawa masa ina kallonsa yana huci yace."Ni kike kira d'an iska."? Muryata na rawa nace"Ni ban ce maka dan iska ba amma nace kaji tsoron Allah akan abinda kake aikatawa wanda kasan haramun ne." Wani kallon banza yayi min da fadin "Saboda kin samu nayi sha'awarki shine kika samu damar fad'a min dukkanin maganar da kike so ko an fada miki ni sa'anki ne da zaki tsaya a gabana kina kokarin zagina."'


Risinar da kaina qasa nayi nace" Allah ya baka hakuri idan akwai maganar data bata maka rai a cikin maganganuna to ina neman afuwa." Da hannu ya nuna min kofa cikin tsawa yace."Fice min a daki banza mummuna kawai." Da sauri na bude 'kofar dakin na fita gabana sai dukan uku uku yake.......Tamkar wani zautacce ya juya jikinsa na kyarma bed ya kwanta ruf da ciki yana murk'ususu mararsa ta cika tayi fam sai ciwo take masa.


Dakin da Haruna ya nuna min na shiga na rufo kofa na samu gefan gado na zauna har yanzu ban dawo nutsuwata ba, sosai nake mamakin al'amarin, a haka idan ka kalleshi zaka dauka mutumin kirki ne sabida a zahiri yana da fuskar salihai ashe ba anan take ba shi d'in mugun shaid'ani ne mane min mata wato yana da manufa a kanta shiyasa ya bukaci zamanta a gurinsa, to kuwa idan hakane dole tayi takatsantsan dashi da dabi'unsa.
Da kyar bacci ya d'auketa saboda tsabar damuwa da tashin hankali.


B'angaransa kuwa yanda yaga rana haka yaga dare ya dinga matagugu yana riqe ciki sai gefin asubahi ya samu sassauci abinda ke damunsa cikin tsanani damuwa yayi wanka da alwala ya shirya shiga massalaci haka ya sakko tamkar wanda yayi shekara akwance tare suka tafi masjid din dasu Haruna domun gabatar da sallar asubahi.


Bayan na idar da sallah na jima hannuna a sama ina rokon Allah ya kareni daga sharrinsa na shafa adduar na mike a nutse na fita falon na jima a tsaye ina sak'e sa'ke kafin na nufi kofar kicin domin shirya abin kari...........Tsaf na shirya kayan karin kummalo na fito dasu ina jerawa kan daning....Shine a gaba su Haruna na bayanshi, 'kasa nayi da kaina tare da risinawa nace" Ranka ya dade Barka da asubah." Banza yayi mun ya wuce benansa, a sanyaye na dago kaina muka hada ido da Haruna ya'ke nayi nace"Haruna kun tashi lafiya."? Yace."Lafiya lau Sumayya ina fata kema kin tashi lafiya."? na amsa da lafiya lau alhmdullhi." Har zai bar gurin sai kuma ya tsaya yace."Sumayya baki karanci damuwa a fuskar Yarima ba."?
Girgiza kaina nayi ba tare da na kalleshi ba nace"Banga komai ba ai ka san shi ba'a gane farin cikin sa da 'bacin ransa tunda kullum fuskarsa a murtuke take da rashin fara'a."
Yace."Hakane to amma yana da kyau mu had'u gabadayanmu muje mu sameshi mu tambayeshi ko munyi masa laifi sai mu bashi hakuri." Shuru nayi ba tare da nace komai ba na cigaba da ayyukana.
Yace."Kinyi shuru bakice komai ba." Nace"To hakan yayi muje." Haruna ya kalli Isa da Hamza yace."Shawarata tayi ko." ? duk sukace tayi muje mu sameshi mu tambayeshi ko munyi masa laifi sai mu bashi hakuri.
Jirana sukayi na gama gyara daning sannan muka hau saman nashi.


Yana kwance cikin bargo yace."Kowaye ya turo kofar, a bude take." Haruna ya bude kofar dakin muka shiga gabad'ayan mu kanmu a kasa muka ajiye gwiwowin mu a kasa gaishe shi muka farayi kafin mu fara neman afuwarsa duk da bamu san laifin da mukayi ba.


Shuru dakin yayi bayan mun gama magana uffan bece mana ba yana kwance cikin bargo fuskarsa na kallon rufin dakin.
Haruna yace"Ranka ya dade a gafarce mu."! Gyaran mirya yayi ya juyo yana fuskantar mu, sunkuyar da kaina kasa nayi ganin fuskarsa a hade gashi kwayoyin idanunsa sun sakeyin jawur! "Babu wani abu da kukayi bana jin dadi ne shiyasa kuka ganni haka da rashin kuzari."
Haruna dasu Isa suka shiga damuwa dajin furucinsa ni kuwa ko gezau banyi ba tunda nasan karya yake kawai ya fadi hakane domin kare kansa, sannu suke masa tamkar bakinsu yayi tsayi, nima sai nabi ayarinsu na dinga yi masa hannu ina rokon Allah ya bashi lafiya.


Gyaran murya yay a karo na biyu yace."Kuna iya tafiya." Haruna yace."Ranka ya dade sai zuwa anjima za kayi wanka ko kuma yanzu na hada maka ruwan wankan." ? girgiza kansa yay yace."Bari anjima ka shigo ka had'a min inaso nayi bacci yanzu." Yace."To godiya nake ranka ya dade a tashi lafiya." Mik'ewa sukayi da niyyar fita, nayi kasa da idanuna ba tare da na kalleshi ba nace"Ranka ya dad'e yana qarko na shirya danning ina nufin gurin cin abinci komai ya kammala idan baka bukatar zama a daning din sai kayi magana na kawo maka nan."
Shuru yayi min, jikina ya bani kallona yake, aikuwa ina dago kai muka had'a ido, a maimakon ya ji kunya na kamashi yana kallona sai ma ya sake k'ureni da jajayen idanunsa dake bani tsoro.
Yun'kurawa nayi zan tashi naji maganarsa a dashe "Ki kawo min nan." na risina da fadin"angama ranka ya dade." da sauri na juya domun fita daga dakin......kallo ya bita dashi yana jin yanda gabansa ke miqewa hannu yasa ya danne jijiyar tashi yana jan tsaki a fili yace."Sabida rashin adalci ki rasa a inda zaki nuna kwad'ayin ki sai a inda be dace ba mtwww! tsaki yaja mai k'arfi yana danneta ita kuma sai miqewa take.


Ina sauka qasa na samu 'Yan uwanshi Shatima da Maddibo har'kasa na durkusa na gaishe su, suka amsa min a sake mussaman Shatima sai murmushi yake min, wuce su nayi da sauri na nufi kicin na dauko wani tire na silver mai fad'i dainng din na nufa na shirya kayan break fast din akai na dauka a nutse na nufi saman da tire din a hannuna


Abin mamaki! samunsa nayi a zaune shida 'yan uwan nashi suna hira, a nutse na ajiye tire din a gabanshi, kai a sunkuye nace"Dan Allah ina neman alfarama."
"Wace irin alfarma." yafada ba tare da ya kalleta ni ba." naji dadi sosai da bai shareni ba nace"Zanje in duba dawakai kasancewar aikin babana kenan to tunda ya kwanta rashin lafiya na dawo da dawaniyyar hannuna bayan nan inaso zan zauna a gurin karatu."


Jim yayi na minti biyu yace."Kije." cikin jin dadi nace"Nagode ranka ya dade." yunkurawa nayi na mike tsaye da fadin"A tashi lafiya." babu wanda ya amsa min a cikinsu. da sauri na kama hanyar fita daga dakin.
Shatima ya kalli Moddibo da fad'in "Wannan yarinyar tana da dirin jiki mai kyau amma kuma bata da wani kyau gata 'baka."
Moddibo dariya yay yace."Kai ina ruwanka da muninta idan biyan bukata nake nema ni bana duba muni ina duba abinda zai gamsar dani." Dariya sukayi tare da tafawa a tsakaninsu, Haushin abinda suke yasa ya mike ya nufi toilet yana jin wani irin d'aci! a cikin ranshi, ashe dai bashi kadai ke ganin kyawun jikin yarinyar ba, har da sauran mutane yaji takaicin yanda Shatima ke kwarzanta kyawun dirin jikinta, brush yay ya fito da fuska

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login