Showing 3001 words to 6000 words out of 150413 words

Chapter 2 - Kwarya Tabi Kwarya Book Complet by Binta Umar Abbale .txt

shiga gida tukkuna aka samu lafiya, jama'ar gurin suka watse kowa ya nufi 'bangaran da yake a cikin gidan.........Nida iyayena Cikin yanayi na ciwo muka shiga gurin mu, da sauri muka zaunar dashi, Tambaya ta ri'ke kafadarsa ni kuma hankali a tashe naje na d'ebo masa ruwa jiki na kyarma nazo na tallafo kansa ina kokarin bashi ruwan, bakinsa ya bud'e ina sa masa ruwan yana dawowa, lokaci guda zuciyoyinmu suka karye nida mahaifiyata hawaye muka fara, cikin karfin hali gami da kokarin janyo maganar yace."Ku daina kuka bashi ne abinda nake bukata ba."!
Zama nayi kusa dashi na rike hannunsa har yanzu hawaye bai da zubo min ba nace"Baba wai dan Allah me yake damunka kwana biyu ka'ki lafiya kullum cikin rashin kuzari da karfin jiki gashi kuma ka'ki ka bari a kira mai kula da lafiya yazo ya duba ka."
A hankali yace."Sumayya ba wani ciwo mai tsanani bane yake damuna zazza'bi ne mai zafi sai hajijiya gami da rashin kuzari to ni dik a tunani na ko shawara ce shiyasa na mayar da hankalina gurin shan maganinta amma yanzu ina ganin dole kije ki kira d'aya daga cikin masu kula da lafiya yazo ya dubani dan ni kadai nasan abinda nakeji a cikin jikina.
Tambaya hawaye ta share a sanyaye ta kalleni da fadin"Kiji can bangaran masu kula da lafiyar ki kirawo daya daga cikinsu yazo ya dubashi ni kaina jikina yay sanyi da wannan rashin lafiyar tasa a tsaitsaye fa ya kai sati hudu yanayi duk da yana shan maganin shawarar babu sauki kullum jikin rikicewa keyi."
Miqewa nayi da sauri nace "Bari naje can gurinsu na samesu." takalma na zura da saurin gaske na kama hanyar sashen masu kula da lafiyar gabad'aya bana cikin hayyacina ina tsananin kaunar mahaifina shiyasa rashin lafiyarsa ta d'aga min hankali mutuka.


"Sumayya." Sunana naji an kira da sauri na tsaya ina waigen bayana.


babu walwala a fuskarsa ya karaso inda nake tsaye kai tsaye yace."Ina Lawi yake ya bar aikinsa kamata yayi ace kafin mu fita gurin taro ya zubawa dokuna abinci yanda zai ishesu yanzu yanzu na shiga gurin na tarar da gabad'aya babu abinci a gabansu idan fa maimartaba ya samu labarin abinda yake zai fuskanci hukunci."


A marairace nace"Buba dan Allah kayi hakuri kada ka kai 'korafi wallahi babana bashi da lafiya tsayin sati hudu yake ciwo a tsaitsaye dukkanin abinda yake dauriya kawai yake dan Allah ka taimaka masa kana bawa dawakan abincin kafin yaji sauqi.


"Ke! saurara da wannan maganar.'' Nayi saurin kallonsa kwalla na kokarin zobomin, Ya cigaba da cewa''Kowa da kika gani akawai aikinsa a masarautar nan nawa aikin ma yafi nasa wahala tinda ni kwana nake a tsaye ina zirga zirga banga dalilin da zai sanya na d'auki nauyin wani na d'orawa kaina ba, ke aikin me kike da ba zaki d'auki nauyin mahaifinki ba kafin ya samu lafiya.


Hannu nasa na goge hawayen da suka zubo min nace" Shikkenan zanyi kokari ganin na dauki ragamar kula da dawakan kamar yanda babana yake yi amma ka san dai muna zaman karatu ranaku uku a sati ko kuma idan mun zauna tin safe sai yamma muke tashi.
D'aga kafad'a yay yace."Ke zaki tsarawa kanki yanda al'amura zasu tafi ni dai na fad'a miki ku kula da aikin ku kada maimartaba yaji wata magana.


Ajiyar zuciya na sauke mai zafi! nace"Shikkenan Buba nagode sosai insha Allahu zan iyakacin bakin kokarina." Gyda kansa yayi ya bar gurin, nima da sauri na wuce domin nufar inda nayi niyya.


Na jima a tsaye a bakin kofar d'akin nasu ina sallama kafin naji an amsa da fadin"Ko wacece ta shigo.'' Jim nayi ina tunanin shiga dan gabad'ayansu maza ne a ciki ina ganin kamar hakan bai dace ba.


Sallama na sakeyi, naji anyi min tsawa! da fad'in "Wai wacece take sallama ne ki shigo ki fadi uzirinki." Shahada nayi na tura kaina dakin....wasu na kwance kan katifunsu wasu kuma na zazzaune daga su sai gajerun wanduna.
Daga bakin kofa na tsaya nace"Dan Allah d'aya yazo ya duba babana Lawi bashi da lafiya."


Shuru sukayi min kowa ya cigaba da sabgarsa, raina ya 'baci! nace"Magana fa nakeyi muku kuna jina." 'Dantala ya zaburo min da hayaniya yace."Ke! babu wanda zai katse abinda yake a cikinmu yaje ya duba babanki idan kina so ayi miki abinda kike so ki shigo ciki muna bukatarki."


Cike da mamaki nake kallonsu nace"aikin ku ne fa mai zai sanya kuce sai nayi muku wani abu sannan zakuyi to ni ba 'yar iska bace idan kun saba latsa 'yan matan dake masarautar to ni ba' irinsu bace kuma wallahi idan bakuyi wasa ba yanzu zanje fadar sarki na sheda masa abinda kuke aikatawa..........A fusace! naga ya miqe yayo kaina zai mareni na kauce da sauri ina kare fuskata....wanda yake da sauqin halin cikinsu ne ya miqe tare da zira rigarsa ya kalleni da fadin" Shige muje na duba jikin mahaifin naki." Da sauri na fita daga dakin gabana sai faduwa yake......Tafiya nake zugwi zugwi ina mamakin al'amarin, kawai naji ana ta'ba min mazaunai! Da sauri na juyo ina kallonsa, murmushi yayi ya sosa kansa ido jawur yace."A gaskiya Sumayya Allah yayi miki baiwa mai mutukar daukar hankali, kina da duk abinda d'a namiji ke bukata a jikin mace kirjinki a cike yake dam-dam uwa uba mazaunai masu masifar rikimin lissafi wallahi tunda kika shiga dakinmu sha'awata ta tashi dan Allah ki bani damar mallakar wannan jikin naki wanda yake kokarin fitar dani hayyacina.


Kallonsa kawai nake wani 'katoton abu ya tokare min a ma'koshi nace"Yanzu Usman ashe kaima halinku d'aya dasu Dantala a zahiri inayi maka kallon salihi ashe kaima baka da d'abi'a mai kyau Usuman dan Allah meye amfanin lalata da kukeyi da 'ya'yan mutane idan fa masarauta ta samu labarin abinda kukeyi ba zakuji dad'i ba.


A sanyaye ya sosa kansa cikin jin kunya yace."Sumayya dan Allah kiyi hakuri wallahi ni ban fiya haikewa 'yan matan masarautar nan ba su Dantala ne masuyi kema yanzu hankalina ne ya tashi sosai shiyasa na gaza hakuri na kai hannuna mazaunanki amma kiyi hakuri dan Allah kada naji maganar a bakin kowa.
Cikin takaici na girgiza kaina tare da juyawa na cigaba da tafiya raina a masifar 'kuntacce.


To koda Usuman ya duba babana nan ya gano cewa hawan jini ne ke damunsa hankalinmu ya tashi nida tambaya muka dinga kuka dan mun riga mun san ciwon hawan jini babban ciwo ne gani muke kamar mun kusa muyi bankwana dashi shiyasa gabadaya hankalinmu ya tashi....Usuman ganin duk muna hawaye yasa ya rarrashe mu tare da bamu shawarwarin yanda zamu kula dashi da lafiyarsa yace "Insha Allahu mutukar aka bi dokar da ake bukata masu dauke lalurar suka bi to zai samu lafiya, Ya miqe tare da fad'in " Zaije yanzu ya kawo masa magungunan da zasu taimaka masa...godiya mukayi masa muna zubar da hawayen tausayi......
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 8:19 AM - ???: *'KWARYA TABI 'KWARYA*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE�_ *bintaumarabbale@gmail.com*




*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊�*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
_________________________
*Littafin na kudi ne....!*
_#300.....0542382124...Binta Umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin.......... Ga masu bukatar VIP Group 600 ne_
_Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d'aya 90899076_88137740_






*SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)


7&8
Tamkar mai tausayin taka k'asa haka yake cire qafa yana tafiya kanshi a 'kasa hannuwansa a goye a baya, Shatima da Moddibo suna gefe da gefansa sai hira sukeyi masa yana dai jinsu da kunne amma ya gagara cewa uffan sai dai idan sun fadi maganar da ta bashi dariya yayi murmushi had'e da girgiza kansa, Yarima Ali mugun miskili ne wanda magana ke masa wuya shiyasa mafi akasari mutane ke ganin kamar dan wulakanci ne 'Dabi'arsa ce ta rashin son magana da hayaniya gami da rashin fara'a 'yan uwansa da iyayensa sun san wannan halin nasa tun yana yaro dashi ya taso, tun kafin su qarasa bakin kofar masu tsaron gurin suka zube gwiwowinsu a kasa sunkuyar da kansu sukayi hade da d'unkule hannuwansu alamun gaisuwa.
Shatima da Moddibo ne kawai suka d'aga musu hannu shi kuwa gefan da suke ma bai kallaba ballantana yasan sunayi.......Shatima ne yasa hannu ya bude narkekiyar kofar da zata sada su da falon Fulani wato mahaifiyarsa, A nutse yasa kafarsa cikin falon tare da sauke ajiyar zuciya, lumshe idonsa yayi yana jin wani irin sanyi na ziyartar zuciyarsa yau dai Allah ya dawo dashi gida gaban iyayensa hakika babu wanda ya kaishi farin cikin wannan rana......Bude lumsassun idanunsa yayi ya sauke su a kanta tana gishingide kan kilishi jakadiyarta na gefanta a zaune tana mata firfita da wani irin mafice, Mama fulani kyataccan murmushi ne a fuskarta ta zuba masa ido tana jin wani irin farin ciki a cikin zuciyarta.


Da sassarfa ya k'arasa kusa da ita yayi zaman raquma a gabanta tare da sunkuyar da kansa yace."Mammah hakik'a yau ni dake ban san wanda yafi wani farin ciki ba nasan zuciyarki tana cike da farin cikin dawowata gida wannan dalilin ne ya sanya na kasa shiga sashena nace lallai sai nazo nayi tozali dake uwa tagari nayi farin ciki dana dawo gida na sameku cikin koshin lafiya keda maimartaba da duk wani makusancina."


Ajiyar zuciya ta sauke ta gyara zamanta hannu ta dora a saman kansa a nutse tace"Allah yayi maka albarka babana nayi mutukar farin cikin dawowarka masarauta lafiya tabbas farin cikin da nake ciki a yau ba zai yafi gaban a kwatanta shi zuciyata tas take da ganinka cikin koshin lafiya babana ka kara girma kayi lafiya ka kara nutsuwa ka cika mutum ta kowane 'bangare babu shakka dole nagodewa ubangiji a bisa wannan karamaci da yayi mana ina rokon Allah ya raya min kai ya albarkaci rayuwarka da zuriar da zaka samu."


Hannunta dake saman kansa ya r'iko yasa a bakinsa ya sumbuta lumshe idonsa yay yana murmushi yace."Mammah nagode sosai da adduarki akoda yaushe ina alfaharin kasantuwarki a matsayin mahaifiyata."


Murmushi tayi tare da girgiza kanta ta mayar da hankalinta kansu Shatima dake zaune a gefe da gefansa, murmushi ta sakeyi tana kokarin magana suka fara gaisheta, hannunta ta d'ora a saman kansu tace"Ubangiji Allah yayi muku albarka ya had'e kanku kuyi zumunci dan Allah tabbas nasan kuma yau kuna cikin farin cikin dawowar d'an uwanku lafiya." Shatima yace.''Hakane Mammah hakika muna cikin farin ciki mara mislatuwa muna yiwa Allah godiya daya dawo mana dashi gida lafiya.


Har yanzu da murmushi a fuskarta tace"Yana da kyau ku rakashi ko wane 'bangare na gidan nan ya gaisa da iyayensa kamar yanda yazo ya gaisa dani."
Moddibo yace."Insha Allahu Mammah." Kallonsa tayi har yanzu yana durkushe a gabanta tace"Babana zakuje sauran sashen iyayenka ku gaisa kafin ka shiga gurinka ka huta nasa hadimai sun shirya maka komai da komai." Hannunta ya sumbata cike da bin umarni yace."Mammah abinda kikace shi za'ayi insha Allah."! Miqewa yayi a nutse ya kalli 'yan uwan nasa da fad'in " ku Tashi muje." Shatima da Moddibo suka miqe kai a kasa suka ce "Mammah a tashi lafiya." Hannu ta d'aga musu fuskarta yalwace da fara'a idonta a tsaye a kansu har sai da suka fita daga falon ta girgixa kanta gami da sunkuyar da kanta kasa addua take a cikin zuciyarta kan Allah ya cigaba da had'a kawunansu suyi zumunci tsakani da Allah.


*Tushen Labari*
Maimartaba Sarki Adamu Abdullahi dattijon mutum ne wanda ya iya mulki gami da jagoranci akan komai maimartaba Adamu Abdullah mutum ne mai tsananin tausayi da jin'kai, baya ta'ba yarda talaka ya kaskanta kuma bai yarda da cuta gami da zalinci ba, al'ummar garin suna mutukar jin dadin mulkinsa gami da yanda yake gudanar da hukunci akan wanda yayi zalinci, Sarki Adamu yana da 'Ya'ya amma dukkaninsu matane d'aya ne Namiji a cikinsu, sai dai 'yan uwansa suna da yawan 'ya'ya maza shi kadai Allah yayiwa albarkar 'ya'ya mata sai ya bashi guda d'aya namiji wanda yake mutukar alfahari dashi kasancewarsa mai tsananin biyayya a gareshi.....Mahaifin Waziri da galadima ya rasu dama a hannunsa suka taso tare da 'ya'yansa tare kuma duk suka gudanar da harkokin karatunsu.........Sulaimanu Dan uwan Sarki Adamu ne ciki daya suka fito shine ya kasance mafi kusa dashi a fada sarki Adamo baya zartar da kowane irin hukunci sai yayi shawara da d'an uwansa wato Waziri Sulaimanu, duk da wannan karamcin da maimartaba keyi masa hakan bai sa ya janye muguwar kiyayyar da yake masa ba da shida zuriarsa kullum burin Waziri Sulaimanu yaga bayan d'an uwansa dan ya tsani ya wayi gari ya ganshi kan karagar mulki.......Shi a yanzu baya sha'awar mulkin tunda shekaru sunja masa yafi sha'awar d'ansa Ciroma ya hau kan kujarar badan komai ba sai dan kada bayan babu ransu a duniya mulki ya cigaba da tabbata a hannun zuriar dan uwan nasa wato Sarki Adamu, shiyasa kullum cikin damuwa yake gami da tunanin ya za'ayi ya ruguza karagar mulkin d'an uwan nasa, Kullum cikin shirya manakisa suke shida d'ansa Ciroma maimartaba sarki Adamu Allah na kareshi daga sharrinsu, Waziri Salmanu ganin ya kwanta ciwo sai jikinsa yay sanyi yana ganin kwanansa ya kare bukatarsa bata biya a kan dan uwansa ba, tabbas jikinsa na bashi mutuwa zaiyi sai kawai ya kira d'ansa ya zaunar dashi suka yanke shawarar karshe a tsakaninsu.......Ciroma mutum ne mara tsoron Allah da tunanin makomarsa, Kai tsaye ya shiga biye biyen malaman tsubbu bai bari ba har sai da bukatarsa ta biya ganin ya durkusar da maimartaba, mugwayen aljannu sun shafe jinsa da ganinsa kana sun kumbura masa jiki yana kwance sai sai komai ayi masa.....Wannan al'amari yayi wa Waziri Sulaimanu dadi mutuka yana kwance rai a hannun Allah amma 'kara tsarawa d'an nasa sharri yake yi.
Hankalin iyalan Mairataba ya tashi mutuka gaya jama'ar gari suka shiga tsananin tashin hankali da damuwar rashin lafiyar data samu shugaba nagari malamai suka dinga bada taimakonsu iyakacin bakin kokarinsu.......Waziri Sulaimanu ya tara su kaf a guri daya yace"Tunda al'amarin ya kasance a haka to shi a matsayinsa na mai zartar da hukunci da yawun d'an uwansa wato maimartaba Sarki Adamu ya wakilta AbdulJabbar wato Ciroma ya zauna kan karagar mulki kafin aga abinda Allah zai zartar.....Da yawa daga cikinsu babu wanda yay na'am da wannan hukuncin to amma saboda gudun tashin hankali da gutsiri tsoma yasa sukayi fatan alkairi ga hukuncin da ya yanke........ba'a wani ja dogon lokaci ba Ciroma ya soma zama a fada ya cigaba da gudanar da mulki cikin rashin iyawa gami da tsantsar mugunta da zalinci.........A take jama'ar gari suka gane inda ya dosa gabad'aya yafi bada muhimanci akan harkar zalinci ko sharia aka kawo gabansa baya iya yanke hukuncin da sharia ta tanadar shi a ganinsa duk abinda yake daidai ne, Jama'a suka dinga k'orafi gami da surutai har labari ya isa kunan gomnati, a lokacin ta shigo cikin al'amarin bata kuma ja wani dogon lokaci ba ta sauke Ciroma daga kan kujerar mulkin, sannan kafin gomnati ta d'ora wani a matsayin sabon sarki sai da ta duba cancanta tukkuna ta za'bi Abdul-aziz ya maye gurbin mahaifinsa tunda shi cuta ta kwantar dashi.......Komai na saurata gomnati ta damqawa Abdul-aziz jama'ar gari suka dinga farin cikin samun sa a matsayin shugaba.......Wannan al'amari yayi wa Waziri Sulaimanu da d'ansa ciwo dan Ciroma kulle kansa yayi a daki ya dinga bankar giya yana tam'bele shi kadai sai zage zage yake yana surutai...........Waziri Sulaimanu kuwa sai muce tsabar bacin rai ne yasa ya had'iyi zuciya ya mutu sai shiga akayi aka ga gawarsa.....Hankalin iyalansa yayi tsananin tashi suka dinga kuka suna tofin alatsine ga zuriar Adamu suna ganin kamar sune sukayi sanadiyar mutuwar mahaifinsu.......Tun daga mutuwar Waziri Sulaimanu gaba mai tsanani ta shiga tsakanin zuria guda biyu har yanzu kuma itace akeyi 'ya'ya da jikoki sai dai kowa na kokarin 'boye bakin cikinsa akan dan uwansa amma daidai da kwayar zarra babu mai kaunar d'an uwansa..........bayan rasuwar Waziri Sulaimanu da sati uku Ciroma yabi dare da rana yaje ya sanyawa Sarki Adamu fillo ya toshe masa hanci murus! ya kashe shi har lahira ya fito daga dakin ba tare da kowa ya ganshi ba.....Shima iyalinsa shiga sukayi suka ga gawarsa al'amarin da yayi masifar tashin hankalinsu, Mutuwar Sarki Adamu ta girgiza zukatan al'ummar gari dayawa yawansu suka dinga kokawa suna fad'ar kyawawan halayensa............
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 8:19 AM - ???: *'KWARYA TABI 'KWARYA*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE�_ *bintaumarabbale@gmail.com*




*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊�*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
_________________________
*Littafin na kudi ne....!*
_#300.....0542382124...Binta Umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin.......... Ga masu bukatar VIP Group 600 ne_
_Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d'aya 90899076_88137740_










*SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah)
11&12
Tun bayan fitar su Satima daga 'bangaransa yake zaune shi kadai a guri guda ya gaza ta'buka komai kallon kasan d'akin kawai yake yana mamakin abinda ke faruwa a masarautar a lokacin da ya tafi karatu yana da kuruciya shiyasa baya saurin gane wasu abubuwan amma yanzu shigarsa sauran 'bangarorin gidan domin gaisawa dasu ya fahimci cewar har yanzu bata sauya zani ba a tsakanin iyalan mutane uku da suke da muhimmacin a masarauta ba'a ga maciji kowanne da akwai mugun abu a zuciyarsa dangane da d'an uwansa, Lokacin da suka shiga bangaran mai babban daki gabad'aya sun hallara a falo ita da 'ya'yanta sun kewaye ta babu wanda yasan abinda suke qullawa sai Allah.......Ganin shigowarsu ne yasa suka daidata nutsuwarsu suna masa barka da zuwa dukkaninsu sai ya'ke sukeyi da kokarin nuna masa kulawa, shi ba yaro bane ballantana ya kasa gane yanayin fuskokinsu dan wasu daga cikinsu sai satar kallonsa suke ta'kasan ido, dalilin daya sa kenan ya kasa zama ya miqe da niyyar tafiya........Uwargida na fara'a kamar gaske tace"Magajin Sarki ka tsaya kaci abincin ma tun safe 'Yan uwanka suka baro gidajan mazajensu suka yini suna shirya maka abun tar'ba."
Ba tare da ya kalleta ba yace."Nagode Gwaggo ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login