Showing 72001 words to 75000 words out of 150413 words

Chapter 25 - Kwarya Tabi Kwarya Book Complet by Binta Umar Abbale .txt

wani abu da zaka nema a gurina na kasa mallaka maka mutukar ina da iko ni ne mahaifin Sumayya kuma na baka ita ina rokon Allah ya sanya alkairi a cikin auranku'''




Magajin sarki fad'ad'a fuskarsa yayi da murmushi cikin jin dadi yace." Nagode sosai da wannan kyauta da kayi min insha Allahu zan samu Maimartaba na sheda masa maganar da duk yanda mukayi nagode kwarai da gaske kana iya tashi ka tafi.'''


Lawi godiya yayi sosai kafin yay masa sallama ya fito fuskarsa cike da annushuwa! kai tsaye bangaran dawakai ya nufa yana tafiya yana addua akan Allah yasa alkairi a cikin al'amarin.






Sai misalin sha biyu da rabi muka tashi daga gurin karatu ji nayi kamar naje gida na kwanta na huta saboda gajiya da tunani duk sun sa karatun ma bana ganewa, har na nufi gurinmu sai kuma na sanja shawara 'bangaransa na nufa domin gabatar da aikina idan yaso idan na gama sai na huta gabadaya.......koda na shiga gurin samun su Haruna nayi a zaune suna hira kallo guda nayi masa naga ramar da yayi girgiza kaina nayi muka gaisa sama-sama na shigesu.


Yana zaune a falo yana kallo nayi sallama, ya amsa tare da 'kure ni da ido, babu yabo babu fallasa na gaishe shi, ya amsa min fuskarsa a sake kamar bashi ba, kicin na nufa, ya dakatar dani.
Cikin 'kosawa na tsaya ina kallonsa yace."Me ya hanaki kizo ki had'a min breakfast. " ?


"Kayi hakuri naje gurin karatu ne kasancewar yau lahadi duk rana irin ta yau muna zaunawa da wuri mu tashi da wuri wannan dalilin yasa banzo akan lokaci ba.''


Yace." Me zai hana kizo gurina duk ranakun asabar da lahadin na dunga karantar dake." cike da mamaki nake kallonsa. Yace."Ko kina ganin ba zan iya ba."! girgiza kaina nayi nace" ba haka nake nufi ba kawai abar maganar yanzu ka fadi abinda kake bukatar kaci."!


"Bana bukatar naci wani abu.'' Na dinga kallonsa ina mamakin maganarsa ganin yana min shu'umi kallo yasa na 'bata rai juyawa nayi zan bar gurin yace." Kin san d'azu muyi magana da mahaifinki ko."?


Wani irin kallo na watsa masa, 'bata fuska yayi yace."Abun naki kuma nema yake ya wuce gona da iri ni kikewa wannan kallon.
Tsaki nayi niyyar ja sai na fasa, nace"To kunyi magana da babana sai akayi me."? Cikin nuna isa yace."Ya tabbatar min da cewa ya mallaka min ke ko kina da ja ne."? girgiza kaina nayi nace"Bani da ja sai abinda Allah ya kaddara a kaina amma ka sani idan ka samu nasarar aurena to zaka sha mamakin abinda zai biyo baya."


Kai tsaye yace."In dai ta bangaranki ne ban damu ba saboda duk girma da karfin da kike dashi baki fi karfina ba." Girgiza kaina nayi na wuce kicin zuciyata nayi min zafi! babu shakka guy nan da gaske yake aurena zaiyi ya lalata min rayuwa, koda na shiga kicin din kasa kata'bus nayi na nemi guri na zauna tare da zabga uban tagumi! iyayena na farin ciki zan auri dan sarki! ni kuma ina 'bakin ciki domin nasan da aniyar da zai aureni babu shakka ina jin tsoran ranar da zai sako musu ni a matsayin bazawara shin wane irin hali zasu shiga idan haka ta kasance wannan shine babban abinda ya dame ni, to a takaice dai sai da na shafe kusan rabin awa a zaune a kicin din ina sa'kawa da kwancewa kafin na mike da sanyayyan jiki na fara aikace aikace na.






Magajin sarki sai da dare ya samu zama da mahaifinsa cikin nutsuwa ya sheda masa abinda yake tafe dashi, maimartaba ya dinga kallonsa yana mamakin maganar dake tafe dashi.


Magajin sarki jikinsa ne yayi sanyi dan ganin yanda Maimartabar ya nuna a lokacin da yaji maganar dake tafe dashi, yace."Ranka ya dad'e naga kamar maganar da nake tafe da ita bata gamsar da kai ba."




Maimartaba yace."Kwarai kuwa maganar bata gamsar dani ba Magajin sarki ka duba wata yarinyar wannan da kake magana akanta ka hakura tsayin wata uku iyayen yaran suka same ni da maganar auran 'ya'yansu nasa albarka a ciki sannan daga baya kai kuma kazo da wata magana, bana so na amince maka jama'a suga rashin adalcina yarinyar nan Sumayya ba ita kadai bace mace a masarautar nan ka duba da kyau ka samo wata sai na shige maka gaba amma wannan dai tunda wani ya rigaka sai ka hakura."




Wani irin gumi ne ya shiga tsatstsafo masa bai ta'ba tsammanin zai samu matsala daga gurin mahaifin nasa ba, yace."Ranka ya dad'e yanda na yarda na amince da yarinyar nan ko Lawisa ban yarda da ita ba, yarinyar nan sumayya tana tsaye a kaina sosai take bani kulawa ta kowane fanni wannan dalilin ne yasa naji ina sha'awar auranta."




Maimartaba ya sauke ajiyar zuciya yace."Nima nasan da haka domin mahaifiyarka na fada min irin kokarin da yarinyar take a kanka babu shakka zanso ka aureta domin ta cigaba da kula da kai sai dai kash!! ba zan iya shige maka gaba akan al'amarin ba saboda dalilina dana fada maka idan nine mahaifinka to na umarceka daka janye maganar auranta ka nemi wata."




Magajin sarki kasa motsi yayi a gurin ya dinga jin zazzabi mai zafi na nema ya rufe shi, Mamma dake gefe guda a zaune tace"Magajin sarki kabi umarnin mahaifinka ka janye maganar auran yarinyar nan kamar yanda ya bukata idan so kake ka had'a mata biyu sai ka duba wata koda a cikin bayin ne insha Allahu zamu shige maka gaba."




Murya na rawa yace."Mamma ke kin san mahimancin yarinyar nan a tare dani ke kika hadani da ita ina ganin duk wacce zan nema ba zata kama kafarta ba yarinyar nada gaskiya da rikon amana mamma kiyi wani abu akan wannan al'amarin."




Girgiza kanta tayi tace"Magajin sarki zan fi kowa so ka auri yarinyar nan saboda ni nasan wacece ita amma a yanzu ni bani da wata magana tunda mahaifinka ya yanke hukunci shikkenan magana ta kar'e sai dai mu roki Allah yasa haka shi yafi alkairi." shuru yayi tare da sunkuyar da kansa kasa






Washe gari da wurwuri na shiga saboda nasan da wuri yake tafiya aiki yasa na shiga sashen da wuri, shuru lokacin dana shiga kai tsaye kicin na wuce na fara aikina, kunun gyada na dama masa na soya masa kosai a gurguje na shirya komai a tire na dauka na fito kenan na hangoshi yana saukowa yanda naga fuskarsa a murtuke yasa nasha jinin jikina! kai tsaye hanyar futa ya nufa, baki na na rawa nace ranka ya dade "Barka da asuba zaka fita baka karya ba kayi hakuri dan Allah bangama akan lokaci b.......kafin na 'karasa ya juyo a fusace! ya doki! tire din hannuna! a take fulas din kunun ya tintsira murfin ya cire ya kwaro min a kirjina mazubin 'kosan kuwa tuni ya fad'i a kasan gurin k'osan ya watse a gurun, rad'ad'in zafi ya gigita ni da sauri na jefar da tire din a kasa ina kiran innalillahi! gami da yarfe ruwan kunun dake rigata ......Fulas din kunun ne ya gangara kusa da kafarsa ya sameshi da yake Takalmin dake kafarsa mai yatsa ne! da sauri ya janye 'kafarsa yana dubawa


Ido jawur nake kallonsa tsabar takaici da bakin ciki yasa hawaye ya kwace min, kallonsa kawai nakeyi bakina na rawa , bangaransa kuwa bai tsammaci hakan da yayi mata zata samu tsautsayi ba yayi mata ne dan ya huce fushinsa sai gashi kuma ya 'kona mata kirji da ruwan kunu!!! a sanyaye ya dinga bin kirjinta da kallo fatar duk tayi ja! ta soma tashi, sai yaji gabad'aya ya saduda dan ya lura ta k'one sosai! Inda nake ya nufo yana karasowa na daga hannu da niyyar marin sa, rike hannuna yayi yana kallona!!! a marairace yace."Sorry banyi tsammanin zaki 'kone ba." Fuzge hannuna nayi da sauri na tureshi na kama hanya zan bar gurin, kawai naji ya ru'ko 'kuguna tsam! ya d'ora ha'barsa a kafad'ata, bakinsa yasa daidai kunnena a sanyaye yace."Kiyi hakuri." Gabadaya ji nayi jikina yay sanyi na dinga zubar da hawayen bakin ciki babu shakka Yarima ya zame min karfan 'kafa ya shiga rayuwata yana yanda yake so da ita.............










*Na kudi ne*
Kada ki karanta min littafi sai kin biya keda kika fita da littafin keda Allah idan kina so ki biya ga yanda abin yake Vip gruop#600 normal gruop#300 account... 0542382124...Binta umar gtbank....idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta whsap da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:26 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
78
Tun bayan tafiyar Haruna na tsinci kaina da fad'uwar gaba, guri na nema na zauna ina kiran innalillahi wa'ina ilahi raji'un domin na tabbata itace zata saukar min da nutsuwa, na dauki kimanin minti ashirin a zaune a guri daya kafin na dan samu sassauci a sanyaye na mike na nufi bandaki bokitin wanka na dauko naja ruwa a rijiya na cika bokitin da ruwa wanka zanyi ko naji sassauci dauka na shiga bandakin dashi............Ina fitowa na samu Tambaya ta shigo tana zaune a tsakar gida tana hutawa, nace"amma yau kun gama aikin da wuri." tace."Eh yau aikin yayi sauri nima nayi mamakin haka ai yau mutumin ki akayi." A sanyaye nace "Wake da shinkafa." Kanta ta d'aga min. na kalleta sosai sai naga kamar tana da damuwa! nace"Tambaya kamar akwai abinda ke damunki." Tace"Wallahi tun safe gabana yake faduwa." Shuru nayi ina kallonta tace."Allah yasa dai alkairi ne amma faduwar gabar ya tsananta!! ajiyar zuciya na sauke nace"Nima haka tun dazu gabana ke faduwa sai dai ki yawaita kiran innalillahi insha Allahu babu wani abu da zai faru."
Tace."Insha Allahu. daki na shiga ina addua a cikin zuciyata, na shirya jikina, dadduma na hau na tayar da sallar azuhur, bayan na idar fitowa nayi na sameta a kwance a rumfa bacci na nema ya dauketa, nace"Tambaya ai gwara ki tashi kiyi wanka kada kiyi bacci lokacin sallah yayi." Tace."Ai naji ba'ayi kiran sallah ba shiyasa na d'an kwanta na matse." nace"Yanzu za'a kira daya da rabi." Kiran sallar ne ya katseni nace"Kinji ko.'' mikewa tayi tana hamma, nace "ai zafi akeyi kawai kiyi da ruwan rijiya nima dashi nayi." tace."aikam dai waye zai sawa kansa ruwan zafi yanzu.
Mikewa tayi nayi sauri fita na zuba mata ruwan wankan kicin na shiga na d'ebo abinci a plate na zauna a tsakar gidan, loma uku kacal nayi naji gabad'aya abincin ya fita daga kaina, duk sona da wake da shinkafa naji bana sha'awa, guri guda na zubawa ido......"Sumayya." muryar babana naji a kaina. da sauri na dago ina kallonsa yace."Me yake damunki kika zabga tagumi." Da sauri nace"babu komai baba." zama yayi kusa dani yace."Sumayya akwai abinda ke damunki tun dazu nake tsaye ina miki magana kina can tunani kinsa abinci a gaba kin kasa ci."
Hawaye ne suka 'kwace min. Lawi jikinsa yayi sanyi ganin yanda take kuka.
A sanyaye yace."Ki fada min damuwarki."? hanci na shaqa nace."Baba wallahi tun dazu gabana ke fad'uwa sai nake ji a jikina kamar wani abu zai faru dani."


Lawi jikinsa yayi sanyi yace."Sumayya dukkan tsanani yana tare da sauki babu abunda zai faru sai alkairi ki kwantar da hankalinki ki daina damuwa a duk lokacin da gabanki ya fadi ki dinga addua kinji ko." Hawaye nagoge yay murmushi cikin sigar so ya kwantar min da hankali yace."Bari na zauna na taya ki cin abincin." murmushi nayi nace."Aikuwa naji dadi baba ka zauna muci tare ina so na samu albarka." hannunsa yaje ya wanko yazo ya zauna kusa dani a nutse yace."To saka hannu muci. ina murmushi nasa hannuna a nutse muka fara cin abincin Tambaya ta fito daga bandaki ta same mu mirmushi tayi ta shiga daki domin kimtsa jikinta, koda muka cinye abincin cewa yayi na bari ya dawo daga masallaci sai mu 'kara wani nace "to." ruwa na zuba masa a buta ya daura alwala ya fita.






To wajejan biyar saura na yamma na isa sashen Yarima na dinga wulkita idona a harabar gurun ina neman Haruna banganshi ba, Sai Hamza na gani a zaune a rumfar masu gadi suna hira, kai tsaye rumfar na nufa a nutse muka gaisa dasu.


Nace."Hamza ina Haruna ne."? yace."Sumayya tun safe rabona da Haruna amma Mika'il yanzu yake fad'a min wai sunje kaiwa Yarima abinci ofis."


Na kalli Mika'il cikin faduwar gaba nace"Kana nufin har yanzu basu dawo ba."? Yace."Eh wallahi basu dawo ba watakila ko Yallabai din ne yace su zauna su jirashi." ajiyar zuciya na sauke nace"Eh haka zata iya kasancewa ai yanzu zaka gansu tunda biyar ta kusa." Suka ce hakane, nace"bari na shiga ciki." suka ce "To sai kin fito." wuce wa nayi ina sauke ajiyar zuciya da godewa Allah.




To har na gama dukkanin ayyukana a shashen babu alamun dawowarsu na shiga mamaki mai tsanani dan idan ba wani gagarimun abune ya faru ba to Yarima baya kaiwa karfe shida a asibiti biyar yake dawowa ko biyar da rabi yau gashi har shida ta wuce ana dab da kiran sallar isha'i bai dawowa, gabad'ayanmu ma'aikatansa mukayi jugum-jugum muna Jimami, Mika'il yace."Bari kawai naje asibitin naga abinda ke faruwa ni dai nafi tunanin aiki ne ya rikeshi." Nace."Idan aiki ya ri'ke Yarima su kuma su Haruna me zai ri'kesu."? Hamza yace."Nima dai abinda na gani kenan." Mika'il yace."Bari dai naje insha Allahu babu matsala." Muna kallo Mika'il ya shiga mota ya tafi gabad'ayan mu muka zauna zaman jiran tsammani.





'Daya daga cikin ma'aikatan dake tsabtace asibitin ne yake shawagi a sa'ko da loko na asibitin da tsintsiya da mazubin shara a a hannunsa duk inda yaga leda ko takarda sai ya dauke, tun daga nesa ya hangesu a kwance k'udaje sai binsu suke, gabansa na fad'uwa ya isa gurin, ganinsu a sheme ido a kafe yasa ya tsorata a guje ya yar da mazubin sharar ya ruga cikin asibitin........Yana haki! ya shiga reception din, jama'a suka bishi da kallo, kai tsaye ofis din Yarima ya nufa, masu gadin gurin suka mike tsaye, tare shi suke yana yun'kurin shiga daya daga cikinsu ne ya buga masa tsawa da fad'in "Kai kada ka karya mana doka mana ka nutsu kafad'a mana abinda ke faruwa." Yana haki! yace."Babu lafiya a cikin asibiti nan can wajejan shuke-shuke naga gawarwakin mutane biyu."" Gabadaya jama'ar dake gurin suka tsorata jin abinda ya fada, gurin ya kaure da hayaniyar da tayi sanadiyar fitowarsa, kafin ma ya tambayi ba'asi suka fara sheda masa abinda ke faruwa. kafin kice kwabo gumi ya jiqashi, hanyar futa ya kama wasu daga ciki suka rufa masa baya masu tsoro kuwa tuni suka silale daga asibitin.


Magajin sarki hankalinsa yayi masifar tashi ganin su Haruna a sheme idanunsu a tsaye suna kallon guri guda, kallo daya yayi musu ya fahimce cewa sun dade da rasuwa, jikinsa ya dinga kyarma ya dinga nanata kalmar innalillahi wa'ina ilahi raji'un! hankici ya dauko ya goge gumin goshinsa ya dago kansa yana kallon jama'ar da sukayi dafifi a kansa, tsaye ya mi'ke ya umarci mutum biyu daga cikinsu akan suje su sanyo safa a hannuwansu domin su harhad'a kwanakun abincin................Jami'an tsaro da 'yan jarida ne suka k'araso gurin, kallonsu yake yana mamakin wanda yaje ya fad'a musu, suna zuwa gurin suka fara aikinsu sai bayan da suka gama daukar gawarwakin a hoto suka dawo da hankalinsu kansa, yana tsaye kamar mutum mutumi k'wayoyin idanunsa sun kad'a sunyi jajawur....."Yallabai ya akayi wannan al'amarin ya faru a cikin asibitin ka wanda muke mutukar alfahari da samuwarsa a wannan jaha tamu." ? Tambayar da suka jefo masa kenan dukkaninsu sun rufeshi had'e da kara wayoyinsu a gurin bakinsa.


Girgiza kansa kawai yake yana kallon Kasan gurin yayinda masu daukar hoto suke ta aikin daukarshi a duk motsin da zaiyi.....ya kai kimanin minti biyar yana kallon kasan gurin kafin ya dago kansa a nutse yace."Ni akayi nufin a kashe sai tsautsayi ya ritsa da wa'innan bayin Allahn kamar yanda ya kwanakin baya d'aya daga cikin bayina ya rasu a sakamakon cin abincin daya kasance abincin cina."


"Ranka ya dad'e " A gaskiya wannan al'amarin yana bukatar kayiwa mutane cikakken bayani shin ya akayi suna hadiman ka suke cin abincin daya kasance naka abun tambaya anan shine a ina za suga abincinka suci? ranka ya dad'e muna so kayi mana cikakken bayani."


Murmushi yayi wanda kana ganinsa kasan na nadama ne yace."Ni nake basu da hannuna." gabad'aya mutanan gurin suka zuba masa ido suna mamakin maganarsa, 'Yan jaridar kuwa caaa! sukayi a kansa, Girgiza kansa kawai yayi ya kalli ma'aikatansa ya basu umarnin su d'aure gawarwakin su had'a guri guda susa a mota sukai masarauta..........Daya daga cikin jami'an tsaron yace.''Yallabai akwai bukatar muje da kai station mu tattauna da kai."
Ba tare da damuwa ba yace "babu damuwa........ Gaba yayi suka rufa masa baya yayinda jan jarida suka bi bayansu a guje suna daukar hotonansu har suka shiga mota, da hannu ya kira d'aya daga cikin ma'aikatansa yace." Lallai a ajiye masa ragowar abincin da mamatan suka ci zaiyi binkice a kansa." Jiki a sanyaye ya amsa ya matsa daga jikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login