Showing 6001 words to 9000 words out of 150413 words
Chapter 3 - Kwarya Tabi Kwarya Book Complet by Binta Umar Abbale .txt
ganin za'a iya kai min abincin sashena idan na samu nutsuwa sai na zauna naci." Ta washe bakinta cike da jin dadi tace"To shikkenan yanzu zansa a kai maka kamar yanda ka bukata."
A nutse ya juya domin yiwa 'yan uwan nasa godiya sai kawai yaga sunyi masa caaa! da ido da sauri ya sunkuyar da kansa yana mamakin kallon da suke masa tamkar basu taba ganinsa ba, babu cikakkiyar walwala a maganarsa yace." My Aunt's ina godiya da hidima." Da farin ciki a fuskokinsu suka shiga amsawa, rufaffun takalmasa yasa ya fita daga falon, a tsaye a samu su Shatima na jiransa ya fito, kai tsaye suka wuce side din Baba Waziri nan ya samu cikakkiyar karba da kulawa gurin matayensa kamar yanda yake tsammani cike da jin kaunarsu yay musu sallama, Bangaran Ciroma da Galadima kuwa bai samu wata cikakkiyar kulawa ba dan kafatanin su adawa suke dashi Shatima da Moddibo ne kawai suke d'an nuna masa kauna da kulawa suma d'in Allah ne kad'ai yasan abinda ke zuciyarsu.......Wannan dalilin ne yasa tunda ya zauna yake tunanin al'amarin a rayuwarsa ya tsani rabuwar kai da lalacewar zumunci! ya fahimci suna masa hassada sosai saboda mahaifinsa ne ke kan mulki dukkaninsu suna zargin kamar shine zai maye gurbin mahaifinsa bayan Allah ya dauki ransa wanda shi kuma basu san mulki da wani abinda ya shafeshi baya daga cikin tsarin rayuwarsa, a wannan zamanin jan ragamar al'umma na da wahala mutuka shiyasa gabadaya baya da ra'ayi maye gurbin mahaifinsa.
Ya jima zaune a gefen katafaran gadonsa daya sha shimfid'u na alfarma irin na saurata kafin ya miqe a nutse ya nufi toilet din wanda shi kansa abin kallo ne duk abinda mutum ke bukata a kwai a cikin toilet d'in, tsaf yayi wanka ya fito daure da towel a k'ugunsa, a bakin k'ofa ya samu wani bawa hannunsa ringume da kayan sawa irin na sarauta.
Gefan gado ya samu ya zauna ba tare da yace komai ba, bawan ya karaso tare da durkusawa a gabanshi yace."Ranka ya dade ni sunana Haruna ni zan dinga yi maka hidima da duk abinda kake bukata na shigo naji kana wanka sai na dau'ko maka tufafin da suka dace.''
A nutse ya d'ago kansa yana kallon kayan dake hannun bawan, manyan kaya ne irin na saurata har da nad'i da katuwar alkyabba sam ba zai iya sanya kayan nauyi a jikinsa ba.
Girgiza masa kansa yayi a nutse yace."Mayar da wa'innan kayan ka dauko min masu sauki." Da saurin ya miqe da kayan a hannunsa ya bud'e shirgegiyar wardorobe din dake kafe a bangon dakin ya ajiye kayan tare da nemo masa irin kayan da yake bukata......Farin yadi filtex mai taushin gaske ya dauko mashi ya jiye kusa dashi kana ya sake komawa wardorbe din ya dauko wani dan madaidaicin akwati shima yazo ya ajiye masa a kusa dashi........Wata iriyar hula naga ya dauko mai tafe da takalminta yazo ya tsuguna tare da cire ledar data lullube hular da takalmin ya d'ora kan kayan ya miqe tsaye da sauri tare da matsawa gefe guda kansa a kasa yace."Ranka ya dad'e na dauko maka dukkanin abin bukata ka duba ka gani idan da akwai wani abinda kake bukata.
Gefan da kayan suke a ajiye ya duba minti biyu yana kallon gurin kafin yace."Jeka nagode." Da sauri ya sunkuyar da kansa kasa gami da fadin"Godiya nake Magajin sarki." yana gama maganarsa ya bude kofar dakin ya fita da saurin gaske........A nutse ya miqe ya nufi gaban mirror din dake cike da kayan shafe shafe da turaruka na mussaman irin na masu sarauta, Cream kawai ya shafa a jikinsa ya shafawa jikinsa turare mai kamshi, kana ya bar gurin, tsaf ya shirya jikinsa cikin farin yadin wanda akayi masa d'inki mai yankakken hannu irin na zaman gida gaban rigar da bayanta anyi aiki da farin zare wanda yake nuni da tambarin masarautar, a nutse ya bude akwatin nan naga tarin agoguna da manya manyan zubonan azurfa kala kala sai sheqi sukeyi, agogo mai sarqa yasa a hannunshi na dama kana ya zura wasu zubonan azurfa a tsayunsa guda biyu na hagu da dama, zubonan suyi masa kyau sosai da sosai. ya mayar da a kwatin ya rufe ya dauki hular yana gyarata hula ce aka d'inkata da wani irin yadi mafi akasari ma masu saurata suke amfani da ita tsayin hular ne ya bashi dariya ya dinga duba hular yana tunanin ajiyeta ya bar kansa a haka sai dai yayi dubarar lankafe saman ta ya rage mata tsayi yasa a kansa kana ya zura takalman dake gabanshi masu kalar hular .....Gaban mirror ya tsaya yana sake duba kansa, murmushi ya dinga yi yana shafa siririn sajen fuskarsa lallai malam bahaushe yayi gaskiya da yake fad'in kowa ya bar gida to gida ya barshi, yaushe rabonsa da sanya manyan kaya a jikinsa, sai yaga shi kansa ya k'arayiwa kansa kyau da kwarjini wannan zungureriyar hular da yake wa dariya yaga tayi masa kyau sosai ta sake fito masa da kewayayyar fuskarsa mai dauke da k'ayataccen sajensa, ajiyar zuciya ya sauke a nutse ya bar gurin mirror kai tsaye hanyar fita daga dakin ya nufa...........Yana fitowa Haruna dake tsaye kamar gunki a kofar dakin yayi kasa da kansa tare da fadin"Barka da fitowa." Ba tare da yace masa komai ba ya wuce cikin falon.....Nan ya ganta a hakimce a kan kujera k'afarta d'aya kan 'daya tana sakar masa kyakkyawan murmushi...........Idonsa a tsaye a kanta ya samu guri ya zauna cikin d'aya daga cikin k'ayattatun kujerun dake kewaye da falon Wani irin zama yayi irin na masu mulki yasa mata idonsa yana kallo fuskarsa babu d'igon annuri.
Gimbiya Lawisa cikin iyayi da iyawa ta ma'kale murya tare da fadin "Barka da fitowa magajin sarki inayi maka barka da dawowa masarauta lafiya."
falon shuru yayi bayan gama maganarta tana jiran amsarsa taji shuru bece komai ba, dago kai tayi tana kallonsa taga yana ta kallon jikinta.......Yarima Ali na da muguwar d'abi'ar san mata dan ko acan amurukan ma shagalinsa ya sha da matan turawa da bakaken fata amma duk kulafucinsa bai ta'ba zina ba sai dai romancing nan yake biyawa kansa bukata, yana da bala'in san mata masu kyau da k'irar jiki, Gimbiya Lawisa nada kyau da lafiyayyan jiki shiyasa ya gaza dauke idonsa daga kanta sha'awarta ce ta d'arsu a zuciyarsa. Ganin tana kallonsa tana murmushi yasa yayi gyaran murya da kyar yace."Daga wane 'bangare kike.''? 'Yar dariya tayi tana kallonsa tace"Yanzu dan Allah baka gane ni ba ? nice fa Lawisa ta gurin Baba Ciroma 'kanwar Moddibo."'
Sajensa ya shafa har yanzu babu fara'a a fuskarsa yace."Ya za'ayi na gane ki bayan rabona daku sama da shekara goma lokacin dana bar gida ina tsammanin baki kai shekaru bakwai a duniya ba."
Tace"Eh hakane kam shekaruna takwas a lokacin daka tafi karatu amma kuma ni kaga ban mance da kai ba."! Shuru yay yana kallonta, Ta cigaba da cewa"Wannan dalilin ne yasa ma na shirya gagarimar walima domin taya ka murnar dawowa gida lafiya.'' Murmushi yayi yana kallonta yace."Nagode 'Kanwata inaso naga ana nuna kulawa akaina nayi farin ciki sosai da wannan karamcin yaushe ne kika tsayar da taron.
Cikin farin ciki da jin dadi tace"Naji dadi sosai daka kar'bi magana ta da mahimanci nagode sosai sannan kuma ranar jumaa ne ranar dana tsayar domin taron walimar." Da ragowar murmushi a fuskarsa yace."To shikkenan Allah ya kaimu ranar lafiya."
Falon yayi shuru Lawisa sai sa'ke-sa'ke take a cikin ranta tana tunanin ko kawai ta fad'a masa tana sonsa tunda taga nan da nan ya kar'bi maganar da ta kawo masa da muhimanci.....tana kokarin tayi magana......Aunty Safiyya d'aya daga cikin yayyunsa ta shigo falon bayanta wasu bayi ne mata guda biyu suna dauke da tire din abinci kai tsaye can gurin daining suka..........Aunty Safiyya ganin Lawisa a zaune tana murmushi yasa tayi saurin kallonta ta kalli 'kanin nata sai kawai taji farin cikin ganinsu a tare lallai babu shakka Lawisa zata taimaka musu gurin ganin bukatarsu ta biya a kansa.....Cike da farin ciki gami da nuna jin dad'i tace"A'a k'anina soyayya akeyi ne.'' Kansa ya sunkuyar qasa bece uffan ba.
Ita kuwa Lawisa sai murmushi takeyi na jin dadi tana kallon aunty Saffiyan tana sunkuyar da kanta.
Kusa dashi taje ta zauna kamar gaske ta dafa kafad'arsa da fadin'' A gaskiya nayi farin cikin ganin ku a tare dama babban burinmu a yanzu kayi aure ka sake zama babban mutum to alhamdullilahi tunda ma 'yar gida za'ayi towo na mai na ne abun yayi dad'i nasan kuma iyayenmu zasuyi farin ciki mutuka, kuma inaso na tabbatar maka da cewar kayi sa'ar matar aure domin dai Lawisa babu abinda ta nema ta rasa na bangaran kyawun hali ga uwa uba kyawun sura."
Ya d'ago kanshi a nutse yana kallonta "Aunty Safiyya waye yace miki soyayya muke? fitowa ta kenan daga daki na sameta a zaune dan sai da ta gabatar min da kanta na gane cewar famliy nace, tazo tana sheda min walimar da ta shirya domin murnar dawowata gida wannan shine dalilin daya saka kika gan mu a tare."
*BINTA UMAR ABBALE*
Shearing ����
2/11/21, 8:19 AM - ???: *'KWARYA TABI 'KWARYA*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE�_ *bintaumarabbale@gmail.com*
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊�*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
_________________________
*Littafin na kudi ne....!*
_#300.....0542382124...Binta Umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin.......... Ga masu bukatar VIP Group 600 ne_
_Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d'aya 90899076_88137740_
*SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
9&10
Sarki Abdul-aziz yayi gadon halin mahaifinsa marigayi Maimartaba sarki Adamu gurin kyawawan halaye sosai al'ummar gari ke jin dadin mulkinsa gabadaya 'yan uwansa sunyi masa mubaya ma'ana sun bashi hadin kai sosai amma banda Ciroma muguwar hassada yake masa da kasantuwarsa a kan karagar mulki Ciroma babu irin qulunboton da ba yayi akan ya ruguza mulkin sarki Abdul-aziz Allah bai bashi nasara ba daga karshe sai ya hakura da biye biyen bokayen ya dawo yana shirya mana'kisa ta karkashin qasa....Sarki Abdul-aziz na da mata biyu Gimbiya Huwaila itace uwar gida ana kiranta da mai babban da'ki haihuwar su bakwai tare amma duk mata ne.....Gimbiya Hawwa 'yar sarkin Agadaz itace matarsa ta biyu ana kiranta da Fulani sai da suka shekara shida da aure ta samu ciki maimartaba ya tsananta addua akan cikin yana addua akan Allah ya azurtashi da samun d'a namiji ya zama magajinsa...........Allah maji rokon bawansa sai ya amsa masa adduarsa a daidai lokacin da mutane ke tsammanin Fulani zata haifi mace sai Allah ya nuna musu ikonsa Aliyu ya diro duniya cikin koshin lafiya da kuzari.....Haihuwa wannan yaro tayi masifar tashin hankalin Ciroma ya rasa inda zai saka kansa yaji dadi, shi duk a tunaninsa Abdul-aziz ba zai ta'ba haihuwar da namiji ba saboda yana ganin duk 'ya'yansa mata ne kamar dai yanda mahaifinsa ya dinga haifar 'ya'ya mata kafin ya rasu.......Mai d'akinsa rasa gane kansa tayi a lokacin dan kulle kansa yake a daki yayi ta surkulle lallai sai yaga karshen jinjirin daka a haifa, wanda tunda ya dira a duniya mahaifiyarsa ta d,daura masa wata 'yar sar'ka a wuyansa mai dauke da ayatulkursiyu a jiki, wannan dalilin yasa duk tsaface tsafacen da yake yi baya tasiri.
'Bangaran Mai babban daki kuwa itama ita da yaranta rasa nutsuwa sukayi dan gabad'ayansu basu tsammanin Fulani zata haife cikin jikinta lafiya ba saboda irin fadi tashin da sukeyi a cewar 'ya'yan wai su ba zasu had'a uba da kowa ba shiyasa tun sanda mahaifin nasu ya auro Fulani Hawwa suka tashi a tsaye dasu da mahaifiyarsu suka dinga jifanta da asiri iri iri wanda ya janyo mata matsala dik lokacin data samu ciki daga zarar yayi kwari sai ya zube hankalinta ya tashi sosai ta dage da azkar gami da rokon Allah ya kareta dan tayi imani cewar al'janu ne ke ra'bar jikinta tunda wani lokacin idan ta kwanta bacci suna zuwa suyi ta tsorata ta.......tunda ta samu cikin Aliyu ta dage da adduar har Allah yasa yayi k'wari gashi cikin ikon Allah ta haifeshi lafiya dalilin daya sa kenan tana haihuwarsa ta daura masa wannan laya mai dauke da ayatulkursiyu saboda tasan tilas ita da yaron su fuskaci kalubale mai girma a masarauta...........Yarima Ali ya taso cikin kauna da so da kulawar iyayensa duk wanda ya kwana ya tashi a cikin gidan yana kaunarsa, Ita kanta mai babban daki ganin kamar maimartaba naso ya gane manufarta akan yaron yasa ta zauna da 'ya'yanta ta umarce su akan kada su sake su nunawa yaron 'kiyayyarsu a fili komai za'ayi ta karkashin kasa za'ayi masa, wannan dalilin yasa suke danne hassadarsu a kansa suke nuna masa kauna ammfa Allah ne kadai yasan abinda ke zuciyoyinsu..........'Bangaran 'yan uwan mahaifinsa kuwa babu wanda ke nuna masa kauna da kulawa sama da Waziri shike jansa a jikinsa sosai yana nuna masa so hakan yana yiwa maimartaba dadi a cikin ransa yana kuma yiwa dan uwan sa addua akan Allah shima ya azurtashi da 'ya'ya masu albarka, Waziri Abdul-raham matansa uku amma duk cikinsu babu wacce ta ta'ba haihuwa sai da ya auri matarsa ta uku da yake bazawarace tana da 'ya'ya a wani a gidan sannan aka gane cewa rashin haihuwa daga gurinsa ne shiyasa yake masifar kaunar 'ya'yan 'yan uwansa.......wannan dalilin yasa Ciroma da Galadima suke jin haushinsa dan ganin kamar yana fifita Yarima Ali akan 'ya'yansu Galadima shine mahaifin Shatima shi kuma Ciroma shine mahafin Moddibbo wanda yaci sunan mahaifinsa shine suke kiransa da suna Moddibo, Ciroma Abdul-Jabbar nada 'ya'ya goma dan duk yafi 'yan uwansa yawan 'ya'ya shiyasa har kullum yake fatan sarauta ta dawo hannunsa, mata shida maza hud'u, cikin 'ya'yanshi akwai mai izzah da taqama tamkar ubanta ne a sarki a cikin masarautar haka take rashin mutunci tare da cin mutuncin duk wanda tayi ra'ayi, Gimbiya Lawisa kyakkyawa ce ta karshe sai dai ko kusa ko alama bata da kyawun hali tana da d'abiar izigilanci da wulakanta mutane mutum komai girmansa bai wuce cin mutunci a gurinta ba........Gimbiya Lawisa tun kafin tayi wayo tayi hankali Allah ya d'ora mata masifar son Yarima Ali a cikin ranta duk da tana yarinya k'ank'anuwa ya tafi karatu hakan besa ta mance kammanin sa ba. shiyasa yanzu take ta murna da farin cikin dawowarsa masarauta sai shirye shiryen walima takeyi domin nuna masa farin cikin dawowarsa lafiya........Da kanta ta shirya tsaf cikin shiga ta alfarma tare da bayin dake take mata baya ta nufi 'bangaransa domin sheda masa abinda ta shirya masa na taya murna..........
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 8:19 AM - ???: *'KWARYA TABI 'KWARYA*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE�_ *bintaumarabbale@gmail.com*
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊�*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
_________________________
*Littafin na kudi ne....!*
_#300.....0542382124...Binta Umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin.......... Ga masu bukatar VIP Group 600 ne_
_Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d'aya 90899076_88137740_
*SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah)
13&14
Aunty Safiyya a nutse take kallonsa kafin tace"Kai kuwa Magajin sarki meye laifin Lawisa dan Allah kada kaje ka dauko mana ta waje gwanda ka duba a cikin gida ina ganin kamar haka zaifi alkairi." Shuru yayi mata tare da sunkuyar da kansa. Tace"Idan ka auri 'yar uwarka a ganina sai kafi samun cikakkiyar kulawa kuma tabbas hakan zai faranta ran iyayenmu dan Allah ka duba maganata da kyau kaji ko."! har yanzu kansa na sunkuye a kasa ya'ki kallonta ballantana ya bata amsa. mirmushi tayi tare da mikewa da fadin"Miskili kenan to kai dan Allah da irin wannan halin naka wacece zata iya zama da kai idan ba 'yar uwarka ba? babu macan da zata juri wannan wulakancin naka."
'Dago kansa yay yana kallonta cikin rashin walwala yace."Aunt Safiyya mai yasa kuke yi min irin wannan kallon ne? wallahi ban san ya ake wulakanci ba a rayuwa ku lura da kyau da'bia tace rashin son doguwar magana shiyasa nayi shuru na kyale ki amma duk irin maganganun da kikeyi ina jinki."
Murmushi tayi tana kallonsa tace"Eh ni zan fadawa kowa hakan d'abi'ar kace shiyasa ma ai nace bama so ka auri bare gwara ka auri ta gida domin sai tafi jurar zama da halayen ka." murmushi yay wanda ya tsaya iya lab'bansa yace."Aunt Safiyya ki bar wannan maganar dan Allah.'' Jin abinda yace yasa Lawisa saurin kallonsa gabanta na faduwa lallai wallahi tasa rai ganin aunty Safiyya ta shiga maganar yasa take jin tamkar ma ta aure shi ta gama.
Aunty Safiyya ta kalleta tare da fad'in "Lawisa kina sonsa ko."? babu kunya tace" Eh aunty. " murmushi tayi tare da kama hanyar fita tana fadin"Ba zan tafi gida ba har sai na bari an tashi daga fada na fadawa maimartaba halin da ake ciki.
Da sauri ya dago kansa yana kallon bayanta cike da mamakin jin abinda ta fad'a......Fuska a kirne ya kalleta da fad'in "Tashi ki fitar min a daki wato dama abinda ya shigo dake kenan? waye ya fad'a miki ina sha'awar auran zumunci dake."?
Lawisa gabanta ya dinga faduwa tana so tayi magana amma ta kasa saboda tsabar kwarjin da yayi mata gashi ya tsareta da idanunsa masu girman da furgita mara gaskiya.
A sanyaye ta miqe tana gyara alkyabbarta hanyar fita ta kama ranta sai tafarfasa yake yi lallai wai duk wannan kyawun nata da kyawun surar jikinta bata burgeshi ba hakika taji takaicin tsawar da yayi mata meye laifinta da zaice baya sha'awar auran zumunci da ita.......masu take mata baya ganin ta fito fusace yasa suka shiga hankalinsu da sauri suka rufa mata baya suna sunkuyar da kansu 'kasa.............
****
Cikin saurin na fito daga gurin mu domin zuwa duba dawakan da babana ke hidimarsu tun safe dana zuba musu abinci ban sake zuwa duba su ba saboda yini mukayi wankin kayanmu nida mahaifiyata wannan dalilin ne yasa ban