Showing 102001 words to 105000 words out of 150413 words

Chapter 35 - Kwarya Tabi Kwarya Book Complet by Binta Umar Abbale .txt

tace"Ai duk sanda kike so kije gaishe da iyayenki ina ganewa na rasa me yasa kike jin kunyata Sumayya." 'Yar dariya nayi nace"Mamma kece Allah yayi miki kwarjini shiyasa nake kasa fada miki.'


Yar dariya tayi tace."Kwarjini har na kai ki sumayya."? da sauri na kalleta, ta daga min kanta tare da fadin"Gaskiya da rikon amanarki suna burgeki sumayya inaso ki sake dam'ke gaskiya hannu biyu duk rintsi kada ki kauce hanya ki tsaya akan gaskiyarki." Nace"Insha Allahu zan kula da maganarki.'




Tace."Babu damuwa kina iya zuwa ku gaisa amma kada ki tafi ke kadai kuje tare da mutum biyu." nace"To shikkenan." Ina kokarin mikewa ta shigo falon, kallo daya nayi mata naji gabana ya fadi, hajiya Karima ce! Mamma tace"Sannu da zuwa hajiya yau kece a gurina."


Cikin ya'ke tace"Fulani kenan ai kin san komai da dalili.'' guri ta nema ta zauna! na dan risina a nutse nace"Barka da yamma ranki ya dade." Wani banzan kallo tayi min kafin ta ta'be baki ciki-ciki ta amsa min. A sanyaye nace"Mamma sai na dawo." da sauri tace"To sumayya ki gaishe min dasu da kyau." Nace"Insha Allahu zasuji."
Hajiya Karima bin ta tayi da ido tana girgiza kanta, sauke ajiyar zuciya tayi bayan fitarta tace"Fulani gurinki nazo."




Mamma ta gyara zamanta sosai tana fuskantarta tace"Ai dama tunda na ganki nasan da akwai magana Hajiya Allah yasa alkairi ne yake tafe dake."




Hajiya Karima gyara yanayin fuskarta tayi tace"Magana ce akan Lawisa naga tunda ake maganar auran nan banji ana saka sunanta ba idan Ali ya fasa auranta ina bukatar karin bayani.


Cike da mamaki take kallonta kafin tace"Hajiya Karima wannan wace irin magana ce haka? a gaskiya banji dadi ba in banda abinki ya za'ayi Babana ya fasa auran 'Yar uwarsa."




Murmushin takaici tayi tace."Haba Fulani ai dole nayi zargin hakan saboda ganin gabadaya an daina zance Lawisa sai na wannan baiwar akeyi ai dole dukkaninmu muyi tunanin ko baiwa tafi 'yar sarauta."




Mamma ta girgiza kanta tana kallonta tace"Hajiya Karima dan Allah ki dinga gyara maganarki ya za'ayi kina babba ki dinga sakin maganganun da basu dace ba, wannan yarinyar Sumayya tuntuni ta 'yantu ta shigo cikinmu dan Allah ki daina irin wannan maganganun basu da dadi.


Tace"Sumayya ta 'yantu amma kuma bata gaji sarauta ba ko.''? Fulani ta kalleta takaici kamar ya kasheta, Hajiya Karima ta cigaba da cewa" Wannan yarinya Sumayya sam bata dace da Ali ba saboda gabanta da bayanta bayi ne mak'as'kanta, wallahi ni rasa wace jaraba Ali ya hango a jikinta ."




"Nagarta da kyawun hali babana ya hango a tare da ita shiyasa yayi sha'awar auranta, Kin san mazan da suke da wayo a yanzu sun daina duba so ko nasaba a aure nagarta da tarbiya suke dubawa kafin su auri mace wanda yanzu samun irin masu nagartar yarinyar nan zaiyi wahala sosai."




Tsaki taja tace"Duk da haka dai Masarauta nada al'ada a tarihin masarautar nan banta'ba jin wanda ya auri baiwarsa ba sai Ali ina ganin kamar zai barwa zuri'arsa abin magana."




Fulani tayi dariya tana kallonta tace"Babu wani abin magana da zai barwa iyalinsa, baiwa itama mutum ce kamar sauran mutane kuma idan Allah ya kaddara auran Babana da wannan yarinya rabo ya shiga tsakaninsu sai kiga ta haifi Sarki duk da take baiwa ma'kaskanciya babu ruwan ubangiji.


Da sauri hajiya Karima tace"Bana fatan nayi tsawan ran da zanga wannan rana dan lalacewa ace d'an baiwa shine zaiyi mulki tunda nake banta'ba ganin wannan kwamacalar ba."




Fulani ranta ya 'baci sosai ta rasa me yasa matar take da izgilanci rayuwar duniya a sannu ake bin ta na sama yana iya dawowa kasa na kasa ya hau sama, mutukar sarki ya auri baiwa ya 'yantata to idan ta haihu d'anta yana da gadon sarauta tunda dan sarki ne gabad'aya basu san mecece sarauta ba babu shakka koda mulki aka basu to ba zasu iya aikata komai ba sai shashanci!


Ajiyar zuciya ta sauke tace"Hajiya Karima magana ta 'kare kije ki kwantar da hankali insha Allahu Babana zai auri Lawisa kamar yanda ya dauki alkawari tun farko."


Ta mike tana gyara lullu'binta tace"To yanzu naji kinyi magana mai kyau ni zan koma gurina." Fulani ta bita da kallo har ta fita daga falon, girgiza kanta tayi tana mamakin halin matar kwata kwata bata da dad'in sha'ani gashi duk maganar da tazo bakinta fad'a take bata taunawa.




Yau Yarima bai dawo gida da wuri ba hankalinmu duka ya tashi, Mamma ta kalleni a nutse tace"Ko zaki kira shi da wayarki ina ganin idan ya fad'a mana halin da yake ciki sai hankalinmu yafi kwanciya.'' Cikin nauyi nace"To shikkenan bari na dauko wayar a daki." a nutse na mike........Zama nayi gefan gado da wayar a hannuna number shi na kira sai da ta kusa katsewa tukkuna ya dauka, ajiyar zuciya na sauke a nutse nace"Ranka ya dade barka da dare." "Barka dai." ya amsa a takaice, nace"Muna nan hankalin mu duk ya tashi baka dawo da wuri ba ina fata lafiya."


Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke yace."Sumayya ina da marasa lafiya ne mata biyu ne zasu haihu haihuwar tazo da tangard'a yanzu shirye-shiryen shiga dasu dakin teatar ake."


A sanyaye nace"Allah sarki wallahi har naji tausayinsu Ubangiji Allah ya sauke su lafiya." Ya amsa da "ameen ya rabbi ki bani Mammana mu gaisa." da sauri na mike da wayar a hannu na sameta zaune a inda take.
A sanyaye nace"Mamma gashi na sameshi a wayar." da sauri ta kar'ba tasa a kunnanta tana kiran sunansa.


Yace."Mamma Allah yayi miki albarka yasa ki gama da duniya lafiya." ta amsa da "ameen babana yana jika wani iri Allah yasa kana lafiya." a sanyaye yace."Lafiya ba lau ba mamma yau na shiga rud'ani mutuka! da sauri tace"Subahanallahi me ya faru da kai."? ajiyar zuciya ya sauke yace."Wallahi Mamma wasu mata biyu ne zasu haihuwa sai wuya suke sha haihuwar ta'ki zuwa daga 'karshe ma sai al'amarin ya rikice suka dinga jijjiga duk sun fita daga hayyacinsu Mamma ashe haka kuke shan wuya gurin haihuwa."?




Cikin damuwa tace"Allah sarki! to Ubangiji Allah ya sauke su lafiya babana dan Allah duk wani taimako daka san suna bukata kayi musu Allah zai baka lada."




Yace."Insha Allahu zanyi iyakacin bakin kokarina akansu dan yanzu na bada umarnin shiga dasu dakin teatar ina ganin haka shine maslaha domin kuwa idan mun tsaya mun jinkirta to ana iya rasa rayukan su.'' A sanyaye tace"Babana Allah yasa ku shiga a sa'a Allah ya tashi kafad'unsu ya sauke su lafiya." Ya amsa da "ameeen ya Allah insha Allahu komai dare zan shigo gida idan naga aiki yayi kyau." Tace"To shikkenan ubana Allah ya bada nasara." sallama sukayi jikinsu duk a sanyaye.


Haka muka cigaba da zama a falon muna jajanta al'amarin dan ni kaina da ban ta'ba haihuwa ba ban kuma san yaya zafinta yake ba na tausayawa musu saboda wahalar da suke sha, har misalin goma da rabi na dare bai shigo ba, alamun bacci na gani a idonta a nutse nace"Mamma kije ki kwanta ki huta naga kamar kina jin bacci insha Allahu zai dawo lafiya." Tace"Wallahi kuwa bacci ne a idona Sumayya nafi so dai na zauna ya dawo naji lafiyar matan nan sun tsaya min a raina wallahi."


Nace"Nima haka Mamma addua zamuyi Allah ya rabasu lafiya insha Allah idan ya shigo komai dare zan tasheki amma yana da kyau kije ki kwanta tunda bacci kikeji kada yasa miki wani ciwon.'' Na fadi hakane domin na kwantar mata da hankali amma bana tsammanin idan ya shigo na tashe ta a bacci da safe sa gaisa......Yunkuri mikewa tayi na mike nima tare da gyara mata nad'in lifayar jikina, hannunta na rike muka shiga bedroom d'inta, gefan gado ta zauna nace"Bari na hada miki ruwan wanka.'' hannunta ta rike da fadin"Sumayya bana jin zanyi wankan nan dazu da yamma nayi kayan bacci zaki dauko min." da sauri nace"To tare da nufar wardrobe dinta, riga da wando masu taushi na dauko mata da hularsu da takalminsu na ajiye kusa da ita ta kalleni tace"Allah yayi miki albarka." kaina a kasa nace"ameeen Mamma." tace"Kina shan wannan maganin dana baki ko."? cikin jin kunya nace"Eh." tace"Idan sun 'kare koda kin tare a d'akinki ki fad'a min nasa a kawo miki wasu na fad'a miki ni ba surukarki bace kada kiji kunyata."
Ina wasa da hannuwana nace"To shikkenan Mamma." tace"Kije ki kwanta kema da safe ma gaisa dashi Allah ya dawo mana dashi lafiya."


Na amsa da ameeen tare da fadin"Sai da safe." Tace"Allah ya tashe mu lafiya." Koda na shiga dakina na jima a zaune ina tunanin rayuwa kafin nayi wanka na kimtsa jikina cikin kayan bacci riga mai hannun shima da wandonta iya gwiwa kayan masu tsantsine shiyasa suka kwanta a jikina, hula nasa a kaina har naja bargo sai kuma na cire sauke kafafuna nayi kasa a nutse na janyo drowar dake gefan gadon, magungunan na shiga fitowa dasu, tunda ta bani su tace na dinga sha kullum banta'ba shaba duk da nasan amfaninsu a tartare dani........Ajiyar zuciya na sauke a nutse na bud'e zumar itace tafi daukar hankalina bakin jarkar nasa a bakina nasha sosai na cire ina dan ya mutse fuskata gabadaya babu zaqi irin na zuma sai kadan bakina ya game da baurin magani, tsigar jikina ta dinga tashi, d'aya bayan d'aya na dinga daukar magungunan inasha ina rintse ido sai dana sha kowanne sannan na had'a maganin nasa a drowar na rufe, brush naje nayi na dawo na kwanta tare da rufe idanawana, waya ta na bari a kunne nasan mybe idan ya shigo ya kira ni sai na ajiyeta a kusa dani kawai......bacci ne yake nema ya dauke ni ina korarsa har dai ya samu nasarar sace ni 'na bingire bacci mai nauyi ya daukeni na dinga wani irin mafarkai marasa dadi........Can cikin baccina naji nauyi a kaina, a razane na bude ido ina kiran sunan Allah, da yake ban kashe hasken dakin ba yasa na gane wanene, da sauri nasa hannuwa na tureshi jikina sai 'bari yake! shima jikinsa na kyarma ya sake qamqame ni yana fitar da wani irin numfashi, a jigace nace"Wai meye haka ne."? muryarsa na dan rawa yace."Sumayya bana cikin nutsuwa ta ina cikin damuwa." jikina ya mutu nace"Ina fata ka samu nasara a gurin aikin ka."? matseni yayi sosai a jikinsa Yace."Na samu dukkaninsu anyi musu aiki lafiya lau amma d'aya yaron data haifa ya mutu." jikina yayi sanyi nace"Allah sarki Allah ya bata lafiya Ubangiji Allah ya bata wani." da sauri ya tashi daga kaina yana kallona, na mike zaune tare da kare jikina da bargo ido na zura masa naga duk ya rame! yace."Baki da hankali kike mata irin wannan fatan taci wuya irin wannan sai ta sake haihuwa." Cike da mamakin maganarsa nace"To meye a ciki ai ba'a kanta a kafara ba kuma ko wace haihuwa da irinta mybe gaba ba zata sha wuya ba."


Girgiza kansa yayi yace."Wannan ba tsari bane ace kullum rayuwar ki na cikin wahala tara 'ya'ya ba alfanu bane mutukar mace nashan wuya a gurin haihuwa sai ta 'kayyad'e ta."


Na dinga kallonsa ina mamakin maganarsa "Tara 'ya'ya shine bai da alfanu."? 'kwarai kuwa mutukar gurin daukar cikinsu da haihuwarsu na barazana da rayuwarki to gwara ki hakura.'' cikin takaici nace" Mace koda haihuwa ko babu haihuwa sai ta mutu! kuma inaso kasani duk macan data mutu gurin haihuwa tayi shahada saboda haka ka daina wannan maganar dik wata wahala mai shigewa ce iyayenmu da kakannin mu a haka duk suka tara 'ya'yansu dan haka dan Allah ka daina wannan maganar sam bata dace ba su 'ya'ya rahama ne sannan kuma a ranar lahira Annabi Muhammad (SAW) zaiyi alfahiri da jama'arsa.........








*Na kudi ne.*
Kada ki karanta min littafi sai kin biya ni! Keda da kika futa da littafin keda Allah! idan kina so ki biya ga yanda abin yake....Vip gruop#600 normal gruop#300....account... 0542382124....Binta umar gtbank....idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:28 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
91
Har yanzu fuskarsa babu sassauci yace."Nasan da haka ba sai kinyi min wa'azi ba a tsarina ni bana son tarin 'ya'ya da yawa bayan haka kuma ita haihuwar wahala gareta mutanan da dana yanzu ba daya bane nada sunfi kwari da karko na yanzu kuwa haihuwa daya biyu sun lalace shiyasa bana son ki haihu da yawa." Murmushin takaici nayi nace"Ni kam wannan magana ta isheni wallahi duk yanda nake so na fahimtar dake yanda al'amarin yake ba zaka fahinta ba saboda haka mu bar maganar iya adadin 'ya'yan da zan haifa a duniya Allah ne kadai yasan yawan su."


Shuru yayi yana kallona, babu alamun nadama a fuskarsa na dinga mamakin halinsa bashi da rufi ko kadan duk abinda yake zuciyarsa fada yake yi kansa tsaye in banda abinsa waye yake gudun rahama ai 'ya'ya rahama ne amma shi tun kafin ma yayi auran ya yankewa kansa hukunci Allah dai yasa kada zama da turawa yasa ya dauki munanan dabi'unsa dan gashi alamu nan."


Kaina na sunkuyar ganin yana kure ni da kallo nace"Ka tafi gurinka dan Allah ko da akwai abinda kake bukata."


Ajiyar zuciya ya sauke yace."Ina bukatar abubuwa guda uku amma nasan da wuya na samu duka.




Kallonsa nayi ya daga min kai da fadin"farko dai ina bukatar naji ki a jikina na biyu ina bukatar abinci na uku kuma nayi wanka."




'Bata fuska nayi nace"Tashi muje falo na baka abincin." girgiza kansa yayi yace."Kije ki kawo min nan ni babu wani falo da zanje." na jima ina kallonsa kafin nayi yun'kurin mikewa sai na tuna da kayan dake jikina da sauri na koma na zauna gabana na faduwa.


Bargon dake jikina yake kokarin janyewa na rike da kyau ina girgiza masa kaina nace"Dan Allah dauko min hijabina gashi can akan kujera.




Cike da mamaki yace."Lallai kin raina ni zaki aika."? girgiza kaina nayi yace."Dallah tashi ni ki kawo min abinci me zaki boye min bayan komai nawa ne."


Idona ne ya kawo ruwa nace"Ni dai dan Allah ka miko min hijabin wallahi kayan masu fitar da tsaraici ne." kallona ya shigayi yana girgiza kai yace."Tsaraici.''? kaina na sunkuyar ina sake rufe jikina da bargon, mikewa tsaye yayi kawai yasa hannu da karfi ya fizge bargon daga jikina, tsigar jikina ta mike da sauri na takure jikina guri guda ina watsa masa harara!


Wani irin kallo yake bina dashi tun ba kirjina ba nasa hannu ina karewa, ajiyar zuciya ya sauke a hard'e yace."Tashi." 'kin tashi nayi na takure jikina hawayen bakin ciki na nema ya kufce min......"Kin san Allah idan baki tashi ba zan aikata miki abinda bakya so yanzu." jin abinda yace yasa da sauri na kalleshi, gani nayi idanunsa ya sauya, gabana na faduwa na mike, ya bini da wani irin kallo da hannu ya nuna min k'ofar fita, ina takure jikina na kama hanyar fita a jikina naji kallona yake shiyasa da saurin gaske na bude kofa na fita.......a gurguje nake hada masa abincin kawai naji motsinsa a bayana, da sauri na juyo kirjina da nasa ya had'u hannuwansa duka ya d'ora akan mazaunaina! ya wani matseni a kirjinsa yana matsa min mazaunai! kirjinsa na doka da karfi! tsaki naja da sauri na janye jikina, bina yake da kallo kamar maye, nayi gaggawar daukar tire din dana shirya masa abincin na barshi a tsaye a gurin.


Ina ajiye tire din na dauki dogon hijabina nasa na zauna kan kujera gabadaya raina ya 'baci da irin abinda yake min.


Koda ya shigo dakin be kalli inda nake ba, yaje ya zauna gaban abincin a nutse ya zuba abinsa ya fara ci, sai da ya kammala tsaf ya tashi ya nufi toilet........jin shuru bai fito ba yasa na shiga tunanin abinda yake a ciki, motsinsa naji nayi saurin kallon kofar toilet din daga shi sai gajeran wando da vest jikinsa ya nuna alamun ruwa wanka yayi, kallonsa nake har ya isa kan gadona ya kwanta hankalinsa kwance ya rufe jikinsa da bargona.......Nace"Bangane ba." shuru yayi min.......nace"kasan bai dace ba ko dan Allah ka tashi ka tafi gurina hakan bai dace ba."


"Sumayya bazan tafi ba yau anan nayi niyyar kwanciya idan kuma kina da karfi kizo ki fitar dani." nace"Wacece ni ranka ya dade Allah ya baka hakuri." mikewa nayi na kama hanyar fita gwara na bar masa dakin akan mu kwana tare nasan halinsa zai iya haike min.


Kawai na ganshi a gabana ido jawur na kalleshi! bai tanka min ba ya murza key a jikin kofar ya zare keyi din ya barni a tsaye!


Hawayen takaici suka zubo min, a gaskiya lamarinsa akwai wuyar sha'ani! juyawa nayi naga ya koma ya kwanta tare da lullube jikinsa da bargo.




Jiki a sanyaye naje na kwanta kan sofa ina kudindine jikina da hijabina, miryarsa naji ciki ciki yace."Ki zo ki kwanta ba zanyi miki wani abuba."


Share shi nayi ina jin wani irin haushinsa a raina, magana yake min nayi masa banza daya gaji sai yayi shuru can kuma na dinga jin saukar numfashinsa a hankali nan na gane bacci ya daukeshi, a hankali na gyara kwanciyata ina addua a cikin zuciyata.




Da asubah kusan a tare muka tashi dan ina jin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login