Showing 39001 words to 42000 words out of 150413 words
Chapter 14 - Kwarya Tabi Kwarya Book Complet by Binta Umar Abbale .txt
cutar dashi, bani da bakin magana! dana sani da nadama suka baibaye ni, dana sani na bar shi ya dake ni ya mare ni nabi umarnin mahaifiyarsa na hana shi cin abincin......Sheshshakar kukanta ne ya ishe shi ido jawur ya dago yana kallonta sai yaga ta d'ora hannuwanta duk biyu a kanta tana zubar da hawaye.
Tausayi ta bashi! ya dafa bango(Garu) ya mike tsaye. da sauri na kalleshi nace"Sannu ina fatan babu inda ke maka ciwo ? bai kalle ni ba yazo zai wuce hanya na bashi ya fita nabi bayansa, samunsa nayi kasan kafet yana maida numfashi.
Gabansa na tsuguna ina kallonsa idanuwansa sunyi jaja wuyar, a sanyaye na sake yi masa sannu ina tambayarsa abinda ke damunsa.''' Kallona yay yace."Babu abinda ke damuna ki daina damunki kanki." Nace" To Alhamdullhi dama haka nake so naji dan Allah ranka ya dade ka dinga yarda da maganata dik abinda kaga inayi a kanka da umarnin mahaifiyarka nake yi ina fatan yanzu zaka gane gaskiyar maganata."
Hannu ya daga min da fad'in "Kije kawai bana san dogon surutu." A sanyaye na mike na kama hanyar fita daga dakin banji dadin gwasale ni da yayi ba..
Bayan fitar ta daga dakin mamaki sosai ya shiga yi akan abinda ya faru! to me hakan ke nufi? ashe dai duk tsayayyar da yarinyar nan takeyi da gaskiyarta 'Yan uwansa na jini zasu kasheshi!? wai shin ma snacks din da yaci na wacece a cikinsu.? bashi da mai bashi amsa, ajiyar zuciya ya sauke ya jingina bayanshi jikin gado har yanzu yana jin zafi a mak'ogwaron sa, yana jin kamar an tsatstsaga masa da reza, pridge ya bud'e ya d'auko ruwa mai sanyi wai ko ya samu sa'ida yana sa ruwan a bakinsa yaji radadi da zugi a mak'ogwaronsa da kyar ya iya had'iye ruwan ya ajiye goran ruwan a kusa dashi yana mamakin al'amarin.
Cikin sauri na fitar da kayan abincin na lodasu a cikin wani buhu mai zurfi dan har kulolin na hada ina ganin suma barinsu had'ari ne d'aure bakin buhun nayi na umarci Hamza da ya dauka ya fita buhun, oma nasa sosai na wanke hannuna kana na koma ciki.
Samunsa nayi tsakiyar falon yana safa da marwa, nace"Kana bukatar wani abune." ? "Kije ki kira min Haruna." yafada yayin da yake kokarin zama kan kujera da sauri nace to na juya na fita.
Tare muka shigo da Haruna yace."Ranka ya dade gani." Da kyar naga yayi maganar." Ungo jeka pharmacy (gurin seda magani) ka kar'bo min wannan maganin." Haruna ya 'karasa kusa dashi da sauri ya kar'bi takardar hannunsa da kudi.
Fita yay da sauri! nima na juya da niyyar fita......"Ke! juyawa nayi ina kallonsa, "Kada ki kuskura naji maganar nan a bakin kowa mahaifiyata ma ban amince ki fad'awa ba kinji ko."?
Da mamaki a tare dani nace" Ranka ya dade mai yasa baka so mahaifiyarka tasan abinda ke faruwa? wannan al'amarin fa bai kamata a 'boye ba, ya kamata ta sani domin ayiwa tufkar hanci da wuri."
"Ke baza a ta'ba fada miki magana kice to ba sai kin kawo hojjojin ki ko."? A sanyaye nace" Ranka ya dade ba haka bane duk abinda kaga na'ki aminta dashi kai tsaye to na duba naga ba mai kyau bane dan Allah ka bari a shedawa mahaifiyarka a'lamarin nan."
"Ke ki kula fa ni babu me shiga tsakanina da 'yan uwana kinji na fad'a miki ban yarda wani abu na cutarwa naci ba saboda haka na fada miki ki iya bakinki ban amince ki fadawa kowa wannan maganar ba.
Na dinga kallonsa ina jin wani irin takaici a cikin raina 'kiri-'kiri yana ganin gaskiya yana takewa sau biyu yana tsallake rijiya da baya amma wai fadi yake bai yarda yan uwansa zasu cutar dashi ba, girgixa kai nayi nace" To shikkenan tunda baka so kowa ya sani insha Allahu babu wanda zan fad'awa."
Kauda kansa yay daga kaina ya tsirawa kasan gurin ido." Nace"Ina iya tafiya."? hannu ya daga mun alamar na tafi, na juya da sauri na bude kofa na fice raina a 'bace! na isa sashen mu...
Na kudi ne..!
Koda zaki ganshi a gruopa na sata ne idan kina bukatar biyan kudi ga yanda abin yake.....Vip gruop#600 normal gruop#300...account... 0542382124...Binta umar gtbank....idan kati zaki turu #400 ne kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:26 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
47&48
"Ke ranar dana zo na kawo Apple din nan kin bashi yaci ko kuwa."? Cike da tuhuma yake min maganar sannan ya wani tsatstareni da idanunsa, cikin zuciyata nace"Ni dai na shiga uku kowa so yake yay amfani dani gurin cimma munufarsa, cikin ladabi nace" Ranka ya dade na bashi sai dai ban sani ba ko yaci ko kuma beci ba dan umartata yayi dana fita daga dakin.
Ajiyar zuciya naga ya sauke a fusace! ya bar gurin, zama nayi a sanyaye ina bin hanyar da yabi kallo nace "Insha Allahu Allah ba zai baku nasarar cutarsa ba." shuru nayi ina mamakin abinda sukeyi gabad'aya sunbi sun tayar da hankalinsu akan sa kowa so yake yaga bayansa sabida suna ba'kin cikin kada ya gaji mulki a hannun mahaifinsa, a gaskiya idan haka sha'anin sarauta yake da bita da k'ulli gami da ma'karkashiya to babu shakka akwai matsala da damuwa acikin al'amarin sha'anin sarautar dai ya zama sai gyaran Allah dan gabad'aya kowa babu Allah a cikin zuciyarsa.
Sai bayan la'asar Jama'a suka tsaigata, koda muka shiga dakin ragal muka sameshi a zaune yana ta abinda ya saba, latse latse a waya, a jiyar zuciya na sauke naji dadi sosai ganinsa lafiya lau, Haruna da 'yan uwansa suka shiga tsaftace dakin, ni kuma na kama hanya na fita daga dakin ganin ko kallon inda nake beyi ba.
Alwala nayi nai sallah na fito na sake zama ina saka wasikar jaki, muryar babana naji yana sallama da sauri na daga kaina sai na gansu shida Tambaya, wani irin farin ciki ne ya ziyarci zuciyata dama kwana biyu dauriya kawai nake da tunaninsu nake kwana nake tashi, da sauri na mike naje na taresu ina dariya nace"Baba sannunku da zuwa naji dadin zuwanku." Tambaya tace"Muna ta sa ranar zuwa Allah bai nufa ba sai yau." Cikin kulawa babana yace."Ai izini na nema gurin Fulani amaryar Maimartaba shine tasa aka kawo mu."
Nace."Aikuwa naji dadi sosai da zuwanku kuzo muje nayi muku jagora." Hannunsa na rike muka nufi dakin..............Yana zaune a inda yake da alama ma baiyi sallah ba cikin zuciyata nace"Saboda rashin kula da addininsa komai aka nufe shi dashi na sharri yana iya kamashi, a zahiri kuwa cewa nayi "Ranka ya dad'e fatan ka wuni lafiya ga Iyayena sunzo domin su dubaka." Dago kansa yayi yana kallonsu, su kuma sun sunkuyar da kansu kasa cikin ladabi da tausasa harshe suke gaisheshi, sai naga shima ya sassauta muryarsa ya amsa cikin kulawa yana nuna musu gurin zama da hannunsa.
Yanda ya tar'bi iyayena da sakakkiyar fuska yasa naji dadi a raina, nace"Baba ku zauna ga guri nan." Zama sukayi kan kujera suna murmushi yanda na lura suma sunji dadin tar'bar da suka samu.
Shuru dakin yay na minti biyu nida iyayena tunani muke shi kuma hankalinsa gabadaya yana kan wayarsa, da alama yana duba abu mai muhimanci a wayar......Muryar babana naji yace."Kar'bi wannan Sumayya ki bashi kayan dubiya ne babu yawa, ranka ya d'ade gashinan babu yawa.'' Da sauri na kar'bi ledar da yake mi'ka min, na isa inda yake na bashi
A nutse yace."Ajiye kan drowar nagode sosai." Ajiyewa nayi da sauri na matsa daga gurin.....d'akin ne ya sake dau'kar shuru na tsayin minti goma kafin babana yace."Ranka ya dade zamu tafi Ubangiji Allah ya kare ya kiyaye gaba munayi maka fatan alkairi har karshen rayuwarka.
Wayar dake hannunsa ya ajiye kan drowar cikin kulawa ya amsa da fadin"Ameen suma ameen nagode kwarai ku sauka lafiya." Babana da Tambaya suka kama hanyar futa suna jin dadi a cikin zuciyarsu bayansu nabi nima raina tas naji dadi sosai da bai wulakanta min iyayena ba.
Har bakin mota na rakasu suka shiga direba yaja suka tafi cike da kauna da kewarsu na koma cikin asibitin... dakin na koma still yana zaune a inda yake ya d'auki wayar yana dubawa, agogo na duba naga biyar shaura, jikina na bani baiyi sallah ba cikin rawar baki nace"Ranka ya dade biyar saura lokacin sallah ya wuce."
Kallona yayi cikin mamaki yace."Waye yace miki banyi sallah ba? lallai yarinyar nan kin raina ni da yawa ni kike tunawa lokacin sallah."? Da sauri nace"Aa ba nufina na 'bata maka rai ba ranka ya dad'e nasan sharrin abar dake hannunka waya tana hana ibadah akan lokaci shiyasa nayi maka wannan maganar." Tsaki! mai karfi yaja ya d'auke kansa daga kaina, juyawa nayi zan fita daga dakin yace."Ke! zo ki d'auke tsiyarku bana bukata."
Da sauri na Juyo ina kallonsa dan ban fahimci maganarsa ba, ledar kayan dubiyar da babana ya kawo masa ya jefo min ta sauka daidai kafafuna. "D'auka ki fita dashi d'aga d'akin nan."! yafada yana min wani irin kallo.
A hankali na sunkuya ina kallon kayan dubiyar manya manyan mangwaro ne masu kyau da nuna duk wanda ya gansu sai yayi sha'awa saboda kyawunsu, cikin ledar na mayar da mangwaron k'walla na taruwa a idona na mi'ke tsaye da ledar a hannuna, cikin rawar murya nace" Me yasa lokacin da'aka baka ka kar'ba harda godiya wannan abin da kayi d'abiar munafukan mutane ne." Uffan bece min ba dan idan da sabo ya saba da tsayayyata bana jin tsoron fad'a masa gaskiya komai d'acinta sai dai ya gaji da marina ko dukuna........."Allah ya shiryeka shirin addinin musulnci." Abinda na fad'a kenan a k'untace na kama hanya zan fita daga dakin naji yace."Da yake Ubanki ne ya kawo min kayan dubiyar ai baki tsaya kin duba kin binkicika ba kai tsaye kika ajiye min sabida kina ganin shi ba zai iya cutar dani ba ko."?
Kallonsa nayi raina bak'ik'irin nace"Babana ba zai cutar da kai ba kuma baza'a hada baki dashi a cuceka ba, inaso na tabbatar maka da cewa akan gaskiya mahaifina na iya rasa rayuwarsa mutum ne shi mai tsoron Allah da gudun duniya idan ma kana zarginsa akan wani abu to ka daina domin kuwa kana daukar hakkinsa.
"Dallah malama fita ki bani guri kin tsaya kaina kina tsara magana ni bana shedar mahaifinki dan ban yarda dashi ba ke bari kiji ke kanki ban yarda dake ba ballanatana Ubanki duk wannan tsayayyar da kike a kaina kallon ki kawai nake."
Cikin sigar k'unsa ba'kin ciki nace"Na lura tunda na hanaka kaina kake zagina kana cin mutuncina to bari kaji wallahi mai kusantar wannan jikin nawa sai salihin namiji nagartacce mai addini maganar rashin yarda daka keyi ka yarda dani ko kada ka yarda dani bai dameni ba domin Allah nake kula da kai kuma nasan yafi kowa sanin zuciyata insha Allahu burinka ba zai cika a kaina ba."! ina kare maganar na bude kofar dakin a zafafe! na fita tare da buga masa kofar da karfin gaske.
Ya jima maganganun yarinyar na yi masa amsa kuwwa a kunne tunda yake ba'a ta'ba mayar masa da raddi masu zafi irin na yarinyar ba, tana samun dama a kansa sosai tana farfada masa ba'ka'ken maganganu iya son ranta yasan kuma ba komai ne ya janyo haka ba illah zulamarsa daya nuna a fili amma yana da kyau rana guda ya nuna mata cewa bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane.
Tunda mukayi haka dashi naji gabadaya zaman asibitin ya fita daga raina addua na dinga yi akan Allah yasa a sallameshi domin mu koma gida na gaji da zama a asibitin na kuma gaji da irin wulakanci da iskancin da yake min, sati biyu da nayi a asibitin nayi asarar karatuna nasan an wuce ni sosai dole idan na koma na nemi wata ta koya min hakan ya sake sakani cikin damuwa kullum fuskata a had'e babu walwala, Dr Rabo shine yake nema ya shige min hanci kusan kullum da daddare sai yayi kirana ofis dinsa idan naje kawai nsai kura min ido yayi ta kallona idan na tambayi ba'asi sai yay murmushi yace."Kawai ya kirani ne domin mu gaisa ya kuma kalleni yaji dadi. cike da takaici nake tambayarsa meye amfanin kallon nawa, kai tsaye sai yace." Shi kadai yasan amfanin hakan, rai a 'bace nake fita daga ofis din.......Ana ya gobe za'a sallameshi dana shiga dakin na sameshi kan kujera daga shi sai gajeran wando farar fatar jikinsa sai daukar ido take kirjinsa cike yake da gashi hakanan saman kafafunsa gashine a kwance bakikirin, ban iya kallonsa a hakaba ba na kautar da kaina da fad'in "Ranka ya dad'e Haruna yace." Kana nema na."? Banza yay dani bai kalli inda nake tsaye ba ballantana ya amsa min. daure zuciyata nayi na sake yi masa magana, ya kalleni a watse yace."Meye tsakaninki da wannan likitan mai ciki kamar rumbu." Dr Rabo gajere ne mai tumbi shiyasa ya kirasa da wannan sunan.
Murmushi nayi dan na sake 'kuntata masa nace"Ranka ya dade kana yawan kushe hallitar Allah kaima fa kana da mukusa a jikinka kasan d'an adam tara yake be cika goma ba."
Rai a 'bace! yace."Ba wannan na tambayeki ba na tambayaki abinda yake tsakanin ki da Dr Rabo." Ajiyar zuciya na sauke nace"Sirri ne a tsakani na dashi bana bukatar kowa ya sanshi.
Naga ya zuba min da'kwa-da'kwan idanunsa yana hararata yace."Wane sirri zaki 'boye bayan abu gashinan a zahiri na sani jama'a sun sani duk daran duniya kina shiga ofis dinsa yana lalata dake shine zaki ce sirri."!!
Gabana ya dinga fad'uwa! wannan wane irin d'an sharri ne? 'kazafi zaiyi mana kenan, tsabar firgici da tashin hankali na gagara cewa komai....Yace."Ko nayi k'arya ne."! Hawaye ne suka zubo min na kalleshi muryata na rawa nace" Allah ya sakamin k'azafin da kayi min insha Allahu sai mun tsaya gaban ubangiji akan wannan magana da ka fad'a.'" Hanyar fita na nufa ina kuka wiwi!! jikinsa ne yay sanyi ganin irin uban kukan data fita tanayi! tsaki yaja ya mik'e ko banza ya samu sassauci a cikin zuciyarsa yarinyar ta jima tana 'kuntata masa yau ya rage kuncin dake damunsa, tuntuni ya gane Dr Rabo sonta yake shiyasa gabadaya ya gaza nutsuwa yana fargaba kada yaje wani abu ya shiga a tsakaninsu mugun kishin Dr yake ya'ki nunawa ne saboda wata manufa tashi, da yarinyar ta amince ta zama mai d'eba masa kewa to da tuni ya 'yanta ta ita da iyayenta su tashi daga sunan bayi su koma mutane masu 'yanci, yana jin tsoron Dr Rabo ya yaudareta ta bashi kanta shiyasa gabadaya shima yaji zaman asibitin ya isheshi.
'Daki na shiga na zauna na dinga rizgar kukan dana dade ina tarawa, a duniya ba'a ta'ba yi min abinda ya sani cikin kunci da bakin ciki ba irin k'azafin da guy nan yayi min wato tunda na'ki yarda dashi da bukatarsa shine ya yanke shawarar 'bullowa ta wannan hanyar na tsani zina da masu aikatata sai gashi yau banji ba ban gani ba anyi min 'kazafi da ita, kuka sosai nake ina rirrike kaina.
Muryar Haruna naji a kaina a firgice na dago ina kallonsa hannu nasa na goge hawayen fuskata nace"Haruna yaushe ka shigo ko motsin bude kofa banji ba.
A sanyaye yace."Ya za'ayi dama kiji motsin bude kofa kina irin wannan kukan." Cikin ya'ke nace"Haruna waye yace da kai kuka nake wani abu ne ya shige min ido shine ruwan hawaye yake futa.
Murmushi yay yace."Ni ba yaro bane ballantana ki yaudareni da wannan maganar akan idona kika fito daga dakin da Yarima Ali yake kina kuka dan Allah yau dai kiyi min bayanin abinda ke tsakaninki dashi dan sau tari ina yawan ganinki kina fitowa daga dakin cikin bacin rai."
Kasa cewa komai nayi ina mamaki maganarsa ashe Haruna yana hankalce da abinda ke faruwa tsakanina da Yarima! a gaskiya nayi mamaki, dan kada ya zargi wani abu mai muni a tsakanina dashi yasa na yanke shawarar fad'a masa haka." Wallahi Haruna na gaji da zaman asibitin nan na gaji da wulakancin da muke fuskanta daga gurinsa nifa sai nake ganin kamar ni kadai ya tsana kullum cikin zagin iyayena yake yana buga min tsawa duk abinda zanyi masa bana gwaninta, wannan dalilin yasa kullum kake ganina ina fitowa daga dakin raina a bace."
Haruna yace."Hakuri zakiyi da yanda kika tsinci rayuwarki a ciki sumayya ki cigaba dayin aikin ki koda kuwa zai ce ki kwanta a kasa ya bi ta kanki baki da za'bi dole kibi umarninsa kasancewarki baiwar dake karkashinsa dole ki d'auki hakurin dukkanin abinda zaki gani, shawarar da zan baki shine ki tsananta addua akan Allah ya baki miji a kurkusa idan kinyi aure shikkenan kin huta da wannan aikin. amma mutukar ba kiyi aure ba to babu shakka zaki cigaba dayi masa hidima har karshen rayuwarki."
Maganganun Haruna sun kashe min jiki sosai na soma hango 'kamshin gaskiya a cikin maganarsa babu shakka idan nayi aure na huta da fargaba da tashin hankali ko banza nasan zan samu sassauci a wani 'bangare.
A sanyaye nace"Haruna nagode sosai na kuma ji dadi da wannan shawarar taka insha Allahu zan duba wanda ya dace dani na aura." Murmushi yayi yace."To babu damuwa Sumayya nima ina cikin layin masu so dan a gaskiya kina burgeni mutuka Sumayya kina da nutsuwa da kamun kai babu namijin da ba zaiyi sha'awar ki zama uwar 'ya'yansa ba."
Kallonsa nake ina mamakin furucinsa, yay murmushi yana shafa sumarsa yace."Ni zan tafi domin na barki kiyi tunani sai anjima." hanyar fita ya kama nabi shi da kallon mamaki har ya fita daga dakin......
*BINTA UMAR ABBALE*
*Na kudi ne..!*
Koda zaki ganshi a gruops na sata ne idan kina bukatar biyan kudin karatu ga yanda abin yake.....Vip gruop#600 normal group #300 account... 0542382124...Binta umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da