Showing 30001 words to 33000 words out of 150413 words

Chapter 11 - Kwarya Tabi Kwarya Book Complet by Binta Umar Abbale .txt

shima ya soma shan jinin jikinsa dan ko alama bai ga wani sashe na jikinsa a gurin ba da wuta ta 'kona shi to da tuni sunga sassan jikinsa a wani gurin.




Binkice sosai sukayi a gurin ba suga komai ba Muddibo ya dinga share zufa yana mamakin al'amarin to ya akayi haka ta faru! ina Magajin sarki ya shiga da wuta bata 'kone shi ba.


A sanyaye jami'an tsaro suka shedawa su Waziri abinda ke faruwa.....Waziri ya sauke ajiyar zuciya yana godewa Allah yace."Ko shakka ba nayi jikina na bani yaron nan yana raye dan da wuta ta cinyeshi to da anga sheda saboda haka gurin dai za a tsananta dubawa watakila ko ya gangara wani gurin ne.


Galadima da Ciroma kasa magana sukayi murnarsu gabad'aya ta koma cikinsu sai muzurai suke gurin gabadaya zuciyoyinsu babu kyakkyawan abu...


Shatima cikin gurin ya dinga kutsawa yana haska wayarsa yaji yaci tuntu'be da wani abu da sauri ya Haska gurin, ganinsa a kwance a gurin yasa ya razana wayar ta fadi da sauri ya dauka ya tsuguna a gurin yana tatta'ba jikinsa jinin dake fita daga saman kansa shine ya tsorata shi, hannu ya dora a kirjinsa nan yaji yana harbawa akwai alamun rai a jikinsa, da sauri ya cire rigar jikinsa ya shiga tsane masa jinin ganin kamar wahalar da kansa yake yasa da sauri ya mike ya fita daga gurin yana waiwayensa......Kicibus sukayi da jami'an tsaron suna sake dubawa ......a sarqe yace musu kuzo gashi can bakin gangare da alama akwai sauran rai a tare dashi." Hankali a tashe suka durfafi gurin suna godewa Allah


Yanda aka fito da Magajin sarki daga gurin zaku dauka ya dad'e da mutuwa dan gabad'aya jikinsa ya sandare ya saki wani police ne ya d'aukoshi daukar jarirai suka fito dashi .......Muddibo tun daga nesa da ya hangosu jinin jikinsa ya tsinke jiki na kyarma ya iskesu yana haska fuskar sa da wayar hannunsa baki na rawa ya kalli Shatima yace."A ina aka ganshi anya ma kuwa da akwai rai a jikinsa."!? a kid'ime yake maganar kana ganinsa zaka gane a cikin rud'u yake. Shatima yace."Can karkashin wani k'aton dutse na ganshi a sume goshinsa na zubar da jini akwai alamar rai a tare dashi."
Muddibo hular kansa ya cire cikin tsantsar tashin hankali ya shiga firfita da ita. Shatima ya shiga mamaki mai tsanani ganin yanda Muddibon ya rud'e sai fadi yake ."Wannan da alama ya jima da mutuwa Shatima duba fa ka gani yanda jikinsa ya sandare.....Dansandan dake dauke da Magajin sarkin a hannunsa yace."Akwai rai a jikinsa kawai taimakon gaggawa za'ayi masa." Muddibo shuru yay da bakinsa dan baya so ya sake wata maganar su zarge shi da wani abun.


Kai tsaye babban asibiti suka nufa dashi, Waziri da Shatima ne kawai ke masa fatan samun lafiya Ciroma da Muddibo Galadima fatan mutuwa kawai suke masa.........Kai tsaye emagancy aka nufa dashi manya manya likitoci suka rufu a kansa domin ceto ransa.......Waziri ne ya umarci Shatima ya sanarwa da Maimartaba halin da ake ciki, koda Maimartaba ya samu labarin cewa yaronsa na raye sujjada yayi a gurin ya godewa Allah, a lokacin ya shirya tafiya asibitin domin duba yaron nasa, Fulani kuwa kawaici ta nuna ta zauna a gida tana addua gami da godewa Allah, Bangaran Uwargida kuwa da suka samu labarin abinda ke da akwai sai murnarsu ta koma ciki suka dinga 'kunci suna zage zage da kyar suka iya danne 'bacin ransu suka shiga mota suka nufi asibitin suna shirya wata mana'kisar.




Ni kaina dana samu labarin cewar yana raye bai mutu ba sai da nayi sallah raka biyu na godewa Allah sannan kafin na tashi sai da nayi masa addua da fatan samun lafiya ingantacciya.


Sai bayan kwana biyu Ya farfado yasan wanda yake kansa babu wanda ya fara kira sai Muddibo hawaye suka sakko masa a kumatu. Maimartaba yace maza aje a kira Muddibo yazo ya ganshi yana daina zargin ya mutu....Muddibo na shigowa dakin ya sauke ajiyar zuciya, tsirawa juna ido sukayi, kawai sai Muddibo ya fashe da kuka tare da riqe hannunsa yace."Sannu Yarima ashe tsautsayi da qaddara ne ya fitar damu naji dadi da Allah ya taikaita mana wahala ina kuma rokon Allah ya tsaremu da sharrin karfe.'' Kamar wani mutumin arziki yakare maganar.


Rintse hannun Muddibon yayi a cikin nasa yana so yayi magana amma bakinsa yayi masa nauyi wani irin sarawa kansa yake ga wata irin ishirwa na damunsa da kyar ya iya furta maganar dake bakinsa. "Bani ruwa." Muddibo yayi saurin daukar goran ruwa dake kan drowar ya bude masa zai sa masa a baki ya kar'ba ya sha da kansa, kadan ya rage ya mika masa goran ruwan kana ya shiga bin dakin da kallo. iyayensa ya gani ya tsaitsaye sai yaji zuciyarsa ta karye, ya kamo hannun Waziri ya rike da kyau yace."Baba ku kwantar da hankalinku insha Allah zan samu lafiya."


Waziri ya tsira masa ido babu abinda ke tayar masa da hankali sai kat'on bandejin dake nad'e a kansa gabadaya hallitar fuskarsa ta sauya ko'ina a kumbure dalilin daya sa ma kenan Maimartaba ya kasa tsayuwa a dakin ganin hallitun yaron nasa sun sauya yasa ya fita daga dakin hankali a tashe.




Kwana biyar da faruwar al'amarin na samu su Haruna domin mu tattauna yana da kyau muje asibitin mu duba jikinsa dan gabad'aya tunda al'amarin ya faru na rasa gane kaina kullum da damuwa nake kwana ina ganin kamar idan na wayi gari za'a zo a fadi mutuwarsa.


Haruna yace."Shawara tayi sai mu bari da daddare bayan munyi sallar isha'i sai muje muga yanayin jikin nasa." Nace"To shikkenan tare ma zamuje da babana shima yana so ya duba shi." Haruna yace." To babu damuwa.




Ina k'okarin shiga 'kofar dawakai Jakadiyar Fulani ta dakatar dani, gaisawa mukayi da juna kafin ta isar da sak'on ta, nace"Fulani na nema na." Karyar da kaina nayi nace"Dan Allah ta tsaya na zubawa dawakai abinci sai mu tafi tare."
Da yake tana da saukin kai tace" Muje na taya ki."


Tare muka shiga gurin, Hira muke sama-sama nake tambayar ta yanayin jikin Yariman sabida nasan ita ba zata rasa sanin abinda ke zuwa ya dawo ba, tace"Jikinsa da sauki wallahi kullum ana ganin cigaba amma zamansa a asibitin nan akwai hadari dan kullum 'yan uwansa mata cikin zurga zurga suke wai sunje dubashi gabadaya babu tsoron Allah a ransu zasu iya cutar dashi saboda irin kiyayyar da suke masa.




Cikin mamaki nake kallonta nace"Yan uwansa na jini su cutar dashi me yayi musu mai zafi wai shin ma nawa duniyar take." ? Jakadiya tayi murmushi mai ciwo tace"Yarinya ni nasan abinda baki sani ba a masarautar nan babu wanda ke kaunar dan uwansa dukkaninsu kisan mummu'ke sukewa junansu kowa na samun dama akan dan uwansa cutarsa zaiyi wannan al'amarin ma da ya faru da Yarima muna zargin dasa hannun ma'kiya kin san gabad'aya kowa ya daura masa kiyayya da kyashi da hassada saboda suna ganin kamar shine zai gaji kujerar mahaifinsa.


Na jima ina mamakin maganar kafin na girgiza kaina nace"Jakadiya mutane idan suna wani abu wallahi har mamaki suke bani mutum fa bai ta'ba tsarawa kansa abinda yake so ba face wanda Allah ya tsara masa nasan ba'a kan komai suke wannan abunba akan mulki ne a ganina sai su bari suga abinda Allah zai zartar ba wai su dinga cutar dashi ba watakila ma bashi ne zai hau kujerar ba wani ne babu fa wanda ya san gaibu sai Allah."


Muna kokarin fita daga gurin Jakadiya tace"Ke da kika san Allah kenan amma su ina mai tabbatar miki da cewar basu san Allah ba, dan da sun sanshi ba zasu dinga aikata munanan ayyuka ba." Ajiyar zuciya na sauke nace"Allah ya kyauta Allah kuma shiryemu baki d'aya." Ta amsa Ameeen ya Allah."




Cikin nutsuwa na gaisheta tare dayi mata jaje akan abinda ya faru. Amsawa tayi kafin ta gyara zamanta tana kallona tare da kiran sunana.
Na amsa ina kallonta, tace"Ina fata baki mance akinki ba ko."? Nace."Eh ranki ya dad'e." Tace."To Alhamdullhi ina so kije asibiti ki zauna da babana ki cigaba da kula dashi kamar yanda kike kula dashi a gida." Nace"Dama yau muka yanke shawarar zuwa duba shi nida su Haruna'' Tace"To babu damuwa suma suna iya zama asibitin ku hadu ku kula dashi har randa za'a sallamoshi ya dawo gida, alhmdullhi kullum jikin nasa 'kara sauki yake.
Shuru nayi ina tunani maganarta tace"Nasan kina tunanin gurin kwanciya ko.''? nace"Eh ranki ya dade." Tace"Kada ki damu babban asibiti ne akwai dakunan da zaku kwanta ku sake babu damuwa ki tafi da 'yan kayan sawarki bana tsammanin ma zakuyi sati daya da zuwa ba'a bashi sallama ba tunda jikin nasa ya soma warwarewa." ajiyar zuciya na sauke da fadin"To babu damuwa ranki ya dade bari naje na shirya kayana." Ta amsa min da to shikkenan. Har na kai kofa ta dakatar dani juyowa nayi ina kallonta tace"Ki kula da kyau ba kowane irin abinci zaki bari yaci ba." ko ba tayi min bayani ba na gane inda ta dosa sannan kafin shigowata gurinta mun tattauna maganar da Jakadiyarta.




Lokacin da zamu tafi asibitin iyayena fatan alkairi sukayi min, na sake jin kwarin gwiwa ganin yanda babana yake kuzari jinin jikinsa ya dawo yanzu bashi da matsalar komai yana fita yayi sabgoginsa hankalinsa a kwance to wannan dalilin yasa naji bana fargabar tafiya asibitin.




Lokacin da muka shiga dakin yana zaune kan gado da tufa (apple) a hannunsa yana ci Gimbiya Lawisa na gefansa suna magana kan kujera kuma daya daga cikin yayyunsa ne wacce bata dade da zuwa ba, ta kawo masa abinci cikin kwando wai lallai sai yaci a gabanta sannan zata tafi.


A nutse nabi su daya bayan daya na gaishe su sannam muka karasa gadon da yake zaune....Haruna ne ya fara magana "Ranka ya dade barka da dare ya jiki munayi maka fatan alkairi ubangiji Allah ya tsare gabanka da bayanka." A nutse ya amsa fuskarsa tana nuna alamun yaji dadi da zuwan mu Isa da Hamza suka gaishe shi dayi masa ya jiki nima a nutse na mika gaisuwata ya amsa cikin sakin fuska harda godiya."
Fita mukayi daga dakin muka zauna a reception muna hira....Kimanin minti ashirin da zaman mu a gurin suka fito daga dakin. Aunty Sakina gaba tayi ita kuma Lawisa tsayawa tayi a kaina tana kallona tace"Ina fata kina gudanar da aikin dana saki."?
Nace"Sosai kuwa ranki ya dad'e kullum ina yi har nake tunanin tambayarki ko kinga sauyi sai da na ganku a tare ke dashi kuna hira na tabbatar da cewa maganin yana aiki."


Murmushi tayi tace"Har yanzu na kasa gane inda ya dosa akan soyayyata Ali mugun baud'addan mutum ne wanda ba'a gane gabansa da bayansa, amma tunda muna da zafafan malamai nasan zasuyi min maganinsa." Nace"Kwarai kuwa ranki ya dade." Tace'' Ki cigaba da gudanar da aikin ki bance ki d'aga kafa ba wai dan ganin bashi da lafiya karki saurara a cikin ko wane yanayi burina aikin da nake a kansa yayi tasiri." Nace"Kada ki damu ranki ya dade tafe nake da sinadaran da kika bani ko yanzu ya shirya cin abinci zanyi dubarar zuba masa.
Murmushi tayi tare da fadin" Na fada miki idan aiki yay kyau zanyi miki kyauta ta mussaman saboda haka sai ki sake zage damtse." Ina murmushi nace "Nayi alkawari." Tana tafiyar takama ta bar Gurin, tsaki naja 'kasa-kasa nace''Dube ta dan Allah jahilar banza da wofi.


Su Haruna na gani sun mike sun nufi dakin, ido na zubawa kofar ina sauraran fitowarsu basu dade a ciki ba suka fito Hamza ya kalleni da fad'in ''Ki shiga ki bashi abinci yana bukata.'' Mik'ewa nayi da sauri na nufi dakin


Yana zaune a inda yake ganin shigowata yasa ya fara yunkurin sauka kasa. da sauri na janye kwandon abincin dake gaban gadon ya zuro kafafunsa a nutse ya mike tsaye bayansa nabi da kallo ganin ya nufi toilet yasa na sauke ajiyar zuciya.


Ina tsaye a gurin ya fito muka hada ido, kaina na sunkuyar kasa ina jin faduwar gaba kada'n kad'an, idan na kalli fuskarsa sai naji zuciyata na karyewa nima yanzu na tabbatar da cewa yana da makiya gaba da baya dalilin daya sa kenan naji zan iya sadaukar da rayuwata a kansa tausayi yake bani.


K'asan kafet ya zauna ba tare daya kalleni ba yace."Ki zuba min abinci nasha magani na kwanta bacci nakeji." Nace"to ranka ya dad'e." Kwandon abincin dake gabana na janyo na fara kokarin fito da fulas din dake ciki......Yace."Kada ki bude wannan dauko wancan na aunty Sakina shine nake bukata dan nayi mata al'kawarin cin abincinta."
A nutse na mayar da fulas din hannuna na janye kwandon gefe na dauko wanda ya bukata.


Cikin nutsuwa na fito da komai na kwandon na dauki plate mai dan zurfi na bude fulas din dake dauke da abincin. pride rice ce a ciki taji kayan lambu da nama amma kuma qamshin da take yasha bambam dana lafiyayyan abinci....Tsirawa cikin fulas din ido nayi ina duba abincin ciki. nan na hango taratsatsin magani a ciki dan wani gefan ma har ya rine da kalar maganin, kallonsa nayi gabana na fad'uwa yanzu ya za'ayi na fad'a masa abinda ke da akwai.


Kallona yayi yana yamutsa fuska yace."Zaman me kike ne ke nake jira fa." murya na rawa nace"Ranka ya dade abincin ya lalace." Wani irin kallo ya watsa min da fadin"Kamar yaya ya lalace."? Nace"Eh duba ka gani wallahi ya lalace gashinan kamshin sa ya sanja."


Tsaki yaja tare da fadin"Kinga bana son wata magana ki zuba min abinci naci koda tsutsa ke fita a cikinsa to tunda nayi alkawari sai na cika." shuru nayi ina sake sake a raina.


"Wai ba zakiyi aikin dana saki ba." Cikin tsawa yay maganar.......Cikin jin tsoro nace"Wallahi abincin bashi da kyau ba zaka ci ba." Ya dinga kallonta yana mamakin maganarta, a fusace! yasa hannu zai Dauki fulas din abincin nayi gaggawar daukewa. bayana nasa fulas din ina kallonsa kwallah ta cika kwarmin idona.


A murtuke yace."Ina wasa dake ko."? girgiza kaina nayi ina nufin aa. Yace."To zuba min abinci bani da lafiya bana son hayaniya." Hannu nasa na dauke kwallar data taru a idona nace"Sai dai na zuba maka wancan dan wannan da kake so kaci bashi da kyau." Yace."Wai cikin ki ko nawa ? ina ruwan ki idan naci lalataccan abinci cikina ne ba naki ba sannan nayi wa 'yar uwata al'kawari zanci abinda ta kawo min."


Nace"Kayi hakuri ba zan iya baka kaci abinda zai cutar da kai ba dan kai amana ne a hannuna." Kallona yayi yana mamakin maganata, yace." Wai Saboda me bakya son naci abincin aunty Sakina ne."? bakina ne ya su'buce da fad'in "Saboda akwai guba a ciki."
Gani nayi ya murtuke fuskarsa "me kike nufi? kina nufin anty Sakina zata cutar dani kome."? kai tsaye na daga kaina " Zata iya cutar da kai tun ba.......! kafin na karasa ya wanka min mari a kumatuna. cikin gigita nake kallonsa bakina na wani irin rawa so nake na fadi karshen maganar amma na kasa sakamakon marin daya waska min. kallon banzan da yake min yasa nayi gaggawar yin kasa da kaina.
*BINTA UMAR ABBALE*




*LAST FREE PEGE*
Kada ki sake ayi wannan tafiyar babu ke 'Yar uwa kada ki saka ganin kyashi a kan abinda kike so ki kauda kanki ki biya #300 ki karanta littafin nan hankali kwance........Vip gruop#600 Normal gruop#300 idan kati zaki turo #400 ne.






*PAID BOOK*
NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
BABBAN YARO
MASHAHURI
SADAUKI OMAR
LADIDI KWADAGA
TSANTSAR BUTULCI
DA WATA A KASA
NIDA YAYA SADAM
YAR BANGAR SIYASA
MADADI


Kai tsaye zaki iya samun wa'innan littafan idan kin tuntu'bi wannan numbers
*08089965176*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:26 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
43&44
Yau dai nayi rantsuwar akan ba zan ta'ba jikinsa ba saboda na lura da gayya yake sani ina matsa masa sassan jikinsa da sunan tausa, na riga na gane ba manufarsa tausar ba burinsa kawai na dinga tatta'ba masa jiki yana sakin nishi da rungume fillo tun ina dau'ka abin nasa wasa har na tsargu da abunda yake a duk lokacin da nake masa tausar ya dinga juye juye a gadon yana matse fillo a kirjinsa idan yana ji da iskaci kuwa ya dinga danne min hannu kenan yana kwantowa jikina wannan dalilin yasa na gane ba tausar yake bu'kata ba.


Kafin goma na dare tayi zurga-zurgar jama'a yayi sauk'i, kamar koda yaushe muka shiga dakin domin yi masa bankwana yana zaune ragal dashi tamkar ba wanda yake jinya ba har wata qiba yayi ya kara haske hakan baya rasa nasaba da irin kulawar da yake samu a gurina , ni na tabbatar da cewa daba dan na tsaya a kansa ba da tuni makiya sun kaishi k'asa amma baya ganin hakan kullum cikin yi min masifa yake yana hantara ta mussaman idan yazo cin abinci nasa ido ko kuma na nuna ga wanda nake so yaci shi kuma sai yace ba zai ci ba, wanda bana so yaci shi zai ci, haka zamuyi ta jayayya da juna har sai Dr ya shigo ya raba gardamar dake tsakaninmu, haka yake hakuri yaci za'bin da nake so.


Su Haruna bayan sun masa sallama sun fita sai nima na kalleshi yana kokarin miqe kafa kan gadon nace"Nifa yau ba zan samu zaman tausar nan ba."?


Ya kalleni da fadin "Dalili."? Kai tsaye nace" Saboda ba itace manufarka ba." Shuru yay yana kallon wayarsa, Nace"Sai da safe." kai tsaye kofar fita na durfafa ina addua a cikin raina.


"Sumayya." Sunana naji ya kira tamkar a bakinsa aka rad'a sunan. tsayawa nayi ina kallonsa. gani nayi yana min sauk'akaken kallo cikin taushin murya yace."Zo muyi magana." Ganin alamar sassauci a tare dashi yasa na koma da baya


Gefansa ya nuna min a hankali yace."Zauna." banyi musu ba na zauna ina kallonsa. hannuwana ya rike a nashi yana min wani irin kallo wanda yasa tsigar jikina tashi, risinar da idona nayi dan ba zan iya jurar hada ido dashi ba.


"Kin same."? yafada a kasalance. Girgiza masa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login