Showing 135001 words to 138000 words out of 150413 words
Chapter 46 - Kwarya Tabi Kwarya Book Complet by Binta Umar Abbale .txt
muka barwa Allah komai sai kaga yayi mana magani nasan suna so su dauki fansa ne akaina."
Yace.'" A kaina zasu dauki fansa bake da baki da laifi ba." nace"Ai kai kafi karfinsu dole su kyaleka su dauki hukunci akaina a ganinsu nice na janyo aka rataye Muddibo shiyasa suke so su dauki fansa akaina.
Tsaki yaja yace."Basu da hankali gabad'ayansu kin san Allah Sumayya dik wacce tayi miki lahani a cikinsu ba zan kyaleta ba koda kuwa harda hajiya Kariman a cikinsu sai na dauki mataki akansu."
Nace"Naji na kuma gode da kokarin ka amma dan Allah yanzu ka hakura ka bar maganar idan suka sake yunkurin wani akaina nima zan baka goyon baya ka dauki mataki amma dai yanzu kayi hakuri ka bar maganar.
Ajiyar zuciya ya sauke ya dauki cokalin ya cigaba da cin abincin, lemo na tsiyaya masa a cup na mika masa ya kar'ba ya kur'ba ajiye cup din yayi ya cigaba da cin abincin nace"Amma ba zan 'boye maka cewar naji ciwon abinda kayi ba.
Kallona yayi yana tauna abincin dake bakinsa a tsanake yace."Me nai miki."? nace" Sabida ka shirya tafiya da Lawisa america sai ka 'boye min kasan dai ni ban isa na hanaka abinda kayi ra'ayi ba."
Tissue ya dauka ya goge bakinsa yana kallona yace."Lawisa ta samu labarin kina dauke da ciki hankalinta ya tashi wanda har hakan yasa take zargina akan nafi bukatar haihuwa dake shiyasa bana baki kwayoyi na nuna mata cewa nima karfina kikafi ta'ki aminta da maganata har tana ikirarin kai maganar gurin Maimartaba wannan dalilin yasa na yanke hukuncin tafiya da ita domin na rarrasheta acan."
Girgiza kaina nayi nace"To menene na 'boye min ni shine abinda yafi komai bani haushi sai dazu da naje gaishe da Mamma take fada min a lokacin nuna mata nayi kawai na san maganar dan Allah ka daina irin haka babu dadi."
Yace."To shikkenan tunda kin dauki hakan da wata manufa Allah ya baki hakuri." nace"Ai dole na zargi wani abu tunda naga kamar kana 'boye min.
Hannu ya daga min da fadin"Maganar ta isa haka kin san dai ke baki isa naji tsoronki ba ko? kallonsa nayi ya cigaba da cewa'' Bana munafurci kamar yanda kika zato kawai Allah ne bai nufe ni da na fada miki da wuri ba tunda yanzu kin samu labari magana sai ta wuce."
Mi'kewa nayi na bar masa gurin dan na lura da cewar ba zai fuskanci abinda nake nufi ba idan kuma nace dole sai na ganar dashi shaid'an zai shiga tsakaninmu.
Har nayi bacci bai shigo dakin ba......sai can naji motsinsa na bude idona ina kallonsa ya kashe fitila yazo ya kwanta kusa dani, jin shuru bai ta'bani ba yasa nasha jinin jikina ina tunanin ko yayi zuciya dan nasan halinsa da saurin fushi! ajiyar zuciya na sauke jin ya janyoni jikinsa ya rungumeni sai nasa hannuwana duka biyun na ratsa jikinsa kesses din fuskata ya shigayi kafin ya had'a bakina da nasa ya shiga tsotsar harshena da le'bena had'in kai na bashi sosai muka shiga biyawa junanmu bukata.
Washe gari cikin walwala muka tashi ni dashi sai abin arziki muke tamkar bamu ta'ba samun sa'bani ba, har bakin kofa na rakashi ya kar'bi wayoyinsa dake hannuna cikin kulawa ya rungumeni jikinsa yace."Ki kula da kanki da babyna." murmushi nai nace"Idan kana kiran babynka sai na dinga jin wani irin dadi a raina wallahi har so nake naga na haihu kana kula dashi."
Murmushi yayi yace."Ni kuma kullum da fargaba nake kwana nake tashi ina jin tsoron ranar da naquda zata kamaki ai ina jin kwanciya zanyi sai an k'ara min ruwa."
Dariya na dinga yi ina kallonsa, yace."Sumayya ina jin tausayin masu haihuwa wallahi shiyasa gabadaya bata burgeni." nace"Ka bar wannan maganar dan Allah dik abinda kaga Allah yayi to yana da manufa wuya bata kisa idan kuma na mutu gurin haihuwa aljanna zan shiga dan haka ka daina damuwa."
Yace"To na daina zan cigaba da yi miki addua." Cikin murmushi nace"Nagode rabin rayuwata." girgiza kansa yayi yana kallona tare da kannare idonsa " 'Dan sake maimaitawa naji sunana." yafada yana min wani irin kallo.......Hannunsa na rike tare da fadin"Rabin rayuwar Sumayya." yasa dariya tare da girgiza kai yace." Wani lokacin idan kina wani abu har mamaki kike bani! duk wannan soyayyar da kike nuna min anjima ba zata hanaki kiyi min rashin kunya ba.
Nace" Allah ya tsarani na raina ka kaifa mijina ne wallahi duk wani abu daka ga inayi maka a kan gaskiya ne, gashi dai mun dade a tare amma ka kasa gane halina."
Agogon hannunsa ya duba yace."Ni zan fadawa kowa halinki sumayya kina da kirki sosai amma baki yarda da zalinci ba kina da amana uwa uba addini bakya wasa da ibadah ke d'in 'yar baiwa ce ina kuma alfahari da samunki a matsayin matar aurena."
Sosai naji dadin yanda yake yabona rungumeshi nayi nace"nagode rabin raina naji dadi daka fahimci wacece ni ina rokon Allah ya dawwamar mana da zaman lafiya a tsakaninmu Allah ya baka ikon adalci tsakanin matanka."
Ya amsa da ''ameen my love yau dai kinsa na makara dubi time." da sauri na duba agogon hannunsa takwas da rabi nace" Gaskiya nayi laifi nasan jama'a nacan na jiranka idan kaje kace su yafe min.'' yana kokarin fita yace." Gurin Lawisa zaki nemi afuwa dan kin cinye mata lokacinta a yanzu dai ba zan samu damar shiga gurinta ba sai na dawo." hannu na daga masa da fad'in "Allah ya tsareka a duk inda kake." ya amsa da ameen ya Allah." Ajiyar zuciya na sauke na zauna kan kujera ina jin wani irin farin ciki a cikin zuciyata, inama ba zamu sake samun matsala da juna ba.
"Aunty Lauratu bana so wani mummunan abu ya biyo baya akan abinda kuke kokarin aikatawa dan Allah kada kuyi mata lahani ku kyaleta ita da cikinta nima insha Allahu zan samu." Lawisa ce take wannan maganar.......Hajiya Karima tace"Wato Lawisa har kin saduda ko? yarinya tayi sanadiyar da aka rataye d'an uwanki ki dinga nuna tausayinki akanta meye amfanin wannan yarinyar idan bamu bi dare da rana mun kasheta ba."!!!
A tsorace! ta kalli Mahaifiyar tata za tayi magana Lauratu tace"Ke! dallah rufe mana baki mara wayo kawai! wato ke har kin amince da dadin bakin da yayi miki ko har kina magana akan mu tausayawa kishiyarki to bari kiji wannan yarinya Sumayya ba zata haife cikin jikinta lafiya ba sai munyi ajalinta."
"Aunty Lauratu dan Allah ku bar al'amarin kada ku janyowa kanku wata masifar kunga garin irin haka Muddibo ya rasa rayuwarsa wallahi ni yanzu duniyar gabadaya tsoro take bani kuyi hakuri da daukar fansar nan kada ku janyo mana tashin hankali."
Hajiya Karima tace"Kinga Lawisa tashi ki koma gurinki tunda ba zaki bamu hadin kai ba, kije kawai kafin ku dawo daga inda kuka nufa komai ya zama tarihi." Lawisa jiki a sanyaye ta mike ta bar musu gurun, koda ta koma sashenta kasa aikata komai tayi ta dinga tunanin yanda zata 'bullowa al'amarin tana jin tsoron mahaifiyarta da kanwarta su janyowa kansu wata masifar gashi Wali baya gari bare ta sheda masa idan ta kira wayarsa bata shiga abin duniya ya taru yayi mata yawa sam bata so suyi tafiyar nan wani mummunan abu ya faru.
Ranar talata ranar ce ta kama ranar tafiya ya shigo gurina cikin shiri sai dai babu walwala a tare dashi, ganin haka yasa na danne damuwata na shiga kwantar masa da hankali ya rungume ni tsam! a jikinsa yana bani hakuri nace"Dan Allah ka daina bani hakuri kana sanyawa gwiwata tana sanyi wallahi." fuskata ya sumbata yana kallona yace."Sumayya dole na baki hakuri tafiyar nan kamata yayi ace dake zanyi domun na kula dake da babyna amma Allah bai nufa ba insha Allahu Allah zai kula min dake."
Nace"Ka gama magana tunda kace Allah insha Allahu zai kare ni cikin kariyarsa, hannuna ya rike muka fita falo tare yace."Sati uku kamar yau ne insha Allah ki kwantar da hankali ki.'' nace"Allah ya kaiku lafiya ya kuma dawo daku lafiya cikin nasara." Ya amsa da ''Ameen ya Allah." Hannuna ya saki da sauri ya kama hanyar fita, naji zuciyata ta karye hawaye suka zubo min da sauri nayi gaggawar shigewa daki dan bana bukatar ya juyo yaga halin da nake ciki, kwanciya nayi kan gado na dinga share hawaye ina jin wani irin kewa da damuwa a cikin raina...
*Na kudi ne.*
Koda zaki ganshi a gruops na sata ne idan kina bukatar biya ga yanda abin yake...Vip gruop#600 normal gruop#300 account... 0542382124...Binta umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne saki kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:28 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
104
Tunda suka tafi na kasa sakewa a gurina haka kawai sai na dinga jin fargaba da tsoro na dinga ganin tamkar wani mummun abu zai faru dani, kawai sai na tsiri zuwa gurin Mamma na wuni a can sai yamma nake komawa gurina, yawan zuwan da nake gurinta yasa ta gane cewa ina da ciki sosai ta nuna farin cikinta a fili tayi ta mamakin al'amarin nidai kunya ta hanani nace mata komai kasa hakuri tayi sai da ta tambayeni watannin cikin na fad'a mata watansa biyar, tace"Amma saboda baku da kirki dake da babana aka rasa wanda zai fada min ga ciki yayi kwari ban san dashi ba haka kuma Maimartaba bai sani ba meye abin 'boyewa a ciki." shuru nayi ba wai dan bani da abin fada ba sabida nasan idan na fad'a mata irin abubuwan da suka dinga faruwa kafin samuwar cikin sai ranta ya 'baci shiyasa nayi shuru domin fada mata bashi da amfani. wayarta ta dauka ta shiga kiran yaron nata, ina daga inda nake ina jin muryarsa suna gaisawa, tace"Babana ashe ka iya munafurci dama."? Da sauri yace."Mamma me ya kawo wannan maganar kuma."? tace"Sumayya nada ciki amma saboda rashin kirki kwanaki dana tambayeka kace babu saboda kana so kayi wasa da hankalina ko." murmushi yayi yace."Afuwa Mammana ni kaina wallahi yarinyar 'boye min tayi sai daga baya na ganshi." tace"To daka tabbatar dashi me yasa baka zo ka fada min ba." Yace."Mamma ki gafarce ni wallahi ina jin kunyar nazo na fada miki cewar Sumayya nada ciki shiyasa nayi shuru da bakina idan ya fito nasan dole ki gani." Tace"Ni ban yarda da maganarka babana watakila dai akwai abinda kake 'boye min." Gabansa ne ya fad'i! yace.'' Haba Mamma me zan 'boye miki kina matsayin uwata dan Allah ki yarda da maganata." Ajiyar zuciya ta sauke tace"To na amince da maganarka amma Sumayya zata dawo gurina ta zauna har sai sanda kuka dawo tukkuna."
Yace."To babu komai Mamma ai kamar yau zamu dawo tunda yanzu gashi har munyi sati guda." Tace."To masha Allah ina rokon Ubangiji Allah ya dawo daku lafiya.'' Ya amsa da ''ameen ya Allah." kashe wayar tayi ta juyo tana kallona da murmushi a fuskarta tace"Kinji yanda mukayi da mijinki ko." nace"Naji mamma nima zanfi so na dawo nan din." Tace"To shikkenan bayan sallar isha'i sai kuje tare da Jakadiya ki dauko abunda zaki bukata." nace"To godiya nake ranki ya dad'e."
Tana wani irin kuka take fad'in "Wallahi na daina yarda kana amfani dani da kwaroran roba(Condem) sai kace karuwa zaka dinga gudun haihuwa dani wato ita wacce kake so ka bari ta dauki ciki ni kuma ka yaudareni ka dibga min kwayoyi yanzu kuma ka dawo kana sa condem to na gane yanxu wallahi idan baka daina ba sai na tona maka asiri."! cikin kuka na fitar hayyaci take maganar."
A fusace! yace." Lawisa kada ki fasa tona min asiri a gida idan kin fad'awa iyayena abinda yake faruwa a tsakaninmu wallahi sai kinyi mamakin hukuncin da zanyi miki! kuma bazan cire condem ba duk abinda zakiyi sai dai kiyi."
Da sauri ta janye jikina tana kuka tace"Ni kuma wallahi na daina amincewa da kai kana cutar dani da mugun halinka sai Allah ya saka min."!! mari ya kwada mata yana huci! yace."ai baki fi karfina ba yanzu zan biya bukata ko kina so ko bakyaso." kafin tayi wani yunkuri ya turmushe ya shiga biyawa kansa bukata ba tare da ya cire condem din ba.........sai da yayi me isar sa sannan ya daga ta yaje yai wanka ya fito ya shirya jikinsa ya fita ya barta cikin yanayi na tsantsar damuwa da tashin hankali.
Tare mukaje gurina da Jakadiya ta zauna a falo ni kuma na nufi dakina domin harhad'a 'yan kayan da zan bukata, ina sanya 'kafata a cikin d'akin santsi ya kayar dani! wata irin fad'uwa nayi cikina ya daki! 'kasa da karfin gaske! rintse idona nayi tare da kiran sunan Allah da karfi! dakin ne yayi duhu! cikin karfin hali nayi yunkurin mikewa! naji saukar duka akaina! fad'uwa nayi ina kiran sunan Allah da karfin gaske nace"Jakadiya."!!!!!! a guje! ta shigo dakin tana amsawa tare da laluben mukunnin fitila, ji tayi an bangajeta an fita a guje! salati tasa da sauri ta kunna fitilar! dakin yayi haske! ganin ta a kwance tana murkususu yasa hankalinta ya tashi! zubewa tayi a gabanta tana kiran sunanta jikinta sai rawa yake.......Cikin karfin hali nace"Jakadiya mutuwa zanyi."!! hawaye ta share tace"Ba zaki mutu ba sumayya Allah zai toni asirin duk wanda yake kokarin cutar dake......da sauri ta mike ta fita nan ta samu masu tsaron gurin a tsaitsaye suna magana tace''Ina fata dai kun gane wanda ya fito yanzu." gabadayansu suka ce "Babu samu nasarar kama ta ma dan kayan dake jikinta irin na bayi ne shiyasa ba muyi tunanin wani abuba." Jakadiya da sauri ta bar gurin dan ba taga amfanin tsayuwarta ba.
Su Mariya ne suka rufu akanta suna mata firfita gabadayansu hankalinsu ya tashi da abinda ya faru da uwar dakin nasu, suna cikin dakinsu suka jiyo ihun ta dalilin da yasa kenan suka fito a gigice!
Ganin jini ya 'bata mata zanin jikinta yasa hankalinsu ya kara tashi shikkenan suma suna cikin gariri dole a tambayesu yanda akayi suka bari ta shigo gurin har ta samu nasara.
Mamma da Jakadiya suka shigo dakin hankalinsu a tashe! lokacin Sumayya ta galabaita mutuka, mamma ganinta cikin mugun yanayi yasa ta fashe da kuka rungumeta tayi jikinta duk ya 'baci da jini tace"Sumayya Allah ya saka miki." jin miryarta yasa na 'kan'kame! hannunta ina nishi! nace"Mamma Lauratu ta samu nasara akaina shikkenan nasan sun kashe min baby." wasu zafafan hawaye suka shigo zubo min........Rungumeni tayi tana tofa min adduoi...cikin wannan hali Shatima ya shigo hankalinsa a tashe yace."Mamma ku kamata muje asibiti a dubata." Mamma ta mike jikinta duk ya mutu ta riga ta futar da rai da cikin da ta kwallafa rai dashi.......
Jin cewar matar mai asibitin ce yasa likitoci suka rufu a kanta sai da suka tabbatar da cewa komai yayi daidai sannan hankalinsu ya kwanta.........Mamma ajiyar zuciya ta sauke mai sanyi lokacin da ta gama sauraran jawabin da Dr Sadiya take mata, tace"Alhamdullh dr dama ni fargabata kada ace cikin ya zube tunda dai Allah ya takaita to sai mugodewa masa kuma sannuku da kokari Allah ya saka muku da alkairi." Dr Sadiya tace"babu komai ranki ya dade an jima kadan zaku iya shiga ku dubata yanzu tana bacci." Mamma tace"To babu damuwa." Dr Sadiya ta bude musu wani daki suka zauna a ciki suna jajanta al'amarin..........A daran Maimartaba da Waziri tare da Mahaifinta Lawi sai da suka zo asibitin suka duba ta basu tafi ba sai da ta tashi suka tabbatar da lafiyarta sannan suka tafi ita kuwa Mamma kasa tafiya tayi tasa Shatima ya shedawa D'an uwan nasa abinda yake faruwa, lokacin yayi ta kiran wayarsa bata shiga tace ya bari da safe sai ya kirashi ya fada masa...............
Hannuwana ta rike tace"Sumayya ba kuka za kiyi ba Allah zaki godewa daya kare ki daga sharrin masu sharri Kiyi shuru ki kwantar da hankalinki ki fada min dukkanin abinda yake faruwa."
Hawaye na share a hankali na soma yi mata bayanin abubuwan da suka dinga faruwa a tsakanina dasu.
Hawaye ta share tana girgiza kanta tace" Wannan rashin imani da rashin tsoron Allah na hajiya karima yana bani mamaki! wato ashe bata hakura ba shine take so ta dauki fansa akanki ai bake kika sa aka rataye danta ba da zata dinga bibiyarki da sharri! ki daina kuka sumayya insha Allah sunyi na farko sunyi na karshe sai an dauki mataki mai tsauri akansu sai sunyi da sun sanin abinda suka aikata miki, dama ita wannan Lauratu shaidaniya ce dan ta kashe mutum ba sabon abu bane a gurinta to wannan karon sai tayi nadamar abinda ta aikata.
Da asubah bayan ta idar da sallah, kira ya shigo wayarta koda ta duba sai taga yaron nata ne a nutse ta daga tare dayin sallama............Murya a sha'ke Lawisa ta amsa tare da fad'in "Mamma ina fata kun tashi lafiya." a sanyaye tace"Lafiya lau Lawisa ina fatan kuna nan lafiya?" kuka ta fashe dashi! Mamma hankalinta ya tashi tace"Lawisa lafiya kike kuka ina babana yake."? Lawisa kasa magana tayi ta cigaba da gurshe'ken kukanta.
Mamma jikinta dik yayi sanyi tace"Lawisa ki daina kuka ki fada min abinda ke faruwa ko fada kukayi dashi ne."? murya a sar'ke tace"Mamma ki gafarce ni nasan idan kikaji abinda yake tafe dani hankalin ki zai tashi."