Showing 141001 words to 144000 words out of 150413 words

Chapter 48 - Kwarya Tabi Kwarya Book Complet by Binta Umar Abbale .txt

kiran wayar yayi ta dauka rai a 'bace tace"Me kuma za kace dani babana."? a sanyaye yace.''Mamma dan Allah kiyi hakuri kada al'amarin nan kada ya d'aga miki hankali Lawisa karya take duk abinda ta fada miki."




Girgiza kanta tayi tace"Babana in dan duk jikina kunne ne to bazan yarda da maganarka ba, Lawisa gaskiya ta fada min nasan halinka babana nasan abinda za kayi da wanda ba zaka aikataba wato zama da turawa yasa ka dauki d'abi'unsu kana gudun rahamar Allah har kana dibgawa iyalinka kwayoyi dan kar su dauki ciki ko."?


Murya na rawa yace."Mamma dan Allah ki tsaya ki fuskance ni kada ki dauki al'amarin nan da zafi ya janyo miki bacin ra......Katseshi tayi ta hanyar fad'in" Na fada maka fa duk abinda zaka fada min bazan yarda dakai ba, aini babu abinda zance da yarinyar nan Sumayya tayi namijin kokari data tsaya kai da fata taki daukar hud'ubar ka da tuni wannan cikin dake jikinta babu shi inda ta amince da tsarinka na rashin son haihuwa yanzu na gane dalilin da yasa kake 'boye min tana da ciki saboda ka samu damar zubar dashi cikin ruwan sanyi to insha Allahu bukatarku ba zata biya ba dakai da Lauratu kuma ka tabbatar da cewa sai Maimartaba yasan da wannan magana." Tana gama maganarta ta kashe wayar ta barshi da tasa a kunne, zamewa yayi yai zaman dirshan a inda yake, yana cikin tunanin mafita kira ya shigo wayarsa yana dubawa yaga Shatima ne hannu na rawa ya daga, Shatima yace."Wai ya akayi ne tun jiya ba'a samunka a waya.'' Jiki a mace yace."Matsalar network ne.'' Yace."Nima sai dana zargin hakan to ya mukaji da wannan abu da ya faru."?


Gumin goshinsa ya goge yace."Wai shin Shatima me yake faruwa ne yanzu muka gama waya da Mamma amma ban fahimci inda maganarta ta dosa ba."




Shatima ya sauke ajiyar zuciya da fadin"Dama yanda take cikin tashin hankali ai bai zama lallai tayi maka bayanin da zaka fahimta ba......... abinda ya faru shine..............Shatima ya warware masa dukkanin abinda ya faru. cikin tashin hankali da damuwa yace."Shatima ina fatan Yarinyar nan sumayya bata hadu da wani tsautsayi ba wallahi gabadaya jikina yayi sanyi jin yanda kace ta zubar da jini da yawa ina jin tsoron wani mummunan abu ya faru da lafiyarta.




Shatima yace."Ka kwantar da hankalinka ma'aikatanka sunyi kokari sosai akanta a daran suka tsaya a kanta sai da komai yayi daidai sannan hankalinsu ya kwanta yanxu haka. ita da abinda ke cikinta na cikin koshin lafiya."


Sanyi yaji a cikin ranshi yace."Shatima nagode kwarai da kulawarka yanzu ina Labarin Lauratu kasan Allah sai na daureta."




Shatima ya girgiza kansa cikin takaici yace." A daran nasa ayi binkice akanta ba'a ganta ba, sai da naje na turke Hajiya Karima tukkuna take sheda min cewa wai itama bata san inda take ba yanda take yi min bayani yasa nagane cewa bakinsu d'aya yanzu dai binkice ya nuna mana cewa Lauratu ta gudu dan babu irin neman da ba'ayi mata ba."




Cikin zafin zuciya Yace."Shatima tun kafin na dawo ku d'aure Hajiya Karima dan wallahi bazan saurara mata ba." A sanyaye Shatima yace." Kayi hakuri abi komai a hankali mana." murmushin takaici yayi yace."Shatima matar nan fa idan ba'a dauki tsatstsauran mataki akanta ba to ba zata fasa abinda take ba kasan Allah tasan inda Lauratu ta gudu idan taji matsa zata fadi gaskiya.''


Shatima yace."Wallahi ina jin nauyin yaron nan Wali bayan haka kuma ga Lawisa a matsayin matarka wannan dalilin yasa gabadaya na kasa wani abu akai shi kansa Maimartaba har yanzu bece komai ba nasan yana tunanin irin hukuncin da ya kamata a dauka a kanta."


"Shatima babu ruwana da wani dangantaka mutukar akan gaskiya ne me yarinyar nan tayi musu suke neman rayuwarta watannin da suka gabata Lauratu har cikin daki ta sameta da asid zata watsa mata Allah ya kareta yanzu kuma sun shiga da niyyar kasheta sai kuma kace akwai dangantaka to inaso na fada maka cewa a yanzu ni Lawisa ba matata bace na saketa.''


Shatima yace." Innalillahi wa'ina ilahi! raji'un! Magajin sarki me yake damunka ne? wane irin abu Lawisa tayi maka da har zaka saketa duka auranmu wata nawa ka yanke wannan d'anyan hukuncin.!!!! Jin yanda Shatiman ke magana a fusace! yasa ya sassauta miryarsa yace."Shatima wannan maganar mu barta dan Allah idan na dawo koma me zai faru sai da ya faru, babban burina a yanzu shine ka cigaba da kulawa da yarinyar nan Sumayya wallahi ita kadaice damuwata a yanzu saboda duk wani abu da zai faru da rayuwarta ta dalilina ne tayi min hallaci a rayuwata tilas nabi mata hakkinta akan dukkanin wanda yayi nufin cutar da ita."




Yace."In dai ta wannan ne kada ka damu Sumayya zata cigaba da samun kariya daga gurina insha Allahu zanyi iyakacin bakin kokarina a yanzu dai babban abinda ya d'aga miki hankali maganar sakin nan shine damuwa ta dan Allah inaso ka fada min abinda yarinyar nan tayi maka ka saketa.''


Ajiyar zuciya ya sauke yace."Shatima yanzu ba zan iya yi maka bayani ba saboda bana cikin nutsuwa amma nayi maka al'kawari idan na dawo zaka san dalilin da yasa na saketa." Jiki a sanyaye yace."Okey to babu damuwa Allah ya dawo da kai lafiya." Sallama sukayi da juna kowanne ya kashe wayarsa cikin tsananin damuwa da fargaba.


"Mamma dan Allah ki yafe masa kada kiyi fushi dashi akan abinda ya aikata kiyi masa uziri insha Allahu Allah zai ganar dashi gaskiya.'' Da sauri ta juyo tana kallona nasan bata san da cewar na tashi a bacci ba shiyasa take mamakin maganata.


A hankali na mi'ke zaune ina kallonta tare da marairace fuskata


Karasowa tayi ta zauna a gefena hannuwanta ta ri'ke a sanyaye tace" Sumayya abunda Babana ya aikata ya zama dole a hukuntashi haba sai kace ba musulmi ba ya dinga abubuwa irin na kafurai sumayya meye abin gudu a haihuwa sabida tsabar butulci irin nasa Allah ya barshi da ransa da lafiyarsa ya bashi kyauta amma saboda butulci ya nuna baya so mutane nawa ubangiji ya jarraba da rashin haihuwa suna so suna nema ido rufe Allah bai basu ba amma ya za'be shi ya bashi rabo irin na haihuwa ya dinga kyamata dole sai na hukuntashi Sumayya saboda ina jin tsoron abinda zai faru anan gaba.


Hawaye na share nace"Wallahi Mamma abinda nake taso ya fahimta kenan ba kowa Allah kewa baiwa irin wannan ba amma idanunsa sun rufe ya kasa fahimtata Mamma idan kinga irin rigimar da mukayi dashi akan wannan cikin dake tare dani sai kinyi mamaki! hakuri nai tayi ina masa addua kullum ina nuna masa gaskiya Alhamdulillahi kafin yayi wannan tafiyar naga fa'idar adduar da nake masa da kansa ya dawo kan hanya ya cigaba da nuna kulawarsa akaina da cikin da nake dauke dashi Mamma kema don Allah kiyi hakuri kiyi masa uziri akan abinda ya aikata na rashin kyautawa."


Shuru tayi tana girgiza kanta, nace"Mamma kada kiyi fushi dashi don Allah insha Allahu Allah ya ganar dashi gaskiya." Kallona tayi tace"Shikkenan Sumayya saboda ke zan yafe masa amma dai duk da haka sai nayi masa fada akan abinda yayi saboda ya kiyaye anan gaba." nace" To Mamma amma dan Allah kada ki fadawa Maimartaba maganar nan bana so hankalinsa ya tashi kuma bana so jama'a suyi masa wani irin kallo."


Murmushi tayi tace."Sumayya babana ku yayi wa laifi amma bakyaso ya tozarta a yau na tabbatar da cewa ke matar rufin asirinsa ce insha Allahu zan bar maganar nan a tsakaninmu kamar yanda kika nemi alfarma ina rokon Allah ya tabbatar da alkairi a tsakaninku.


Cikin farin ciki na amsa da "ameeen Mamma nagode kwarai da gaske."




Dr Sadiya ce ta shigo dakin, ganina a zaune muna magana yasa tayi murmushi tace"Alhamdulillahi jiki yayi kyau ko."? Mamma tace"Aikuwa jiki yayi kyau Allah ne abin godiya." Tace."Yanzu Dr ya kira ni a waya yake tambayata ya yanayin jikin naki dalilin da yasa ma kenan na shigo na duba na gani amma naji dadin ganinki a haka ina fatan babu abinda yake miki ciwo." ? ina kokarin magana kira ya shigo wayarta murmushi tayi ta daga wayar cikin ladabi tace"Eh gani ma a dakin muna tare da ita alhamdulillahi jikinta yayi sauki Dr baby kuma na cikin koshin lafiya." shuru tayi tana sauraransa kafin tace"Okey to bari na bata wayar." da sauri ta miko min na kar'ba a nutse na gaisheshi, ya amsa cikin kulawa yana tambayata nace"Babu abinda ke damuna baby lafiya lau kamar yanda Dr Sadiya ta fada maka.'' Shuru nai ina sauraransa, nace"Eh yana motsi sosai." Hamdala yayi ga Allah yace."Sumayya nasan Mamma tana cikin 'bacin rai dan Allah ki tayani bata hakuri kafin na dawo."


Cikin tausasawa nace"Kada ka damu insha Allah zanyi maka kokari Allah ya dawo daku lafiya." ajiyar zuciya mai sanyi ya sauke yace."my lov banda kamarki a duniya." da sauri na kalli Mamma ina jin tsoron kada taji abinda yace...... ya cigaba da cewa'' Tun dana sauka a america nake cikin kad'aici banta'ba tsammanin ina sonki da gaske ba sai da nayi nesa dake." ajiyar zuciya na sauke sosai nake jin dadin kalamansa yace."Idan na dawo koni ko Lauratu ko hajiya Karima dan ba zan barsu sukai labari ba.''' Da sauri nace"Kayi hakuri komai ya wuce insha Allahu dama nace maka Allah ba zai barsu su cimma manufarsu ba kada kayi saurin yanke hukunci." Yace." wancan karon haka kikace nayi hakuri na kuma hakura wannan karon kam ba zanyi ba sai na dauki mataki." shuru nai ina sauraransa yace."Yanzu Dr Sadiya zata sallameku kuje gida ki kwanta ki huta kisha maganguna kinji ko." nace"To shikkenan." Shuru yayi na minti biyu kafin yace."Me kike so nazo miki dashi."? dan murmushi nai wanda yasa Mamma barin gurin kunya ta kamani nace"Komai ka siyo min inaso. " kawai sai na kashe wayar da sauri na mika mata ta kar'ba a nutse tace"Zakuje gida yanzu zan kawo miki magunguna insha Allahu duk sati zan dinga zuwa har gida ina dubaki." nace."To shikkenan nagode." Murmushi tayi tana kokarin fita tace"Ranki ya dade kinfi karfin komai a wannan asibitin."


Lokacin da muka shiga masarautar a hargitse muka sameta jama'a sun cika a bangaran Ciroma sai surutai ne ke tashi yayinda kowa ke fadar albarkacin bakinsa akan abinda ya faru da Hajiya Karima da Kanwarta Lauratu.




Kai tsaye Mamma ta umarci Direba daya wuce damu gurinta ko zama bamuyi ba jakadiya ta shigo hankali a tashe! Mamma ta kalleta cikin alhini tace"Jakadiya wai shin me yake faruwa ne a masarautar nan ko'ina ya hargitse shin ina Maimartaba da 'Yan uwansa." ?


Jakadiya jiki a mace! tace"Ranki ya dade Allah ne ya saukar da ikonsa akan Hajiya Karima da kanwarta Lauratu........Tun sanda da Lauratu ta gane cewa asirinta ya tonu sai tayi yunk'urin 'barin gari tare da kayanta Allah cikin ikonsa sai ya saukar mata da tsautsayi mai munin gaske! a titin Zaria tayi mummunan had'ari! motar da take ciki ta 'kone k'urmus! ita kanta ta gama 'konewa labarin faruwar al'amarin yasa Hajiya Karima ta yanke jiki ta fad'i a gurin gabadaya dai yanzu an rasa yanda za'ayi da ita dan gabadaya ta sandare babu abinda yake amfani a jikinta sai numfashinta dake fita sama-sama! Khalisat itace ke kuka tana farfad'ar irin sharrin da iyayenta suka dinga k'ullawa gashi tun ba'aje ko'ina ba ya koma kansu......Yanzu haka Maimartaba da sauran 'yan uwansa suna tare da Maigirma Ciroma domin shi kansa a lokacin rud'ewa yayi ya dinga hawaye yana nadamar abinda ya aikata a baya da kyar aka kamashi aka shiga dashi daki ana tausar zuciyarsa.




Jikina a sanyaye na nemi kujera na zauna ina mamakin hukuncin ubangiji na yarda da cewa Allah baya bacci kuma baya barin hakkin wani akan wani tun aduniya yake fitar dashi Hajiya Karima da 'kanwarta sun nufe ni da sharri sai gashi Allah ya mayar dashi kansu babu abinda zance da Ubangiji akan sakayyar da yayi min.




Mamma kuwa cewa "Tayi dama ai alhaki kyukoyo ne sukenan kullum cikin shirya mugunta gashinan Allah ya mayar dashi kansu Allah ya karemu yasa mufi karfin zuciyoyinmu." a tare muka amsa da ameen nida Jakadiya, Tace."Ki had'awa Sumayya ruwan wanka tayi ta samu karfin jikinta." Jakadiya da sauri tace"To ranki ya dad'e." ta kalleni a nutse tace"Kinga yanda Allah yayi musu ko." ? nace" na gani Mamma wallahi jikina duk yayi sanyi na rasa me yasa mutane suke shagala da duniya suke mantawa da Allah da ranar lahira wannan al'amarin da faru ya kamata ya zama izina ga masu irin halinsu."


A sanyaye tace" Sumayya kin san ita shiriya ta Allah ce sai yaso zaisa mutum ya shiryu amma idan ba hakaba ai yaci ace hajiya Karima ta gane gaskiya a lokacin da hukuncin rataya ya sauka akan d'anta Muddibo amma da yake beso ba sai ya rabu da ita ta cigaba da tafiya akan rashin gaskiya watakila wannan abu da ya faru da ita shine zai zama sanadiyar shiriyarta." A sanyaye nace"To ubangiji Allah ya shiryeta da dukkanin masu hali irin nata." Ta amsa da ameeen ya rabbi kije kiyi wanka sai kici abinci kisha magani." Nace."To mamma nagode da kulawarki akaina." murmushi tayi tace."Sumayya babu kalmar godiya a tsakanina dake dukkaninn abinda nayi miki kaina nayiwa.'' murmushi nayi na mike a nutse na kama hanyar dakin da nake, ina kokarin shiga jakadiya ta fito tace"Ranki ya dade na hada miki ruwan wankan na kuma fito miki da kayan da zaki sanya.'' nace"Sannu jakadiya nagode da kulawa." murmushi tayi ta wuce ni kuma na shiga dakin ina jin wani irin farin ciki a cikin raina insha Allahu karshen matsalata yazo zan cigaba da samun nutsuwa da kwanciyar hankali na har abadah.






*Na kudi ne*
Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abin yake....Vip gruop#600 normal gruop#300 account.... 0542382124....Binta umar gtbank....idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:28 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
108




*Sumayya Allah ya baki lafiya��*




Bugun kofar da akeyi ne yasa na shiga tureshi daga jikina murya na rawa nace"Dan Allah ka saurara min haka kana ji fa ana bugu nasan Jakadiya ce tazo tayi aikinta dan Allah ka dagani kada Mamma ta fito.


Yana cigaba da abinda yake yace."Sumayya bazan iya ba ki barni kawai." kirjinsa na ture hawaye na kokarin zubo min nace" Dan Allah ka sauks." hannu yasa ya rufe min bakina ya kalleni da jajayen idanunsa kansa ya girgiza min alamun nayi shuru. kallonsa kawai nake ya mayar da kansa kirjina ya cigaba da sha'aninsa..........Jakadiya dai sai hakura tayi da bugun ta bar gurin, tana tsaka da gyare-gyare a falon Mamma ta fito daga dakinta ta shirya tsaf sai kamshi take, ta kalli Jakadiya a nutse tace" Sumayya bata fito bane."?




Jakadiya tace"Eh ranki ya dade na jima ina bugun kofar bata bude ba watakila bacci take." Mamma tace" To babu damuwa zuwa anjima sai a tasheta ta karya." Jakadiya tace"To ranki ya dade a kawo miki kayan karin nan gurin ko zaki hau daining din."


Tace."Kawo min nan jakadiya bana san hawa daining din saboda kafafuna." Jakadiya da sauri ta nufi gurin cin abincin ta shiryo komai a tire ta kawo gabanta ta ajiye.
A nutse ta hada mata tea kana ta zuba mata sinasir da miyar taushe wacce taji tantakwashi da man shanu! Mamma tace"Ikon Allah Jakadiya aiki baya miki wahala yanxu tashinki har kinyi wannan girgikin."? Jakadiya tai murmushi tace."Ranki ya dade ai jiki ya riga ya saba shiyasa aiki baya min wahala tunda na fahimci Sumayya tana san wainar shinkafa da sinasir yasa yau na shirya yi muku a matsayin abin karyawa.".




Mamma tace"Aikuwa kin kyauta Jakadiya mungode yau kam sai ki huta kada kiyi abincin rana wannan ma ya ishemu."




Jakadiya tace"To ranki ya dade godiya nake." gurin ta bari taje ta cigaba da ayyukanta.




Mamma ta gama karyawa jakadiya ta gyara gurin tsaf ta kunna tiraran wuta ta dawo ta zauna kusa da ita suka cigaba da hira.




Lawisa ce tayi sallama ta shigo tayi ado sosai tai kyau.! cikin sakin fuska Mamma ta amsa mata tace"Lawisa kece a tafe."?




Lawisa cikin ladabi ta samu guri ta zauna da fadin"Eh wallahi Mamma nice ina fatan na sameku lafiya."?






Mamma tace"Lafiya lau alhamdullilahi." Jakadiya ta gaisheta ta tashi ta basu guri.




Gurin ne yayi shuru na minti uku Mamma tace"Ina maigidan naki ne nasan yau dai baya fita da wuri."


Lawisa tace."Ai na dauka yana nan gurinki tunda ya fito sallar asubahi bai koma ba."


Mamma tace" Bai shigo ba watakila ya tsaya wata sabgar ne ko suna tare da Shatima." Ta bude baki kenan za tayi magana sukaji motsin fitowarsa.




Yanda ya fito a hargitse ido jawur ko waye dole ya gane abinda ke faruwa.....Mamma ta bishi da wani irin kallon mamaki!


Sunkuyar da kansa 'kasa yayi yana shafa sajensa.....Simi-simi ya karaso gurin, Lawisa kasa tayi da kanta tana jin wutar kishi a kirjinta.




Mamma tace"Babana ashe dama kana ciki.''?


A sar'ke yace."Eh wallahi Mamma tayi kirana a waya ne wai cikinta na ciwo lokacin dana shigo kina daki baki fito ba shiyasa baki sani ba.".




Kallonsa take cike da zargi tace"Cikinta na ciwo idan akwai wanda zai fara sani nice ko kuma jakadiya kadai kasan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login