Showing 87001 words to 90000 words out of 150413 words

Chapter 30 - Kwarya Tabi Kwarya Book Complet by Binta Umar Abbale .txt

munafuka tashi ki futa ko kuma yanzu muyi miki duka wallahi wane irin binkice za'ayi bayan mun san gaskiyar lamari zaki zo ki nayi mana kukan munafurci."




Ta kusa da ita tace"Lami ki daina kuka haka dan Allah ku dauko mata igiyar akwai alamun gaskiya a maganar yarinyar nan watakila zarginta kawai muke saboda haka ki dauko mata igiyar."




Shuru lami tayi tana nazari kafin tace."Uwani wallahi ba zance miki ga inda igiyar nan take ba lokacin dai da'aka shigo da gawarsa na ganta a daure a hannunsa, sai dai ku duba gurin da'a kayi masa wanka ko zaku ganta."


Uwani tace"to bari na duba." Mikewa nayi da sauri nabi bayanta, sako da loko na gurin muka duba tsaf ba muga igiyar ba jikina yayi sanyi muka fito daga gurin, Uwani tace"Muje Shara mu duba mugani ko anshare.......Muka zazzage sharar a gurin duka muka tona babu igiya, Uwani tace"Kinga ni babu alamun igiyar nan a gurin, amma bari a kira wa'inda sukayi masa wankan."


Uwani da sauri ta fita ni kuma na jingina a jikin bango(garu) ina tunanin al'amarin, tare suka shigo su uku ita ta hud'u, had'a ido mukayi da Hamza na hango firgici a tare dashi, Uwani tace"Hamza kune kuka wanke gawar Haruna to binkice ne yazo ana bukatar igiyar hannunsa mahaifiyarsa ta tabbatar da cewa lokacin da'aka shigo da gawar akwai igiyar a hannunsa."




Labaran yace."Tabbas kuwa ni ne na kwance igiyar daga hannunsa, na ajiye a gurin." Salisu yace."Kwarai kuwa nima na ganta da idona wallahi." Hamza cikin dauriya yace."Nima naso naga lokacin da kake kwance ta sai dai yanayin tashin hankalin da nake ciki yasa shaf na manta ban dauketa ba." Nace"To gashi dik mun duba guraran da kuka zauna ba muganta ba." Cikin firgici Hamza yace." Ku muje mu sake dubawa." Dukkaninmu muka bi bayansa, ya dinga lalube a gurin baiga komai ba, yana sharce gumi ya dago muka hada ido sai yayi saurin dauke kansa yace."Amma al'amarin nan akwai ban mamaki gashi duk an duba ba'a ganta ba." shuru babu wanda yayi magana yace."Ku muje mu duba shara." Uwani tace"Wace shara kuma bayan duka mun duba." A sanyaye ya tsaya yana kallonmu, ajiyar zuciya na sauke ina wani tunani, anya kuwa babu sa hannun Hamza a gurin kashe abokinsa? nace"Uwani tunda ba'a ganta ba ni zan tafi Allah ubangiji ya tona asirin munafukai." Uwani ta amsa da ameeen ya Allah." gurin na bari na barsu suna sake tattauna maganar.


A ranar yini nayi cikin zullumi da tunanin yanayin furgicin da naga Hamza ya shiga na dinga tunanin anya kuwa be san wani abu daya shafi 'batan igiyar Hannun Haruna ba? tsabar damuwa da tunani ya janyo min ciwon kai mai tsanani idanuna sukayi jawur tamkar wacce taci kuka ta koshi nan kuwa tsabar fargaba da damuwa ce, Tambaya ganina haka yasa ta shiga damuwa ta dinga rarrashina da bani kulawa, ganin yanda duk ta tashi hankalinta yasa na sassautawa kaina tunani kawai na mika al'amarin ga Allah na cigaba da addua akan Allah yayi gaggawar tona asirin wa'ina suke shirya wannan mugun abun.






*Bayan sati hudu*
Al'amura sunyi sauk'i masarautar ta samu nutsuwa kowa ya kwantar da hankalinsa ya koma harkokinsa harshi Magajin sarkin ya koma aiki dama tunda gwamnati tayi dogon binkice ta gane daga inda badak'alar ke fitowa yasa ta bada umarnin bude asibitin tare da kira ga Jamaa cewa su cigaba da shige da fice a asibitin babu abinda zai sake faruwa da yardar Allah." Wannan kira da gwamnati tayi ga al'umma yasa kowa ya kwantar da hankalinsa, Asibitin *Zinariya* ya ci gaba da gudanar da aiki kan tsari da sanin ya kamata.........Al'amarin yayi masifar 'bata rayukan wa'inda suke adawa da samuwar asibitin dukkaninsu sai suka yanke shawarar karshe akan asibitin amma ba zasu aikata aikinsu ba sai ankwana biyu tukkuna sai kowa ya sakin jikinsa sai su kuma su gudanar da abinda suka shirya,


'Bangaran Yarima ya samu sabbin hadimai kamar yanda Acp ya bukata, kuma kamar yanda yayi alkawarin kawo jami'an tsaro guda biyu ya cika al'kawarinsa ya kawo jami'ai gudu uku tare da amincewar gwamnati, sosai gurin yayi lafiya kowa yana gudanar da aikinsa yanda ya kamata, jami'an tsaron sunsa ido sosai da sosai dan ba kowa suke bari ya shiga sashen kai tsaye ba sai sunyi binkice a kansa tukkuna suke bari ya shiga, mutukar kuwa Yarima baya nan to basa barin kowa ya shiga har sai ya dawo nima ina gama ayyukana nake fitowa.




'Karfe hudu da rabi na ranar talata na fito daga gurin karatu kai tsaye sashen Yarima na nufa domin gudanar da aikina, tun daga nesa na hangoshi a tsaye a bakin kofar shida jami'an tsaron, fuskarsa kadai na kalla na hango tsantsar bacin rai a tare dashi,


Koda na k'arasa gurin nan na fahimci akan abinda yake faruwa, wato yana so ya shiga sashen Su kuma sun hana shi sunce yayi hakuri mai gurin ya dawo daga aiki! Muddibo ya dinga huci yana sakar maganar da duk tazo bakinsa, Daya daga cikinsu yace."Ranka ya dade ba wannan muke nufi ba ai mun san kai ba zaka ta'ba cutar dashi ba muna so ka fahimci yanda tsarin namu yake Shugabanmu dashi kansa mai gurin yace kada mu bar kowa yana shiga sai da izininsa saboda haka kayi hakuri idan ya dawo ya bamu umarni sai mu barka ka shiga."




Muddibo ya dinga wani irin huci! yana zaginsu, gami da fad'in "Idan mai gurin ya dawo zai nuna musu muhimancinsa a gurinsa." a hankali nace"Ranka ya dade barka da yamma." ko kallona beyi ba ya bar gurin, Da sauri daya daga cikinsu ya bude min kofa da fadin"Maza shiga kiyi aikin ki ki rabu dashi." Da sauri na shige ina mamakin al'amarin, to me ya kawo Muddibo sashen Yarima bayan yasan baya nan? idan an bude masa ya shiga me zaiyi a ciki, ina ayyukana ina tunanin al'amarin, sai bayan magariba na gama aikina na fito lokacin sun fito daga gurin sallah bude min kofa sukayi na fita tare dayi musu bankwana,


Ganin gari yayi duhu yasa na kara sauri domin isa gurinmu kawai naji an tare ni!! gabana ya fadi ina dago kai muka hada ido dashi! ido jawur yake kallona cikin dauriya nace"Ranka ya dade kana bukatar wani abu ne."? Wawan mari! ya kwada min na fadi a gurin! tsaye na mike ina kallonsa hannuna dafe da kumatuna! wuya na ya shaqe na dinga kakari!! sai da ya galabaitar dani tukkuna ya sake ni! na sake faduwa a gurin! Ya tsuguna gabana yana kallona ina kallonsa makogwarona ya bushe kamas! Yace."Zan saki aiki a sashen Yarima wallahi tallahi idan kika kuskura kika ki aikatawa sai nabi dare da rana na kashe ki."!!!! Gabana ya dinga faduwa! ya cigaba da cewa'' Kin saba lalata mana aiki to wannan ce damarki ta karshe mutukar banga biyan bukatata ba to ki tabbata zakiyi kwanan barzahu! sai na kasheki.''!!! nace"Ranka ya dade babu mai kashewa sai Allah haka kuma babu me rayawa sai Allah! mutukar kaga na mutu to kwana nane ya k'are."


Hancina ya kaiwa duka! a take ya fashe! jini ya shiga shatata! ido jawur nake kallonsa, sai huci! yake! nace"Ranka ya dade wane irin aiki zanyi maka."? Murmushin mugunta yayi yace."Wato kinga uwar bari ko."? shuru nayi ina kallonsa hancina na cigaba da zubar da jini! Hannu yasa a aljihu ya d'auko wani abu a d'aure a takarda! " Wannan maganin nake so kisa masa a lemo." Kar'ba nayi ina kallonsa, yace."Kin gane ko."? kaina na daga masa! ya yunkura zai mike tsaye na kwance maganin na watsa masa a fuskarsa! da sauri na mike tsaye! zan gudu, ya tad'o kafata na fad'i a gurin! cikin fitar hayyaci na 'kwallara 'kara! wanda yayi daidai jin saukar wani irin bugu a kaina! idanu na na rintse na zube a gurin ina kiran sunan Allah! Muddibo na jin sawun mutane da sautin maga
na yasa da saurin gaske ya bar gurin..............










*Na kudi ne*
Kada ki karanta min littafi sai kin biya keda kika futa da littafin keda Allah! idan kina so ki biya ga yanda abin yake Vip gruop#600 normal gruop#300 account... 0542382124...Binta umar gtbank idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:27 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
85
Hayaniyar mutane na dinga ji sama-sama a kaina na mika hannu cikin mawuyacin hali nace"Ku taimake ni ku kira min iyayena mutuwa zanyi." Rumfa sukayi a kaina suna so su tantance abinda ke faruwa, cikin bushewar makogwaro na sake cewa"Uwani ku taimaka min ku kira min iyayena mutuwa zanyi." Uwani tasa salati tana fadin"Ai wannan Sumayya 'yar gidan Lawi ce." Da yake da karfi tayi maganar babu wanda beji ba, Tambaya turmutsawa tayi cikin mutane ta iske inda d'iyarta ke kwance cikin jini! dan dutsen da Muddibo ya buga mata yayi nasarar fasa mata kai.
Jiki na kyarma ta zube a gabanta hawaye na shatata a fuskatarta hannu tasa ta tattaro ta jikinta ta rungumeta tana kuka had'a kiran innalilihi wa'ina ilaihi raji'un.! Mika'il ne ya karaso gurin da toch a hannunsa yana haskawa dawowarsu kenan yaje ya dauko Yarima daga asibiti ya samu labarin abinda ke faruwa shine yazo ya ganewa idonsa, aikuwa ganin Sumayya cikin mawuyacin hali yasa a guje yaje ya shedawa Yallabai din halin da ake ciki.


Tare suka zo gurin da jama'i guda d'aya lokacin Sumayya ta suma dan bata san wanda yake kanta ba, Tambaya kuka kawai take tana jijjigata gami da kiran sunan Allah tana langwa'bewa! Jama'ar dake kewaye dasu suna ganinsa suka bashi hanya, ganinta cikin jini ya daga masa hankali, tsugunawa yayi yana kallon fuskarta, Tambaya ta fashe da kuka da fadin"Ranka ya dade ka taimaka mana kada mu rasa ta." Maganarta ce ta dawo dashi nutsuwarsa ya kalli Lawi dake gefe a tsugune ya had'a uban tagumi! yace."Me ya faru da ita."? Lawi yace."Wallahi ranka ya dade dukkaninmu bamu san abinda ya faru ba kawai dai munji ihunta ne koda muka zo gurin sai muka ganta kwance cikin jini."


Juyawa yayi ya kalli jama'ar da sukayi dafifi a gurin, yace."Kowa ya tafi.' da sauri suka watse! ya kalli Tambaya jiki a mace yace."Zamuje da ita asibiti domin taimaka mata." Tana kuka tace"Allah ya saka maka da alkairi." Hannu yasa yana kokarin daukarta, Lawi yace."ranka ya dade da kanka." Kansa kawai ya girgiza masa shi yanzu meye ba zaiyi wa yarinyar nan ba watakila ma gurin bashi kariya ta had'u da tsautsayi koma dai menene idan ta farfad'o tilas tayi masa bayani.
Mikewa yayi da ita a hannunsa, Mika'il da security dinsa sukayi gaba da sauri, Tambaya da Lawi suka rufa musu baya.


Bayan mota ya kwantar da ita, ya dan gyara ta domin ya samu gurin zama ya kallesu sun bashi tausayi mutuka ciki kokarin kwantar musu da hankali yace."Insha Allah da kafafunta zata dawo ku daina damuwa kuyi mata addua." Lawi ya sauke ajiyar zuciya da fadin"Ubangiji Allah ya tashi kafad'arta." ameen yace tare da bawa Mika'il umarnin tafiya, sai da motar ta 'bace wa ganinsu sannan suka nufi sashen su cikin halin damuwa gami da rokon Allah sassauci!


Tun mota yake bata taimakon gaggawa dan bakinsa da nata ya had'a ya dinga hura mata iskar bakinsa gabadaya jikinsa ya baci da jinin dake fita ta goshinta, hannusa guda yasa ya danne inda jinin ke zuba ya cigaba da bata taimako irin nasu, cikin ikon Allah kuwa suna daf da shiga asibitin ta farfad'o Allah ya godewa ya rike hannunta tsam a cikin nasa.


Cikin kwarewa da sanin makamar aiki ya tsayar da jinin dake zuba daga goshinta, duk wani taimako da yasan tana bukata sai da yayi mata ya samu nutsuwar zuciyarsa, zama yayi gefanta tare da rike hannunta guda, fuskarta ya tsirawa ido tana ta bacci dan sai da yayi mata allura kafin ya fara aikinsa.


Ajiyar zuciya ya sauke ya tsirawa ties ido babban burinsa yarinyar ta samu nutsuwa ta sheda masa abinda ya faru da ita, tabbas yana zargin wasu daga cikin ma'kiyansa ne suka soma farautar ta, shi kam ya rasa yanda zaiyi da rayuwarsa da makiya.




Agogon hannunsa ya duba karfe daya da rabi na dare, ashe ya jima a zaune yana tunani, hannunsa dake cikin nata yayi nufin cirewa ta rik'e! sai yayi saurin kallo ta yana kiran sunanta




Jin muryarsa ta doki kunnena yasa nayi gaggawar bude idona! idanuwanmu ne suka had'u, kawai hawaye ya kwace min na rintse hannunsa dake cikin nawa ina kallonsa hawaye na ambaliya a fuskata,




Jikina ya matso sosai jikinsa har rawa yake yace."Sumayya sannu kinji ko ki fada min inda ke miki ciwo."


Hannuna na dora saman goshina naji shi a nannad'e! cikin sanyi jiki ya dauke hannuna dake gurin yace."Zai daina ciwo insha Allah! kiyi hakuri kinji ko." Kaina na daga ina kallonsa tausayinsa na ratsa zuciyata.


Yace."Ko zaki tashi zaune."? kaina na girgiza alamu A'a. Dakin yayi shuru na minti biyar kafin yace." Zaki iya yi min bayanin abinda ya same ki."?


Kai na d'aga alamun "E" ya sake matsowa kusa dani murya a kasa yace." Ina sauraranki.




Muryata na rawa nace"Muddibo ne." da sauri ya kalleni nasan mamaki yake jin na ambaci sunan Muddibo.




Yace."Muddibo ne sumayya me yayi miki." ? nasa hannu nagoge hawayen dake zuba, nace"Aiki ya sani nace ba zanyi ba shine ya kwada min mari hakan be isheshi ba ya dauki dutsen wuta ya buga min akaina kashe ni yayi niyyar yayi kamar yanda ya fada zuwan mutane gurin yasa ya gudu.




Gani nayi ya sunkuyar da kansa fuskarsa kamar ta nuna alamun rashin yarda


Nace"Dama nasan ba zaka yarda ba." ya kalleni babu walwala a fuskarsa yace."Sumayya dole nayi kokwanto akan hakan shin wane irin aiki ne ya sakiyi masa kikai masa gardama."'?




"Magani ya bani yace." Lallai na zuba maka a lemo." Kallona yayi yana mamakin maganata! nace"Ni kuma na kwance maganin na watsa masa a fuskarsa."


Cike da mamaki yake kallona kafin yace." Sumayya me yasa kike da tsaurin ido ne? saboda kawai Muddibo ya baki magani kisa min a lemo sai ki watsa masa a fuska sa'anki ne ko kuwa ? Muddibo zai iya daukar mummunan mataki akanki."


Raina a bace nace"Akan na kashe wani gwara ni a kasheni dama aini baiwa ce kowa yana iya amfani dani ta kowace hanya amma nayi rantsuwa ba zan taba bari amanar Allah ta cini ba."!




Girgiza kai yake yana kallona yace."Kwarai ina yaba miki! bisa namijin kokarin da kike gurin ganin kin kare raina da lafiyata, amma me yasa baki bi umarnin muddibo ba, me yasa baki kar'bi maganin ba idan yaso ke kuma sai ki san yanda kikayi kika zubar dashi a wani gurin, na tabbata tsaurin idon da kikayi masa ne yasa yayi miki wannan mumman dukan, Sumayya inaso ki san da cewa ni kad'ai ne zaki iya yiwa zafin kai! na rabu dake amma baki isa kiyiwa wanda yake sama dake tsaurin ido ya kyaleki ba."


Shuru nayi ina nazarin maganarsa, eh kamar yanda yace dana sani na yaudareshi na karbi maganin daga bisani sai na zubar kawai. wani lokacin ne idan zuciyata ta dauki zafi ni kaina bana iya tank'warata."




"Kin tabbata cewa Muddibo ne ya aikata miki wannan mummunan abun."? Kaina na daga ina goge hawaye, Yace." Lallai za'a ramawa kura aniyarta dan ba zan k'yale Muddibo ba sai naci mutuncinsa wallahi tallahi sai yayi daya sanin ta'ba lafiyarki, ni akan wannan zan dauki mataki a kansa daga baya kuma sai ya shedawa Police Maganin me ya baki kisa min a lemo."


Dad'i naji a cikin zuciyata jin cewa zai dauki mataki akansa, nace"Daka dauki mataki akan yunkurin kashe ka da yake ina ganin shi yafi amfani tunda ni ba'a bakin komai nake ba a cikin masarauta kamar yanda ka gama fada yanzu."




Girgiza kansa yayi ya rintse hannuna da nashi yace."Sumayya a cikin masarauta ba'a bakin komai kike ba kamar yanda na fada miki yanzu amma sanadiyar faruwar wannan al'amari masarauta zata san kina da muhimanci a tare da ita."
Lumshe idona nayi kawai na tsinci kaina da d'amke hannunsa dake cikin nawa, gabad'aya muka had'e yatsun hannunmu guri guda tamkar masu d'aukarwar junanmu al'kawari.


' Dakin ne yayi shuru na tsayin lokaci kafin naji ya kira sunana, idona na bude ina kallonsa, yace."Kiyi bacci kada kisa damuwar komai a cikin ranki kinji ko." Lumshe ido nayi a hankali nace"Dan Allah kayi hakuri kabar maganar kada kayiwa Muddibo wani abu ni dama babban burina ka gane gaskiya ka amince da dukkanin gaskiyata."




Ido ya zuba min kafin ya shiga girgiza kansa yace."Sumayya ba zan ta'ba yafewa kaina ba mutukar na bar jininki ya zuba a banza ni d'an halak ne kuma nasan abinda ya dace ."


Shuru nayi ina tunanin abinda zai faru a gaba bana so garin d'aukar fansa wata masifar ta faru a tsakaninsu nafiso kawai ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login