Showing 66001 words to 69000 words out of 150413 words
Chapter 23 - Kwarya Tabi Kwarya Book Complet by Binta Umar Abbale .txt
goma sha biyar yana aikin shafa mata ruwa a fuska bata motsa ba, jikinsa ya dinga kyarma yana addua Allah yasa itama ba mutuwa tayi ba.......Ruwan ya ajiye a hankali ya gyarata a jikinsa rigarta ya cire yayi saurin kauda kansa yana sauke wani irin numfashi, ya kai minti biyar yana kallo gefe guda kafin ya dan juyo a hankali yasa hannunsa a ruwan ya d'ebo ya yayyafa mata a jikinta ya cigaba da shafawa a kirjinta, hannunsa na mutsika nonowanta yana ya'ki da zuciyarsa kada ta rinjayeshi, yafi bukatar ta farfad'o tayi rayuwa a duniya.
Ido jawur ya cigaba da shafa mata ruwa a sassan jikinta yana sakin wani irin nishi mai wahalar gaske.
Ganin gashin idanunta na motsi yasa ya sauke ajiyar zuciya, alhmdullhi ya fad'a sai ya saurin de'bo ruwan da yawa ya yayyafa a fuskarta, a firgice ta bude idonta tana kalle-kalle a dakin, wayarsa ya dauka yana haskata, ta dinga kallonsa shima yana kallonta, jikinta tabi da kallo taga babu riga ballanatana breziya duk ya cire mata ga sanyin ruwa tana ji da tashin tsigar jiki, hannuwanta tasa ta rufe kirjinta zafafan hawaye suka shiga zubowa a fuskarta bakinta na rawa take so tayi magana amma ta kasa fargaba da tashin hankali sun dabaibayeta
A kasalance yace."Kina iya saka kayan ki ko na sanya miki.'' Kallon banza na watsa masa ina masa kallon macuci azzalami wato duk guje-guje na sai da yasan yanda yayi yazo ya cutar dani
Hannu nasa na goge hawayen fuskarta, Yace."Kisa kayanki mu fita daga cikin duhu da sauro." Banzar harara na watsa matsa tare da dauke kaina
"Kada ki 'kara hararata ballantana kiyi min tsaki sai ranki ya 'baci.''' A zafafe nace" Sai me idan raina ya 'baci! ashe da sauran 'bacin rai bayan wannan da nake ciki, wato ka samu labarin a inda nake shine ka biyo dare kazo ka biya bukatarka a kaina ko."!?
Kallona yay da yanayi na 'bacin rai a tare dashi yace."Idan ina so nayi wani abu dake ba sai na biyo dare na fakaici idanun mutane ba, ko can baya ni ne banga dama ba banyi ra'ayin yin abinda nake so dake ba dan haka ki daina wannan maganar sam ba wannan dalilin ne ya shigo dani ba''
A fusace! nace"To ai sai ka fada min dalilin daya shigo da kai! gashi nan ka tu'be min riga kaima ka cire botiran rigarka wane irin iskanci ne yasa zaka tu'be min rigata bayan bana cikin hayyacina."
"Sumayya bana neman wata magana mai tsayi na fada miki ba wannan dalilin ne ya shigo dani dakin nan ba ki yarda ko kada ki yarda be dame ni ba ki tashi kisa kayanki mu fita daga cikin duhu."
Tsaki! mai karfi naja nace"Babu abinda zan......Bakina ya murd'e min ya tsira min jajayen idanunsa, nan na hango tsantsar damuwa da tashin hankali a cikinsu.
Mutsika min le'buna yake cike da muguna hawaye suka dinga karakaina a kuncina, sai da ya gaji dan kansa ya sakar min baki.
Kaina na sunkuyar kasa hawayen azaba na zubo min .
Rigata ya dauko zai saka min da sauri na daga hannu zan mareshi! ri'ke min hannu yayi ya murd'e da kyau! yace." Marina zakiyi irin na kwanakin baya." Shuru nayi ina kallonsa, yace."Ki kiyaye aikata hakan idan kuma kin'ki watarana kina ji kina gani zan 'balla miki hannu babu abinda ya dameni." Yana gama maganarsa ya jefa min rigata a jiki da fadin "Dallah dauka kisa ki tashi."
Babu yanda na iya haka na dauki rigar nasa hannuna daya murde sai zafi yake min.
Mikewa tsaye yayi yana mayar da botiran rigarsa, yace."Ina d'aya yarinyar take?" Shuru nayi masa, ya buga min wata irin tsawa da fadin"Ba magana nake ba." Nace"Muddubo yazo ya fita da ita."
Shuru yay yana kallona na dauke kaina tare da nufar kofar fita, sawun tafiyarsa naji a bayana da sauri na 'kara gabana ina addua a cikin zuciyata
Jugum-jugum! na samu iyayenta Tambaya taci kuka ta koshi kanta sai ciwo yake mata, ina shigowa suka mike tsaye suna godewa Allah! Tambaya rungumeni tayi tana kuka hade da dudduba jikina, nace"Tambaya dan Allah ki daina kuka wuya bata kisa kuma Allah zai bayyana gaskiya dukkaninku ku kwantar da hankalinku
Babana ya rike hannuna a sanyaye yace.''Sumayya dole hankalinmu ya tashi ana tuhumarki da aikata mummunan abu ba zamu ta'ba samun nutsuwa ba sai gaskiya ta bayyana babu shakka duk wanda ya aikata wannan abu bashi da imani tunda gashi yayi nasarar kashe mai rai."
Cikin faduwar gaba nace"Waye ya mutu a cikinsu.'' A sanyaye yace."Isa ya rigamu gidan gaskiya yanzu haka gawarsa na ajiye sai da safe za'ayi jana'izarsa." Zubewa nayi a gurin ina fadin "Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!! Tambaya tasa hannu ta rungumo ni ina kuka muka shiga daki tana rarrashina.
Yanda naga dare haka naga rana, tsabar fargaba da tashin hankali ya hanani rintsawa, 'bangaran Magajin Sarki ma hakan take a zaune ya kwana yana tunanin yanda zai 'bullowa al'amarin babu shakka akwai saka hannun Muddibo a cikin faruwar wannan al'amarin ya rufewa iyayensa maganar ne saboda gudun tashin hankali dan mutukar Maimartaba ya tabbatar da cewa Muddibo ne ya aikata wannan mugun abun to zai dauki mataki akansa kamar yanda yake yankewa duk mai laifi hukunci, 'Bangaran Ciroma da iyalansa kuwa zasu sake 'kullatarsa dashi da iyalansa gaba gami da 'kiyayyar juna zata sake nunkuwa akan tada shiyasa kawai yace matsalar ta faru ne daga man da'akayi suyar doyar dashi, amma dole ya zauna da yarinyar da tayi aikin ya tsorarta da ita domin ya tabbatar da zarginsa.
Kasa tsayawa nayi na karya kummalo na nufi sashensa, nan na samu Haruna da Hamza a harabar gurin sunyi jugum-jugum! ganinsu ya sanya hawaye suka 'kwace min koda na karasa inda suke kasa magana nayi kallonsu kawai nake ina share hawaye.
Haruna yace." Ba kuka zakiyi ba Sumayya addua ya kamata kiyi." Nasa hannu na goge fuskata "Haruna ya mukaji da hakurin rashin Isa."! Sunkuyar da kansa yayi murya na rawa yace." Hakuri da godiya Isa ya rasu yayi shahada muna rokon Allah ya gafarta masa." A sanyaye na amsa da "ameeen ya rabbi dan Allah kuyi hakuri da faruwar wannan al'amari Haruna kunsan ba zan ta'ba cutar daku ba, wallahi dana san akwai guba acikin doyar nan ba zan kawo ku muku ba kai kanka kasan yanda mutanan gidan nan ke dauki ba dadi akan Yarima burinsu suga bayansa Allah bai nufeshi da cin doyar ba sai ku gashi sunyi nasara sun kashe wanda beji ba be gani ba amma babu komai zasuje su tarar da Ubangijinsu."
Hamza yace.Hakane maganarki Sumayya mu bamu ga laifinki ba wallahi saboda tuntuni mun riga mun san halinki ba zaki cutar damu ba sabida haka ki kwantar da hankalinki duk wanda kikaga ya mutu to dama can kwanansa ya kare Allah yasa ta wannan sanadin Isa zai rasa rayuwarsa muna rokon Allah ya kar'bi shahadarsa.''
Jiki a sanyaye na amsa da ameen ya rabbi ni zan shiga gurin Yarima." Suka ce to sai kin fito."
Yana tsaka da saukowa daga benan shi na shiga, sai na tsaya har ya karasa saukowa, kauda 'bacin raina nayi na gaishe shi. a dakile ya amsa min. nace"Me zakace dangane da abinda ya faru jiya."? Harara ya watsa mun yace." 'Yar jarida ce ke da zaki titsiye ni da tambaya."?
A dake nace"Dole na titsiye ka da tambaya saboda duk abinda 'yan uwanka keyi maka baka ta'ba yarda gashi sanadiyar cin doyar da aka zuba maka guba a ciki wani yaci ya mutu ina fatan yanzu ka gazgata maganata."
"Kinga Sumayya ba wannan ne a gabana ba wanda ya mutu dama can kwanansa ya 'kare mai yasa su sauran da suka ci doyar basu mutu ba, bana son zargi akan abinda mutum baida tabbas a kai nayi binkice na gane ba guba ce ta janyo faruwar al'amarin ba man da yarinyar tayi suyar doyar dashi shine ya gur'bata saboda haka kada na sake jin kinyi wata magana akan wannan al'amarin idan na sake jin kin sako wani nawa a ciki sai ranki ya 'baci!
Kallon shashasha nayi masa nace"Ai dama ba zaka ta'ba yarda ba sai ranar da suka kai ka 'kasa sannan zaka yarda da abinda ake fada maka! kai me 'yan uwa kullum baka so ace ga abunda sukayi maka su kuma kullum cikin shirya maka mugun abu suke ka'ki ka gane ka dauki son duniya ka d'ora musu idan sun kashe ka iyayenka su sukayi asara su kuwa ranar zasuyi kwanan farin ciki bukatarsu ta biya a kanka."
Har na 'kare maganata idanunsa na tsaye a kaina, yace.''Idan sun kashe ni ina ruwanki."? shuru nayi ina kallonsa ya cigaba da cewa 'yan uwana ne ba naki ba ko Wu'ka suka dauko suna yankar namar jikina idone naki kullum ina fad'a miki cewa ki fitar da kanki akan abinda be shafeki ba kin'ki kije kiyi tayi yanda suke farautata kema ba zasu barki ba." Yana gama maganarsa yazo ya wuce ta gabana fita yayi daga falon, da sauri nabi bayansa na sameshi tsaye shida hadimansa suna magana nan na gane gurin jana'izar Isa zasu tafi! a sanyaye na nufi gurinmu ina share hawaye shikkenan Isa ya mutu mutumin kirki sarkin fara'a da barkwanci Isa bashi da abokin fada kullum zaka sameshi da carbi a hannunsa, duk wanda yasan Isa dole ne ya fad'i halinsa nagari.
Koda na koma gurinmu shuru na same shi Tambaya bata nan shima babana baya nan jikina ya bani dukkaninsu sun nufi gurin jana'izar Isa, juyawa nayi nima da niyyar naje can inda ake jana'izar sai kuma nayi wani tunani gurin nasan akwai dandazon mutane ina iya zuwa wata hatsaniyar ta tashi, can kuryar daki na shiga na kwanta a shimfidata rufin dakin na tsirawa ido ina tunanin rayuwa hakika da ina da inda yafi nan da tuni na gudu dan masifar ta isa haka! tunani nake akan maganarmu dashi ta dazu na yarda da maganarsa da yake cewa nima ba zasu barni ba saboda yanda nake saka ido sosai akansa da dukkanin abinda suke aikatawa, ni kaina na rasa me yasa nake damuwa dashi da lafiyarsa sam! bana kaunar abinda zai cutar dashi ko ya ta'ba lafiyarsa inda shi kuma kullum yake nuna min na tsaya a matsayina babu ruwana da 'yan uwansa babu shakka da zan iya dauke idona daga kansa da abinda suke masa to dana zauna lafiya, amma ba zan iya ba saboda ina tsananin tausayawa mahaifiyarsa da mahaifinsa da suka qallafa ransu a kansa, hawaye masu dumi ne suka zubo a kumatuna nasa hannu na goge wasu na sake zubowa hakika ina cikin tsaka mai wuya ina rokon Allah ya kawo mana mafita dani dashi da dukkanin wanda yake da damuwa a cikin zuciyarsa.............Haka na yini a kwance lokacin sallah ne kawai yake tayar dani, Tambaya bata shigo gidan ba sai dab da magariba ta shigo kai tsaye kicin ta nufa ta ajiye kayan abincin hannunta, tsakar gidan na fito muka hadu tace"Ashe kina ciki dama."? kaina na daga nace "Tun dazu dana shigo na tarar bakwa nan bacci ya dauke ni." Tace."Ayya ai bayan futar ki can gurun Iyayen Isa naje akayi jana'iza dani la'asar nayi kuma na nufi gurin aikin abinci shiyasa ban shigo da wuri ba." Nace"Sannu da aiki nima nayi niyyar zuwa sai na fasa saboda gudun abinda ka iya zuwa ya dawo.''
Tace."Ai gwara da baki je ba dan ni kaina zaman hakuri nayi a gurin Lami da sauran mutane sun had'u sai gulma sukeyi suna zaginki dauke kaina kurrum nayi na rabu dasu sukayi su gama." Girgiza kaina nayi cikin 'kunar zuciya nace"Tambaya kada ki damu Allah yana tare da masu gaskiya kedai ki tsananta addua a gurin Allah ya bayyana gaskiyar lamari." Tace!"Addua kullum cikin yin ta nake Insha Allahu Allah sai ya kare ki daga sharrin masu shari.'' Ameen nace na dauki buta domin daura alwalar sallar magariba....
*Na kudi ne*
Kada ki karanta min littafi baki biya ba keda kika futar da book din keda Allah idan kina so ki biya ga yanda abin yake....Vip gruop#600 normal gruop#300 account.. 0542382124...Binta umar gtbank idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:26 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
77
Sosai ya rike 'kuguna ya matseni a jikinsa yana sauke wani irin numfashi yun'kurin k'wace jikina nayi ya sake matseni a raunane yace."Ba zan sake ki ba sai kin yafe min." Hawaye suka sake xubo min nace"Me kayi min kake neman yafiya a gurina ni ai baiwa ce zan iya kwanciya kabi ta kaina kaga dan ka 'kona ni ai ba wani abu bane."
Saukar hannushi naji a kirjina yana shafawa, "am sorry my love." a hard'e ya fadi maganar, yanda yake shafa fatar gurin yasa tsigar jikina duk ta tashi, gabadaya naji gwiwata tayi sanyi, a raunane nace"Sake ni na yafe maka." K'in saki na yayi ya cigaba da shafar gurin 'kunar yana sauke min hucin numfashinsa a wuyana, jikina yay la'asar ikon Ubangiji Allah ya had'ani da nataccen mutum........"Ki bari na duba miki." Da sauri nace."Nifa ban 'kone ba ka sake ni na tafi na yafe maka."
Da sauri ya juyo dani kafad'una ya rike ya kurawa fuskata ido kafin naga ya sauke idonsa inda k'unun ya zubawa ido ." ina kallonsa yasa bakinsa yana hura gurin, nayi saurin ture kansa gabana na bugawa, a buge ya dago yana kallona da jajayen idanunsa, dauke kaina nayi daga kallon fuskarsa dan gabadaya ni yanzu al'amarin sa tsoro yake bani.
Hannu yasa ya juyo da fuskata yana wani marairaice fuska yasa harshe yana lashe bushashshen hawayen daya bushe a fuskata......mirya na rawa nace"Dan darajar Allah ka bari babu kyau fa abinda da kakeyi ka sakeni na tafi wallahi na yafe maka."
Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke naga ya daidaita nutsuwarsa hannuna ya rike ya fara tafiya.
Turjewa nayi cikin faduwar gaba nace"Ina zaka kaini." ?
"Zan duba miki 'kunar ne." Girgixa kaina nayi nace"Ka barta kawai in Allah ya yarda ba zata tashi ba.'' Ido ya tsira a gurin kafin ya sauke ajiyar zuciya ya kalleni, dauke kaina nayi saboda bana son kallon kwayoyin idanunsa, "Sumayya.'' kallonsa nayi saboda yanda naji ya ambaci sunan nawa ya cigaba da cewa" Maimartaba ya umarce ni akan lallai na janye maganar aurena dake."
Ajiyar zuciya na sauke lokaci guda naji wani irin farin ciki ya mamaye zuciyata.
Girgiza kansa yayi yace.''Nasan jin wannan maganar yasa ki farin ciki ko.''' shuru nayi ina kallonsa! girgiza kansa yayi yana wani murmushi yace."Ni yaro ne mai biyayya gami da bin umarnin iyayena saboda haka zanyi kokari ganin nabi umarnin mahaifina ammafa ki sani duk hanyar da nasan zanbi na hanaku rayuwar jin dadi dake da masoyin naki na sani mafita a nan shine ki mallaka min abinda nake 'kulafuci idan na samu ko sau daya ne to zan barki ki zauna lafiya da mijinki.''
Yanda yake maganar ya nuna min da cewa tabbas zai iya aikata komai akaina da Haruna, jikina ne yayi sanyi na dinga jin tsoron sharrinsa kasa magana kawai nayi na zuba masa jajayen idanuna.
"Baki ce komai ba." Yafada yana sake nani'kar Jikina.''
''Yallabai bani da abinda zance maka saboda na fahimci kayi nisa kuma baka tsoron Allah akan biyan bukatarka babu komai duk abinda zakayi mana kaje kayi Allah yana kallonka.''
"Okey! wannan maganar taki ta nuna min cewa ba zaki bani abinda nake bukata ba."
Kai tsaye nace"Wai shin sau nawa zan fada maka wannan maganar ne? na fada maka cewa ba zan ta'ba amincewa da kai akan sa'bon Allah ba ranka ya dad'e ba zan baka kaina ba koda kuwa zaka sa min bakin bindiga a mak'ogwaro na wallahi akan na baka kaina sai dai ka kashe ni."!!!
Ya dinga kallona fuskarsa tana rikicewa da wani 'bacin rai gabad'aya kammaninsa sun sauya! nima idanuna nasa masa ina tabbatar masa da gaskiyar maganata........Motsin bude kofa ne yasa gabad'aya muka kalli bakin kofar, gimbiya Lawisa ce ta shigo cikin shiga ta alfarma da alama kwalliyar ta mussaman ce, ganinmu daf da juna yasa nan take yanayin fuskarta ya sanja da zallan 'bacin rai.
Matsawa nayi daga jikinsa na sunkuyar da kaina gabana na wani irin fad'uwa, Gimbiya Lawisa ta karaso kusa damu shashshekar kukanta naji tana magana........ da sauri na dago kaina ina kallonta ina kuma mamakin abinda take fada, tana wani irin kuka ta cigaba da cewa"Yanzu meye a jikin wannan mummunar yarinyar da har kake rungumeta a jikinka ashe dama ba aikin abinci kawai take maka ba tana biya maka bukatarka idan ta tas........Wani gigitacan mari ya kwada mata ido jajawur yace."Kada ki sake jifan mu da wata mummanar kalma kawai saboda kin shigo kin tarar damu daf da juna sai ki fassara da wata manufa ta daban! wallahi idan kikayi wasa akan wannan dalilin sai na janye maganar auranki dama ba sonki nake ba takura min akeyi.'
Lawisa gumi ya dinga yanko mata kai amma Yarima baida kirki a gaban baiwa ya kwada mata mari yana fadin ba sonta yake ba.sunkuyar da kanta tayi takaicin duniya ya isheta wai shin ya za tayi ta janyo hankalinsa a kanta, tsaki yaja mai karfi ya wuce ya bar mu a tsaye a gurin..
Ganin ya futa yasa nima nayi yunkurin barin gurin, da sauri ta tari gabana na kalleta ta kalleni cikin tashin hankali tace''Sumayya ki fada min abinda ke tsakaninki da Magajin sarki." Cikin jarumta nace"Ke me kika gani a tsakaninmu."? a fusace tace"Wace irin magana kikeyi wannan ki bani amsar tambayata." nace"To babu wani abu dake tsakanina dashi."
"Babu abunda ke tsakaninki dashi na ganku dab da juna." Cikin