Showing 54001 words to 57000 words out of 150413 words
Chapter 19 - Kwarya Tabi Kwarya Book Complet by Binta Umar Abbale .txt
uwar gida duk wannan zaman a sashen Yarima nayi." Tace"To alhmdullhi ina fatan dai babu wata matsala." nace"Babu matsala ki koma kiyi kwanciyarki." Tace"To shikkenan ." Tana fita daga dakin na sauke ajiyar zuciya, riga da zani na dauko nasa a jikina na karkade shimfidata kwanciya nayi tare da tsirawa rufin dakin ido, tunani nake akan abinda ya faru dani....da gaske yake daya samu galaba a kaina sai ya cutar dani gaskiya banta'ba ganin butulu irinshi ba dole ne na nemawa kaina mafita gaskiyar magana kenan dan ba zan bari ya cutar da rayuwata ba, da wannan tunane tunanen bacci mai nauyi ya dauke ni...
*Na kudi ne!*
Kika karanta baki biya ba Allah ya isa! idan kina so ki biya ga yanda abin yake...Vip #600 normal #300 account.. 0542382124...Binta umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:26 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
65&66
Muddibo zama yayi a kan kujera ya dafe goshinsa abin duniya ya taru yayi masa yawa shima ji yake tamkar ya fashe da kuka saboda tsabar bakin ciki da takaici.
"Muddibo wane mataki zamu dauka akan wannan al'amarin dake faruwa wallahi ni har na gaji da abu daya kullum yaron nan gaba yake yi yana barinmu a baya yanzu yanzu Muzanbil yazo yake sheda min cewa gashi can a gurin taro sai mubaya ake masa jama'a sai addua suke masa gami da fatan nasara a rayuwarsa wannan al'amari yayi masifar daga min hankali ta inda har na rasa tunanin da zanyi."
Muddibo fuskarsa ya bude yana binsu da kallo ido jawur yace."Wallahi nima gabadaya kaina ya kulle na rasa wane mataki zan dauka akan Yarima duk wani tarko idan muka d'ana masa sai ya tsallake na rasa daga inda matsalar take."
Aunty Safiyya tace"Matsala fa daga gurin wannan mutsiyaciyar yarinyar take itace ke saka ido a kan komai duk aikinmu itace take wargazawa daba dan hakaba da tuni hakan mu ya cimma ruwa a kansa,
Muddibo yace."Nima na soma zarginta akan hakan to lallai kuwa zata janyowa kanta dan wallahi zan iya kasheta mutukar bukatata zata biya.
Uwargida tace"Dan Allah ku bar wannan maganar tukkuna ni yanzu so nake dani daku mu zauna muyi tunani akan wannan asibitin da aka bude masa inaso muyi tunanin wane mataki zamu dauka a kan hakan.
Muddibo shuru yayi yana girgiza kafarsa yace"Hajiya bani da imani akan bukatata wallahi zan iya kashe rayuka ina ganin tunda asiri da sharri ya kasa tasiri akansa kawai zan sa a cinnawa asibitin wuta kowa ma ya huta kuma bazan gudanar da aikina yanzu ba sai jama'a sun soma zurga zurga a cikin asibitin tukkuna zan sa a sa wuta in yaso kowa ya guje shi dan naji masifar haushi da yanda jama'ar gari ke nuna masa kauna wannan shine mataki da zamu dauka.
Uwargida murmushi tayi tace"Muddibo shiyasa nake kaunarka nake kuma sanya ka a cikin al'amurana saboda kasan abinda ya dace hakika wannan shawarar taka itace abar dubawa naji dadi sosai daka samo mana mafita idan ta kama har shi wutar cinye sai mu huta kaga mun yar da kwallon mangwaro mun huta da kuda.
"A'a kada ayi haka sai zunubin namu yayi yawa ina ruwan jama'ar gari kuma Yarima Ali shi muke so muga bayansa saboda haka idan abin ya kasance da haka shi zamu sawa wuta ba jama'ar gari ba." Aunty Bishira ce take wannan maganar bayan taci kukanta ta koshi.
"Ke kinga Bishira ki daina wannan maganar ashe akawai sauran imani a tare dake, babu ruwanmu mu kan mai uwa dawabi zamuyi ko ba haka bane."? aunty Safiyya ta 'kare maganarta tana kallon Muddibo." Yace." Kwarai kuwa ni na rasa wace irin zuciya ce da Aunty Bishira jama'ar garin ba sune suke 'kara masa karfin gwiwa ba na tabbata idan asibitin ya tashi da wuta mutane suka 'kone suka mutu to kowa zai kiyaye kai kansa asibitin gudan faruwar matsala kinga bukatarmu tabiya mun ruguza shi."
Uwargida tace"Muddibo rabu da Bishira dan Allah mu cigaba da abinda yake gabanmu." Gabadaya suka zuba masa ido yana cigaba da tsara musu yanda al'amarin zai kasance.
Ni dai ina ganin Maimartaba ya shiga gida nima na bar gurin dan gabadaya hayaniyar dake tashi a gurin nema take tasa min ciwon kai, daf da gate din sashen Sumayya naji an kira sunana ina juyowa muka hada ido da Dr Rabo ashe yazo taron, murmushi nayi na tsaya ina kallonsa har ya karaso inda nake tsaye, da murmushi a fuskarsa yace."Baby Sumayya kinyi wuyar gani." ina yar dariya nace"Dr Rabo barka da hantsi ya gida ya iyali.''?
Yace."Alhamdullhi ina fatan kina lafiya ko da yake ai ga alamu nan sun nuna kina cikin koshin lafiya Sumayya ashe haka kike da kyau.'' hararasa nayi ina dan bata fuska nace"Ka saba fada min wannan maganar dan ka bata min rai dan Allah ka daina bana so."
Murmushi yayi ya shafa sajensa yana kallona yace."Kin san Allah ba karya nake ba kina da kyau sosai sai dai ba kowane zai fahimci hakan ba sai wanda yasan meye kyau, mafi akasari maza sun dauka fari shine kyau basu san ba haka bane dan wallahi da wata farar macan gwara babu zaki ga wata fari ne kawai amma sam bata da k'ira da cika irin wanda namiji ke bukata ke kam Sumayya kin cika mace ta kowane fanni na jima banga macen da ta tara irin abubuwan da kike dashi ba.
Cikin kankanin lokaci na murtuke fuskata ashe Dr Rabo kare min kallo yake har yana kwarzanta kirar jikina, dauke kaina nayi sabida takaici na rasa ma abinda zance masa, ina jinsa yana surutu na juyo domin na fada masa cewa zan tafi dan banga amfanin tsayuwata ba dashi ba na tsani namijin da zai dinga nuna zulama a kaina.....Magana zanyi Yarima shida Shatima da wasu fadawa biyu suka karyo daga wata hanya, sunkuyar da kaina kasa nayi gabana na wani irin faduwa.
Yarima tun daga nesa yake so ya tabbatar da abinda yake gani a kofar gate dinshi, Yarinyar nan ce Sumayya da Dr Rabo suke zance a gurinsa saboda sun raina masa hankali! mugun kishi ne ya rufe shi, nan take yayi kici kici da fuskarsa, Shatima nayi masa magana yana amsawa ciki ciki takaici ne fala cikin zuciyarsa.
"Dr Rabo ni zan shiga gida kaina ne ke ciwo dan Allah ka gaishe min da yaranka idan ka koma gida." Yana yar dariya yace."Ba zaki tsaya yarima ya karaso ba naga sai wani sauri kikeyi kada dai kice min har yanzu tsoransa kike."
Kallonsa nayi ina mamakin maganarsa nace"Dr Rabo Allah ne kadai abin tsoro ba wani mahalu'ki ba." Maganata tayi daidai da karasowarsa gurin kuma nasan yaji......da sauri nayi gaba ba tare da nayi kuskuran kallonsa ba nace"Dr ka sauka lafiya." Gabadaya harshi bina sukayi da kallo suna mamakin abinda na aikata wanda ya dace ace na tsaya na kwashi gaisuwa gurin Yarima amma na kad'a kaina na wuce! na bar gurin, ba Yarima kadai ba har Shatima sai da yaji haushin abinda nayi......Yarima Ali kuwa kasa tsayawa yayi yay cikakkakiyar sallama da Dr Rabo hannu kawai ya daga masa ya shige ciki Dr Rabo anan ya sake gazgata zarginsa akan cewa shima son yarinyar yake.
Koda suka shiga cikin gidan kasa samun nutsuwa yayi gabadaya hankalinsa ya tashi ganin yarinyar sannan babban abinda ke duguzuma masa zuciya ganin Dr Rabo ya tsayar da ita suna hira a bakin kofarsa sai yake ganin kamar da gayya sukayi masa haka yaji gabadaya ya tsani Dr Rabo duk da ya kasance abokinsa amma a yanzu bashi da babban makiyi kamarsa.
Shatima ya dafa kafadarsa a nutse yace."Na lura abinda yarinyar nan tayi maka a gaban Dr Rabo ya bata maka rai ni kaina raina ya baci wallahi kayi hakuri yanzu zansa a kirata ta nemi afuwarka." Girgiza kansa yayi yace."Rabu da ita kawai kada ka kirata zata shigo da kanta idan ta shigo ni zan mata hukunci daidai da abinda tayi min." Shatima yace."Okey yanzu me ka fuskanta a tsakaninta da Dr Rabo."? kai tsaye yace."Sonta yake." Shatima yayi dariya yace."Lallai idan bakayi da gaske ba zaiyi maka shigar sauri."
Cike da mamaki yace."Ban fahimci maganarka ba." Shatima da murmushi a fuskarsa yace."Kana son yarinyar nan alamu sun nuna min hakan wannan dalilin yasa na fadi wannan maganar.
Baki a sake yake kallonsa yana mamakin yanda akayi yayi saurin gane shi.
Shatima yace."Yanayin yanda aka kasa 'boye bacin ranka da kishinka yasa na gane tsananin son da kakewa yarinyar naji dadin hakan sosai kuma yarinyar ta dace da kai domin duk ta had'a abubuwan da ake bukata ina maka fatan alkairi."
Rai a 'bace yace."Shatima kai yanzu ta ina ka hango dacewa ta da yarinyar nan ka dube ta da kyau kuwa ka gani na rasa wacce zan aura sai ita."
Shatima yace."Gaskiya ka bani mamaki Ali yanzu dan Allah wace dacewa kake nema bayan wannan ? meye aibun yarinyar nan Sumayya ta cika mace kuma ta kai ta zama matar Sarki governor ko shugaban kasa, tana da kyau daidai misali kana tana da kyawawan halaye to me kuma ake nema a gurin 'ya mace."?
Girgiza kansa ya shiga yi yace."Shatima mu bar wannan maganar dan Allah yarinyar nan bata dace dani ba saboda bata da ilimin da zatayi goyayya dani ta kowane fanni."
Shatima yace."Mutukar tana da ilimin addini to baka da matsala dan wani ilimin boko ba wani abun damuwa bane ilimin addini shine abin dubawa saboda haka ina me baka shawara akan kayi wani abu akai idan kuma ka tsaya wasa nima zan shiga kawai dan dab'iun yarinyar da kyawun halayenta na burgeni ina so na aureta mace mai hankali da nutsuwa kodan na samu 'yaya masu tarbiya.
Yarima Ali shuru yayi yana kallon Shatima da ya dage yana ta gwarzanta kyawu da kyawawan d'abi'un yarinyar..........Yace."To shikkenan naji maganarka zan zauna nayi nazari akai." Shatima yace."Yawwa ko kaifa wallahi sosai nayi maka sha'awar auran yarinyar saboda kun dace da juna."
Bayan fitar Shatima tunani ya shiga yi akan maganarsu, shima yasan yarinyar nada kyawawan halaye wanda ko wane namiji zai sha'awar auranta, to amma ai idan ya zauna yayi duba na tsanaki zai fahimci cewar yarinyar bata dace da ta zama matarsa ba saboda ita din ma'kas'kanciya ce a gurinsa a kasan sa take babu yanda za'ayi ya auri baiwarsa a matsayinsa na Yarima dan Sarki babu macan data dace dashi sai Yar sarki ko yar wani mai mulki ko Lawisa ma zai aureta ne badan yana sonta ba kawai dai abinda yasa ya kwantar da hankalinsa da auranta saboda ya hango akwai mamora a jikinta shine dalilin da yasa bai damu ba, amma abin kunya ne abokananshi su san matsayin matarsa Sumayya sam ba tsaran auransa bace, amma zai duba ya gani yana ganin ko ya aureta ba zaiyi yarda ya haihu da itaba zata zame masa matar biyan bukatarsa. wannan shawarar ya yankewa kansa.
Bayan kwana biyu al'amura sunyi sauki kullum da safe idan na fita daga gurinmu gurin karatu nake tafiya acan nake yini nayi ta karatun al'kur'ani da sauran littafai sai yamma likis nake dawowa, Tambaya da babana duk basu san da cewar na daina zuwa sashen Yarima ba tinda kullum ba'a gida nake yini ba shiyasa basu gane komai ba..........Koda Haruna ya same ni da maganar kasa 'boye masa nayi saboda na riga nasan irin kaunar da yake min, Haruna ya dinga mamaki al'amarin yace."Sumayya a gaskiya nima ban goyi da bayan ki cigaba da zuwa ba, kiyi zamanki idan Fulani ta kira ki kan maganar sai ki san abinda zaki ce mata." nace"To shikkenan da wannan muka rufe maganar Yarima muka shiga hirar soyayyarmu.
Yarima Ali tun bayan damuwa da rashin zuwanta har abun ya soma damunsa kullum idan zaici abinci sai yayi takaici da bacin rai dan Suwaiba sam bata iya girki ba wani sa'in inda ta ajiye abincin haka take zuwa ta tarar da abunta beci ba, wani lokacin kuma idan yaci loma daya yaji babu dadi kiranta yake yayi tai mata masifa irin wacce yake min akanta yake huce fushinsa, Suwaiba ta dinga data sanin zuwanta sashen dan komai tayi masa bata gwaninta.
Umartar Gimbiya Lawisa yayi data dinga kawo masa abinci dan baya tsammanin zai iya tunkarar mahaifiyarsa da maganar daina zuwa yarinyar yasan dole ta binciki dalili shiyasa ya kasa tunkararta sai ya Umarci gimbiya Lawisa da ta dinga kawo masa daga sashen su, Lawisa abin nema ya samu kullum xata zauna ta tsara masa girke girke safe da rana da dare ta barbade da maganin mallaka ta kawo masa sashensa, ta zauna yana ci suna hira babban burinta maganinta yayi tasiri a kansa, aikuwa ha'kan ta ya cimma ruwa dan yanzu sun daina fad'a yana nuna mata kulawa farin ciki tamkar ya kasheta......
Bayan wata biyu al'amura suna ta tafiya cikin nutsuwa yanzu na manta na daina fargabar abinda zai biyo baya tunda naga har an dauki tsayin wannan lokaci fulani bata kirani da wata magana ba sai hankalina ya kwanta sosai na cigaba da karatuna maganar auranmu da Haruna kuwa an tsayar da lokaci wata shida mai zuwa Mahaifina da Mahaifin Haruna har gaban Sarki sukaje suka sheda masa abinda ke faruwa, Sarki ya nuna farin cikinsa kana kuma yasa mana albarka.......Tsakanina da Haruna soyayya mai karfi ta sake 'kulluwa Bangaran Lahira kuwa abun nata sai a hankali dan daukar gaba tayi dani ta daina yi min magana, na tambayeta dalili taki fada min sai nima kawai na tattarata na watsar da ita na cigaba da sabgogina hankalina a kwance..
Bangaran Magajin Sarki kuwa sai godiyar Allah Cikin nasara da yardar Ubangiji ya fara aiki a asibitinsa yayin da jama'ar gari ke zirga zirga cikin asibitin domin nemawa kansu da 'ya'yansu lafiya kamar yanda ya fada a ranar Walima haka Asibitin na dauke da 'kwarrarun ma'aikata wa'inda suka san aikinsu wannan dalilin ya sanya hatta da manyan mutane masu kudi suke zuwa a dubasu a asibitin, alhamdulillhi bukatarsa ta biya ta kowane b'angare sai abu guda dake damunsa shine yanda zai tunkari Hadimarsa ya fada mata cewar ya yanke hukuncin auranta kamar yanda ta bukata ya amince zai aureta ita da Lawisa a rana daya, kullum da tunanin yanda zai tunkare ta da maganar yake kwana yake tashi gabadaya kunyar hada ido yake da ita sabida abin da yayi mata, amma yana ganin tilas yaje ya samu mahaifiyarsa ya shirya mata wata maganar akan rashin zuwan yarinyar gurinsa.
Karfe takwas da rabi na dare ya samu mahaifiyar tasa a kishingide akan dadduma ta idar da sallah tana jan carbi, a nutse ya zauna a gabanta tare da mika gaisuwarsa, ta amsa da fuska a sake tace"Babana aiki ya 'boye ka bana ganin ka a kan lokaci."
Murmushi yayi yace."Wallahi kuwa Mamma wannan dalilin yasa ma na yanke shawara cewa kullum kafin na fita zan dinga shigowa mu gaisa sabida wani lokacin bana shigowa gida da wuri sai can dare.
Tace"Aikuwa dai hakan shine daidai ina fatan komai yana tafiya cikin nutsuwa da kwanciyar hankali." Yace."Alhmdullhi mamma komai na tafiya daidai jama'a da yawa najin dadin alkairin da kukayi musu kullum cikin yi muku addua sukeyi." Murmushin jin dadi tayi tace"Alhamdullhi dama babban burinmu shine mu faranta ran mabukata kaima Allah ya saka maka da alkairi ya baka ladan abinda kake yi.".
"Ameeen Mamma na." Dakin ne yayi shuru na minti biyu kafin ya dago kansa a nutse yace."Mamma wannan yarinyar dake yi min hidima kwana biyu ta dauke kafarta ta daina zuwa ni ban san dalili ba rashin samun zama yasa ban shigo na sheda miki ba sai yanzu dana shigo gidan da wuri nace bari nazo na sheda miki halin da ake ciki ko zaki aika a kira ta gani gata gaki sai ta fad'i abinda akai mata ta daina zuwa tayi aikinta ."
Fulani mikewa tayi zaune tana kallonsa da mamaki a fuskarta tace"Babana har tsayin wane lokaci sumayya ta dauka bata tare da kai."?
*Na kudi ne*
Idan kika karanta baki biya ba Allah ya isa! idan kina so ki biya ga yanda abin yake...VIP gruop#600 normal group #300 account... 0542382124....Binta umar gtbank....idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:26 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
63&64
'Bangaran Yarima Ali kuwa al'amarin ne ya dinga bashi mamaki! kamarshi yarinyar nan ta fitar da hannu ta tsinka masa mari! wannan al'amari ya girgiza mutuka kaf a tarihin rayuwarsa ba'a ta'ba cin mutuncinsa kamar na yau ba amma babu komai yasan duk abinda ya faru shine ya janyowa kansa kamar yanda yarinyar ta fada kafin ta fita, yana ganin dole ya hakura da ita komai k'ulafucinsa kuwa tunda raini da wulakanci ya soma shiga tsakaninsu, lallai dole ya kafa tarihi da yarinyar dan tunda yake babu 'ya macan da ta ta'ba yi masa abinda ta aikata masa, mari!! abin ya bashi mugun mamaki ta yanda har ya rasa wane irin hukunci zai yanke akanta
........Yana ganin ko kawai yabi shawarar ta ta farko wato ya aureta tunda taki bashi hadin kai idan ya biya bukatarsa sai ya saketa dan shi abin kunya ne a gurinsa ace itace matarsa sam bata kai matsayin da zaiyi zaman aure da ita ba, amma dole zai zauna yayi nazari da tunani akan al'amarin yanzu babban burinsa ya wulakantata kamar yanda ta wulakanta shi ta mare shi ba tare da taji tsoron abinda zai biyo baya ba, da kyar ya iya barin falon duk jikinsa yayi sanyi nadama da kunyar hada ido da yarinyar duk ya dameshi.
Washe gari da zazzabi na tashi na dinga daurewa domin bana so iyayena su fahimci abinda ke damuna.
Muna gama karyawa na nemi guri na kwanta ina lumshe idona babu abinda ke damuna sai al'amarin daya faru jiya har yanzu na kasa yanke hukunci.
"Sumayya ya kika koma kika kwanta kuma ki tashi kiyi wanka ki shirya jikin ki yau ai kaya zamu sa masu kyau tunda Walima za'a gudanar.
Tambaya ce take wannan maganar a lokacin da take tsaye a kaina.
bude idona nayi ina kallonta, tace"