Showing 90001 words to 93000 words out of 150413 words
Chapter 31 - Kwarya Tabi Kwarya Book Complet by Binta Umar Abbale .txt
bar maganar kada yace zai dauki mataki kan abinda akayi min.
Hannuna ya saki ya mike kallo na bishi dashi, ya nufi toilet, ajiyar zuciya na sauke a hankali na rintse idona ina addua cikin zuciyata.
Motsin fitowarsa tasa na bude idona ina kallonsa naga ya shimfida dadduma, da alama sallah zaiyi idanuwa na mayar na rufe ina tunanin iyayena yanzu ko wane irin hali suke ciki? nasan dai duk inda suke suna cikin tashin hankali da damuwa mai tsanani! hawaye suka zubo min a kumatu hannu nasa da sauri na goge ina kokarin danne kukan dake kokarin kufce min.
b'angaran Magajin Sarki kuwa nafila yayi raka biyu ya daga hannu sama ya roki Allah sosai akan abubuwan dake faruwa da rayuwarsa da makusantan sa yanzu abun ya wuce kansa har yazo kan masu kula dashi, tunda an kasa samun galaba a kansa to bari a sabauta hadiman sa, gaskiya magana dole ya dauki mataki akan al'amarin dan yana ji yana gani jinin yarinyar dake tsaye a kan rayuwarsa ya tafi a banza ba dole ya nunawa Muddibo kuskuransa, ya jima hannu a sama yana rokon Allah kafin ya shafa adduar a fuskarsa ya mike a nutse ya nufo gadon da nake kwance.
Cikin bacci na jishi a jikina, nayi saurin bude idona ina kallonsa yana kokarin kwanciya kokarin mikewa nayi yayi saurin rike hannuna! Girgiza min kai yayi a hankali yace."Ki kwanta mana." Murya na rawa nace"To ka tashi daga kusa dani.'' a hankali yace."Dan gurin dana kwanta bai isa ya tsare miki gurinki ba kiyi hakuri ki kwanta babu abinda zai faru sai alkairi."
A sanyaye na dinga kallonsa ina mamakin karfin halinsa Tamkar wata matar auransa haka yake Mu'amula dani.
"Gaskiya ni bazan kwanta gado daya dakai ba saboda haka bari kawai na sauka kasa.'' Yunkurin sauka nake ya rike kafaduna! cikin kulawa yace." Saboda na kula da motsin ki yasa zan kwanta kusa dake amma tunda bakya so shikkenan bari na sauka." kallo na bishi dashi lokacin daya sauka daga gadon ya koma kan doguwar kujera ya kwanta, tausayi ya bani ganin yanda yayi sanyi yana min magana cikin kwantar da murya na amince da cewa abinda ya faru ya girgizashi mutuka yanzu kuma na gane cewa ina da muhimanci a rayuwarsa tunda gashinan a zahiri ya nuna tashin hankalinsa..........Na jima ina tunane tunane kafin bacci ya d'aukeni! bacci mai cike da munanan mafarkai marasa dadi da ma'ana.
Kiran sunana da ake yasa na bude idona da sauri ina kallonsa yana tsaye a kaina, hannu na dora saman kaina ina jin wani irin ciwo a gurin, a nutse yasa hannu ya cire hannuna, "Sannu." kaina na d'aga ya cigaba da cewa"Kinga gurin yayi fushi ko."!? kaina na girgiza a hankali na fara kokarin mikewa ya kama hannuna, kallonsa nayi ya girgiza min kai da fadin"Kada kice komai taimaka miki zanyi kiyi alwala ko." Shuru nai masa, ya fara kokarin dora hannuna a kafadarsa, yana so ya rike kuguna. da sauri nace"Dan Allah ka barni zan iya komai da kaina. Bai saurare ni ba, ya ratsa hannusa a k'uguna, ya sani a jikinsa sosai muka nufi toilet, kallona yayi yace."Babu inda ke miki ciwo ko."? ganin yanda ya damu yasa nace"Eh babu kaina ne ke ciwo." Cikin rarrashi yace."Bari kiyi sallah sai muje gida kiyi break kisha magani insha Allahu zaki samu sauki."
Kaina na dauke jin wani irin abu dangane dashi, ya miko min brush da fad'in" Maza ki wanke bakin ki idan kuma ba zaki iya ba nayi miki ko."? saurin kar'ba nayi na nufi inda famfo yake, a nutse na wanke bakina cikin dubara nai alwalar, ya karaso gurin hannuna ya rike muka fita daga toilet din.
Farin hijabi irin na ma'aikatansa ya samin a wuyana ya gyara min dadduma na tayar da sallah.
Zama yayi kan kujera da wayarsa number Acp ya kira, suka gaisa cikin mutumci yayi masa bayanin dukkanin abinda ke faruwa, Acp yace."Tabbas biri yayi kama da mutum ranka ya dade a binkicenmu na baya sai da naso na fuskanci wani habu daga gurinsa to alhamdulillahi dama barinmu mu kama wanda yake da hannu acikin al'amarin sabida haka ka kwantar da hankalinka insha Allahu yau din nan zamu dam'keshi dole ne yayi mana bayanin yanda al'amuran suke faruwa." Yace."Okey to babu damuwa amma bana so ku shiga masarautar da niyyar kamashi kuje gurin aikinsa ku tozartashi acan sannan ku daureshi ku tafi dashi, bayan kun dam'keshi ka kira ni a waya inaso dik wani bayani da zaiyi ya kasance ina gurin." Acp yace."Babu damuwa insha Allah zan kira ka idan komai ya kammala." Sallama sukayi ya kashe wayar, ido muka had'a! naga fuskarsa ta rikice da zallar 'bacin rai! a gaskiya ban ta'ba tsammanin ina da kima a gurinsa ba.
A marairaice nace"Don Allah ka bar maganar nan wallahi idan nice na yafe."
Wani irin kallo yayi min kafin yace."Kada ki sake wannan maganar idan kina so mu zauna lafiya dake kiyi shuru da bakin ki Muddibo kashe ki yayi niyyar yayi kina tsammanin idan kin bar duniya zanyi rayuwa mai dadi? dole ne nabi kadin jinin daya zubar miki."
Kallonsa na dinga yi ina mamakin maganarsa nace"Mutuwa dole ce a gurin ko wane musulmi koda Muddibo ya kasheni nayi shahada kuma na rataya a wuyansa sabida haka dan Allah ka daina wannan maganar.
Ya jima yana kallona kafin yace."Ke! Sumayya bari nayi miki maganar k'arshe daga yau na 'yan taki kin zama mai 'yanci kuma insha Allahu a cikin satin nan za'a daura min aure dake! inaso ki zauna a k'arkashina cikin tsaro! dan na fahimci cewa ma'kiya zasu huce fushin su a kanki to zan aureki ki zauna a karkashina mu cigaba da rayuwa cikin inuwa daya.
Cikin tsabar kad'uwa da firgici nake kallonsa, ya daga min hannu tare da fadin"Bana bukatar naji komai daga bakin ki na gama yanke hukunci." Mikewa yayi tare da fad'in "Tashi muje gida." Na mike jikina a mace! gaba yayi nabi bayansa ina mamaki abinda yake shirin faruwa da rayuwata, Yarima zai aure ni sabida ya ceci rayuwata! ko kuma dai zai aureni ne saboda ya biya bukatarsa a kaina kamar yanda ya kud'urta a can baya, wannan tunane tunane ne ya dameni a fakaice na dinga kallonsa ina so na karanci abinda ke cikin zuciyarsa.
*Na kudi ne..*
Kada ki karanta mun littafi idan baki biya ba, idan kina bukatar ki biya ga yanda abin yake....Vip gruop#600 normal gruop#300 account.. 0542382124.....Binta umar gtbank....idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta whsap da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:27 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
86
Duk yanda naso na karancin abinda ke cikin zuciyarsa kasawa nayi dan gabad'aya tunda muka shiga mota ya sanja fuskarsa ta rikid'e sosai tamkar wanda bai ta'ba dariya ba, na dinga satar kallonsa ina mamakin sauyawarsa, har muka shiga masarautar wata magana ta fatar baki bata had'ani dashi ba......"Mika'il Ka wuce damu can sashen Mahaifiyata." Da sauri na kalleshi, hankalinsa nakan direba yana bashi umarnin inda zai ajiyemu, Mika'i da sauri ya juya mota ya hau hanyar da zata sadamu da sashen mahaifiyar tashi......Alhamdullilahi naji yace kafin yasa hannu ya bude kofar motar, yana fitowa nima na fito kaf ma'aikatan dake gurin suka bar abinda sukeyi suka zo suna mika gaisuwarsu gurinsa, nayi mamaki sosai da ganin ya tsaya yana amsa musu, gaba yayi da sauri nabi bayansa, jama'ar gurin suka bi bayanmu da kallo domin dayawa daga cikinsu sun dauka ba zata dawo da rai da kafafunta ba saboda yanda aka fita da ita jina-jina da jini.
Tana zaune kan kilishi da carbi a hannunta muka shiga falo tare da sallama a bakin mu. zamanta ta gyara ta amsa sallamar tare da tsira mana ido fuskarta kadai ta isa ta nuna mana cewar taji dadin ganinmu, cikin sanyi jiki nake tafiya kaina a kasa, dan shi har ya karasa kusa da ita ya zauna suna gaisawa, gurfana nayi a gabanta kawai naji ta janyoni ta rungume kam a jikinta sai saukar hawayenta naji a bayana, kawai naji nima zuciyata ta karye hawaye ya dinga kokarin kwace min.
Cikin rarrashi yace."Mamma dan Allah ki daina kuka ai gatanan da ranta bata mutu ba kamar yanda Muddobu yayi niyyar kasheta." buka Da sauri ta kalleshi tana mamakin furucinsa. kansa ya daga mata yana so ya tabbatar mata da gaskiyar maganarsa,
A sanyaye ta dago ni tana kallon fuskata, cikin alhini ta dora hannunta saman raunin dake goshi na murya na rawa tace"Sannu kinji ko."? kaina na daga mata cikin kokarin danne damuwata nace"Mamma ki kwantar da hankalin ki insha Allahu babu wani abu da zai sake faruwa dani dukkanin mai nufin mu da sharri zai koma kansa."
Ajiyar zuciya ta sauke tace"Sumayya jiya da kyar na iya bacci saboda wannan tashin hankalin daya faru, shin wai su waye sukayi kokarin halakar dake ne."? Shuru nayi tare da sunkuyar da kaina kasa
Ta daga kai tana kallonsa domin karin bayani, yace."Mamma kamar yanda na fada miki da farko hakane Muddobo shi kadai ya nemi ya halakar da ita kawai saboda taki bin umarninsa.
Cike da mamaki mai tsanani tace"Ni kuwa wannan al'amarin ya bani mamaki mutuka sumayya me muddibo yake so kiyi masa kika gaza har ya kai matakin daukar dutsen wuta ya buga miki.
Murya na rawa na shiga fada mata dukkanin abinda ya faru......Mamma kuka take sosai tana girgiza kanta, gabad'ayan mu hankalinmu ya tashi muka dinga rarrashinta, da kyar tayi shuru ta rike hannuna kam! "Sumayya ke 'yar halak ce kuma kin cancanci komai a gurina hakika kina d'aya daga cikin mutane da ba zan ta'ba mantawa dasu ba a tarihin rayuwata, kina da gaskiya da amana kin rike amanar dana baki duk rintsi kina kokarin kare lafiyar gudan jinina ni kuwa me zanyi miki a duniya wanda zai birgeki." ta karasa maganar tana rintse hannuna da nata.....mirmushi nayi a sanyaye nace"Ranki ya dade wallahi banyi wannan aikin domin ki biyani ba, duk abinda nakeyi akan Yarima inayi ne saboda Allah da manzon sa, Mamma wallahi bana bukatar komai a gurinki..........Mirmushi tayi tana kallona tace"Sumayya babu macan data dace da Babana sai ke ina rokon alfarma a gurinki dan Allah ki aureshi domin ki cigaba da kula dashi." Kaina na sunkuyar gabana na faduwa naji yace."Mamma ki kwantar da hankalinki dama nima hukuncin dana yanke kenan zan aureta saboda kyawun halinta da kuma tsayayyarta akaina sannan kuma zan aureta ne domin ganin ta k'ubuta daga gurin masu farautar ta, tunda duk iya kokari sunyi domun suga bayana Allah be nufa ba wannan dalilin yasa suka dawo kanta tunda itace garkuwata to idan suka kasheta suna ganin bukatarsu zata biya a kaina." ajiyar zuciya ya sauke kafin ya cigaba da cewa" Mamma na riga na yanke hukunci akan Muddibo sai dai duk abinda zai faru ya faru na shedawa Acp dukkanin abinda ke faruwa kuma ya tabbatar min da cewa zasuje su kamashi a gurin aikinsa, dole sai tabbatar mana da gaskiyar lamari."
Fulani shuru tayi tana nisawa kafin tace"Babana ba zan hanaka ka dauki mataki akan wannan lamari ba, idan ya kasance da saka hannu Muddibo cikin faruwar wannan al'amari to duk matakin da hukuma zata dauka a kansa daidai ne saboda haka yanzu zan sa aje fada a sanar da mahaifinka cewa yazo shida 'yan uwan nasa a zauna ayi magana." girgiza kansa yayi yace."Hakan yayi yana da kyau kowa ya sheda cewa Muddibo shine wake d'aya a cikinmu ke Sumayya ki nutsu sosai duk wani abu da kika san ya faru to kiyi bayani yanda kowa zai fahimta, kaina na daga gabana na wani irin faduwa.
Fulani wayarta ta dauka ta kira jakadiyarta tace maza taje fada ta sanar da Maimartaba tana da magana dashi da 'yan uwansa su Waziri.'' Jakadiya da sauri ta amsa ta mike ta fita.
Ya kalli mahaifiyar tasa a nutse yace."Mamma inaso Yarinyar nan ta zauna a gurinki bana bukatar ta sake koma sashen su har abada ta bar gurin sai dai taje da niyyar gaishe da iyayenta.
Murmushi tayi tace"Babana babu damuwa Sumayya zata zauna a gurina har zuwa lokacin da za'a daura muku aure.''' Yace."To nagode kwarai da gaske Mammana." Falon ne yayi shuru kowa na sa'ke-sa'ke a zuciyarsa, ni dai gabad'aya hankalina a tashe yake ina tsoron abinda zai faru idan jama'a suka sheda cewa Muddibo shine yake farautar d'an uwansa shin idan kowa ya yarda da maganata iyayensa zasu yarda kuwa? wace irin fahinta zasuyi min......shigowarsu falon yasa hankalina ya dawo daidai lokaci guda na shiga nutsuwata kaina a kasa, na gaishesu, Maimartaba ya dinga kallona yana girgiza kansa, a nutse ya kalli yaron nasa da fadin"Ina fatan yarinyar nan bata hadu da wata matsala ba."?
Yace."Ranka ya dade Allah ya kiyaye bata samu rauni mai muni ba amma hakika wanda ya aikata mata wannan mugun abu ranta yaso ya d'auka.'' Waziri yace."Subahannallahi! wai shin ke Sumayya ya akayi al'amarin nan ya faru dake muna so kiyi mana bayanin komai."
Mamma tace"Eh shine ai yasa na tura nace kuzo dukkaninku dan mu tuntuni tayi mana bayani kuma mun gamsu mun yarda da cewar yarinyar nan ba zata 'kir'kiri karya domin ta d'orawa wani sharri ba, a gaskiya idan kukaji wanda ya aikata mata wannan mugun abu sai kunyi mamaki amma inaso kafin ta fara bayani maimartaba ya bada umarnin kiran iyalan 'yan uwansa."
Maimartaba yace."Fulani maganarki tayi ma'ana yana da kyau Huwaila na gurin nan yana da kyau Hajiya Karima na gurin nan yana kuma da kyau ace Hajia Kubra da Falmata na gurin nan domin kowa yaji bayanin da wannan yarinya za tayi."
Gabad'ayansu suka amince da maganarta, da sauri ta kira Jakadiyarta tace maza taje ko wane sashe tace maimartaba nada bukatar ganinsu domin tattauna muhimiyyar magana." Jakadiya da sauri ta tafi cika umarni.
Shuru falon yayi bayan kowa ya hallara, Maimartaba ya kalleni a nutse yace."Sumayya dukkaninmu ke muke saurare muna bukatar muji komai daga gurinki."
Ajiyar zuciya na sauke a hankali na dago kaina sai naga dukkaninsu sun zuba min ido yanayinsu ya nuna min cewa ni suke saurare.
Kaina na sunkuyar cikin nutsuwa na fara magana.......................'Karya kike munafuka."!! Hajiya Karima ce ta katseni tana wani irin huci! ta mike tsaye tana nuna ni da hannu 'Karya kike algumguma! kice Muddibo shine wake d'aya 'bata gari! a masarauta me Magajin sarki yayi wa Muddibo da zai kasheshi."!?? Maimartaba ya buga mata tsawa! Mijinta Ciroma shine ya zaunar da ita gumi! sai karyo masa yake, Hajiya Karima ta koma ta zauna tana muzurai idanunta sunyi jajawur saboda tsananin tashin hankali.
Sai da kowa ya samu nutsuwa tukkuna maimartaba ya umarceni dana cigaba da maganata, Na cigaba da cewa"Ranka ya dad'e na rantse da wanda raina yake a hannunsa wannan maganar dana fad'a ba karya bace Muddibo shine ya tareni cikin dare bayan fitowa ta daga sashen Yarima, ya umarceni dana kar'bi magani lallai yana so na zubawa Yarima a lemo ya kuma tabbatar min da cewa mutukar na sake lalata musu aikinsu akan Yarima to sai ya kasheni, koda na kar'bi maganin a hannunsa sai na kwance na watsa masa shi a fuskarsa, na tabbatar masa da cewa ni ba za'a hada baki dani akashe mai rai ba! kafin nayi wani yunkuri ya dauki wani dutsen wuta dake gurin ya tad'e kafafuna na fadi a gurin kawai ya dinga buga min a kaina ina karewa , sawun mutane yasa ya jefar da dutsen ya bar gurin......to tun daga sannan ban san inda kaina yake ba."
Maimartaba yayi shuru yana girgiza kansa gabadaya yanayin fuskarsa ta sauya da zallan 'bacin rai! Ya kalleni a nutse yace."Sumayya koda ba kiyi rantsuwa da Allah da mazon sa ba, na tabbatar da cewa ba zaki zauna ki shirya wannan maganar ba, Tabbas ni na amince da maganarki Muddibo zai iya aikata wannan abu saboda wata manufa tashi." Ya kalli su Waziri da duk fuskokinsu suka nuna alamun alhini da tashin hankali mussaman Ciroma da duk ya muzanta a gurin sai gumi yake idanunsa sun kada sunyi jajawur saboda tashin hankali!
Maimartaba yace."Inaso gabad'ayan ku ku amince da maganar yarinyar kada wanda ya saka kokwanto a cikinta yarinyar nan Sumayya ni na amince da cewa ba za tayi wa muddibo k'arya ba sannan kuma inaso dukkaninnku ku kauda kanku akan irin hukuncin da zan yanke a kansa mutukar hukuma ta tabbatar mana da gaskiyar magana a kansa."
Hajiya Karima ta fashe da kuka mai tsanani! tace"Ranka ya dad'e ka tsaya ka nisa tukkuna kayi binkice akan wannan al'amari wallahi na tabbatar Muddibo ba zai aikata wannan mummunan akin ba a duniya me magajin sarki yayi masa da zai kashe shi, ranka ya dad'e ka duba maganata."
Maimartaba yace."Karima ki kwantar da hankalinki kamar yanda Magajin sarki ya sheda mana cewa yanzu haka Muddibo na hannun hukuma to ba zamu yanke hukunci ba sai mun tabbatar da gaskiya kan maganar saboda haka ki daina kuka kina tashin hankalinki dole Masarauta ta nuna fushinta akan abinda ya aikata.
Da bakin zaninta ta fyace hanci ta kalli Magajin sarki murya na rawa tace"Ali dan Allah kayi hakuri da