Showing 138001 words to 141000 words out of 150413 words

Chapter 47 - Kwarya Tabi Kwarya Book Complet by Binta Umar Abbale .txt

Tace"Lawisa ai yanzu hakama a cikin tashin hankali nake dan jiya da daddare Kanwar mamakin Lauratu ta shiga har gurin Sumayya tayi yunkurin cutar da ita dan yanzu hakama muna asibiti."




Lawisa taji gwiwarta tayi sanyi jikinta na rawa tace"Mamma dan Allah kuyi hakuri Aunty Lauratu ba zata aikata haka ba." cike da mamaki tace"Lawisa kin san halin kanwar mamanki nima na san halinta na kuma nasan abinda za tayi da wanda ba zata aikata ba Lauratu shigarta prison nawa saboda aikata munana ayyuka shine Mahaifiyarki ta hada baki da ita suke bibiyar rayuwar Sumayya saboda su dauki fansa akan abinda ya faru."




Lawisa kuka kawai take gabadaya kanta ya kulle ta rasa wane irin tunani za tayi dama tasan dole sai asirinsu ya tonu shiyasa tun kafin su aikata ta hanasu saboda gudun abinda zai faru dasu.


Mamma tace"Ki daina kuka ki fada min abinda ya hadaki da mijinki." Hawaye ta share ta dan juya ta kalli toilet yana ciki yana wanka bayan ya gama sasakarta wallahi tai rantsuwa da Allah sai ta tona masa asiri tunda ya kasance azzalimi.




Cikin kuka da nadama ta shiga fada mata abubuwan da suke faruwa. Mamma ta shiga tsantsar tashin hankali dajin abinda Lawisa ke fada mata, babanta shike gudun haihuwa har yana saka kwaroron roba sabida kada ya samu zuria! wannan al'amari yayi masifar tashin hankalinta, waiwaya tayi bayanta tana kallon Sumayya dake bacci! cikin zuciyarta tace"Wannan yarinya babu abinda zance dake a duniyar nan kinyi min hallaci tabbas samun irin masu halinki zaiyi wahalar gaske........Ajiyar zuciya ta sauke tace"Lawisa daina kuka ki saurareni." hawaye ta share tace"Ina jinki Mamma." Tace"Kiyi hakuri kinji ko insha Allah haka ba zata sake faruwa ba, sannan duk ranar daya kuma zuwa zai sadu dake da kwaroro a jikinsa kada ki amince dashi! idan kun dawo gida zan dauki mataki akansa inaso kuma ki rufa asirin maganar nan dan idan kin fito kin fada kin tonawa kanki asiri sannan kuma kin tona asirin mijinki amma hakikanin gaskiya babana bai kyauta miki ba amma kada ki damu zan dauki mataki akansa." Zuciyarta tayi sanyi tace"To shikkenan Mamma nagode sosai Allah ya kara girma." Sallama sukayi ta kashe wayar tana jin sanyi a cikin ranta, tana juyowa suka hada ido ya fito tun dazu kuma komai kunnensa. hannu ya mika mata da fadin" Bani waya ta." jiki a sanyaye ta mika masa ya kar'ba yana kallonta yace."Sai da kika fada mata ko."? hawaye ta goge tace"Ya za'ayi ba zan fada mata ba kana cutata.'' Yace'' To kin janyowa kanki saki." kallonsa tai gabanta na mugun faduwa! yace." Na fada miki cewa duk ranar da kika kuskura kika fitar da sirrina wani yaji to zan miki hukunci da bakiyi tsammani ba munyi haka da Sumayya kuma ta kiyaye ke da yake baki da mutunci kika kira mahaifiyata ko? to kisa a ranki cewa daga yau ke ba matata bace."!! Ihu! ta kurma! ta zube a gurin tana kuka da rokonsa akan kada ya saketa ya tausaya mata, fizge kafarsa yayi yasa kayansa ya fita daga dakin ransa a mugun bace.






*Na kudi ne*
Koda zaki ganshi a gruops na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abin yake....Vip group #600 normal gruop#300 account.. 0542382124...Binta umar gtbank....idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number.
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:28 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�
106
Koda nayi wankan sai naji dadin jikina na shirya tsaf na fito falon kawai sai na samu Tambaya ita da Mamma a zaune suna hira. wani irin farin ciki ne ya lullubeni dama tun ina asibiti nake tunaninta gwara Baba shi yaje tare dasu Maimartaba, fuska a sake na zauna ina gaisheta ta amsa cike da kulawa kallon da take min ne yasa na gane cewar taji dadin ganina kalau tace" ya jikin naki." ? nace"Jiki yayi sauki alhamdulillahi." Mamma tace." Da kikayi wankan Kinji karfin jikin naki ko."? nace"Sosai kuwa Mamma naji dadin dana gasa jikina." tace." To haka akeso sai kici abinci kisha magani nima zan shiga nayi wankan." nace"To mamma a fito lafiya." Tambaya tace"Ranki ya dade a fito lafiya watakila kafin ki fito ni na tafi." Mamma tace"A'a Tambaya kada ki tafi ki bari na fito tukkuna." Tace."To shikkenan ranki ya dade.'' Mamma mikewa tayi ta shiga dakinta..........Tambaya ta kalleni tare da sauke ajiyar zuciya tace" Sumayya naji dadin da wannan mata bata samu nasara akanki ba jiya dai saboda tsabar fargaba da tashin hankali kasa rintsawa nayi sai da na samu labarin dawowarku daga asibiti hankalina ya kwanta dalilin da yasa kenan na shigo domin na duba lafiyarki."


Nace."Tambaya duk mutumin daya dogara da Allah to babu shakka Allah na tare dashi, Lauratu tayi nufin cutar dani Allah ya kareni daga sharrinta wannan kad'ai ya isa ya nuna mana 'Kadaitakar Ubangiji sun nufe ni da sharri na mayar da al'amarin gurinsa shi kuma ya mayar musu da sharrinsu kansu Allah nagode maka."


Ajiyar zuciya ta sauke tace"Sumayya ni kaina na 'kara jin tsoron Allah a zuciyata wannan abu da ya faru da Hajiya Karima da k'anwarta ishara ce Allah ya nunawa masu irin halinsu." Nace"Hakane Tambaya yana da kyau duk wani musulmi ya tsarkake zuciyarsa ya kuma kadaita Allah shi kad'ai kada ya hadashi da abokin tarayya sannan kada ya zalinci wani idan an zalince sai ya barwa Allah da sannu zai saka masa abisa zalinci da akayi masa Allah kasa mufi karfin zociyoyinmu."


"Ameeen tace tana girgiza kanta.......Mamma ta fito daga dakinta cikin kamala gabadaya falon ya cika da kamshin turaranta, Jakadiyarta ce a bayanta hannunta rike da tarin kayan sawa. gurun zamanta ta zauna da mirmushi a fuskarta tace" Tambaya na barki kina jirana ko."?




Tambaya ta sunkuyar da kanta tana murmushi tace"Aa ranki ya dade babu damuwa ai ina fata kin fito lafiya."? tace"Lafiya lau Jakadiya bata wannan kayan na hannunki.'' da sauri Jakadiya ta mika mata kayan.....Tambaya tasa hannu biyu ta kar'ba fuskarta yalwace da fara'a.


Mamma tace"Kije kiyi amfani dasu daga yau ki daina amfani da kaya irin na bayi a masarautar nan kun zama masu 'yanci insha Allahu idan Maimartaba ya samu nutsuwa zamu zauna dashi za'a sanja muku gurin zama.




Cike da murna da farin ciki nace."Mamma godiya suke da wannan karamanci Allah ya saka da alkairi ya kara girma." Murmushi kawai tayi ba tace komai ba, Tambaya godiya kawai takeyi bakinta yaki rufuwa addua take gami da fatan alkairi. Mamma ta dakatar da ita da tare da fadin" Godiyar ta isa haka duk wani abu da taga anyi musu a masarauta sun cancanta ne saboda haka babu kalmar godiya a tsakaninsu. Cikin tsantsar farin ciki Tambaya tayi mana sallama Jakadiya tabi bayanta tare da kayan da Mamma tayi mata kyautarsu


Sai Bayan La'asar Maimartaba ya shigo, cikin nutsuwa na gaisheshi ya amsa cikin kulawa tare da tambayata yanayin jikina, nace"Naji sauki sosai." shuru gurin yayi na yan mintina kafin ya kira sunana na amsa a nutse tare da sunkuyar da kaina kasa, Yace."Kiyi hakuri abubuwan da suka faru dake inaso ki daukesu a matsayin kaddara insha Allahu abu makamancin wannan ba zai sake faruwa dake ba."


Nace"Ranka ya dade insha Allah magana ta wuce a gurina na barwa Allah komai suma wa'inda suka aikata mugun abu akaina na yafe musu har abada sannan kuma ina nema musu shiriya daga gurin Ubangiji." Yace."To alhamdulillhi dama haka akeso mutum ya kasance mai saukin kai da saurin afuwa." Ya kalli Mamma a nutse yace."Hajiya Karima ta samu nutsuwa kuma tayi mana bayanin yanda duk al'amura suka kasance yanzu haka tana can cikin damuwa da tashin hankali tayi kuka tamkar ruwan hawayenta zai 'kare gabadayanku tana neman afuwa a gurinku keda Sumayya tayi alkawari akan insha Allahu ba zata sake aikata abu makamancin wannan ba, na yafe mata saboda na yarda da tubanta kuma inaso ku yafe mata mussaman ke Sumayya." Mamma ta sauke ajiyar zuciya a sanyaye tace"Ranka ya dade shiriya dai ta Allah ce amma wallahi gani nake kamar karya take so take a kuma sakin jiki da ita ta sake aikata wani mugun abun yana da kyau a dauki mataki a kanta."




Girgiza kansa yayi yace."Fulani ki kyautata zaton alkairi akanta a yanda take kuka take rokon gafara yasa na gazgata tubanta saboda haka kema inaso ki cire shakku akanta kiyi mata kyakkyawar addua.'' Tace."To shikkenan ranka ya dade Allah ya yafe mata ya yafe mana baki daya. Yace."Yanzu jikin Ciroma ne yayi tsanani nasa an daukeshi an kaishi asibiti hakika yana bukatar addua dan bai san inda kansa yake ba."
Gabadaya daga ni Har Mamman jikinmu ne yayi sanyi dan jin yanda Maimartaban ke mana bayanin yanayin jikin d'an uwan nasa.


Uwargida da tawagar 'ya'yanta ne suka shigo falon, kallo muka bisu dashi jiki a sanyaye suka samu guri suka zazzauna.......Maimartaba ya bisu da kallo cikin nutsuwa yace."Ina fatan dai lafiya." ? Hajiya Huwaila ta fashe da kuka tana girgiza kanta, kawai sai suma su aunty Safiyyan suka shiga kuka.




Falon ya rikice da koke-koke! Maimartaba yasha jinin jikinsa tabbas ruwa baya tsami banza.




Mamma ta matsa kusa da Ita kafad'arta ta dafa cikin nutsuwa ta shiga kwantar mata da hankali akan tayi shuru dukkanin abinda yayi tsanani maganinsa Allah.




Huwaila ta kama hannunta ta rike tana hawaye tace"Fulani ki gafarce ni hakika na dade ina cutar dake da d'anki bana kaunarku kullum cikin shirya muku mugun abu nake, babu irin jifan da banyi miki ba Allah na kareki Aliyu kuwa babu irin abinda ba muyi masa ba nida 'ya'yana Allah yana 'kareshi Wannan yarinyar Sumayya ita ta zama garkuwa a gareshi dan duk wani abu na cutarwa da zamu nufeshi dashi itake wargazashi sosai muka dinga tsoratar da ita akan hakan amma da yake yarinyar arziki ce ba taji tsoro ba ta cigaba da bashi kariya hakika samun jajirtattun mutane masu tsoron Allah irin wannan yarinya zaiyi wahalar gaske! a lokacin da hukuncin rataya ya sauka akan Muddibo dukkaninmu hankalinmu ya tashi domin mun dauka zai fad'o sunayenmu a cikin wa'inda suke bashi gudumawa domin cikar burinsa sai mukaji shuru har aka rataye shi sunayenmu basu fito ba wannan abinda ya faru da Sumayya yasa gabadaya jikinmu yayi sanyi muka ga dacewar muzu mu nemi afuwa a gurinku akan abubuwan da suka faru a baya hakika mun tsorata da irin mutuwar da Lauratu tayi ga Hajiya Karima cikin wani irin mugun yanayi mara kyau ga Ciroma a kwance rai a hannun Allah babu shakka hakkin wa'inda suke zalinta ne ya sauka a kansu Ranka ya dade muna neman gafara a gurinka kema Sumayya ki yafe mana abinda muka aikata a gareki." Cikin kuka ta 'kare maganar.




Gabadaya shuru mukayi muna jajanta al'amarin, ni banyi wani mamaki sosai ba sabida dama na riga na san abinda yake faruwa.....Maimartaba da Mamma ne naga hankalinsu ya tashi gabadaya ma sun kasa magana.


Aunty Bishira tazo ta kama kafafun Mahaifin nata tana hawaye tace"Ranka ya dade kayi hakuri da abinda muka aikata ka gafarce mu kada kace ka yafewa duniya mu."


Girgiza kansa yayi a nutse yace."Bishira ni bani kukayi wa Laifi ba gurin Allah zaku nemi afuwa da gurin wa'inda kuka zalinta wato Magajin sarki da matarsa idan kun rokesu sun yafe muku to nima na yafe muku ina kuma rokon Allah ya kara shiryar min daku akan tafarkin addinin musulunci." Hajiya Huwaila ta sauka kasa gaban Mamma ta gurfana tana hawaye tace"Fulani ki yafe min abinda nayi miki na cutarwa." Mamma murya na rawa tace"Na yafe miki Huwaila Allah ya yafe mana gabadaya.




Gabana ta gurfana tana hawaye ta rike hannunta, gabadaya 'ya'yan nata suka kewaye ni suna rokona gafara, da sauri nace"Ni wallahi ba kuyi min komai ba idan ma kunyi min na yafe muku har abadah." godiya sukayi suka koma gurin zamansu Maimartaba yace."To Alhamdullhi yanzu sai mu jira dawowar Magajin sarki gabad'ayanku sai ku nemi afuwarsa Allah yayi mana afuwa baki daya." gabadaya muka amsa da "ameeen ya Allah."






*******
Bayan sati daya masarautar ta dan samu nutsuwa amma ba sosai ba tunda har yanzu Ciroma na kwance a asibiti an kasa gane abinda ke damunsa ta bangaran Hajiya Karima ana tunanin ma ta samu matsalar 'kwa'kwalwa dan kullum sai anyi mata allurar bacci da daddare ake samun nutsuwa gabadaya dai al'amarin sai addua............Maimartaba guri na mussaman yasa aka gyarawa iyayena komai na bukata aka sa musu sannan yasa aka dinkawa mahaifina manya kaya yana amfani dasu kuma kullum yana tare da Maimartaba a fada, Hankalina ya kwanta sosai ganin iyayena cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.........






Ana saura kwana biyu su dawo ya kira wayata bayan mun gaisa da juna yace na kaiwa Mamma wayar yana so yayi magana da ita, koda na kai mata wayar k'in kar'ba tayi nayi nayi da ita ta'ki 'karba jiki a mace na koma dakin da wayar a hannuna, ya sake kira a sanyaye nace"Ta'ki kar'bar wayar." Shuru yayi nace"Wai dan Allah wane laifi ka kuma yi mata wanda yasa take fushi da kai haka, kwanakin da suka wuce naga idan ka kira wayarta tana dauka har ku dad'e kuna hira amma cikin satin nan gabad'aya ta'ki sauraranka kusan kullum ma da damuwa take wuni."




Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke! yace." Lawisa na saki shine take fushi dani."


Gabana ya fadi! jin abinda yace, nace"Ranka ya dade mai yayi zafi! kaida 'yar uwarka zaka saketa me tayi maka? haba kai kuwa ka barta taji da abu daya mana iyayenta babu lafiya kai kuma ka saketa ina ganin ko wane irin laifi tayi maka ai bata cancanci irin wannan hukuncin ba."




"Sumayya Lawisa ba matar rufin asiri bace " shuru nai ina sauraransa ya cigaba da cewa" A lokotan baya kafin na gane gaskiya na ta'ba cewa dake idan kika sake kika fitar da sirrina wani yaji zanyi miki mummunan hukunci ko."? Nace."Eh kwarai haka ya faru."


Yace."A lokacin da kinyi gangancin fad'awa mahaifiyata bana san haihuwa zan sake ne sai Allah yasa kika kasance mai hankali da hangen nesa mai kuma rufe sirrin mijinta wannan janyo miki kima da martaba a idona sannan kuma ba kiyi zuciya ba kika cigaba da nuna min gaskiya har Allah yasa na gane na dawo kan hanya madaidaiciya hakane ko ba haka bane."?


Da sauri nace"Eh hakane." Yace."Ita Lawisa saboda ta raina ni ta kuma raina maganata sai ta kira Mamma a waya ta fad'a mata duk abunda yake faruwa, wannan dalilin yasa na yanke igiyar aurena dake kanta."




Murya na rawa nace"Gaskiya wannan ba hukunci bane! me yasa ku maza daga zarar mace tayi muku laifi sai ku saketa ku dinga adalci mana laifinka shine a kan gaba akan nata me zai sanya ka yanke mata irin wannan hukuncin a kan gaskiyarta ni dai don Allah ka mayar da ita dakinta shine farin cikina."




Yace."Sumayya ba zan mayar da Lawisa ba dama can ni bana sonta wallahi ke nake so." Kuka nasa nace"Ni kam idan baka mayar da ita ba bazan ji dadi ba kuma idan kana so na tabbatar da maganar kana sona to ka mayar da ita dakinta shine farin cikina."




Da sauri yace." Bana so kina kuka bana kusa dake my lov akan me zaki dinga zubar da hawayenki akan Lawisa kiyi hakuri ki bar maganar nan ni ke kadai kin isheni rayuwa."


Nace"Ni dai bazan yi hakuri ba har sai ka mayar da ita zan daina zubar da hawaye kuma ko ka dawo ba zakaga walwalata ba." murmushi yayi yace."To shikkenan ki daina kuka zan duba maganarki."




Hawaye na share nace'' to zuwa dare ka yanke hukunci kuma kada naji sa'banin abinda nake tunani." murmushin dai ya kuma yi yace."Sumayya zuciyarki tana da kyau wallahi wace macace ce take son kishiya ai na dauka murna zakiyi dana saketa."




Murmushin takaici nayi nace"Haba sai kace ba mace ba zanyi murna dan ka saki matarka ciwon ya mace na 'ya mace ne kai da kanka kace dani na fitar maka da sirri sai ka sake ni to me zai sanya nayi farin ciki akan hakan nasan nima hakan na iya kasancewa dani."


Girgisa kansa yayi kamar tana gurin yace."No Sumayya ba zan iya rabuwa dake ba idan kuwa kaddara ta gifta a tsakaninmu nasan nida jin dadi har na qare rayuwata.''


Murmushi nayi nace"To na amince da maganarka yanzu sai naji labari mai dadi akan Lawisa." yace."Okey to inaso dan Allah ki cigaba da rarrashin Mammana kafin na dawo." nace"Kada ka damu insha Allahu zata yafe maka mutukar ka janye sakin da kayiwa Lawisa." Yace."Zanyi tunanin hakan." sallama mukayi da juna na kashe wayar tare da ajiyeta a kusa dani....








*Na kudi ne..*
Koda zaki ganshi a group na sata ne idan kina bukatar biyan kudin littafin ga yanda abin yake.....Vip gruop#600 normal gruop#300 account... 0543282124.....Binta umar gtbank....idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:28 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
105
Cikin tsananin damuwa ya shiga kiran wayar mahaifiyar tashi, Mamma na ganin kiran wayar da sauri ta daga dan ta dauka Lawisan ce ta sake kira, jin muryarsa yasa da sauri ta datse kiran ta ajiye wayar gefanta, sake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login