Showing 27001 words to 30000 words out of 150413 words
Chapter 10 - Kwarya Tabi Kwarya Book Complet by Binta Umar Abbale .txt
abu zaiyi mata........"Ki wace ki bani guri kullum kina cikin tufafi d'aya sai kace jaka."
Na sake kallonsa zuciyata sai zafi take kamar na mayar masa da martani sai dai na daurewa zuciyata da sauri na bar gurin, kicin na nufa, koda na shiga kicin din kasa aikata komai nayi na tsaya jikin drowars ina sa'ke-sa'ke! yanzu dai koda nayi masa abincin baci zaiyi ba tunda ya fad'a min to ina ganin idan nayi abincin na ajiye tamkar nayi albazazzaranci ne. wata dubara ce ta fad'o min ina ganin itace mafita a gareni.
Zama nayi kan wata kujera ta mussaman wacce aka tanade ta domin hutawa, sai da na dauki kimanin mintuna ar'ba'in kana na mi'ke na dauko tire din da nake jera masa abincin sabbi fulas na jera a kai na fita daga kicin din hannuna rike da tiren kai tsaye gurin cin abincin na nufa, na jera tsaf tamkar da abincin a ciki.
Da sauri na baro gurin nesa dashi na tsuguna nace"Yallabai na kammala." ko kallona beyi ba ballanatana ya amsa min, miqewa nayi da fadin" A tashi lafiya'' da sauri na nufi kofar fita.
Kallo ya bita dashi yana sauke wata zazzafar ajiyar zuciya, akan idonsa ta fita daga falon, ya tsirawa fuskar wayarsa ido ta nayi masa gizonta a idonsa......Ya'ki yay da zuciyarsa ya miqe ya nufi danning din domin ganin abinda ta girka, dan yayi wa mahaifiyarsa al'kawari akan ya daina cin abincin waje sai na yarinyar tunda da ita ta amince masa, A kwanakin da suka gabata yana aika Haruna restaurant yay masa take a way da safe kuma ruwan tea kawai yake sha da biscuits...... Zama yay kan kujerar daning din a nutse ya fara kici-kicin bud'e fulas din, yana budewa yaga wayam babu komai. da sauri yasa hannunsa kan d'ayan tunkafin ya bud'e ya nuna masa da babu komai a ciki.......Cike da takaici ya daga fulas din yana duba cikinsa tamkar me neman wani abu. Lallai ashe yarinyar bata da mutunci ashe bata girka komai ba amma tazo ta jera fulas a daning sai kace wacce tayi abin arzi'ki! sosai ya shiga mamaki abunda tayi, kafin kuma al'amarin ya shiga bashi dariya.
Ya dinga dariya shi kad'ai ya mi'ke ya nufi 'kofa da niyyar fita Haruna zai kira yazo ya samo masa abinda zaici dan yunwa yake ji.
Moddibo ne ya shigo falon a lokacin da yake daf da fita, tsayawa yay yana murmushi, shima Muddibon murmushi yay masa ya bashi hannu suka gaisa da juna.
A nutse yace."Ina zuwa na ganka cikin manyan kaya ina Shatima yake.''? Muddibo yace." Shatima na gurin aiki ni kuma zanje gurin bikin birthday din wani friend d'ina shine na keso muje tare ko babu komai kaga gari na lura tunda ka dawo kullum kana gida baka san zuwa ko'ina.''
Sajensa ya shafa a nutse yace."Okey jira ni nayi wanka na kimtsa jikina dama yanzu yanzu nake tunanin kiran Haruna ya samo min abinda zanci babu damuwa yanzu idan mun fita sai mu tsaya a gurin cin abincin." Muddibo yace."Okey to babu damuwa muje ka kimtsa a nutse sai mu fita." Sai suka nufi saman a tare suna maganganun da suka shafe su......
*BINTA UMAR ABBALE*
*Please kuyi sharing��*
2/11/21, 8:19 AM - ???: *'KWARYA TABI 'KWARYA*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE�_ *bintaumarabbale@gmail.com*
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊�*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
_________________________
*Littafin na kudi ne....!*
_#300.....0542382124...Binta Umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin.......... Ga masu bukatar VIP Group 600 ne_
_Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d'aya 90899076_88137740_
*SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
37&38
Shigar 'kananun kaya yayi a jikinsa kasancewar ana d'an busa sanyi yasa ya d'ora jacket wacce ta sauko har gwiwarsa hular sanyi yasa ya sunkufe kanshi, ya sakaye idanunsa da bakin galishi, Moddibo sai tsokanarsa yake yana kiransa da bakin bature wai idan ba wanda yayi masa farin sani ba babu wanda zai ce ya had'a jinsi da bakar fata, murmushi kawai yake bai tanka masa ba, suka sauko a tare suna hira Moddibo farin ciki fal a zuciyarsa yana addua Allah yasa bukatarsa ta biya a kansa.
Su Haruna na ganin fitowarsu suka mike suna mika gaisuwa, ya tsaya yana magana dasu shi kuma Moddibo parking area ya nufa direba ya mike tsaye da sauri ya karaso gurin, Moddibo key ya kar'ba daga hannun Direban ya bashi umarnin tafiya....a nutse ya karaso gurin yana kallon Moddibon dake zaune a cikin motar yana sa mata key yace."Meye Amfanin direba za kayi draving da kanka.
Moddibo na murmushi yace."Yau d'aya naji ina sha'awar tuqa mota da kaina shigo kawai mu tafi." Jim yay na minti biyu ya kama murfin motar zai bud'e, da sauri Yakubu direba ya bude masa ya shiga ya mayar da murfin ya rufe da fadin"A sauka lafiya ranka ya dade." Hannu kawai ya daga masa Moddibo yaja motar suka bar gurin.
Hira suke sosai a tsakaninsu Yarima Ali ya saki jikinsa da Moddibo yana ganin dan uwansa ne dake kaunarsa ba zai ta'ba cutar dashi ba, yayin dashi kuma Muddibon ke Allah Allah su isa gurin birthday din ya cimma manufarsa a kansa, Yanayin Moddibo bai nuna cuta da zalinci ba sosai ya saki fuskarsa sai fara'a yake yana nunawa d'an uwan nashi kauna da kulawa, Magajin sarki ya sake sakin jikinsa dashi yana ganin ba zai ta'ba cutar dashi ba.
Gurin birthday din ya cika da samari da 'yan mata 'ya'yan manya masu kudi duk wanda ya hallaci gurin birthday diin
Nura promise to d'an gayu ne kuma ubanshi mai kudi ne kuma mai mu'kami ne
Guri na mussaman aka tanadar musu suka zaune a killace Magajin sarki sai sake tamke fuskarsa yake ganin yanda idanun 'yan mata yayi caaa a kansa, gaskiya yayi dakacan zuwa gurin a rayuwarsa ya tsani kallo mussaman daga gurin mace...........Cikin k'ayatarwa Nura ya yanka cake kafin a shiga rabon kayan ciye ciye. A nutse ta k'araso gurin da suke zaune hannunta dauke da tire da yake cike da kayan ci da sha, ajiyewa tayi kan tevur din dake gabansu ta zauna kusa da Moddibo suka gaisa tana satar kallon Yarima Ali wanda shi kuma tun zamanta a gurin yayi kici kici da fuska.
"Moddibo ganinku yayi wuya tun bayan kammala karatunmu kowa ya watse ko a waya bama gaisawa yanzu dai kafin taro ya watse inaso ka bani number wayarka.
Muddibo yace." Wallahi kam Latifa al'amura ne sukayi yawa ina fatan kina lafiya ya mutan gida." Da murmushi a fuskarta ta amsa kafin tace"Wannan d'an uwanka ne naga kuna yanayin kama da juna."
Muddibo murmushi yay ya kalli gefan da yake zaune yace."Kingdom kenan Magajin sarki kenan shi muke sa ran ya gaji sarautarmu."
Latifa zare ido tayi tana kallonsa tace"Ashe masu 'kasar ne a gabana Yallabai barka da wannan lokacin." tafad'a tana kallonsa, Ba tare da ya kalleta ba ya amsa ya mayar da hankalinsa gurin Moddibo da fadin"Yana da kyau mu tafi kamar yanda na fad'a maka inaso na samu abinda zanci..
Moddibo yace."Okey me zai hana kaci abincin gashi nan Latifa ta ajiye mana ina ganin ba sai munje restaurant ba.'' tevur din ya kalla ya dauke kansa daga gurin, yana da kyankyami ba kowane abincin yake iya ci ba.
Latifa ce ta shiga bud'e mishi ledar da aka rufe abincin tana fadin "bisimillah ranka ya dad'e." Ya sake kallon abincin a karo na biyu...Shinkafa ce akayi mata wata irin dahuwa sai kayi da gaske sannan zaka gane shinkafa ce taji kayan lambu da nama sai kamshi take daya plate din kuma gasheshshen nama ne da akayi mishi had'i da ganyayyaki sai manyan lemuka masu sanyi......A nutse yasa hannu kan cokalin ya d'ebo abincin yasa a bakinsa, yana taunawa yaji tes din abincin be masa ba daurewa yay yaci cokali uku ya ajiye tare da goge bakinsa da tissue.
Moddibo yace.''Ya naga ka ajiye cokalin." Girgiza kansa yay yana ya mutsa fuska "Alhamdullhi wannan da naci ya isa." Moddibo na dariya yace."Ashe ba yunwa kake ji ba dama." Ta'be bakinsa yayi yace."Ina jin yunwa sosai dan rabona da wani abincin kirki tun jiya da daddare kawai tes din abincin ne beyi min ba."
Muddibo murmushi yay a cikin zuciyarsa yace."Ai tunda dai kaci magana ta 'kare. A zahiri kuwa cewa yay ."Okey bari ni na gwada na gani ko zan iya ci." Shiru yay yana kallonsa. Moddibo a maimakon yaci na plate din dake gabansa sai ya janyo sabon plate ya bude ya fara ci a nutse....Lokacin Latifa ta jima da barin gurin..Moddibo abinci yake ci yana satar kallonsa ta kasan idonsa.
Yana zaune yaji kansa na juyawa amai na taso masa, daurewa ya dinga yi yana danne aman sabida jama'ar dake gurin, Moddibo ya kalleshi hade da fadin"Ya dai dan uwa naga sai ya mutsa fuska kake.'' Hannu yasa cikin Aljihu ya dauko hankici ya tsane gumin goshinsa a kasalance yace."Wallahi kaga ina zaune kawai nake jin jiri ga wani amai na taso min.
Cikin kulawa ya ajiye cokalin hannunsa da fadin"Subahanallahi kodai abincin da kaci ne ya janyo maka hakan." Cikin damuwa yace.Mybe shine amma nafi tunanin yunwar dana tara ce ta janyo hakan kai dai yi sauri ka gama mu tafi gida dan na soma ganin dishi dishi a cikin idanuwana.
Moddibo ya mike tsaye da sauri da fadin"Ina zan ga nutsuwar cin abinci bari na kira Nura yazo ku gaisa mu wuce kawai.'' yana gama maganarsa ya kusa cikin mutane domin kiran abokin nasa.
Tare suka dawo gurin da Nura, Magajin Sarki ya danne abinda ke damunsa suka gaisa da Nura yay masa fatan alkairi sosai kana ya mi'ke gaba yay ya barsu suna magana.
Cikin mota Muddibo ya sameshi yay gaggawar bude motar ya shiga ya zauna kunnar motar yay hankalinsa a kansa yace.''Kodai mu tsaya a hospital ne dan naga kana jin jiki sosai." Girgiza kansa yay yace."Muje gida kawai a yanzu babu abinda nake so sai kwanciya daga baya sai a kira Family doctor ya duba ni."
Moddibo yaja motar da fadin"To Allah ya sawwake.
"Ameeen yace yana rintse idanunsa.......sosai Muddibo ke sharara gudu kan kwalta ya kalleshi da fadin" Muddibo tafi a hankali mana." Muddubo yace."Ina sauri ne mu isa gida ka kwanta ka huta gabadaya Hankalina ya tashi wallahi bana k'aunar ganinka cikin damuwa.
Murmushi yay yana kallonsa yana sake jin kaunarsa a cikin ransa yace."Nagode sosai dan uwa amma kayi tu'ki a nutse zamu kai gida da yardar Allah"
Muddibo murmushi yay yace."Insha Allah." Rage gudun motar yay motar ta cigaba da tafiya a nutse.....ajiyar zuciya ya sauke ya rintse idanunsa yana jin yanda wani irin mahaukacin amai yake taso masa kansa sai juyawa yake tsigar jikinsa na tashi, sake rintse idonsa yay yana kiran sunan Allah................"Innalilihi wa'ina ilaihi raji'un."!!! kalmar daya ji Muddibo ya furta kenan da sauri ya bud'e idonsa da yake gani dishi-dishi dasu, gani yay motar ta 'kwace daga hannun Muddibo sun nausa cikin bishiyu motar sai tangal-tangal takeyi tana dukan duwatsu da manya manya bishiyu. kafin yay wani yunkuri yaga Muddibo yay fittt! ya fice a motar murfin ya koma ya rufe gam!
Kansa na juyawa yana kiran sunan Allah yasa hannu kan sitiyarin motar yana kokarin tsayar da ita ai kamar kara ingizata yake motar ta sake nausawa cikin gurin, sai kawai ya shiga kalmar shahada yana ganin kamar lokacin sa ne yayi.
Muddibo mi'kewa yay da sauri ya shiga karkade jikinsa gabadaya bai damu da daddaujewar da yayi ba shi dai tunda Mota ta nausa da Ma'kiyansa cikin daji shikkenan ajiyar zuciya ya sauke yasan ko shakka ba yayi dole yau yayi kwanan barzahu......Wayarsa ya dauko cikin aljihu cikin tashin hankali ya shedawa Waziri abinda ke faruwa....
Gabad'aya masarautar hargitsewa tayi masu koke-koke nayi masu salati nayi, masoyan Yarima Ali irina mune muke cikin tsananin tashin hankali dan ni dana samu labarin al'amarin sai da na d'auki buta na zagaya band'aki(Ummu Siyama kince wai me yasa ba'a sa star din littafi tana kashi😂 to gashinan Sumayya ta zaga bayan gida cikinta ya karta lol)
'Bangaran iyayensa kuwa gabad'aya Maimartaba rikicewa yay ya dinga salati yana neman fad'uwa, Fulani har ta fishi dauriya da tawakkali dan labarin abinda ya faru yana riskarta "Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! ta ambata dalilin da yansa kenan ta samu kwarin gwiwar tausar mijin nata.
Gabadaya maimartaba jikinsa saki yay ya zauna kan kujera zufa na karyo masa, a yanda Muddibo ya sheda musu yanda accident din ya kasance basa tsammanin zasu sameshi da rai........Waziri Galadima da Ciroma tare da fadawa suka shiga mota domin riskar gurin da accident din ya afku.
Fulani kuwa kad'aita kanta tayi da Ubangijinta tana kuka tana yi wa yaron nata adduar samun rahamar ubangiji dan gabad'ayansu sun fitar da rai a kansa suna ganin gawarsa kawai za'a kawo cikin gidan.
Bangaran Uwargida kuwa tamkar ta zuba ruwa a kasa tasha saboda dadi dan bayan Muddibo ya shedawa Waziri faruwar al'amarin ita ya kira ya tabbatar mata da cewa aiki yay kyau Magajin sarki sai dai wani kuma dan yana da tabbacin wannan ya she'ka barzahu." Murna da farin ciki kamar ya kasheta. a take ta dinga kiran yaranta tana fada masu abinda ya faru, tace dukkaninsu suzo gidan suna kuka gami da nuna alhininsu amma Allah ne kadai yasan abinda ke zuciyoyinsu. aikuwa hakane ya kasance kowacce da kuka take shigowa gidan harda masu fadin" Magajin Sarki Allah ya jikanka muna murna ka dawo gida xamu zauna da kai ashe ba zaka dade tare damu ba zaka koma ga mahallincin ka, wayyo Allah mutuwa Kinyi mana yank'an kauna......Abinda wasu daga cikinsu ke fada kenan suna kuka da fyatar majina......
*BINTA UMAR ABBALE*
*Please kuyi sharing��*
2/11/21, 8:19 AM - ???: *'KWARYA TABI 'KWARYA*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE�_ *bintaumarabbale@gmail.com*
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊�*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
_________________________
*Littafin na kudi ne....!*
_#300.....0542382124...Binta Umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin.......... Ga masu bukatar VIP Group 600 ne_
_Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d'aya 90899076_88137740_
*SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
*LAST FREE PEGE🥰*
wannan pege din shine 'karshe 'yar uwa kina so ki karanta littafi ki nishad'antu ki fad'akantu amma kuma kike ganin kyashin biyan #300 akan abinda za'ayi tsayin wata biyu ko uku ana baki kina farin ciki kina dariya, dan Allah mu dai nayi wa junanmu ganin ido wallahi rubutun nan akwai wuya meye #300 ko #600 dan kin biya marubuciya kin karanta labarinta, idan kina bukatar ki biya kudinki sai ki duba bayanai na na sama, kada ki zauna sai an sato kin ganshi a gruops ki karanta akwai 'karanta a ciki da zubar da aji kina karanta littafin da akayi doka akai ke kanki ba zakiji dadin hakan ba #300 ko #600 ta biya miki bukata🥰 masoya na asali sai na ganku😇
39&40
Kiran sunan Allah kawai yake yana kici kici da sitiyarin motar duk a kokarinsa naganin ya tsayar da motar, inaa! motar tuni ta k'wace ita nausawa kawai take cikin sa'ko gami da kwazazzabai tana cin tuntu'be da duwarwatsu gami da manya manyan bishiyun da suke gurin, da sauri ya dauke hannunsa daga kan sitiyarin motar ya fara kici kicin bude motar lokacin wuta har ta soma tashi, motar tayi duhu da haya'ki! tari mai karfi ne ya sar'ke masa shi da sauri ya dafe kirjinsa yana salati.....Motar ce ta daki wata rusheshiyar bishiyar kuka a take ta wuntsila zata kifa cikin ikon Allah ya wuntsilo can gefe ya fad'i kansa ya bugu da wani k'aton dutsan wuta dake dashe a gurin.........Kirjinsa ya rike yana janyo numfashi gami da kiran sunan Allah numfashin sa ne ya dauke jikinsa ya saki ya fadi a gurin jini duk ya wanke masa fuska da rigar jikinsa.
'Karasowar su gurin yayi daidai da tashin wuta motar ta dinga ci da wuta wani irin haya'ki na tashi. a gigice Muddibo ya durfafi gurin yana ihu! gami da kiran sunansa "Magaji sarki?"!!! gurin sai da ya amsa sabida yanda yake wani irin ihu! yana fizgewa dole sai yaje gurin.
Waziri hawaye ya shiga sharewa yana ta ambaton Allah a cikin zuciyarsa, Galadima da Ciroma kuwa Allah ne kadai yasan abinda ke zuciyoyinsu a zahiri dai idan ka kalli fuskarsu zaka ga alamun tashin hankali da damuwa amma mugun dadi da farin ciki sukaji a cikin ransu bukatarsu ta biya wanda suka tsana ya bar duniya.
Jami'an tsaro ne suka iso gurin Tare da Shatima da labari ya sameshi yana gurin aiki kuka sosai yake yi daya iso gurin yaga yanda wuta taci ta cinye motar ko kyallin Dan uwan nasa ba'a gani Shatima shine ya kewa Magajin sarki kauna ta gaskiya shiyasa ya shiga mugun tashin hankali da ya samu labarin faruwar al'amarin..Durkushewa yayi a gurin ya rufe fuskarsa da tafukan hannayensa yana kuka hade da nemawa dan uwan nasa gafara.
Jami'an tsaron ne Suka durfafi gurin suna haska fitilar su, Shatima mi'kewa yay yabi bayansu shima Muddibon sai ya mike da sauri yabi bayansu, Shatima wayarsa ya kunna yana goge hawaye yana dube dube a gurin.
A tsanake jami'an tsaron suka binkita cikin motar dake tashin hayaki kad'an kad'an duk ko ina sun duba basu ga wani abu da ya dangace shi ba, misali koda wutar ta cinyeshi ai bazu rasa ganin koda agogonsa ba hakan zai tabbatar musu da zarginsu.
Babban cikinsu ya kalli Muddibo dake haske haske a gurin yace."Bana tsammanin fa wutar ta tashi da Yarima a motar nan dan ba muga wani abu wanda zai tabbatar mana da zarginmu ba."
Moddibo gabansa ya fad'i! da sauri yace."Ku dai kara dubawa yanda wutar nan ta tashi bana tsammanin zata bar wani abu daya dangance shi amma ku tsananta binkice a gurin sosai." Yana maganar yana laluben gurin gumi ne kawai ke tsiyaya a jikinsa,