Showing 147001 words to 150000 words out of 150413 words

Chapter 50 - Kwarya Tabi Kwarya Book Complet by Binta Umar Abbale .txt

a yanzu shine addua domin ita kadai tafi bukata Lawisa a yanzu ina mai tabbatar miki da cewa Hajiya tayi nadama dan tsabar tension (damuwa) ne ya sanya mata shiga cikin wannan yanayi kullum yini take tana kuka da sambatu sai anyi mata allurar bacci ake samun lafiyarta saboda haka kada ki sake kamanta wata mummunar magana akanta insha Allahu Allah ya ganar da ita gaskiya, shi kuma baba addua zamu bishi da ita dan yayi mutuwa irin wacce ake bukata alhamdulillhi ya mutu da kalmar shahada a bakinsa wannan shine babban abin alfaharinmu."


Lawisa zama tayi kasan kafet tana kuka tana kiran innalillahi Khalisat kanwarta tazo ta rugunmeta suka cigaba da zubar da hawaye, Hajiya Karima kukansu ne ya tasheta daga bacci ta mike a firgice! ganin Lawisa yasa ta sauko daga gado ta zauna a gabansu kawai sai itama ta fashe da kuka tana girgiza kanta.


Muniru yace."Shikkenan kun tasheta yanzu idan ba Allah ne ya takaita ba zata fara surutai." kallonsa tayi tana girgiza kanta tace"Munniru kun mayar dani mahaukaciya ko. "? girgiza kansa yayi yana kallonta! ashar! ta d'ura masa tana wata irin zabura! tace" Nayi maka karya kenan."? ganin tana kokarin mikewa tsaye yasa Wali yace da Munniru maza ya fita, sai kawai ta dawo kan Wali din ta dinga cusa masa ashar yana rirriketa.....Lawisa ta taimaka masa suka zaunar da ita akan gado, sai kawai ta fashe da kuka tace"Lawisa Babanku ya mutu Lauratu kanwata data rage min itama ta mutu wuta ta cinyeta ni yanzu meye amfanin zamana a duniya wayyo Allah na shiga uku na lalace."!!!! da karfin gaske take maganar tana buge buge hade da d'ora hannu akanta.....Wali hankalinsa ya tashi da sauri ya fita daga dakin Lawisa da Khalisat suna kuka suka rirriketa tana fizgewa.




Wali tare suka shigo dakin da Magajin sarki da sauri yace."Ya dauko masa allurar da ake mata, Wali ya dauko ruwan allura da sirinji ya karba da sauri ya had'a allurar yace su rike da kyau Wali ya rirriketa yayi mata allurar.....Lumshe idonta tayi tana kallonsa magana a hard'e tace"Magajin sarki ka yafe min zalinci da mukayiwa matarka."


Tausayi ta bashi sosai cikin nutsuwa yace."Hajiya mun yafe miki insha Allah." Daga kanta tayi sai kawai ta 'bingire a jikin Wali bacci ne ya dauketa, dukkaninsu ajiyar zuciya suka sauke.




Ya kalli Wali a nutse yace."Insha Allahu yanzu zan kira Dr Nasir 'kwararran likitan 'kwa'kwalwa ne shi zai tsaya akan lafiyar Hajiya da ikon Allah zata dawo daidai gabadayanku inaso ku kwantar da hankalinku."
Wali yace."Mungode kwarai magajin sarki Ubangiji Allah ya saka maka da alkairi." Ya amsa cike da tausayinsu ya kalli Lawisa dake share hawaye yace."Kiyi hakuri ki daina kuka addua zakiyi mata." Kai ta daga murya a dushe tace"Insha Allahu zan cigaba dayi mata addua."






To bayan sadakar bakwai na Maigirma Ciroma masarautar ta d'an samu nutsuwa dan Maimartaba sauran 'yan uwansa sun cigaba da zaman fada, Shima Magajin sarkin ya koma aiki yayin da hajiya Karima ke samun kulawa tare da taimakon Dr Nasir wanda yake tsaye akanta alhamdulillhi ana samun cigaba sosai tunda ta daina surutai da zage-zage sai dai kuma yawan koke-koken da takeyi ne yake damun 'ya'yanta Dr yace su kwantar da hankalinsu shima kukan da yardar Allah zata daina tunda dai tana cigaba da shan magani.




Tunda suka dawo yake tare da Lawisa tsayin sati biyu kenan tsakaninsa da Sumayya sai ido dan ko sashen Mahaifiyar tashi ya shiga gaisuwa ce kawai take shiga tsakaninsu sai hirar yau da gobe babu wata mu'amular aure da suke yi saboda Mamma ta kafa ta tsare bata barinsa ya ke'be da matarsa komai idonta akai ita kanta Sumayyan abin na damunta kawai dai tana daurewa ne amma tana bukatar mijinta a kusa da ita, Yau lahadi baya fita da wuri ya shigo sashen lokacin Mamman bata fito ba yaji dadin haka dan haka kai tsaye D'akin da take ya nufa, ya bude kofa a hankali ya mayar ya rufe harda murza key! ajiyar zuciya ya sauke ganinta a kwance tana bacci ga santala santalan cinyoyinta a waje!


Xama yayi kusa da ita tare dasa hannunsa kasan mararta yana shafawa, da sauri ta bude idonta jin yanda d'an dake cikinta ya ke motsi shi kansa yana jin yanda babyn nasa yake naushin hannunsa.


Ido suka had'a ta mike zaune tana gyara rigar baccinta data tattare, gaisheshi tayi ya amsa tare da fadin"Kina kina kwance kina bacci babu abinda ya dameki dani ko."?


A nutse tace"Bangane maganarka ba." yace."Ina nufin kina cikin kwanciyar hankali ni kin barni ina watangaririya." murmushi tayi tace."To ya kake so nayi maka? nima wallahi kwana biyu ba jin dadi nake ba baby yana damuna da motsi.'' Ya cigaba da shafa mararta yace."Lafiya kenan idan basa motsi ai ke kanki ba zakiji dadi a jikinki ba yanzu ma zuwa nayi mu gaisa dasu."




Tace"Su waye zaku gaisa."? Kai tsaye yace."Twins d'ina mana." Dariya tasa tana kallonsa yace."Kema kin mayar dani sakarai ko."? girgiza kanta tayi yace."Hakane ma Lawisa nayi min wani irin kallo a lokacin da nake siyan kayan baby iri biyu ke kuma yanzu kina min dariya jikina na bani tagwaye zaki haifa min."...




Shuru kawai nayi ina kallonsa da mamakin maganarsa, wai tagwaye koda yake babu yanda Allah baya shirya lamarinsa.....Kafafuna yaja na kalleshi yace."Ki kwanta yau ni zanyi miki awo." tank'washe kafata nayi ina jin tsoro kada ya tsiro da fitina dan tunda naga kwayoyin idanunsa sun sauya nasha jinin jikina......"Wane irin awo kuma bayan wanda Dr Sadiya tayi min jiya." a kasalance yace "Nawa awon na mussaman ne." A dan tsorace! nace"Aikuwa bana bukata." kokarin sauka nake ya hawo gadon nace"Dan Allah ka sauka kaje falo gani nan." Girgiza kansa yayi yace."Kada ki bari aji kanmu dake kawai ki barni nayi abinda ya shigo dani domin kin san duk abinda zakiyi ba zan janye ba gwara ki hakura ki bani hadin kai."




Jikina ne ya mutu na dinga kallonsa, ina jin tsoron abinda zai faru......kwantar dani yayi a hankali yayi dubarar cire min rigar jikina, tunda ya fara sarrafa ni gabad'aya jikina ya rikice sha'awar dana tara ta tashi jikina na sakar masa muka shiga biyawa kanmu bukata...








*Na kudi ne*
Koda zaki ganshi a gruops na sata ne idan kina bukatar biyan kudin karatu ga yanda abin yake....Vip group #600 normal group #300 account... 0542382124...Binta umar gtbank....idan kati zaki turo #400 sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:28 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)


109&110
Koda na fito daga toilet din tsaf na samu dakin jakadiya sai goge goge take ita kuma Mamma na zaune a gefan gado ta dauki yaran duka ta rike a hannayenta kallo guda za kayi mata ka hango tsantsar farin ciki a tare da ita, Jakadiya da sauri tazo ta rike ni tana fadin"Sannu Sumayya." kaina kawai na daga mata muka karasa bakin gadon ta rike dani, Zama nayi a hankali nace"Mamma sannu." cike da kulawa tace"Sumayya aike za'ayi sannu." sunkuyar da kaina nayi ina murmushi......Tace "Amma nayi mamaki da wannan haihuwar taki sumayya me yasa kina jin ciwo tun yamma baki fada ba.


Kaina a kasa nace" Mamma wallahi ban tashi da wani ciwo mai tsanani ba kawai dai Allah ne ya kawo min haihuwar da sauki."


Girgiza kanta tayi tace"To Alhamdulillahi ina rokon ubangiji Allah yasa ki d'ore da haka ina fatan kuma babu inda yake miki ciwo."? nace"Babu Mamma sai dai ciwon mara kadan kadan.'' tace"Sannu insha Allah shima da ankwana biyu zaki daina ji." Ta kalli jakadiya da fadin" Ki duba mata kaya masu kauri tasa a jikinta sai ta kwanta ta huta." Jakadiya da sauri ta bude wardrobe tana dubawa




Riga da zani na atamfa ta dauki min ta taimaka min nasa a jikina, rigar sanyi nace ta dauki min nasa a jikina, ina kokarin kwanciya Mamma tace"Ki daure kici abinci sumayya." nace"To Mamma. Jakadiya ta fita da sauri minti biyar ta shigo hannunta da plate din abinci.


Kar'ba nayi a nutse nayi bisimillah na fara ci muna hira Jakadiya ta kunna turaran wuta a dakin ta nufi bandaki ruwan wanka ta hada ta fito dashi a madaidaicin baho, Mamma tace"A wanke musu jikinsu sai a goga musu zaitun.'' jakadiya ta mika hannu domin kar'bar babyn Mamma ta mika mata hassan din da fadin" shi zaki fara wanke wa dan na lura kamar bashi da hakuri sai tsotsar hannunsa yake da alama acici ne." Jakadiya na dariya ta kar'beshi Tace."Kinga shi kuwa wannan bacci yake tunda ya bude idonsa sau daya bai sake ba yana ta bacci." Dan murmushi nayi bance komai ba, Tace."Ai da safe su Tambaya zasuji labari mai dadi sumayya kin iya haihuwar a tsanake babu fargaba da tashin hankali."


Nace"Mamma kullum dama ina rokon Allah ya sassauta min idan nazo haihuwa Allah maji rokon bayinsa ya amsa min adduata."




Mamma tace"Aikuwa dai sumayya dukkanin wanda zai rike addua yana tare da nasara a rayuwarsa...........Tare suka shigo dakin shida Lawisa, Mamma tace"Yanzu ashe sai da kaje ka taso ta da tsohon daran nan." Yana kokarin magana Lawisa tace"Wallahi Mamma gwara da yaje ya tasoni nazo naga irin kyautar da Allah yayi mana." zama tayi a kusa dani fuska a sake tace"Sumayya sannu." Nace"Yauwa sannu ranki ya dade.'' tace"Ina fata dai baki manta dani ba a lokacin da kike nakuda." Dariya nai ina kallonta nace"Haba yaushe zan manta dake nayi miki addua sosai kuma insha Allahu ta kar'bu." Mamma tace"Aikuwa Lawisa ki kwantar da hankali adduar mace mai naquda bata da hijabi insha Allahu kafin tagwaye su girma kema kin samu rabonki." Tace."Ameeen ya Allah Mamma."




A nutse ya karaso kusa damu ya tsaya, Mamma ta kalleshi taga duk yayi wujiga wujiga tace."Babana wai tare da kai akayi nakudar ne."? girgiza kansa yayi yace."Ko daya Mamma ni a lokacin ma data haihu ina toilet wallahi sai fitowa nayi naji kukan baby.''


Tace."Ai abun da mamaki sai dai ba'a mamaki da ikon Allah!! naga kayi firgai firgai ne shiyasa nayi zaton ko ka taimaka mata."


Dariya yasa yace."Mamma ina ni ina wannan ya'kin ai sai ku na dai sha matsa a gurinta kafin Husaini ya fito." Mamma ta kalli yaron tana murmushi tace."Allah sarki ai daka ganinsa zai yi hakuri." Murmushi yayi yana leqa fuskar yaron.




Koda Jakadiya ta gama wanke Hassan din Lawisa ce ta kar'beshi ta shiryashi tsaf tasa shi a towel yace na kar'beshi na gwada bashi nono. kunya ta hanani na fito da nonon kawai sai yazo yana kokarin daga min riga a nufinsa ya fito da nonon.....a fakaice na buge hannunsa, na fito da nonon ina kokarin sawa yaron a baki, ko kunyar mahaifiyarsa baya ji ya tsuguna yana nuna min yanda zanyi, ni dai gabadaya kunya ce ta rufe ni itama Mamma basarwa tayi sabida ta riga tasan halin rashin kunyar yaron nata.




Cikin ikon Allah yaron ya janyo ruwan nonon cikin dubara irinta 'ya'yan zamani ya shiga zu'kar nononsa gabadaya muka dinga mamakin wayon yaron, Mamma tace"Dama yaran yanzu da wayonsu ake haifarsu, sai dana tabbatar da cewa nonon ya isheshi na cire masa sai na mikawa Lawisa shi ta karbeshi tana goge masa baki, Hussainin na karba na fara kokarin sa masa nonon a baki, yaron kasa kamawa yayi sai ya fara kuka, Mamma tace" Allah sarki shi bashi da wayon dan uwanshi ki kama masa nonon a hankali zai iya." Cikin dubara na kama kan nonon nasa masa a baki yana mamula a hankali kafin ya kama sosai ya shiga tsotsa, ajiyar zuciya na sauke ina godewa Allah a bisa ni'imar da yayi min.


Washe gari da safe kowa ya samu labarin haihuwar aikuwa sasheh cika yayi da jama'a wasu na fita wasu na shigowa kaina ya dinga ciwo saboda hayaniya, aikuwa Lawisa na sheda masa cewa kaina na ciwo yace a rufe sashen kada a sake bari kowa ya shigo kana ya umarceta data bani wayar yana so muyi magana.


Kar'ba nayi tare da sawa a kunnena yace."My lov kada ki janyowa kanki lalura garin san gwanintarki kin son jama'a suna ta damunki da hayaniya please dan Allah ki kwanta ki huta nace kowaye yazo kada a bude masa kofa, sannan kuma kada kisawa jikinki ruwan zafi sosai ki sirka kafin kiyi wankan."


Nace"Kayi hakuri ni kaina wallahi so nake na kwanta abin ya gagara gabadaya mutane sun hana duk wanda yazo burinsa na saurareshi wannan dalilin yasa nake tsayawa muna gaisawa.'' Yace."Ni dai na fada miki ko auntis d'ina ne suka zo ban bada damar a bude musu kofa ba." " Yar dariya nayi nace Babbar magana kenan." Yace."Kwarai kuwa keda kin dauka abin wasa ne my lov lafiyarki ita kadai nake bukata kin haihu lafiya bana so hayaniyar mutane tasa miki ciwon kai."


Nace"Ka kwantar da hankalinka babu abinda zai sameni insha Allah jama'a kuma dole kayi hakuri dasu." Yace." To shikkenan zanzo na kasa na tsare a sashen duk wanda yaga ina gurin sai ya juya ya tafi " Dariya nasa ina mamakin rashin kawaicinsa, yace."Wato kin mayar dani sakarai ko."? da sauri nace"Aa ranka ya dade kayi hakuri sai kadawo ko." ajiyar zuciya ya sauke yace."Ki bawa Lawisa wayar zamuyi magana." Sai da yay maganarta wallahi na tuna tana dakin, cikin jin nauyi na mika mata wayar ta karba a sanyaye sukai magana.






To haka kwanakin haihuwata suka cigaba da tafiya cikin kwanciyar hankali da kulawa ta kowanne bangare Mamma na iya bakin kokarinta a kaina haka nan itama Tambaya nayin nata kokarin akaina da 'yan tagwayena da suka amsa sunansu Hassan da Hussaini Maimartaba kullum sai ya aiko da safe an daukesu an kai masa yayi musu addua sukan jima a gurinsa kafin a dawo min dasu..........Uwargida Huwaila ita ke shigowa kullum da Yamma ta gasa min jikina tayiwa yara wanka, ita kuma jakadiya itake kula damu da safe su aunty Safiyya kuwa shatara ta arziki suka had'o mana nida tagwayena kowanne da akwatinsa saqe da kaya, na samu kyautuka muhimmai ranar suna kowa kokarinsa ya faranta min nida 'ya'yana taro akayi sosai kuma aka tashi daga taron cikin koshin lafiya






*Bayan wata hud'u*
Yara sunyi wayo sosai dan har an fara koya musu zama......a lokacin ne kuma Allah ya azurta Lawisa da nata rabon ranar da suka tabbatar da cikin ita da mijin nata suka dinga murna da farin ciki......Ina zaune a kan kujera da Hussain a hannuna yana min rigima Ya shigo tunda na ganshi cikin walwala nasan akwai magana.


Zama yayi kusa dani tare da kar'bar yaron yana jijjigashi yace."Wai kukan me yake."? nace"Watakila yunwa yake ji wallahi kaga hassan duk ya shanye ruwan nonon." Hannu yasa kan nonon yana latsawa, na ture hannunsa da fadin"Kai kam kafiye wasa." Yace."Sumayya ban yarda ba kodai mitsininsa kikayi nasan Hussani da hakuri fa.".


'Yar dariya nayi nace"Sai dai idan kaine ka mintsineshi." shiru yayi min yasa yaron a kafada yana jijiigashi! Mariya ce ta fito daga kicin hannunta rike da fida cike da madara....har kasa ta durkusa ta gaishe da sauri ta miko min fidar ta bar gurin, nace"Kawoshi na gwada bashi madarar ko zai sha. miko min shi yayi na kar'beshi sai harbe harbe yake ina sa masa fidar a baki ya kama yana tsotsa


Ajiyar zuciya muka sauke a tare dashi, dan tsokana yasa hannu yana jan kafar Hassan dake kwance a gefena,


Murya na rawa nace"Dan Allah kada ka tsokaneshi kasan rigimarsa tafi ta Hussani." yace.""Ai so nake suyi ta baki wahala idan kikayi zuciya sai kiyi musu kani ko kanwa."




Wani irin kallo na watsa masa." dariya yasa tare da lakuce min hanci.....nace"Haba kai yanzu idan na samu ciki sai kayi murna ka duba fa kaga irin wuyar da nake sha da yaran nan."




Yana mirmushi yace."Meye a ciki sumayya a wuya bata kisa ko yanzu kika samu ciki ina farin ciki wallahi nasan ke 'yar baiwa ce Allah zai rangwanta miki."




A sanyaye nace"Hakane amma dai ni inaso yaran suyi kwari tukkuna idan kuma Allah ya kawo sai nagode masa." Yace." Yawwa 'yar albarka kinsan Lawisa ma Allah ya bata nata ko.'' na kalleshi cike da farin ciki nace"Ya za'ayi na sani tunda ba fada min kayi ba.".




Yace."Yau muka tabbatar da cikin tana can sai murna take." Nace"Kai kuwa ai dole tayi murna wallahi nima na tayata farin ciki Ubangiji Allah ya rabasu lafiya."


Ya amsa da ameeen yana min kallon kasa-kasa.....walwalar fuskata na rage nace"zaka fara ko."? Yana munafikin murmushi yace."Ki kira wa'innan yaran su dauki babys d'in nan muje daki."




Zum'bura baki nayi nace"Ni babu wani daki da zanje." Matsoni yayi yana sumbatar wuyana yace."Idan kuwa hakane lallai za'ayi abun kunya dan zan iya danneki a falon nan babu abinda ya dameni da hadimanki."


A sanyaye na kalleshi, girarsa ya daga min daso ya tabbatar min da maganarsa




Mariya na kwalawa kira da sauri tazo nace Ki goya Hassan kuje can gurin Mamma." da sauri tace"To ranki ya dade." Mikewa yayi ya shiga daki......ban bi bayansa ba sai da na tabbatar da cewa Mariya ta tafi da yaran sannan na bishi dakin.






*BAYAN SHEKARU GOMA*
Alhamdulillahi abubuwa masu kyau da marasa kyau sun faru a cikin wannan shekarun da suka wuce a cikin abubuwa masu dadi da suka faru a cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login