Showing 114001 words to 117000 words out of 150413 words

Chapter 39 - Kwarya Tabi Kwarya Book Complet by Binta Umar Abbale .txt

gami da bin umarnina! ina sonku ina kaunarku kuma ina bukatar ku zauna lafiya da juna, ke Lawisa kece babba yana da kyau ki kama girmanki bani da matsala da Sumayya domin nasan halinta zata girmamaki ta kuma mutuntaki! ki ajiye maganar sarauta a gefe bana so ki dinga nuna mata asalinki ki dinga daukar kanki daidai da ita Sumayya ba mutuniyar banza bace." Wani irin kallo Lawisa take masa ya za'ayi ma ta daidaita kanta da baiwa abinda ba zai t'aba yiwu bane."


Ya cigaba da cewa" Kowacce na zaune a gurinta ban amince ku dinga ziyartar junanku ba sai da k'wakkwaran dalili ina ganin hakan shine maslaha a gare mu baki daya. daga karshe nake mana adduar fatan alkairi tare da rokon Allah ya dawwamar mana da zaman lafiya a zamantakewar auranmu."


Cikin nutsuwa na amsa da "Ameen ya rabbi." Ajiyar zuciya ta sauke a cinkushe tace"Naji ni kayi min fada amma ita ba kace mata komai ba.''




Cikin kulawa yace."Bangane abinda kike nufi ba."? "Kace na dauki kaina daidai da ita na zauna lafiya da ita ka nuna min muhimancinta amma me yasa ita baka nuna mata cewa ina da muhimanci a tare da kai ba."


Shuru yayi yana kallon kasan kafet! ni kam mamaki ta bani na dinga kallonsa ta gefan ido ina jiran naji abinda zai ce, a nutse ya kalleni yace."Ke Sumayya Lawisa nada mahimanci ba sai na fada miki ba ki bata girma a matsayinta na uwargidanki."




Murmushi nayi nace"To insha Allah zan cigaba da bata girma da muhimanci, ranki ya dade kada ki damu ni ba zan raina ki ba Insha Allahu."


Murmushin dole tayi ta kauda kanta gefe, yace."Lawisa kin gama kwana biyun ki yau bangaran Sumayya zan tare nayi mata nata kwana biyun."


Ya mutsa fuska tayi da kyar tace"To shikkenan." yace."Ina fatan kina shan magungunan dana baki kuma ina fatan gurin ya dena zafi."?


Cikin shagwa'ba tace"Wallahi har yanzu yana zafi da kyar ma nake tafiya ni kam gwara ka kwana a gurinta ko na huta." Dariya ya kyalkyale da ita yana kallonta tana matso hawaye.


Takaicin abinda suke yasa na mike a dake! nace"To ni zan tafi ." da sauri ya kalleni ya wani marairace fuska yace."My love kina jina da Lawisa ko wai ni take kora daga sashenta sabida na ina jin dadi da ita."


kamar na kwad'a masa mari saboda 'bacin rai! na ta'be bakina had'e dayin gaba ba tare dana tanka masa ba."


Da sauri yace."Kada ki fita kizo ki taimaka mata da ruwan zafi! idan yaso itama sai ta ramawa kura aniyarta." Murmushi nayi na juyo ina kallonsu nace"Haba ai kai da ka 'bata kai zaka gyara ni meye nawa wallahi ranki ya dade kada ki yarda ki barshi ya fita sai kin hukuntashi." Dariya ya dinga yi yana kallona ita kam kallon mamaki naga tana yi min, na saki mirmushi duk dan na nuna mata cewa banji haushi ba nace" Sai anjima." juyawa nayi da sauri na fita daga falon da kyar na k'arasa gurina na zauna kan kujera tare da rufe fuskata da hannuwana! innalilihi na dinga ja a zuciyata kafin na samu sassauci cikin sanyin jiki na mike na nufi daki kwanciya nayi ba tare dana warware lifayar jikina ba, tsabar bacin rai da nake ciki ya dinga nema ya sa min ciwon kaina hawaye ne ke kokarin zubowa ina mayar dasu, nasan idan basu zuba ba bazan samu kwanciyar hankali ba, sai kawai na barsu suka dinga zuba a kuncina haka na dinga juye-juye a bed din ina mamakin kaina! kishi ne dani irin mai wahala idan banda abin son zuciya irin nawa menene na damuwa dan yayi auratayya da matarsa.........Zuciyata tace"Duk da haka abinda sukayi miki basu kyauta ba abin kamar da akwai cin fuska a ciki, meye dan sunyi rayuwar aure sai sun fito suna fad'a miki gabad'aya ita dashi basu da addini........Hannu nasa na goge hawayen fuskata na gyara kwanciyata rufin dakin na tsirawa ido ina tunani yanzu yana can yana rarrashinta dan naga sai wani lalla'bata yake kafin na fito, gaskiya halin namiji sai shi, wallahi banta'ba tsammanin zai so Lawisa ba sai gashi lokaci guda yana nuna mata kauna da kulawa a gabana.


Agogon bango na duba har nayi mintina ar'bain da fitowa daga sashen bai shigo ba, na sake jin 'bacin raina ya nunnku! rufe idona nayi na cigaba da nanata kalmar innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! da haka bacci mai nauyi ya dauke ni.


Bacci nayi sosai sai wajejen la'asar na tashi! na dinga mamakin tsayin lokacin dana dauka ina bacci! jikina a mace nai wanka na kimtsa jikina kana na tsaya kan dadduma domin gabatar da sallah! ban tashi daga kan daddumar ba sai dana gabatar da la'asar tukkuna na tashi daddumar na ninke tare da ajiyeta a inda aka tana da kai tsaye falo na nufa ba tare da na cire hijab din jikina ba.




Suna zaune a guri guda ganina yasa duk suka mike tsaye, cike da mamaki! nace "Meye haka daka ganina duk kun razana."


Sunkuyar da kansu sukayi ba suce komai ba, nace"Daga yau dan Allah kada wacce ta sake ganina ta razana kuma bana so kuna sa gwiwarku a kasa gurin gaisheni."




Mariya tace"Ranki ya dade ai dole ne mu girmamaki domin kin cancanta." Nace"Nasan da haka ai ni bana so ku d'aura min izzah ne! duk girman da zaku bani ku bani mustad'a'a kada yayi yawa."


Gabad'ayansu suka amsa da "To ranki ya dade insha Allahu zamu kiyaye." ajiyar zuciya nayi tare da zama kan kujera, Sakina tace"Ranki ya dade ko a kawo miki abinci nan."?


A nutse nace." Me kuka girka." ? "Ranki ya dade damubun shinkafa ne." murmushi nayi nace"Aikuwa kun burgeni wallahi jeki kawo min." da sauri ta mike ta nufi gurin cin bincin, waya ta na cigaba da dubawa har ta gama jera kayan abincin a teble din dake gabana,
Kokarin zuba min take na ajiye wayar da fadin"Kuje kawai zan zuba da kaina." godiya sukayi min da sauri suka fita.


Ina kokarin bud'e fulas naji zubowar abu a pant d'ina, gabana ne ya fad'i! da sauri na mi'ke na shiga toilet domin na tabbatar da zargi! ina tsugunawa shine ya fara zuba! "shikkenan! abinda na fad'a kenan ina girgiza kaina, kai amma wannan abu bai kyauta ba! ruwa nasa na wanke jikina na gyara gurun na fito, na kimtsa jikina, falon na koma na zauna gabadaya jikina ya mutu da ganin al'adata ango naso ya gwangwaje abu yayi masa cikas! ta'be bakina nayi a zahiri nace" Gwara haka sai muga 'karyar kwad'ayi! ko yaya zaiyi idan ya ankara! dariya nayi na girgiza kaina fulas din abincin na bud'e! 'kamshi ya bugi hancina dambun yayi shar-shar dashi yaji gyada da zogale sai kamshin man gyad'a yake, da sauri na zuba wanda zai isheni nayi bisimillah a nutse na fara ci ina gyada kaina tamkar kunnena ya tsinke dan d'adi gaskiya sunyi kokari sosai domin dambun ba 'karamin dadi yayi ba.






To a haka na kasance a sashena ni kad'ai har bayan isha'i bai shigo ba raina ya 'baci mutuka gashi girman kaina ya hanani kiransa a waya babu irin sa'ke-sa'ken da zuciyata ba tayi min ba, daga karshe dai daki na shige nayi shirin kwanciya zama nayi gefan gado da romot a hannuna tashar larabawa na kama naga suna drama irin tasu, kawai sai na shiga bargo na kwanta tare da cigaba da kallon film din kasancewar ina dan jin labaraci yasa na dinga fahimta sosai film din ya dauke min hankali! kawai naji an turo kofar dakin.




Ido muka had'a dashi yana sanye da shadda fara kal! tasha aiki kafarsa sanye da bakin takalmi kansa kuwa hula ce 'baka irin mai tsayi wacce ake d'ora nad'i a kai.


Mi'kewa zaune nayi ina masa barka da zuwa! ya zauna kusa dani yana kallona yace."Kinji shuru ban shigo ba ko."? kaina na daga ina kallonsa, sosai yayi min kyau a ido kayanmu na hausawa nayi masa kyau sai dai bai fiye sakawa ba yafi amfani da 'kananu ......Ya cigaba da cewa"Bayan barin ki gurin Lawisa nida Shatima muka nufi can masarautar kazaure domin gaisuwa da bangajiya dawowar mu kenan yanzu."


Nace"Ayya! sannu gaskiya kunsha hanya dama nima da naji shuru baka shigo ba nace mybe ko kaje asibiti ne ashe tafiya me nisa kukayi.''




'Kure ni da ido yayi yace."Da kikaji shuru ban shigo ba me ya hanaki kiran waya ta." ? shuru nayi dan saboda nasan ban kyauta ba."




Yace."Lawisa tafi ki wayo ke kuwa kin zauna girman kai kin dauki kanki daidai dani kina ganin idan kin kira wayata kin zubar da ajin ki ko.'??


Da sauri nace"Wallahi ba haka bane nima yini nayi ina bacci sai gefin la'asar na tashi sai nasa wayar a chaji dama kuma yanzu nake tunanin kiran ka."




Ta'be bakinsa yayi yace."Kyaji dashi dai.'" a sanyaye nace"Dan Allah kayi hakuri idan hakan ya 'bata maka rai."




Sakin fuskarsa yayi yace."Na yafe miki yanzu dai ina bukatar abinci.'' cikin jin nauyi nace"Sai da nayi maka yanzu." cike da mamaki yake kallona yace."Kada dai kice min baki ci abinci ba har yanzu."




"Naci abincin mana." yace."Karya kikeyi kin zauna da yunwa tun safe." Nace"Wallahi naci abinci na koshi dan kafin na tashi a bacci hadimai sun shirya komai."




Ajiyar zuciya ya sauke yace."Amma kuma kika ce zaki shiga kicin." ina wasa da yatsun hannuna nace"Ai nafi bukatar na girka maka da hannuna domin na samu lada."




Kallona yake yana murmushi yace."To nagode amma kada kiyi abu mai wuya kiyi min indomee.'" cike da mamaki na kalleshi! girarsa ya daga min girgiza kaina nayi nace"Ranka ya dade indomee ba abincin bace ba zata gamsar da kai ba."




Shuru yayi yana kallona yace.'' Okey to ai bana so ki wahala ne shiyasa nace kiyi min indomee amma tunda kina bukatar ki bani abinci mai gamsarwa babu damuwa nima nafi son haka naci na koshi na samu kwarin jikina." Yana min wani irin kallo ya karashe maganar, murmushi nayi na mike a nutse nace"Bari na shiga kicin din! mikewa yayi da fadin"Okey kafin ki gama bari na shiga gurin 'Yar uwarki muyi sallama." shuru nai masa muka fito tare ni na nufi kicin shi kuma ya kama hanya ya fita.




Fatan doya nayi masa na gama aikina tsaf na shirya masa duk abinda zai bukata tire din abincin na kai dakina na ajiye a gefa agogo na duba ina mamakin dad'ewarsa daga zuwa yin sallama ya share gindi ya zauna awarsa daya da fita, zuciyata tace watakila yana gurun mahaifiyarsa ki dinga yi masa uzuri! ajiyar zuciya na sauke tare da dauke kaina daga kallon agogon dake kafe a dakin............Mikewa nayi na shiga toilet domin sake kimtsa jikina pad na sanja na fito sai na ganshi a zaune gaban kayan abincin yana bud'awa, da sauri na karasa kusa dashi, yace."Kinji shuru ban dawo ba ko."?
"Umm." nace, yace." Ina can gurin Mamma! ga wannan ma tace a kawo miki wai ke kadai zaki ci kada ki bani." akushin dake gabansa na kalla! ya mi'ko min, nasa hannu na kar'ba a nutse na bud'a kaza ce guda anyi mata dahuwar magani sai kamshi take! da sauri na rufe ina kallonsa, hankalinsa nakan abincin gabansa, da sauri na kar'ba ina kokarin zuba masa yace."Mamma ta huttashe dani da kazar amarci."


Kallonsa nayi da mamaki a tare dani! yace."Ai na bud'a na gani ta dafo miki kaza tayi lugub! wai harda cewa ko roma kada na d'and'ana." yanda ya fad'i maganar a sakarce ya bani dariya nace"Ban hanaka ci ba idan kana bukata sai na baka."


"Kawai ki bud'e ina bukata." nace"To shikkenan ka gama cin abincin." Shuru yayi yasa spoon din dake hannunsa a nutse ya fara cin abincin...........Kad'an ya rage nace"Ka daure ka karasa ladan ka." girgiza min kai yayi yace."Na koshi haka ko kina so na kasa moruwa."? girgiza kaina nayi na mika masa tissue ya goge bakinsa, nace"To ya na zuba maka roman kazar ne."? ya mutse fuska yayi yace."Kici kayanki bana jin zan iya cin wani abu yanzu." Nace"To shikkenan nima ba yanzu zanci ba sai da safe zansa a d'umamin."


"Okey." yace ya dan kishingida yana kallon guri guda, a zuciyata nace"Abin yazo kenan! mikewa nayi na harhad'a kwanakun abincin na dauka na fita dashi, firji na kicin na bude nasa kwanon kazar na rufe da safe nake so naci a tsanake.........Dakin na koma na sameshi a inda yake har yanzu kuma guri guda yake kallo, sai dana zauna sannan ya dago kai yana kallona....








*Na kudi ne*
Koda zaki ganshi a gruop na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abin yake....Vip gruop#600 normal group #300 account... 0542382124....Binta umar gtbank....idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:28 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
96
Fulani na kashe wayarta ta kira Jakadiya tace maza taje fada ta shedawa Maimartaba cewa tana son magana dashi. Jakadiya da sauri ta tafi domin cika umarnin uwar gijiyarta, Maimartaba tunda yaji wannan kiran na gaggawa yasan ba lafiya ba.


Koda Maimartaba yazo ta sheda masa abinda yake faruwa ransa ya baci yace"Yanzu ashe har yanzu ba daina wannan al'adar ba."? Tace."Wallahi basu daina ba sunayi shiyasa na kira ka na sheda maka abinda ke faruwa saboda bana so su watsa mummunar magana akan wannan yarinyar babana ya tabbatar min da cewa babu wata mu'amular aure data shiga tsakaninsa da ita saboda tana cikin hali na rashin tsarki! yanda yayi min bayani haka yayi wa uwargida bayani amma ta nuna bata yarda ba tana ganin kamar yana kokarin kare matarsa ne shi kuma ya tabbatar min da gaskiyar magana."


Maimartaba yace."Na rasa ranar da Huwaila za tayi hankali yanzu ace da girmanta da komai taje kar'bar zanin gado ai wannan zubar da kima da mutunci ne da kin fada min tun na kan Lawisa dana dauki mataki amma yanzu ma bata 'baci ba da kaina zan shiga sashenta na gargad'eta akan abinda suke shirin aikatawa."




Maimartaba na shiga sashen Uwargida ya samesu su biyu ita da Hajiya Karima sai 'kus-'kus suke, ganinsa yasa duk suka nuna alamun rashin gaskiya, a nutse ya zauna yana kallonsu sai rige rigen gaisheshi suke.


Ya dinga amsawa yana nazarinsu duk alamun rashin gaskiya ya bayyana a tare dasu.




Ya kalli Uwargida rai a 'bace! yace."Yanzu abubuwan da kukeyi a masarauta shine daidai."?


Sunkuyar da kanta tayi a sanyaye tace"Allah ya taimakeka me yake faruwa ne."?


Yace."Ashe tambayata kike abinda ke faruwa bayan kin san komai."


Tace."Ranka ya dad'e a gafarce ni nasan akan abinda kake magana kasan wannan abu al'adar masarauta ce babu laifi dan duniya ta tabbatar da nagartar matan da Magajin sarki ya aura Ita dai Lawisa kowa ya tabbatar cewa cikakkiyar macace ita wannan d'iyar bayin ce bamu tabbatar ba tunda babu yanda banyi dasu ba akan su nuna min abin kwanciyarsu suka qi kaga wannan na nuna mana cewa akwai lauje cikin nadi watakila yarinyar nan ba cikakkiyar mace bace."




Cikin takaici yace."Huwaila wannan abun da kuke jahilci ne tsantsa, a shakarun baya da masarauta ta mayar da abun al'ada akwai jahlici da duhun kai a tare da ita, yanzu kai ya waye muna da ilimin addini daidai gwargwado to me zai sanya mu dinga fallasa sirrin aure! to daga rana irin ta yau na soke wannan al'ada kuma kada naji kada na gani wata a cikin ku ta tayar da wata magana akan matar Ali ba lallai sai jini ya fita a jikin mace za'a san budurwa ce ni wannan yarinya Sumayya bana shakka akanta saboda haka magana ta mutu anan ba na ganku kuna magana kasa-kasa ba to mutukar naji maganar nan ta watsu dukkanin ku sai na dauki mataki akan ku.""


Hakuri suka shiga bashi suna sunkuyar da kansu, mikewa yayi ya barsu gurin ba tare da ya tanka musu ba.




Yana fita Uwargida taja tsaki tana girgiza kafarta tabbas Fulani ce ta turoshi yazo yaci mata mutunci.....Hajiya Karima tace"To wai da yazo yana wannan fad'an waye ya fada masa halin da ake ciki ne."? cikin takaici tace"Waye zai fada masa idan ba Fulani ba itace ta turoshi yazo yayi mana tujara." Hajiya Karima taja tsaki da fadin"Kin san Allah Huwaila na tsani na bude ido na ganta da ina da yanda zanyi a kanta to da tuni nayi shegiyar mata ce da asiri baya cin jikinta.


Uwargida ajiyar zuciya ta sauke tace"Babu abinda banyi ba amma na kasa tasiri a kanta Fulani ta riga tayi nisa tasha gabana tunda itace mai d'a namiji ai sai abinda na gani duk abinda Maimartaba yake da umarninta baya san 'bacin ranta ita da d'anta yanda yake nuna mana rashin kulawa nida 'ya'yana yana damuna mutuka wallahi na rasa yanda zanyi na tarwatsa rayuwar su ita da d'anta.


Hajiya Karima cikin 'bacin rai tace"Huwaila sai dai kiyi hakuri kina gani dai Muddibo garin yunkurin 'kwatar hakkinsa aka kasheshi muna ji muna gani muka hakura muka rasa shi! kema hakuri zakiyi ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login