Showing 18001 words to 21000 words out of 118783 words

Chapter 7 - MAZAUNA GIDA COMPLETE By HAERMEEBRAEH.txt

26 Oct 2025

653

Ramai kwarai ainun.

"Mama ! bari na kai wa Yah Umar shima tare suke yana waje,"

Ramai ke ta zazzare ido jin an kira ta da Mama, taji matuqar daɗi kuwa a ran ta.

Ɗaukan gora ɗaya na zob'o ɗaya na kunun aya tayi ta saka cup ta sa hijab ta tafi kai masa a waje.

Yana zaune cikin motar ya qurawa hanya ido yana jin kamar ya fada gidan ya gan ta ko zai samu sauqin abinda yake ji game da ita a qoqon zuciyar shi ta fito.........



*Wai ni Umarrrr what do u mean? Iyyee? Nace what is ur nufi ne akan Jameelaa?*
[11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻












WRITTEN BY HAERMEEBRAERH








PAGE 9:









Bai san sanda wani qayatattacen murmushi ya kub'uce masa ba a kyakkyawar fuskar shi,sai ya sa hannayen shi biyu ya gyara zaman rigar shi a jikin shi, sannan ya bude qofa ya fita waje tare da kafe ta da idanun shi da yake wani lumshewa, yauce rana ta farko da Jameelah ta ji kunya wai dan namiji yana kallon ta.

Buɗe mata mota yayi ta zauna tare da zuba masa kunun ayar ta miqa masa, shanye wa yayi bayan yayi bismillah ya na ci gaba da kallon ta ya miqa mata cup din ta sake cika masa ya shanye, cike da murmushi da jin kunya ta ce,

"Yah Umar ya qare fa"

"Auu ai ban kula ba ma ni"

Dariya suka yi tare, sannan ya kafe ta da ido ya ce,

"Kin san wani abu kuwa Jameelahhh?"

"Sai ka fada Yah Umar"

"Kina da kyau mai ban mamaki Jameelah, the more mutum yana kallon ki, the more yana ganin kyaun ki na qara fitowa,"

Cike da jin nauyin shi ta ce,

"Yah Umar kenan, ai dik wani mai kyau a zamanin nan namu ya bi bayan ka, in ana neman mutum     kyakkyawa aka same ka an gama nema an hutadda kowa,"

Umar ya ji daɗin kalaman ta,dan kuwa yau ce rana ta farko da wata mace ta taɓa zama ta yi masa irin wannan kalaman duk da cewa ya na samun mata masu nuna suna son shi sosai, babu wadda ta taɓa yi masa irin kalaman Jameelah, kashe murya ya sake yi sannan ya ce,

"Da gaske kike yi ko wasa?"

"Da gaske nake Yah Umar ba na biyun ka wajen kyau,"

"Kice in muka yi aure yaran mu za su fi kowanne yara kyau tinda mu ɗin kyawawa ne,"

Sakin baki tayi ta na kallon shi qirjin ta na d'agawa da sauri da sauri dan tsabar farin cikin jin kalaman shi, wata kwallar farin ciki ce ta taru mata ta sauke ƙwayar idanun ta qasa ta na wasa da robar kunun ayar da ya qare, matsawa ya ɗan yi kusa da kunnen ta cikin murya mai ɗaukan hankali ya ce,

"Ko ba zaki iya auren namiji kyakkyawa wa ba Jameelaaahhh?"

Da sauri ta fita daga motar tana dariya ta tsaya a jikin motar ta na sauke numfashi, ita a dole wai taji kunya, murmushi Umar yayi ya shafo kwantaccen sajen shi wanda ke haɗe da dogon gemu mai cika da tsaho irin na matasan da ke ji da k'walisa,a hankali take tafiya zuwa cikin gida ta na ji a jikin ta Umar na bin ta da kallo dan kuwa idanun mutane bai taɓa sanya ta jin kamar za ta faɗi ba ta riga ta saba da idanun maza na bin surar jikin ta da kallo, ta tabbata Umar ne kawai ke da wannan damar da ya sanya jikin ta sauyawa,ta na shiga ta tarar da Ramai a tsakar gida da alama leqawa za ta yi kiran ta suka haɗu a hanya,cikin yin qasa da murya Ramai ta ce,


"Daga kai ruwa kin je kin yi zaman ki,ai da kiran ki zan je na yi,"

"Ai gani na dawo, bari su tafi na baki labari,"

Mamalo da Umaimah na ta hira ta qarasa dakin, zama tayi suka sake gaisawa da Mum sannan Mum ta miqa mata abubuwan data kawo masu,daga bisani ta ce zasu tafi,Ramai ce ta shiga ta na neman waje a bakin gado ta zauna ta ce,

"Ku ɗan jira kaɗan yanzu zaki ga baban nasu ya dawo, sai ki yi masa maganar da muka yi dake ɗazu da kan ki, dan zaifi ɗaukan abun da mahimmanci,"

"To shikenan bari mu yi alwala muyi sallah kafin yazo,"

Ko rufe baki mum bata gama yi ba Baba yayi sallama ya shiga gidan, a bakin qofa ya tsaya suka gaisa sannan Ramai ta masa bayanin ko su ɗin su waye, cike da fara'a Baba ya ce,

"Allah sarki, barkan ku da zuwa muna fa godiya sosai yanda ake kula mana da Jameelah Allah ya qara zumunci,"

Anan su Jameelah da Mamalo da Umaimah suka koma d'akin su Mamalo dan su ba wa iyayen nasu waje su tattauna akan abinda ya kawo su Mum,sannan Mum ta ci gaba da magana ta ce,

"Babu komai Malam, dama yanzu nake faɗawa Maman Jameelahn ni da mahaifin su Umaimah muna neman izinin ka akan ka bamu Jameelah ta koma wajen mu dan mu haɗa ta da Umaimah su dinga zuwa makarantar boko, dan kuwa na taɓa tambayar ta ko tana zuwa makarantar boko amma sai ta sanar dani cewar baka da ra'ayin ilimin boko,ilimin zamani na da matuqar amfani ga rayuwar 'ya mace Malam, domin kuwa yana taimakawa al'ummar Annabi Muhammad sosai ta fannoni da dama, misali kuwa shine aikin asibiti,mace na iya zama lauya ta tsaya wajen kare wa mata 'yan uwan ta hakkin su akan fyad'e ko wata cutarwa da ake masu a rayuwar zaman aure ko zamantakewar yau da gobe, in mace na da ilimin boko ko yawan gulmace-gulmace da dambace-dambace da kuma rashin abinyi yana raguwa a unguwanni da cikin al'umma baki ɗaya,dan kuwa za ka samu irin matan da suka yi ilimin boko da na addini da aji,sannan yawan gasa da sa miji yayi abinda bai da ikon yi yana raguwa,dan Allah ka min wannan alfarmar ka bamu ita mu taimaka ma rayuwar ta itama ta taimaki al'ummar annabi kamar yanda nake yi, dan ni din ma'aikaciyar jinya ce,"

Tinda ta fara magana Baba ke nazarin maganganun ta,tabbas tana da hujjoji masu qarfi, amma ba zai iya bada Jameela mai son abin duniya ta tafi gidan masu hali ba, shi in so samu ne da da tsayayye ma aurar da ita zai yi ya huta, amma kuma kunyar matar yake ji baya so ya yi mata musu,amma duk da haka Baba ya rufe ido ya ce,

"To baiwar Allah na ji bayanan ki kuma na gode da soyayyar da kuke yiwa jini na, Allah ya kare maku zuri'a daga tab'ewa, amma gaskiya Jameelah dai bana da ra'ayin sanya ta a boko, ni da ina da tsayayyen miji ma aure zan yi mata, dan haka ki yi hakuri a bawa Alhajin shima haƙuri, a hakan ma zumuncin da ake mana ina jin daɗin shi sosai,"

Dik yanda aka kad'a aka raya Baba yaqi aminta ya bada Jameelah daga qarshe haka Mum ta hakura da suka tashi tafiya sai aka kira Umaimah da ga d'akin su Mamalo suka wuce, suna tafiya Jameelah ta shiga d'akin nasu da murna dan jin hukuncin da Baban nata ya yanke akan komawar ta gidan su Umaimah,nan Ramai ta zauna ta rattab'a mata bayani sala-sala, jin yace bazata koma gidan su Umaimah ba sai kawai ta saka uban kuka, kuka ta yi tayi mai sauti tana sambatun Baba baya son ta huta a rayuwa yafi son ta yi ta zama cikin talauci da quncin rayuwa.

Yah Umar ya matsu ya ji me iyayen Jameelah suka yanke akan wannan lamari da Mum ɗin shi ke bashi labari amma Mum ta qi qarasa maganar ta saboda fad'awa duniyar tunani da ta yi,ta yi nisa cikin nazarin kalaman Baban Jameelah suka isa gida, tabbas mutum ne shi talaka amma ya na riqe da k'imar sa da martabar sa baya son mutuncin shi ya tab'u, lallai gidan su Jameela akwai tarbiyya da sanin ya kamata.

Bayan sun je gida sunyi sallah sunci abinci ne Dad na zaune yana shan tea Mum ta faɗa masa yanda suka yi da mahaifin Jameelah, Yah Umar na d'akin shi yana karatu Umaimah ma na nata d'akin itama. Dad ne ya ajiye mug ɗin da yake hannun sa ya ce,

"Lallai na dad'e ban ga talaka mai kamun kai kamar wannan ba, amma kina ganin in har Umar zai amince ya aure ta ba zamu haɗa su aure ba? Ta haka ne zamu sanya ta makarantar boko dan ta sake samun ilimi sosai da zai amfane ta, a yanayin tarbiyyar dana kula tana da shi musulunci zai alfahari da samun yarinya kamar ta dan kuwa zata yi amfani da ilimin ta wajen taimakon mata har ma da mazan ma,"

"Wannan gaskiya ne Daddyn Umaimah,na ji daɗin maganar ka sosai dan kuwa ni kaina nayi wannan tinanin, tinda yana son ta yi aure ai sai ta zama surukar mu, amma kuma kana ganin Umar zai yarda? karatun shi fa?"

"Babu komai zamu iya mu kai komai na aure, ya zamana dai an san yaron mu ne zai aure ta, in yaso sai mu sanya ta makarantar bokon a can gidan su ta fara zuwa,tare da amincewar mahaifin ta amma, daga sanda Umar ya kammala karatun shi sai a daura masu aure ta tare ko ya kika gani?"

"Gaskiya Honey shawarar ka tayi kyau sosai, Allah ya zab'a mana abinda yafi alkhairi,"

"Ameen"

Da wannan shawarar suka tashi zuwa makwancin su.



**********************


Har ranar asabar ta yi Jameelah bata daina kuka da roqon Baba akan ya barta ta koma gidan su Umaimah ba, a ranar da safe Jameela ta tashi idanun ta sun yi mata qanana saboda kuka da ta kwanayi, haka ta shirya zuwa makaranta dan samun sauqin rad'ad'in da take ji a zuciyarta, a hanya ko ci kan ki bata ce wa  Mamalo ba da ke ta yi mata surutu, ko kanzil Jameelah bata ce mata ba,Mamalo da ta kula oganniyar bata da niyyar yin magana sai taja bakin ta ta tsuke bata sake cewa komai ba har suka isa makaranta.

Koda Malam Haroon ya shigo ajin su ya kira Jameelar shiru ta yi kamar bata ji shi ba, wadda ke zaune kusa da ita ce ta maimaita mata mai yace nan ta fara masifa ta na fad'in ai ta ji shi dan ita ɗin ba kurma bace bata ga damar amsawa bane sai yaya? Umaimah ce ta kama hannun ta ta na lallashin ta akan ta yi hakuri ta daina fushin da basu san dalilin yin shi ba,

Nan take Haroon ya ji dik ta fita a ranshi, a da yana yi mata kallon mai hankali ashe ba wani hankali a tare da ita, fita yayi yana tina yanda malamai ke masa bayanin halin ta tare da ganin wautar shi na bata monitan ajin, ko shi yasa yaran suka yi ta nuna basu son ta ranar saboda bata  da kirki?

A cikin satin sai da Haroon ya gane wace ce Jameela, a satin ya kwace muqamin monitan da ya bata ya miqa shi ga Umaimah.

Jameela ko a jikin ta kuwa dan dama ta gaji da playing good girl da take faman yi ba riba,a haka Haroon ya fara sabawa da Umaimah har shaquwa mai qarfi ta shiga tsakanin su.

In an tashi break ya kan yi wa Umaimah karatu na musamman, nan da nan Umaimah ta wuce sauran 'yan ajin su a karatu.


***********************

Cikin wata iriyar murya da ke nuna tsananin matsuwa da buqatuwa take magana,

"Haba Haroon, in baka biya min buqata ta ba wajen wa ka ke so naje? Ko so ka ke na fara kawo maza gidan yayan naka?"

"Amma dai Aunty baki da tsoron Allah kwata-kwata a rayuwar ki, mata da dama mazan su na tafiye-tafiye na tsahon shekaru ma ba iya sati biyu ba ko wata ɗaya, kuma suyi hakuri su riqe amanar auren su, amma ke ba zaki iya yin hakan ba? ke kenan chatting ɗin banza da wasu mazan da auren ki, sannan babban abin takaicin wai qanin mijin ki uwa ɗaya uba ɗaya kike neman ya biya maki buk'atar sha'awar ki wannan wace iriyar musiba ce haka fisabilillahi?"

"Kai ka san wannan Haroon ni ban san haka ba, laifin waye dan na nemi qanin mijin nawa? Kana da masaniyar cewa yayan ka ba irin yanda ban dashi ba akan ya dinga tafiya dani wajen kasuwancin shi amma yaqi, ba zan taba iya hakuri har na tsahon sati biyu ba babu shi a kusa da ni, ya na da kud'in da zai yi duk wata zirga-zirga da ni amma ya ki yin hakan,ai ni din ba dutse bace ina da bukatar miji na a kusa kuma na sanar da shi ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba amma ya k'i ji"

"Aunty fita ! Fita min a d'aki bacci zanyi bana son abinda ki ke yi min,"

"Sai dai ka rife ina ciki, ba inda zani"

Takawa tayi kusa da shi tare da cire doguwar rigar da ta dora akan wasu tallatattun kayan bacci da ta saka, wani irin qamshi ne mai sanyi ya ziyarci hancin Haroon, kafe ta yayi da ido idanun shi sun sauya kala zuwa jawur saboda ɓacin rai dan kuwa kwata-kwata bata bashi sha'awa ba duba da yanda ya tsani zina da dikkan dangogin ta kuma cewar ya na yawan yi wa kan shi addu'ar Allah ya tsare shi daga zina da dikkan abinda ya shafi zina har qarshen rayuwar sa, shi yasa Allah yake kare shi da jin sha'awar Aunty Hauwa'un a duk sanda ta zo masa da buqatar ta,kafin yayi wani yunquri ta fada jikin shi qirjin ta ya na gogar nashi,a kid'ime Haroon ya furta kalmar,

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, Allahumma ajirni fi musib....."

Da sauri ta rufe bakin ta da nashi, ta fara sumbatar shi,wata iriyar bangaza ya yi mata ta bugu da jikin ginin d'akin nashi, nan da nan goshin ta kuwa ya kumbura ya tashi ɗaukan rigar ta yayi ya wurga mata, tare da d'aga murya cikin tsananin bacin rai ya ce mata,

"Allah ya saka mini abinda ki ka yi min ba zan taɓa yafe maki ba azzaluma mai cin amanar auren ta, Allah ya shirye ki ya yaye maki wannan jaraba da musiba da take tare da ke, wannan wanne irin zamani ne lalatacce haka ni namiji ban neme ki ba ke mace ki ke nema na? Ki bar min daki ko na illa taki yanzun nan mara hankali da tunani kawai,"

"Ni ka wulaqanta haka ko Haroon? Ni ka tozarta Haroon? Tabbas sai na wulaqanta ka kamar yanda ka wulaqanta ni, zaman gidannan sai ya gagare ka Haroon, mu zuba mu gani ni da kai wa ye mai nasara,"


"Nasara tana a wajen Allah kuma a wajen shi nake neman tsari da ke da dikkan sharrin da ke tattare da ke, komai zaki min zan barshi akan qaddara ta ce a hakan kuma ba zan yi fushi ba, zan godewa Allah a dik yanda yaso ya ganni, kuma ta Allah ba taki ba,"

"Mu zuba mu gani, mara rabo kawai,"

"Gaki nan babbar mara rabo, kina da aure ki ke neman qanin mijin ki,"

Ɗaukan rigar ta tayi ta saka tare da ficewa a d'akin nashi ta daki qofar a yayin futar ta.

Rintse ido yayi yana sauke numfashi mai zafin gaske, ya zai yi da wannan jarababbiyar mata, gata bata fushi da duk abinda zai yi mata gobe ma sake dawowa zata yi, dik yanda ya so ya mata rashin mutunci sai dai in yayan shi bai yi tafiya ba amma sai ta sake fito masa da wani sabon salon, har abin key ɗin d'akin shi sai da ta sa aka cire gaba ɗaya saboda rufewa da yake yi ta ciki.

Hango sanda ta ke masa kiss yayi a idanun sa cikin sauri ya sa hannun sa na dama yana ta goge bakin shi tare da zubar da hawaye gami da yi mata Allah ya isa.

"Ya Allah ka kare ni daga sharrin wannan baiwa taka, kar tayi galaba akaina, Allah ka kare ni daga aikata zina har qarshen rayuwa ta"

Kad'e wajen kwanciyar shi yayi sau uku tare da bismillah ya yi addu'ar bacci ya rufe ido ko bacci zai ɗauke shi ya manta da abinda ya faru,amma sai bacci ya qi zuwa masa sam a wannan daren, shin me zai yi ya taimaki rayuwar shi ne?

'Ina ganin maida hankali zan yi akan kasuwanci na, na daina dawowa gidannan ko a shago sai ina kwana musamman sanda Yah Ishaq yayi tafiya, in ba haka ba zuciya bata da qashi ban san sanda matar nan zata iya ribata ta ba, ya Allah ka agaza ma rayuwar maraya'

Da wannan tinanin bacci ya ɗauke shi cike da mafarkai kala-kala wanda suka sanya shi tashi cikin mamaki.

"Me zai sa nayi mafarkin ta kuma? Bayan ba wata alaqa ta soyayya a tsakanin mu?.......
[11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻   MAZAUNA GIDA  💅🏻












WRITTEN BY HAERMEEBRAERH















PAGE 10:








Tunda ya farka yake ta qoqarin kawar da tinanin mafarkin da yayi akan ta amma ya kasa mantawa, har ya gama shiryawa dan zuwa makaranta bai bar tunanin ta ba, daga qarshe sai ya sakar wa zuciyar shi ragamar ci gaba da tunanin ta dan yin hakan shine kawai mafita a gare shi a wannan lokacin.

Yau Aunty Hauwaa har qarfe takwas na safiya ta yi ta na d'aki bata fito ba,saboda kai ya kumbura mata ya yi him ta gaban goshin ta, ga wani azabbben ciwon kai da take ji ta rasa inda za ta saka kan ta ta ji daɗi a ran ta,cikin ran ta take ayyana,

'Ni yaron nan ya tozarta haka,ai kuwa daga daren jiya yayi na qarshe, ko ya biya min buqata ta ko kuma na rusa masu kyakkyawar alaqar dake tsakanin shi da dan uwan shi dani yake zancen in ya san wata bai san wata ba'

Bangaren Haroon kuwa yana zuwa makaranta da ita ya fara tozali, murmushi tayi masa sannan ta sauke kan ta qasa tana kallon qur'anin ta, kafe ta yayi da ido yana tuno mafarkin da yayi da ita, da sauri ya fara korar shaid'an sannan ya buɗe murya ya fara karatun qur'ani, nan da nan kowa ya nutsu suka bashi hankalin su, Jameela ce take tab'o Umaimah wadda hankalin ta gaba ɗaya na kan karatun da ake yi masu.

"Ke Umaimah, dallah tambayar ki zan yi,"

"Dan Allah ki bari

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login