Showing 117001 words to 118783 words out of 118783 words
ne sukai ta yaba Kyau da kwarjini tare da kud'in Umar, dan kuwa ko a jikin shi ya nuna shi din ya shaqi nera.
Nan da nan suka sake girmama Jameelaah a zuqatan su, ace tai zaman aure da irin wannan zankad'ed'en miji ta dawo ta auri tsoho sa'an baban ta?
Sai da suka rungume junan su sannan Humairah ta sake shigewa jikin Jameelaah,Jameelah ce ta bude motar ta sanya ta ciki, tare da sumbatar kuncin ta, sai d'aga masu hannu suke yi bayan sun wuce Jameelaah ta share qaramar k'wallar dake idanun ta, suka koma ciki da mijin ta abin son ta wato Malam Tsalha.
Tin daga wannan lokacin Umar yake kai Humairah wajen su Ramai, tayi masu weekend, wani satin kuma wajen su Mum, wani sati kuma gidan Jameelaah, ba qaramin jin daɗin ziyarar da take yi ba take, wataran kuma Sapnah zata kai ta gidan iyayen ta da gidan su Umaimah da Aunty Hauwaa, ganin su take yi suma a matsayin kakannin ta, Humairah da Ummee 'yar gidan Umaimah sun zama best friends kuma best sisters, komai tare suke yi saboda makarantar su ma ɗaya ce,Muhammad ma makarantar su ɗaya ya yi girman jiki shima kamar Humairah, dan tsaurin ido cewa yake shi yayan su ne, saboda dik inda mace take namiji ne gaba da ita, shi ke kula da ita.
Bayan shekara biyar Bukar da yayi aure ne suka je gidan Ramai dan kai gaisuwa, matar Bukar fiddausi anan maqotan su ya gan ta ya ji yana son ta har aka yi musu aure tare, ta yo girki mai daɗi guda biyu, ɗaya na gidan su Bukar ɗin ne ɗaya na gidan iyayen ta,dik zubi ɗaya ta yi musu ba bu bambamci, hatta da mazubin dik a abu iri ɗaya ta saka, saboda ba ta son kowa ya zargi ta fifita wani sama da wani.
Ramai na alfahari da samun suruka kamar fiddausi, dan bata ɗauke ta a uwar miji ba a uwa ta ɗauke ta, dan haka itama a d'iya ta ɗauke ta, in taje ta tadda wanki, ko wani aikin Ramai bata yi ba to zata zage suna hira tana yi mata aikin, dik wani abu in bata iya ba bata jin nauyin tambayar Ramai, saboda yanzu ita ce uwa a wajen ta, gane hakan da Ramai tayi ba qaramin jin daɗi take yi ba, ko ba komai itama ta sake samun wata d'iyar.
Matar Bukar na ɗauke da ciki wata biyu, Bukar da ya kaita zai gudu, wai kunya yake ji ace matar shi na da ciki, Ramai tace ohhh ji soko ita mace bataji kunya ba sai shi namiji, haihuwa inda rai da rabo ai an fara yi kenan, in Fiddausi ta koma gida kuwa tai ta tsokanar shi, in ya neme ta tace itama kunya take ji, sai yayi ta bata hakuri sannan take yarda.
A tsakanin waɗannan shekarun Jameelaah da Sapnah Allah ya azurta su da samun haihuwa, dika maza, Tsalha ya saka sunan Malam Jameel, inda suke kiran shi da Abbah, Umar kuwa ya sanya sunan Baban su Sapnah, dan kuwa zaɓi ya bata ita kuma ta sanya sunan mahaifin ta, Abdulqadeer, suna ce nasa Abdul.
Tin daga nan haihuwa ta buɗe masu, in sun ziyarci juna suna hira suyi ta faɗin, ikon Allah sai da d'iyar su ta girma ta isa kaiwa d'akin miji sannan haihuwa ta buɗe masu.
Jameelaah tace indai aka aurar da Humairah zata rufe haihuwa, akwai kunya aje sunan nata haihuwar sannan a tafi na d'iyar ta, Sapnah sai tace ai ba komai haka Allah ya qaddara, kar ta bi na mutane, in haihuwa ne bata yi ba zasu ce bata haihu ba, yanzu da ta haihu, kuma zasu sa mata ido, ba a iyawa ɗan Adam, dan haka ta rungumi dik abinda Allah ya bata kawai.
**********************
Dr. Aeeshaah Humairah Umar likitan yara ce yanzu a asibitin Ameenu Kano, dake cikin garin Kano burin ta ya gama cika a yanzu ita da Ummee, twins ma wasu mutanen ke kiran su, dik da cewar Ummee tafi Humairah tsaho, ita kuma Humairah tafi Ummee cika, shape din ta irin na Jameelaah ne sak, ta dai qi amincewa ne dan ana ce mata 'yar lukuta, dik da ba wata qiba sai cikar qirji da mazaunai.
Ummee ta samu miji daga dangin su Umaimah, wan da ake kira da Abbas, (Ba Abbas din Fauziyya ba fa na littafin MUGUN MIJI NA MASOYIYAR MARUBUCIYAR KU HAERMEEBRAEH) ma aikacin gidan talabijin na NTA ne dake a Lagos, Humairah kuwa ta samu nata ne a nan asibitin su, shi kuma likitan Mata ne kamar mahaifin ta mai suna Imraan, Dr. Imraan iyayen shi ba wasu masu hali bane, kusan shi ke kula ma da su, amma Alhamdu lilLAAH akwai rufin asiri, ya mallaki gidan kan shi da abin hawa.
An saka ranar auren su a tare, dan haka Iyayen amare an fara gyaran amare sosai ba kama hannun yaro, lokuta da dama sunfi haɗuwa a gidan su Jameeelaah dan kuwa Jameelaah har yau bata sake da su Mum ba tana jin nauyin abinda ta yi mata a baya, dik kuwa da qoqarin da Mum take akan ta saki jikin ta, amma inaa ta kasa hakan, dan haka wataran gidan su Jameelaahn Ummee da Humairah suke zuwa, ta yi masu gyaran jiki, ko ta koya masu wasu abubuwan da ya dace ace sun iya.
An daura auren Ummee da Humairah, akan sadaki daidai aljihun mazajen su, aure ne daya halarci zuri'a kala-kala, ta kowanne ɓangare dangi sun halarta, dangin Ramai dana Malam Jameel, dangin mum dana Dad, ga bangaren su Sapnah, ga wajen angwaye,suma dangin uwa da uba duk sun halarta.
Biki dai sai wanda ya gani, rabon da na ga amare sun sha kwalliya mai kyau irin wannan har na manta, doguwar riga ce fara tass mai kyallin stones masu haske, an kama daga qirjin su aka sake ta daga qasa, dogon hannu gare ta sai mayafin ta mai cikar ado, aka yafa masu saman daurin da aka kafa masu da gwaggwaro irin na wannan zamani, da ake yayi, fuskar su ta sha kwalliya, sun sha kwalliya mai qayatarwa ga abinci nan cima kala-kala ko a KFC albarka😂.
Ana nan ana ta shan dinner kowa ka gani cikin farin ciki yake, yau ga Ramai ga kaji da snaks, amma ba handama ba had'ama, taci iya cin ta ta kauda kai tai hamdala, tare da sanya albarka a auren jikokon nata.
An kai amare gidajen su lafiya, inda Humairah take zaune anan garin Kano a unguwar Gedi-Gedi, Ita kuma Ummee sun lula ta jirgi sun tafi Lago shine your eyes, suna zaune a unguwar Yaba.
Bayan watanni shida Matar Bukar ta haihu, Jameelaah ana ta hidimar suna, Sapnah da su Umaimah da Aunty Hauwaa ana ta aikin d'ura sobo a gorina, Mum da Ramai suna ciki suna ta hira suna ganin yanda 'yan uwa da abokan arziqi ke ta taimaka masu wajen yin abinci da kuma ganin komai ya tafi dai-dai, Humairah ce kwance tana danna waya suna hira da mijin ta, sai shagwab'a take yi masa akan sai ya kawo mata agwaluma, tana jiran shi ya bata hakuri ta bari har ta koma gida taqi, gashi tin safe bata karya ba har 1pm tayi, ganin bai da zaɓin daya wuce na ya je ya nemi dik inda agwaluma take ya kai mata ne yasan shi ya miqe daga office ya ɗauki makullin mota ya fita gefe daya kuma yana nan yana ci gaba da magana da ita ta waya.
"To gani nan na tafi, wannan babyn in ta/ya zo duniya sai na mammake shi/ta, wahala iya wuya na sha ta, zanci soyayyan quli quli sabuwar suya, zan ci awara mai yaji, zan sha kankana, ga abinci masu gina jiki sosai ba za a daure a ci ba sai k'walama,"
"Ni kake yi ma faɗa ko? Bari ka ga na sa kuka a waya in an tambayen na ce cewa kai zaka zo ka d'auken ba za ai suna da ni ba, sai dai su zo sunan naka babyn,"
Qamewa a inda yake ya hau bata hakuri, dan Humairah na da iya shege in tace zatai abu, to kuwa zata yi ɗin, sai da taji ya yi nadamar faɗan daya mata sannan ta fara dariya tace,
"In banda abinka banda hankali ne da zan hau maganar ciki da su,"
"Yo na sani,"
"Kace mi??"
"Ah ah cewa nayi bari na kashe naje na siyo maki, bye love u,"
K'wafa tayi tana murmushi, ta san sarai yayi magana da ita, tashi tayi dan zuwa ta taya su aiki, Sapnah ta kira ta ɗauke da kwanon tuwon shinkafa miyar taushe, ya ji naman rago, sai zobon da suka gama qullawa ta bata.
Tana ganin kwano ta fara tura baki,ahaka tana qi tana qi Sapnah ta sa ta ci mai yawa, kowa a wajen ta burge su sosai,dan kuwa wanda basu san alaqar su ba ganin ta suke mara kunya tana sangarta d'iyar ta a gaban kowa.
(Mutum kenan kayan Allah, ka nuna ma ɗan ka gata ace ka sangarta shi, yayi laifi ka hukuntashi ace ka tsane shi, ka barshi ya lalace ace baku da tarbiyya😂 ya ilahi which one man go do na? Bama ɗan ka tarbiyya iyakar iyawar ka, ka toshe kunnen ka daga surutun mai surutu, as long as kasan akan dai-dai kake, to kowa yaci kan shi )
Rayuwar su haka take ci gaba da tafiya cikin nishad'i da walwala cike kuma da arziqi da wadata,sai dai abinda ba a rasa ba na yau da gobe dan kuwa rayuwar dama yau fari ne gobe tsimma, yau zuma ce gobe kuma mad'aci, yau arziqi gobe talauci,haka rayuwar kowa take tafiya.
*Alhamdulillahi dika-dika anan na kawo qarshen novel dinnan mai suna MAZAUNA GIDA, ina fatan Alkhairin dake ciki Allah ya sa mutane su amfana da shi, akasin haka kuma Allah ya shafe shi cikin rubutu na da zuqatan bayin shi. Allah ya sa ka ma dik wanda suka karanta da alkhairi sukai comments masu daɗin karantawa, Allah ka saka ma mutan group dina na HAERMEEBRAERH NOVEL GROUP da alkhairi ka haɗa da GROUP ƊIN GIDAN ƊAN LITI ya Allah ka haɗa da dikkan hausa novel groups ɗin dake karanta wannan labari. Allah ka sanya mu a aljannah ta sanadiyyar karanta abun alkhairi ko wanne iri ne.*
*Ya Allah ka sa rubutun nan nawa da nake yi su zame min alkhairi a ranar gobe qiyama,Allah ya sa na kafa hujja da su a gaban ka ya Allah kar su zame min hujja akai na.*
*Wadda dik na batawa sanadin wannan novel a yafeni, masu ciki Allah ya sauke ku lafiya,masu yara Allah ya raya ya yi musu albarka, masu neman haihuwa Allah ya bada masu albarka.*
*Fidda Allah ya qara maki hakurin rashin da kika yi ya kawo masu albarka, Yaya Barira Allah ya jiqan ki ya yi maki rahama, Allah yaraya abinda kik bari da imani*
*HAERMEEBRAEH ❤️CE*