Showing 63001 words to 66000 words out of 118783 words

Chapter 22 - MAZAUNA GIDA COMPLETE By HAERMEEBRAEH.txt

26 Oct 2025

637

an kawo min ga Ramai da ta yi min wani, kar ki damu, in baki karya ba ma ki zo, sai mu karya tare,"

Mamalo ji tai kamar an buga mata guduma, dan sarai ta san da yanayin zagi aka mata wannan kalamai,amma bata damu ba tayi murnar haihuwar qawar ta ta, waya tai ma Sadeeq ta nemi izinin shi,nan take ya amince mata kuwa ta je, nan da nan ta gama shiri ta fita, a hanya ta bi ta kai masa keys din gidan nasu, ya amsa ya yi mata Allah ya kiyaye, da gargad'in ta kula da kan ta, in ya samu sararin ɗinkunan zai biyo yaga jaririyar sai su koma gida tare.

Adaidaita sahun a qofar gidan su Jameelaa ya tsaya, motoci wajen guda hudu ta gani pake a qofar gidan, a tinanin ta ko dangin mijin Jamelan ne, sai da ta shiga, taga gidan gaba ɗaya ya sauya dan kuwa an sauya labulaye, da wasu daga kayayyakin parlourn, Jameelaa har kujeru taso a sauya, amma hakan bai samu ba, sai ta hakura.

Da sallama Mamalo ta shiga lokacin sha ɗaya na safiya ta gota ma,Jameelaa ce zaune ta ci uban ado sai walqiya take yi, ta sha zinaren da Umar ya sai mata as a gift na haihuwar ta,Mamalo idon ta kamar ya faɗi qasq dan tsabar kyaun da taga Jameelaa tayi mata, wasu had'ad'd'un 'yan mata ne zaune da manyan wayoyi a hannun su sai hira suke yi, kowaccen su in ka dubi kayan jikin ta kasan ta sha nera.

Gaida su tayi, suka daga mata hannu sai masu cewa

"Sannun ki"

Zama tayi a kujera Jameelaa ta dawo ɗauke da jaririya a hannu ta miqawa wata da ake kira da Kabeerah, sai santin kyaun yarinyar suke yi suna ɗaukan ta a hotuna, Mamalo gyaran murya tayi tace,

"Mejego manya, an samu kai qalaou? ALLAH ya raya mana, ya sanya albarka,"

"Ameen, ya kike? Ya me gidan?"

Ko amsar Mamalo bata jira ba ta ci gaba da hira da qawayen ta masu kudi, qarshe dai Mamalo ta sa ta kwashe kayan da aka ci aka sha a wajen ita da sabbin qawayen ta.

Haka ma Ramai aiki tayi ta sanya Mamalo, Mamalo ta gaji sosai saboda a lokacin nan cikin ta ya fara yin nauyi, suna nan zaune har bayan azahar Sadeeq bai zo ba, zama tayi shabar alamar ta gaji,can sai ta miqe ta d'akko jakar ta tare da wayar ta, kiran Sadeeq ta gani da yawa suna zaune a wajen ba wanda ya damu yace ana mata waya, tana ta hidimta masu,

Message din shi ta gani yana mata magana akan ya san tana nan ana manne da jaririya sun yi d'iya ta manta da shi, anjima yana nan tafe su wuce.

Wata kwallar baqin cikin bai san me ya faru ba ne ta kwaranyar mata a idanun ta, da sauri ta share, ta dauki jakar ta ta danna masa kira, bayan ya dauka yayi sallama ta amsa tace masa,

"Ba sai kazo ba, ka je ka bude mana gida gani nan dawowa yanzun nan"

Ba wanda tayi wa sallama ta sa kai ta fice, ranta yayi matuqar baci da irin walaqancin da Jameelaa ta yi mata, qawayen ta wannan tazo wannan ta tafi ta ma sa ran ko Umaimah zata samu zuwa amma shiru, tana hanya tana zancen zuci, ta samu abin hawa sai gida.

Da kuka ta faɗa jikin Sadeeq, shi kuwa a gigice ya kama ta yana son jin me ya same ta sai da tai kukan baqin cikin daya tokare mata zuciya sannan ta labarta masa dik abinda ya faru, sannan ta qara masa da cewa,


"A yanda muka taso da Jameelaa, ni nayi sadaukarwa kala-kala akan ta amma ita a kullum bata da burin da ya wuce ta ga tana muzanta, ni mai iya yin dik wani aiki ne dan ta haihu ba tare da gajiyawa ba, amma duba ka ga yanda take ta wulaqanta ni gaban qawayen ta sabbi masu kudi, ni na tashi a banza kenan, naso umaimah ma taje dana danji sanyi-sanyi araina, amma bata je ba ni Fateemaa nayi alqawarin ko da bashi da saida kayan dana mallaka ne sai na bawa Jameelaa mamakin abin da ta aikata min, sai na nuna mata ba ita kadai bace zata fantama da kuɗi ba a duniya..........[08/09, 10:18 pm] Aunty Hameeda: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻















WRITTEN BY HAERMEEBRAERH











PAGE 28:










Haroon ne zaune cikin motar da Ishaaq ya sai masa sabuwa dal yana jiran su Umaimah dan kai su gidan Jameelaah haka nan shi dai bai son Jameelaah har yanzu, dan ganin ta ya ke yi irin mutanen nan masu halayya biyu, amma da alama su ba su gane ta ba, ita ɗin ma ba son shi take yi ba dan ta ga alama ya gama gane ta tsaf, shi yasa bai son Umaimah na rab'ar ta sosai.

Sai da suka gama b'ata lokaci sannan suka fito yana ganin shigar Sapna ya b'ata rai, sai da ya bari ta zo daf zata shiga ya d'aga kai yace,


"Ince dai ba ni zaki bi a haka ba ko?"

"To da wa zan bi? A mota fa muke,"

"Habaa hajiya, gaskiya ko ki sauya mayafi ko ki sauya kayan jikin ki dika, dibi wata muguwar tsagu da akai ma skirt din ki, dibi saman rigar ki ke a ganin ki wannan shiga ta dace da mace mumina?"

"Ya ustaz Attaqwa hahuna anyi nuni da saitin zuciya so a zuci abun yake ba wai a shiga ba, ba kayan da zan sauya nidai sai dai kace kawai ba zaka d'auken a motar ka ba na hakura,ko na hau adaidaita sahu,"

"Kin manta da ayar da tace a faɗa ma matan annabi da muminai su sanya jalbab? Ba dole sai hijabi ba koda mayafi ne ki saka amma wanda zai rufe ko ina na jiki to Shima jalbab ne, kuma sutura da zata rufe jiki dikkanin shi itama jalbab ce,ke yanzu amma gaba daya kinyi shiga ta tabarruji sannan ga uban turare kin fesa wanda tin kan ki iso na ke jin qamshin jikin ki sannan kice attaqwa hahuna? Kina tinanin in har akwai taqawa cikakka a zuciyar bawa a jikin shi ba za a same ta ba? Tinda a iya sani na zuciya ke juya jiki, ban hana ki dan tozarci ba, na hana ki ne kawai saboda ke kina daga cikin ahalina yanzu, mun zama ɗaya Aunty Hauwaa Yayata na ɗauke ta ta jini ba iya matar wana ba,dole inna ga wani nata ya yi ba dai-dai ba na nusar dashi, last warning ki koma ki sauya kayan jikin ki ko minti nawa zaki ɗauka ina jiran ki,"

Maganganun shi sun shige ta sosai, amma kunya take ji ta koma ya gan ta musamman tsagar bayan ta, sai yanzu ta ji kunyar fita a haka,

"Dan Allah ki je ki sauya muna jiran ki, na san ba zai tafi ba sai dake, mutuncin ki yake kare maki jikin mace na da daraja da qimar da ba kowanne jaki da doki ya kamata ya gani ba sai muharramin ta, jikin mace yana da matuqar qima da daukakar da yafi dukiya da dik wani abu mai mahimmanci, tinda ko gobara akai aka ce komai ya qone zakiji an fara tambayar anyi asarar rai? Ki je ki sauya, baya son jikin ki ya zama makamashin wuta ne, kije...."

"Ya isa haka Umaimah say no more please, na fahimce shi tin farko ban san ya zan na wuce ta gaban shi da tsagar skirt dina bane kunya nake ji,"

"Muje na raka ki, muje wajena na baki hijabi,"

Jan ta Umaimah ta yi, sukai ciki ta aje mayafin ta, ta bata hijab madaidaici kalar kayan ta, ita kan ta sai tafi jin daɗin da sakewa a cikin hijabin unlike da ta sa mayafi sai tai ta ja dan rufe wani wajen da bata son ya fita.

Koda suka dawo Haroon fuskar shi ɗauke da murmushi suka shige suka ja sai gidan mai jego Jameelaah.


Ramai na ta haɗa kaya tana sharar kwalla dan kuwa an kawo mai aiki mai suna kulu, da kulun gatsal Jameelaa ke kiran ta, dik da cewa matar ta girmi Ramai, Umar kuma yana ce mata Iya, d'akin da Ramai ta zauna nan aka kai mata dan qullin kayan ta, Kulu ta iya aiki sosai, ga iya girki musamman na gargajiya, Umar yaji daɗin samun ta a matsayin wadda zata na taimaka masu.

Jameelaa ta buɗe abubuwan data samu tana gani sai murna take da jin daɗi, dan kuwa ta tara sutura ba kadan ba, daga ita har jaririn ta, ga kudi da ta samu ta biya bashi har da ragowar 30k a sama ta samu, dubu biyar ta bawa Ramai a ciki, Ramai kuwa ranta ya baci k'warai ina laifin ta bata dubu goma? dik aikin data tiqa a suna da kafin sunan ya tashi a banza kenan?  Umar ya bata kudi wanda Jameelaa bata san nawa bane sai son sanin nawa ne aka bata take yi amma Ramai ta damqe abun ta ta kuma kwashi kayan gara, sai da ta haɗa buhu da kayan sawa dana abinci da tarkacen abubuwa dai harda flask.

Umar yaso maida ta ta kafe zata tafi ya wuce office kawai, dan haka ya fita bayan ya bata saqon gaida Baba da yi masa godiyar basu ita da ya yi.

Motar su Haroon ce ta tsaya, suka fita dikan su shi kuma Haroon sai ya wuce kasuwa, tare da alqawarin komawa qarfe uku dan maida su gida, tinda azumi ake su yi masu abin shan ruwa.

Da sallama suka shiga Kulu ce taje ta buɗe qofar, bayan gaishe-gaishe  ta wuce d'akin ta, Jameelaa na zaune bayan fitar Ramai, tana kallo tana bawa baby nono taga su Umaimah sai ta hau murna tana fad'in,

"Ahhh lale maraba da Umaimah, sannun ku Aunty hauwaa, barka da zuwa, qawata ammmm???"

"Sapnah,"

Sapnah ta tuna mata da kan ta, sai Jameelah ta qara qashe baki ta ce,

"Yauwa mai sunan mutanen can, sannun ku da zuwa bismillah ku zauna"

'Allah ya sa kun zo da kayan barka, ko dake na fi son kuɗi akan kaya na gaji da amsar kaya haka kud'in ne dai ko dubj ɗari zaku bani ba za su yi min yawa ba'

Wata leda ta gani a hannun Aunty hauwaa baki ta qara washe masu sosai tana masu maraba,

"Gashi azumi ake yi da an kawo abin motsa baki,"

"Wannan sai ku masu jego miqo ta nan wajen Goggon ta"

Miqawa Umaimahn babyn tayi suka dinga ɗaukan ta, wannan ya ɗauka wannan ya aje,hira sukai tayi ta na ba Umaimah labarin yanda sunan ya gudana bayan tafiyar ta.

"Kaiii amma nayi missing na kuwa so mu haɗu da Fateemaa, mun jima bamu haɗu ba sosai da sosai, anya tin kafin auren ta ma mun haɗu kuwa?"

"Gaskiya bana jin kun hadu, ai ta kusan haihuwa itama a wannan watan inshaa Allahu, kin ga sai kije suna,"

"Haka ne Allah ya kai mu,"

"Ameen"

Hira suke tayi kamar ba za a daina ba lokacin sallah yayi, Aunty Hauwaa ce ta miqawa Jameelaa ledar hannun ta, aiko kamar jira take yi haka ta cafke tana ta zabga godiya, dik sun zaci a sakin fuskar ta ne da mutunci da take dashi ya ta yi hakan, Aunty hauwaa ce ta tambayi bandaki Jameelah ta nuna mata hanyar waje, dan ba toilete a kowanne daki sai nasu, wajen ta fita Sapnah tace,

"Ohhh aunty Hauwa dama ki bari na shiga a matse na ke da fitsari,"

"Da kina zaune da fitsarin kuma baki yi magana ba? To da ban ce zani ba a zaune zakiyi shi? nima a matsen na ke sai ki jira ni,"

Matse qafa Sapnah ta yi tace taje ta na jiran ta ta dawo, ganin haka yasa Jameelaa tace ma Sapnah ta shiga na dakin su.

Da sauri ta cire hijabin ta ta shige band'akin dake cikin d'akin su ita da Umar dan nan ne kaɗai ke da band'aki dika gidan, sai ko na waje, daga shigar ta d'akin ta ci karo da komai a baje, gadon ba gyara, komai 1-1, ganin haka sai kawai taji ba zata iya shiga bayin ba, dan bata san me zata tarar ba fita tayi, ta wayance tace,


"Bari na jira Aunty Hauwa na shiga naga alamar kamar d'akin me gidan ne, d'akin miji ai ba a barin kowa ya shiga zan iya matse shi har ta gama"

"Ohhh su Sapnah manya,"

Haka dai sukai ta mata tsiya tana yaqe dik sai ta raina Jameelaan, dan dai ko mace bata zama mai tsananin tsafta ba ana so a same ta dai ba qazama ba, amma da alama parlourn ma dan mai aiki ta gyara ne da ba zai ganu ba, ai gwanda ta shiga na tsakar gidan ta san mai aikin ta gyara shi.

Suna nan Aunty Hauwaa ta dawo, ita ma ta shiga sai da tai fitsarin ta sannan ta yi alwala ta koma suka yi sallah, Umaimah ma tayi sallah suka ci gaba da hira, sun dad'e ba su haɗu sun yi hira haka ba.

"Yanzu ya zaki da maganar makaranta?"

"Wai yace haka zan koma kulu tana riqen ita, ni dai gaskiya ba zan iya karatu da yarinya ba a bari na yaye ta kawai sai na koma,"

"Ai yara ba su hana karatu, ki yi hakuri ki ci gaba,"

"Shikenan zan duba na gani"

Suna zaune Umar ya dawo, Sapna na shafa powder, Umaimah na tsokanar ta akan a mota suka zo a mota zasu koma ba mai gani a hanya balle ta damu da powder.

"Ke kika sani sai dai na shafa ɗin, kika ishen mijin ki zan aura,'

"Aiko da na yi farin ciki da hakan,"

"Sannu da dawowa Yah umar"

"Yauwa yau kune a gidan namu, ance kin zo suna kin tafi da wuri"

"Eh Yah kasan shi baya son yawan fita,"

"Yayi dai-dai ai nima bana son yawan fitan nan"

"Sarkin surutu yau me ya sami bakin ki?"

"Ina yini?"

"Hummm lafiya,"

"Dama ka san ta ne?"

"Mun haɗu randa aka kai ki surutu gare ta kamar redio,"

Dariya suka yi tayi har Sapnan Jameelaa kuwa ranta ya baci ganin yanda Umar din ya sake da Sapnah ana wani hira jefi-jefi ta dinga sanya baki gaba ɗaya sai ta ji jikin ta ya mutu.

Qarfe uku dai-dai Haroon ya iso dan ɗaukar su Umar ne ya shigar da shi gidan da kan shi nan ya ga baby again bayan sun gaisa da Jameelaah kafin su tafi saida ya aje kuɗi yace na baby ne, Jameelaa sai washe baki take yi Haroon kuwa sai b'ata rai yake saboda ya gama gano ta yar son abin duniya ce.

Bayan sun tafi Umar ya dami Jameelaa da maganar su Umaimah da Sapah, da yanda suka fara haɗuwa,cikin hasala da b'acin rai ta ce,

"Kai ni dan Allah ya ishe ni haka bana son surutun tsiya, sai wani zancen Sapnah kake ma mutane, ko dai son ta kake yi ne?"

"So kuma Jameelah Wanne irin so ? dan Allah ki daina wanan maganar tinda baki son maganar su na daina, kawai ina qara yi maki bayani ne akan yanda muka haɗu da ita, dan na kula kin b'ata rai da kika ji na san ta tin da,"

"To dai magana ta qare haka dan Allah ni, bana son na sake jin zancen wata wai ita Sapa take kowa oho,"

Umar ne yayi dariya sosai sannan ya kwantar da kan shi a bayan ta, tare sa saqalo qugun ta a hannayen shi ya ce,

"Ohhhh mata ta na kishi na ashe har haka? To kar ki damu Umar naki ne ke kaɗai,ba zan taɓa haɗa ki kishi da wata ba,"

Qara kwantar da jikin ta tayi a jikin shi,tana dariya itama,

"To to ya isa haka dagani gwanda ke, nikam inni sa'imun"

Bin shi tayi zata yi masa cakulkuli sai ga Kulu zata tambayi me za a dafa, basarwa suka yi Umar ya shige daki ita kuma ta kame kamar ba ita ba.

********************

"Aunty Hauwaa ni kam mutumin nan ya bani tausayi "

"Wa kenan?"

"Mijin Jameelaa mana matar wan umaimah"

"Ke fa kina da matsala sapnah yanzu mene na tausayin nashi? Mutumin da Allah ya azurta da komai na rayuwa dai-dai misali, wata nakasa kika ga yana da ita?"

"Kwarai kuwa dan kuwa bai yi sa'ar mata ba, ki duba d'akin ta kiga baqar qazantar dake ciki, wai a ce nan ne dakin miji? Ga wani uban wari daga ji daga toilet yake fita, shi yasa na qi shiga, namiji bai sa'ar mace me tsafta ba ai abun tausayi ne,kuma fa ki ga da alama bata aikin komai, karatun ma ta samu dama miji na son taci gaba amma wai ita bata so, wannan wace irin mace ce, ga son abun duniya, kiga da Haroon ya bata kudi ya ce na baby ne kamar za ta kifa,"


"Hhhhhhh baki da dama wajen bata lokaci ki karance halayen mutum, to yana baki tausayi ta ya za ki taimaka masa? Dan na san halin ki sarai yanzu sai kice zaki taimaka, wannan dai ba almajiri bane balle ki bashi sadaka,"

"Shi kam ba abinda zan yi masa dan taimaka masa amma dai kam akwai gyara,"

Umaimah ce ta aje naman da taje cirowa a freezer ya qanqare da kyar ta ciro ta ji suna hirar yayan ta sai tace,

"To ko dai za ki je a ta biyu ne? Kin ga sai ki taimaka masa kawai,"

"Keeee Umaimah rabani da shiga gidan qazama, ni mijina ni zan fara bare shi a leda kamar yanda zai bareni a leda shi kuma yayan ki second hand ne fa,"

"Baki abin magana aikin kuke ko surutu?"

"Yah Ishaaq sannu da dawowa gaskiya zan fara azumin magana, kowa ya d'aukeni a mai surutu, inna daina magana zanga wanda zaku na kira da me surutun,"

"Ai shi surutu ko ka daina yana nan maqale da kai, tinda shi kamar ciwon qanjamau ne da ka fara baka iya bari,"

"Zan baku mamaki kuwa" in ji Sapnah.

Ranar haka Umar da Sapnah suka kwana tinanin junan su, ba wai tinani irin na soyayya ba, tinanin umar akan sapanah shine yawan surutun ta, ita kuma tana tausaya masa akan qazantar da yake zaune ciki gashi Kyakkyawa kuma ɗan gayu...........







*In ba iyayi ba da kuma wata qullaliya a qasa meye na tinanin juna, Umar ina tausaya maka in Jameelaa tai leqe ta gano da tinanin wata kai bacci😂*
[08/09, 10:18 pm] Aunty Hameeda: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻















WRITTEN BY HAERMEEBRAERH












PAGE 27:












Tin daga wannan ranar Mamalo bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login