Showing 96001 words to 99000 words out of 118783 words
nan da izinin ka nayi shi, dan haka tafiya ma da izinin ka zan tafi"
Wasa da dariya sukai tayi Mum taji daɗi da ɗan nata ya warware, ya bar ma Allah komai , a hanya suna komawa ya labarta mata yanda suka yi da sapnah bai boye mata komai ba, Mum tayi ta dariya, tace
"Yaran zamani salon ku daban ne"
Da dare bayan Dad ya huta daga tafiyar da yayi, Umar da Mum suka gabatar masa da maganar Sapnah, fada ya fara yi ba dan bai son Sapnah ba shi a cewar shi a maida Jameelaa, Umar kuwa baya son ya bata ta a idon Mahaifin shi, a bar ta da laifin da tai ita da Allah dan haka yace,
"Daddy, ni ke auren Jameelaa, ni nake zaune da ita, ni na san wanne iri ne halayen ta, Daddy dan son Annabi kar ka ce na maida ta, da da halin maida ta dana hakura da komai na maida ta kodan Humairah, amma ba zan iya ba, ba iya wannan ne laifin ta ba, laifin ta babbane a wajena, da wajen ku,da zaka ji daka ban izini ko a hanya kar mu gaisa, amma ba zan so na bata ta a idon ka ba, dan Allah kar ka ce na maida ta,"
"Kwantar da hankalin ka magana ta wuce , Allah ya sanya albarka a auren naku kaida Sapnah, ita kuma Allah ya sa rabuwar kuce tafi alkhairi,"
"Ameen Daddy,"
Daga baya suka ci gaba da hira suna wasa da Humairah.
*************************
Lokacin yin period ɗin Jameelaah ya gota sosai amma shiru kake ji ba bayani ta shiga damuwa iya damuwa, a kid'ime ta bazama zuwa asibiti, ko da taje ana mata gwaji aka gano tana ɗauke da ciki wata biyu, dai-dai watannin ta a gidan su kenan, kuka ta sanya tana kiran ta shiga uku ta lalace, ina zata saka ran ta, wannan kalmomi su suka zama mata kamar tasbihi, a iya watannin nan da ta zauna ta tina baya, sai ta hau kiran ta shiga uku ta lalace ina zata saka kanta.
Wannan cikin baida laulayi irin na Humairah, shi yasa ma bata gane komai ba, sai shegen ci da take yi.
"Likita dan Allah ka markaden cikin nan a zubar, in na barshi asiri na zai tonu,"
"In ma na rufa maki asiri anan, a lahira zai bankade, bamu zubda ciki asibitin nan, kinga mun ɗauki report ɗin ki, ki tabbata ba abinda ya samu cikin nan, in kika zubar ko ba anan ba zamu kai ki kotu, dan kuwa zan sa a dinga bibiyar ki a ga me kike aikatawa"
"Yau ni Jameelaa na ji jaraba, kai baka taimaka min ba kuma ka hana a taimaka min, wannan wace iriyar masifa ce na jawa kai na,"
"Bansan kalar ta ba, amma ke kin fini sanin ta tinda ke kika dakko ta,"
"Ni ba da kai nake ba... , kaga dai ba da kai nake ba, kar ka shiga maganar da ba ruwan ka,"
"Ke malama fita min anan wasu matan masu hankali na jira na,"
"Ni waya ce maka hauka nake,"
🤷🏻♂ kafad'a ya d'aga sannan ya nuna mata hanyar fita, tana tafe tana masifa, da Allah ya isa akan takunkumin da ya sa mata.
Gida ta je ta rasa yanda zata yi ta faɗa ma Ramai tana da ciki, in ma ta faɗa ta na da ciki to na waye? UMAR? KO BOKAYEN BOGI??????..........
*TAMBAYA A GAREKU MAKARANTA,SHIN CIKIN WA JAMEELAAH KE ƊAUKE DA SHI?*[09/09, 10:36 am] Aunty Hameeda: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 41:
"Wai ni aman me nake ganin kina yi ne haka? Gashi yanayin ki duk ya sauya kamar na mai ciki, "
Kuka ta fashe da shi kwuyan ta har yana kumbura dan tokare mata wuya da kukan yayi , ta shiga cikin tsananin tashin hankali, da can kafin aure bata yi cikin shege ba sai yanzu da girman ta da 'yarta, tinda dai ta tabbata wannan ba cikin Umar bane,sun dad'e rabon su da su kaɗai ta da juna.
"Daga tambaya sai kuka?"
Tattaro nitsuwar ta tayi, tayi gyaran murya sannan ta ce,
"Ramai dole na yi kuka mana ciki fa gare ni, kuma gashi uban d'an ya koren daga gidan shi, dan Allah ku maida ni kodan yarana,"
Zuciyar ta na ta harbawa ta zabga wannan qaryar, a ranta take ayyana.
'Allah ka rufan asiri su yarda su roqi Umar ya maida ni d'aki na'
"Alhamdu lilLAAHi, kaiii amma na ji daɗi sosai da samun wannan cikin naki, Allah ya sauke ki lafiya,.....a gaskiya tinda muka samu ya yafe mana,bazan iya cewa ya maida ki ba, iyaka zan sanar da shi kina dauke da ciki, ya rage na shi ya hakura ya maida ke, ko kuma ya barki anan ki haihu ya amshi abin haihuwar shi,"
"Dan Allah Ramai kar ki ce haka , kimin kyakkyawan fata na koma gidan miji na"
"Kyakkyawan fata kam ina yi maki in ban maki ba wa zan yi wa? Allah ya tabbatar mana da alkhairi,"
Bari mahaifin ku ya dawo, sai na sanar da shi meke faruwa.
Da dare bayan Baban Jameelaa ya dawo ya kammala komai, suna zaune yana kallon labarai, Ramai ke sanar da shi abin farin cikin da Jameelaah ke ɗauke da shi.
Baban Jameelaah ya ji daɗi shima, yayi mata addu'a da fatan alkhairi, sannan yaci gaba da kallon shi, shiru ne ya biyo baya,bata ji yayi maganar maida ta d'akin ta ba.
Kuka ta fara da shan majina,ta tabbata asirin ta ne zai tonu,
"Me ya faru kuma?"
"Ammmm....Malam wai fa ita so take a sanar da mijin ta, ya maida ta d'akin ta,"
"Hummmm d'akin ta kuma na ina kenan? Dakin da ta yi wa tofin Allah tsine da ayyukan ta? Ai d'akin nan ina jin kam in ba wani iko na Allah ba ya haramta a gare ta kenan, saboda yanda Mahaifin Umar ya min magana da shi kan shi Umar ɗin na tabbata ba zasu so sake maida ki gidan su ba,ba inda zani, sai dai zan sanar da shi kina ɗauke da gudan jinin shi saboda gaba ya san yana da d'a ko 'ya dake ya rage nashi ya maida ki,ko ya barki anan"
Rintse idon ta tayi hawaye masu zafin gaske suna zuba a kuncin ta, kan ta jingine da kujera da kyar ta tashi daga qasan ta yi masu sai da safe ta koma d'akin ta, wayar ta ta jawo, ta danna no Umar ,ta yi ta ringing bai d'aga ba, a zaton ta fushi ya yi ,bata san baya kusa da wayar bane.
Haka ta kwanta cikin tsananin damuwa da zubda hawaye.
***********************
Ɓangaren Umar kuwa yana zaune gaban Iyayen shi ya kasa ya tsare, shi a dole sai an kai maganar shi gaban manya,ba zai iya zama ba Sapnah ba na tsahon lokaci.
"Gwanda ma ka cire soyyar ta mai zafi a ran ka, kar ka manta abinda ya janyo mana fad'awa cikin tashin hankali komai zaka yi kana yin shi baya-baya Umar"
"Mum ina son ta, kowa ya san inda suke inda basu da d'a'a da Ishaaq bai auri yayar taba,"
"Dole mu san komai daga tushe, mu nemi asalin ta, da na iyayen ta, kai inda hali ma har da dangin ta dika, saboda ba zamu sake kwatanta abinda mukai a baya ba na rashin bincike"
"Wannan gaskiya ne, mahaifiyar ka tayi gaskiya, Umar mun yi kuskure a baya na rashin bincika asali da kuma sanin wace ce Jameelaah, munyi hanzarin yarda da ita kasancewar ta boye mana ita din wace ce, so zan yi bincike sosai akan Sapnah kafin mu shigar da magana wajen manya, kuma mahaifiyar ka ta baka shawara mai kyau, ka yi komai a hankali, kar ka zurfafa,"
Jikin Umar yayi sanyi, tabbas gaskiya suka faɗa masa, amma da soyayya ta so ta sake makantar da shi, Allah ya sa yana da iyayen da suke masu hangen nesa, sun nusar dashi gaskiya saboda kar a maimaita mistake ɗin baya.
Haka suka yi ta tattaunawa akan abinda ya kamata su yi, Umar daga baya ya musu sallama, bayan ya shafa kan Humairah da tai bacci a jikin Dad ya koma d'akin sa.
Koda ya shiga d'akin ya hango wayar shi na haske, da sauri ya qarasa kiran Jameelaah ya gani,sai ya qi d'agawa, sai da ta katse sannan ya suba wayar sosai anan ya ga ashe ba kiran farko kenan ba, wajen 26 missed calls ta yi masa, yaso d'agawa amma ya sa a silent ya yi addu'ar bacci ya kashe fitila ya kwanta a hannun daman shi, ya ba wayar baya.
Jameeelaah na ta kira bata gaji ba sai da bacci ya ɗauke ta a haka.
Da asuba da ta tashi ta tura masa message ta sanar dashi ya kamata yaje gidan su akwai wata magana mai matuqar mahimmanci da take son suyi.
'Ko me zata ce min Oho?'
Da safe bayan ya gama shirin office ya karya, ya ɗauki Humairah yana ta yi mata wasa, yanzu ta sake sosai da gidan da mutanen cikin shi, in ta fara kewaye gidan da rarrafe sai an kamo ta.
Yana mota ya aje jakar shi, zai tada ta, kiran Jameelaa ya shiga wayar shi tsaki yayi, sannan ya d'aga a hasale, dan ya gaji da wannan baqin nacin nata.
"Assalamu alaikum"
'Ya Allah! this gurl is going to kill me with her sweet voice'
Dakewa yayi kamar muryar ta bata affecting din shi yace,
"Wa'alaikumussalam, dan Allah meye ne? Kiie ta kirana kamar na ci maki bashi?"
"Da bashi ne dana yafe maka amma abinda ke tattare dani yafi qarfin bashi, dan haka kazo Baba na son ganin ka anjima"
"Too meye wannan shi kuma? Meye naci da yafi bashi?"
"Sai kazo zaka ji,"
Bayan ta kashe wayar, Umar bin tashi wayar yayi da kallo, kamar an rubuta me Jameelaah ke son sanar da shi a jiki, can ya tada motar shi ya nufi gidan su Jameelaah, ba zai iya bari sai yamma ba, bai san me zai je ya zo ba, bai san wani abu mai mahimmancin da za a kira shi akai ba a gidan su duba da yanda suka rabu.
Kiran ta ya sake yi yace,
"Baba na gida? In yana nan gani nan zuwa yanzu"
"Eh yana nan, amma kayi sauri kan ya fita,"
"Ki tsaida shi mana ki faɗa masa gani nan zuwa ba shi yake nema na ba dama?"
Cikin faɗa faɗa yake mata maganar, ji tayi kwalla ta taru a idon ta, Umar ya daina son ta, a da ko b'ata rai baya yi da ita, yanzu har faɗa ma yake yi mata.
(Ya sake ki ma balle faɗa)
Da sauri ta tashi ta sauya riga, ta saka wata mai kyau daga wanda Ramai ta bata, dan har yau Umar bai sake buɗe gidan su ba,balle yace a kwashi kayan ta ko a bar su.
A qofar gidan su Jameelaah motar Umar ta tsaya, ya ɗauki wayar shi ya sanar da Jameelaah ya iso, tai sauri ta sanar da Baba yana son ya wuce office, Yana cikin waya da ita ya ga Baban na fidda machine din shi da Umar din ya sai masa.
Da sauri Umar ya katse wayar ya isa gare shi, Umar na son dattijon sosai ba kaɗan ba, dan kuwa mutumin kirki ne shi , kama masa yayi suka fidda tare da gaida shi,
"Ahhh malam Umar,kaine da safe haka? Lafiya qlou, ya kuke, ya amarya ta me qiwa,"
"Kowa lafiya Baba, amaryar ka na gaida ka"
"Ina amsawa, ai ta ci gaba da qiwa in Maman ta ta haihu kaga shikenan an sake min wata matar ko kuma aboki tayi ta yanga ma Alhaji ni na yafe,"
"Haihuwa kuma Baba? Wace zata haihu?and Baba kace na zo amma naga kamar fita za kayi,"
"Ikon Allah, ai na zaci kazo ne kunyi magana da ita Jameelaa ta waya akan abinda ke faruwa, dan yanzu take sanar dani zaka zo,"
"Ni kuma ce min tai kana nema na, dan haka ban wuce office ba na zo nan naji maqasudin kiran"
"Ohhh Allah na gode maka da wannan yarinya, mu je daga ciki, ba za a yi wannan magana a waje ba,"
Bayan sun zauna a parlour Baban Jameelaah ya bayyana masa komai da ke faruwa, ai kuwa nan da nan ran Umar ya baci,
"Ciki dai ba nawa ba ne Baba sai dai a tambaye ta inda ta same shi, amma ni kam indai wata biyu ne ba nawa bane, raboda na da ita yafi wata biyu bai dai cika uku ba amma tabbas yafi biyu, ina take Baba a kira ta tayi bayani da kan ta,"
Kwala mata kira Baba ya yi ta fita cikin zumud'i da farin ciki, dan ta hango su a waje suna hira suna dariya, ta tabbata komai ya wuce d'akin ta zata koma,
Ta bulbulewa Ramai ɗan turaren nata, data fara amfani da shi, ta shafa powder qirjin nan an matso shi a riga, abinda Umar ya fi so kenan, zuwa tayi ta zauna ba ko mayafi balle hijabi,
"Jameelaa ashe baki da mutunci, kin rantse sai kin kunyata mu a idon duniya, sai kin sa ɗan mutuncin da ya rage ake ganin mu da shi ya gama qarewa? JAMEELAAH CIKIN WA KIKE ƊAUKE DA SHI, IN BAKI FAƊAN GASKIYA TSAKANIN KI DA ALLAH BA NA YAFE KI MA DUNIYA"
Cike da tashin hankali Ramai ta shiga itama, kallon Jameelaah dikkan su suka fara yi, ja da baya ta dinga yi dan ta gudu, sai buge Ramai dan bata san ta shiga ba, da sauri Ramai ta kife ta da wani hatsabibin tafi, sannan ta nuna mata tsakiyar parlourn tace,
"Zaki sanar damu gaskiyar wake da cikin jikin ki ko sai na lallasa ki?"
"Dan Allah kuyi hakuri zan faɗa, wayyooo Allah na na shiga uku na lalace, ni....ni....niiiimaaa bann sann na...naaawayee baaaaa"
Ta saki wani irin kuka mai quna a zuciya, ita kan ta tana cikin rud'ani,
"Bamu gane hausar baki san na waye ba, maza dubu ɗari nawa kika bi, Jameelaaaaaah ashe abun naki azimun ne haka?ya rabbi ka gafarta mana laifi na ne komai dake faruwa,"
Kuka Ramai ta sa sai da ta samu wajen zama saboda takaici, wannan wacce irin rayuwa ce,
"Kin dai tabbata ba nawa bane ko? Dan kinfi kowa sanin ba nawa bane ko,"
D'aga kai tayi ta rushe da sabon kuka, miqewa yayi ranshi a matuqar bace, dole yaje a gwada jinin shi kar yana ɗauke da mummunan ciwo bai sani ba, bai san sanda ta fara neman maza ba da auren shi akan ta.
"Baba na wuce office, Allah ya sake sadamu da alkhairi,"
Baba kunya tasa tinda ya duqa bai d'ago ba, wasu siraran hawaye ne ke sauka a idon shi,da wanne ido zai daga ya kalli yaron? Ta gama zubar masa da qima da mutuncin shi, ganin Umar zai fita ne ya sa ta zabura ta bishi a guje, ta qanqame shi, sai da yaji kamar ya taba wutar lantarki alokacin da jikin shi ke jiqe.
Tsayawa yayi cakkk, ya lumshe ido, Jameelaah ce mace ta farko da ya fara sanin auratayya da ita, kuma taɓa ta ne kadai ke sanya shi a hali na buqatuwa da mace, amma yau ji ya yi yana jin matsanaciyar tsana da haushin ta, tura ta baya ya yi da qarfi, ta bugi jikin window, sannan ya nuna ta da yatsan shi manuni ya qanqance ido cike da masifa amma ya kasa furta komai.
"Abban Humairah ka rufan asiri ka maida ni d'aki na, dan Allah ina son ka fiye da tinanin ka, ban san ina son ka haka ba sai yanzu, dan Allah ka manta da komai ka maida ni,"
"Tsakanin ki da Allah zaki iya manta me kika yi min?"
Shiru tayi tana zubda hawaye, daga baya ta kad'a kai, alamar ba zata iya mantawa ba,
"Balle kuma ni da kika cutar, kar ki sake kirana a waya, kar ki sake neman inda nake, sannan kar ki sake danganta shegen cikin ki da ni,"
A guje ya bar qofar gidan nasu da motar shi, ita kuma sai ta janyo hijabin dake kan igiya ta saka, qafarta ko takalmi babu ta fice...................
*In ka shuka alkhairi zaka girbi alkairi, in ka shuka sharri shi zaka girba*
[09/09, 10:38 am] Aunty Hameeda: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 42:
Tafe take a qasa sai yanka zufa take, saboda saurin da take tayi dik ta galabaita, haka ta isa gidan bokan qaryan ta, shagon rufe yake da kwad'o,sai ta zauna dan ta huta kafin nan sun iso.
A wajen baccin gajiya ya ɗauke ta, bata tashi farkawa ba sai da aka kira azahar, miqewa tayi ta kade jikin ta ta yi sallama a gidan da shagon yake ta dad'e tana sallama kafin wata dattijuwa ta leqo dogare da sanda, alamar dayar qafar ta na da matsala gaida ta Jameelaa tayi, sannan ta tambaya mai zama a shagon nan yana nan kuwa?
"Baiwar Allah wanne daga ciki? Sule ko Bashari?"
"Su biyun dik da ban san sunan su ba amma akwai fari akwai baqi, kuma farin gajere ne, baqin dogo,dan Allah ki taimaka min ki sanar dani inda zan gan su tin safe nake zaune ina jiran su ba ko ɗaya a cikin su,"
"Allah sarki, yarinya ai basa nan, sun tafi Habuja neman kudi, shi Sule ya saida adaidaitan shi suka tafi habuja dan su fara sana'a a can, yau watan su ɗaya da kwana tara da tafiya, ke ɗin wace ce?"
Kuka Jameelaa ta fasa mai qarfi, sai shasshekar kuka take tana kumawa, dattijuwar nan ta dogara sandar ta ta dafa kafad'ar Jameelaa? Sannan tace,
"Kema wani abun suka yi maki ko? Tafiyar yaran nan an kawo qarar su tafi a qirga, na yi iya qoqarin da zan na raba Bashari da Sule amma abun ya faskara, abotar su tayi qarfi ainun qarfin da dik wani yunquri da nai dan raba su abun ya gagara,"
Dukan cikin ta ta fara yi tana kallon dattijuwar tana mata bayani, idon ta na tsiyayar da hawaye sinyi jawur kamar garwashi.
"Ciki ne da ni kuma nasu ne, ban san waye uban cikin dake jikina ba.....na zo su wanken baqin cikin da nake ɗauke da shi a cikin rashin sanin su ɗin ba bokayen gaske bane, gashi sun ninninkan baqin ciki da azabar da nake ciki, ina zan sa kai na,"
Kuka mai tsanani ta fashe da shi, dattijuwar ta kama baki tace,
"Na shiga uku ni Delu, bokan ci kuma? Me ya haɗa Bashari da bokanci na san wannan dan iskan Sulen ne zai koya masa wannan shegantakar, yarinya kinga tin kan dare ya maki ki