Showing 60001 words to 63000 words out of 118783 words
ji tayi an fara qwanqwasawa a hankali, lullub'in ta ta gyara sosai sannan ta je dan bud'ewa, Haroon ne a tsaye ya ci babbar shadda an baza masa ɗinkin babbar riga sai qamshi ke tashi a jikin shi,sai ta gan shi ya sauya mata kamar ba shi ba kafe shi tayi da ido ta na qare masa kallo, shi ɗin ma ita yake kllo kafin daga baya cikin zolaya ya ce mata,
"Shin amaryar nan kuwa zata bawa angon ta damar shiga ciki Ko sai ta gama kalle shi a bakin qofa?"
Wayyooo kunyar ta ina za ta shiga ta buya? ji tayi kamar qasa ta bude ta shiga dan kunya,da sauri ta matsa ta koma kan sallaya ta zauna, ta duqunqune kan ta a mayafin ta ta na dariya qasa-qasa.
Dariya yake yi mata dan ganin yanda take jin kunya bayan ta gama shagala da kallon shi bata ma san ta yi ba, a hankali ya furta
"Sallah kika yi ne?"
"Eh"
"Ok nima bari na rage rigar nan sai muyi nafila kawai, ina da alwala,"
Ajiye ledar hannun shi yayi ya rage rigar jikin shi, sannan ya tsaya a gaba tana baya,a haka suka yi raka'a biyu bayan sun idar ya jagoranci yin addu'a, sannan ya yi mata addu'ar da ango ke yima amarya wadda tazo a sunnah,daga baya ya ce mata,
"Ke d'aliba ta ce na san kin san farillan sallah da sunnoni da na alwala dana wanka, sai dai abu ɗaya, ban taba ganin kin gwada a gabana ba musamman shi wankan, dan haka yau zaki gwada a gabana na ga ko kin iya,"
Da sauri ta cire lullub'in da tai har fuskar ta ta kalle shi, taya za ta iya wankan janaba gaban namiji namijin ma da take jin kunya kamar shi? Cikin tura baki gaba ta ce,
"Gaskiya ni sai dai na faɗa maka yanda ake yi, kuma in baka yarda na iya ba ka tuna mana ko rannan da ka koya mana a gida nafi Jameelaa iyawa har kyautar hisnul muslim ka bani,"
"Ni dai ban tabbatar ba dan kuwa da baki ki ka faɗa na ji a kunne na, yanzu tinda kin zama halal d'ina kawai sai ki gwada a gabana na gani,"
Idon ta ne ya ciko da k'walla tana jin qirjin ta na bugawa saboda shiga damuwa da ta yi a hankali kuma ta gano inda ya dosa da kalaman shi
Murmushi yayi ya cire hular kan shi a qalla saqon shi ya isa ta fahimci me yake nufi, janyo ledar da ya zo da ita yayi gaban su ya buɗe gasasshiyar kazar da yaje har Markaz ya siyo musu, qamshin kazar kaɗai ya isa tsinka yawu,balle mutum yayi ido biyu da ita har ya kai baki, hummm (an tadan da tsohon kwadayi na na 1877)
Sai da suka ci suka sha sannan suka kora da madara, dan kuwa Umaimah bata tsaya fulako ba irin na su oo, ci ta yi ta qoshi ta yi hamdala daga qarshe ta tashi ta kwashe sauran dan ta adana a fridge ya amsa ya ce,
"Yau daren naki ne gimbiya ki huta ba sai kin yi wahala ba bari na taya ki,"
Sunkuyar da kan ta tayi ta shige toilet, ta wanke bakin ta sannan ta fita, kayan bacci ta ɗauka masu kyau ta saka sannan ta koma ta kwanta, ya dad'e kafin ya koma d'akin ,cikin shirin bacci ya shiga d'akin, ganin ta yayi ta kulle idon ta kamar mai bacci, siririyar dariya ya saki dan ya san idon ta biyu,sai ya kashe fitila a cikin duhun ya taka ya isa inda take.
Kuma kenan kashe wutar zaku yi dan ku kore ni tinda ba gani nake ba a duhu, sai da haske nake gani....
Washegari ko da na kalli Umaimah kuka ne kawai ban yi mata ba, saboda kun dai san Ustaz kuma malamin islamiyya yayi karatu sosai, to fa Ustazu ya fassara mata karatun nan sala sala, kuma da alama ta fahimta da kyau, idanun ta sun kumbura sosai saboda kukan da ta sha.
Haroon ma idon shi kamar wanda ya yi kukan,tea ne a cup mai zafi da kauri ya had'o mata ya tallabo Umaimah jikin shi yana bata, sai kuka take mai cike da shagwab'a tana zubo da hawaye, a hankali Haroon ya ce,
"Dan Allah Mar'atussaliha ki yi hakuri ki sha, in ki ka sha za ki ji daɗin jikin ki, dan Allah ki daina kuka sai in dinga jin kamar zan yi kuka nima, kin ga dai yanda ki ka sani kuka nima jiya saboda kukan da ki ka dinga yi ko?"
Karb'a tayi ta na sha a hankali ba jimawa ta shanye tas, ji ta yi tana son qari dan kuwa yunwa take ji kwarai, cake deb'o ya bata ta ci sannan ya bata ruwa ta sha, hamdala ta yi Haroon sai ya aje sauran ya yi kissing din wuyan ta, kwab'e baki ta yi kamar zata yi kuka,qarasa kwantar da ita ya yi a faffad'an qirjin shi ya na lallashi,cikin kunnen ta yake rad'a mata,
"Shiiiii ba abinda zan sake yi miki har sai kinji sauqi, sai dai dole ne na faɗa maki cewar tun jiya nake yi maki addu'ar Allah ya saka maki da mafificin alkhairi,kin shayar dani zuma wadda zaqin ta ba zai taɓa gushewa a ƙwaƙwalwa ta da zuciya ta ba, har yanzu ina jin zaqin ta a baki na da gangar jiki na, na san kuma har abada ba zan daina jin zaqin nata ba, ina roqon Allah da ya yi wa iyayen ki albarka ya sanya su a aljanna maɗaukakiya, domin sun reni fulawa mai kyau da qamshi tare da zaqi,"
"Gentle dan Allah ka daina zuga ni haka, ameen na gode da addu'o'in ka tare da yabawar ka a gare ni,amma daga yau ba zan sake kiran ka da gentle ba saboda ka sauya daga Gentle ka koma wani abu na daban,"
"Ohhhh Mar'atussaliha, na roqe ki da ki ci gaba da kirana haka, wataqila sunan ya zama linzami ya bini na zama ina maki komai cikin gentleness,ko ya kk ce?"
juyawa ta yayi tana kallon shi, daga baya ta kwantar da kan ta, saboda kunyar shi take ji, buga qofar akai da alama sun samu baqin safe ne.
Zuwa yayi ya bude gidan aunty Hauwaa ce ɗauke da kulolin abinci, gaisawa suka yi ta bashi zata juya ta tafi ya ce,
"Ba zaki shiga ciki bane?"
"Niii kaza miji na zakara? In shiga ciki kuma in yi me? Amaryar ka mai raki jiya har gidana muna jin kukan ta, kai kuma da yake ba hakuri a lamarin naka ko ka d'aga mata qafa,tinda nake da kai baka taɓa zuwa inda nake daga kai sai gajeren wando da vest ba amma kalle ka yanzu a gabana, dan haka ban isa shiga gidannan ba nan da wata ɗaya ma albarka"
Kunyar duniya ba irin wacca bata kama Haroon ba sai da ya yi danasanin yi mata tayin shiga gidan, shikenan Umaimah ta janyo masu abin magana har gidan yayan shi an ji su, cikin dariya,Aunty Hauwaa ce ta juya tace masa,
"Kaii wasa fa bane maka ba abinda muka ji, sai anjima in mijina ya tafi kasuwa zan shigo, ba zan shiga na dad'e ba yana can yana jira na"
"Aunty Hauwaa 1-0 zan rama ne"
Suna dariya gaba ɗayan su suka bar wajen, aje abincin yayi a parlour yaje ya d'aga ta, sun riga da sun yi wankan su tun safen tsaf suke sai qamshi ke tashi a jikin su, kayan daya sanyawa Umaimah ne ke bata kunya, wata riga ce iya cinyar ta, gashi gashin ta da ya sha kitso qanana ya sake shi zuwa wuyan ta, a da ta dan d'aure abunta da band saboda ba wani tsaho ne da shi sosai ba, amma shi yana sha'awar ganin su a wuyan nata shi yasa ya cire band ɗin.
Yayi yayi taci abinci ta kasa saboda ya riga ya bata tea, shine dai ta zuba masa ya fara ci kuwa, sai da ya qoshi ya je ya wanke baki suka koma baccin gajiyar biki.
***********************
Mamalo ce taje asibiti dan duba baban Jameelaa, can suka hadu bayan dubiya Mamalo ke fad'awa Jameelaa tana da ciki itama, nan kuwa Jameelaa ta taya ta murna, daga haka ta fara gaya mata irin tanadin da ta yi wa cikin ta in ta haihu, da irin kud'in da za a kashe, sai Mamalo ta ji dik ta muzanta ta dan kuwa ba ta da irin wannan kuɗin da zatai hidimar bikin suna irin na Jameelaah, tinani ne fal ran ta lokacin da take komawa gida na yanda zatai itama ai suna mai qayatarwa irin na Jameelaah..................
*Ikon Allah wai na kwance ya faɗi, in fa baki da gashin wance kar ki ce zaki yi kitson wance, habaa Fatsun Sadeequu*
[11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMMAERH
PAGE 26:
Tsabar azaba Jameelah sai da ta suma wanda da kyar aka samu ta farfaɗo, Umar na manne da babyn a qirjin shi yarinya ce kyakkyawa Jameelah ta haifa masu, nan take Umar yaji ya kamu da tsananin qaunar yarinyar da tausayin mahaifiyar ta tare da qauna mai tsanani, ji yake yanzu a duniya bayan iyayen shi ba shi da wasu wanda suka fi soyuwa a rayuwar shi sama da matar shi da diyar shi sai kuma qanwar shi Umaimah, alqawarin tsantsar so da kulawa tare da yi masu dik abinda suke so indai zasuyi farin ciki kuma bai fi qarfin sa ba sannan bai sabawa addini ba ya yi musu tsakanin shi da Allah.
A nan take ya sanya mata suna Nana A'i'shaa, yana burin dama sawa abinda ya haifa wannan suna mai albarka idan mace ce,Mum taji daɗin hakan sosai, domin kuwa suna ne mai daraja sunan matar ma'aiki da ya fi so bayan Nana khadeejah.
Nan da nan zancen haihuwar Jameelah ya bazu kafin yamma mutane an cika gida sai shiga ake ana daukan jaririyar ana sanya mata albarka, Jameelaah kuwa na nan a kwance idon ta rufe dik jin ta take yi bata da k'wari a jikin ta, tea ne mai yawa da kauri Ramai ta kindimo a babban kofi, tare da farfesun naman rago ta shiga uwar d'akin ta zauna a gefen gadon da Jameelah ke kwance ta ce,
"Tashi ki ci ki sha ko kin samu qarfi a jikin ki, kowa ya maida hankali akan jaririya na gode Allah ma daya sa ina nan, da haka za a barki ko ki mace ko ki rayu ba mai asara sai ni da uban ki,"
Jameelaah da kyar ta iya tashi ta zauna tare da taimakon Ramai, tabbas Mum ta dan ji kunyar abinda suka yi na kyale Jameelah kowa ya maida hankali akan jaririyar, sam sun sha'afa da Jameelaan suna ta yi wa yarinya wasa da ba gane me ake yi take ba, dan haka sai ta hau kame-kame ta na bada hakuri, amma haka Ramai ta d'aure fuska ta ciyar da Jameelaa sosai, sannan ta je waje dan duba ruwan da ta ɗora, se taga bai ba saboda bata jima da sawa ba ta koma ta ci gaba da zama kusa da Jamelaan, yarinyar aka miqa mata ta amsa, wani hawaye ne na tsananin qaunar jikarta ta ya kwaranya a idon ta, cikin jan majina ta ce,
"Allah ya raya mana A'i'shaa, ya yi mata albarka, ta yi kama ainun da mahaifiyar ta sanda na haife ta, kamar an tsaga kara,"
Cike da jin daɗi Umar yace,
"Ke nan zata yi kama da ita sak idan ta girma ko Mama,"
Ai nan fa Ramai ta samu waje ta dinga fad'in qarya da gaskiya akan kyau irin na Jameelaah, Umar kuwa sai jin daɗi yake yi, Mum dik kunya ta kama ta dan kuwa har labarin sanda Jameelaan ta fara al'ada da qirgan dangi sai da ta bawa Umar, ruwa na can ya tafasa ya tafarfashe, Jameelaah sai sheqa bacci take abun ta.
Mum ce ta je ta haɗa ruwan wankan ta aje komai da ake buqata sannan ta shiga dakin cikin sakewar fuska tace,
"Umman Jameelaa zaki yi mata wankan ne ko naje na yi mata kawai,"
"Subhanallahi na manta na ɗora ruwan zafi fa, bari nayi mata kawai ke yi wa jinjirar,"
Tashin Jameelaah suka yi daga baccin wadda kan ta ya rage ciwo sosai dan kuwa ta ji daɗin abinda taci da kuma hutun da ta samu, ruwan ba mai zafi sosai ba aka haɗa mata aka yi mata wankan da shi, haka ma wanda ta zauna ciki, ba shi da mugun zafin nan shima, (irin wannan ruwan ko hawan jini gari mutum ba zai yi masa illa ba)
Mum kuwa ta yi ma jinjira wanka ta shiryata cikin kaya masu taushi da laushi kalar pink na jarirai,Ramai kuma ta shirya mai jego ta yi sharr sai sheqi take yi, Umar komai akan idon shi ake aikatawa yaqi fita sannan bakin shi yaqi rufuwa saboda farin ciki.
Da dare Umaimah suka iso da Haroon Umaimah dake tana da jikin qiba nan da nan ta yi dumurmur da ita gwanin ban sha'awa, tana ganin Mum ta rungume ta itama ɗin tayi kewar ta sosai sai suka rungume juna.
"Mum ina mai jegon? A ban babyna na dauka,Allah ya raya mana ya yi albarka,"
Jameelaa dai sai ido ta haihu ta ga qarshen zance jikin ta qaura yayi mugun yin magariba, ashe haka iyaye suke ji? Haihuwa babban abu ne ashe ta ke raina lamarin, iyaye girman su mai girma ne ainun, dole ne kowa ya girmama iyayen shi, son Ramai da Baban ta sun qaru a ran ta k'warai a wannan lokacin.
Cikin mutunci da girmama juna suka gaisa da Umaimah har saida Umaimah ta yi mamakin sauyawar Jameelahn ganin yanda qawar ta ta ta yi laushi da wuri, dariya sosai tai tayi tana tsokanar ta.
Har qarfe taran dare ba su tafi ba, mutane sun dan zazzo na kusa da aka sanarwa da haihuwar,qarfe tara da rabi Haroon yace zasu tafi Umaimah tai ta shagwaba ita a barta, dama a kusa da juna suke a zaune, dan haka kawai bai ce komai ba, sai zura hannun shi yayi ta bayan ta ya shafi bayan ta, qafewa tayi da maganar da zata yi tayi, ba wanda ya kula da me ke faruwa, cikin sarqewar murya ta ce,
"Mum zamu wuce,"
"Har kin gama shagwabar?"
"Yah ai na yau ne kawai, gobe in nazo sai an gama suna zan koma,"
Ta kalli Haroon tare da murguda masa baki, cikin salon soyayya,(ba da rashin ta ido ba faaa)
Mum ma tashi tayi dan komawa gida, drivern su ne ya zo dan komawa da ita gida,Ramai anan zata kwana, saboda kula da mai jego.
Bayan kowa ya tafi ne Jameelaah da Umar na d'aki sun saka jaririya a gaba suna kallo, kowa na fadin albarkacin bakin shi.
Ramai ce ta shiga kitchen ta dumama naman da ta dafama Jameelaah ta ciko kwano da shi, tare da singumemen bread sai ta haɗa tea mai shegen kauri, ta je d'akin da ta sauka ta aje a qasan carpet ta zauna ta na ta lodawa cikin ta, sai santi take tana zuba surutu tana fad'in,
"Ina nan daga nan har ayi arba'in ba inda zani, ni inda hali ma sai na dawo nan in ta yi masu reno, Jameelaan ta koma makaranta, irin wannan dabge haka, kullum bawa in zaici nama sai qwarori amma nan gashi ka cika kwano ka ci ba mai ganewa ko ace dan me,"
Sai da ta tashi da shi tass ta saki gyatsa mai qarfi sannan ta mayar da kwanon ta wanke hannu taje ta kwanta.
Washe gari da asussuba ta tashi ta dora ruwan wanka, ta dora abincin kari, farfesun kaza ta yi mata ta saka yan kayayyakin mata a ciki,
Dankalin turawa ta fere ta soya shima, irin suyar tsoffi yankan manya manyan gaske, wanda bai saba cin irin yankan ba ba zai ji daɗin shi ba, ta kai ta aje.
Bayan ta gama ta je dakin su ta kwankwasa qofar, Umar ne ya fito, dauke da Baby a kafadar shi, Jameelaa na zaune bakin gado tana saka takalmi zata fita dan yin wanka, d'aure take da towel ta yafa wani akan ta,bayan sun gaisa da Umar ne ta cewa Jameelaah cikin fara'a,
"A kwana a hantse sai kyakkyawa, maza taso na sille ki ki zo ki karya, ba a son me jego tana zama da yunwa,"
Wanka ta yi mata sosai, ta sa ta zauna a ruwan da ta dafa da bagaruwa kadan ba da yawa ba sai kuma aloevera da ta wanke ta b'are cikin ta tafasa ya dan huce dai-dai yanda za a iya zama a ciki, sannan ta zauna sai da ya huce sosai sannan ta fita, sai surutu takewa Ramai akan me yasa ba zata bari a gama suna ba sannan ayi wannan wankan na tarkace,
"Ke ja can ga kaza can ma ki gama ki cinye tass ai gyara yanzu kiks fara yi ba d'aga qafa har sai kinyi arba'in, gobe ma ruwan da zaki zauna har da qarin ganyen magarya zan saka a ciki danya wanken dattin jikin ki tass,"
"Ramaiii ni dai gaskiya bana son abu mara daɗi ba zan ci ba dik wani abu me d'aci kar ma ki fara ban dan ba san ci ba ko na sha"
"Kar ki damu ba masu d'aci bane muje na samu na wanke jinjirar itama,"
Jameelaa cikin wani dakken leshi ta shirya dan yana daga cikin burin ta dama daga randa ta haihu har bayan suna ta yi ta sanya kaya masu matuqar kyau da burge dik wanda ya gan ta.
Jaririyar ma kaya masu tsada aka sanya mata Ramai ta share gidan ta kunna turaren wuta sannan ta saka na garwashi gidan sai qamshi yake yi.
Bayan sun karya ne Jameelaa ta hau social net ta hau sanar da qawayen ta 'ya'yan masu kuɗi ta haihu an sami mace sai sanya albarka ake ana mata alqawarin zuwa ganin jaririya, kiran Mamalo tayi ta sanar da ita ta sauka fa, itama tana nan da nata tulun,
"Wayyooo kin sauka? Masha Allahu, ina nan tafe yau inshaa Allahu, yanzun nan Sadeeq ya fita shago, zan sanar da shi sai na taho,"
"Sai kin zo to,"
"Me zan taho maki da shi na ci ?"
Wani murmushin rainin hankali tayi sannan ta ce,
"Habaaa Mamalo wanne irin me zaki kawon na ci kuwa? Yanzu haka farfesu ne sun kai kala hudu gabana, daga gidan su Umar ma