Showing 30001 words to 33000 words out of 118783 words

Chapter 11 - MAZAUNA GIDA COMPLETE By HAERMEEBRAEH.txt

26 Oct 2025

650

gidan kafin mai gadi ya buɗe masa, a zaune ya gan su akan tabarma kowacce riqe da littafan ta suna hira, sanye ya ga Jameelaa da babban hijab, mamaki ne ya kama shi dama gidan su daya?

Suna ganin shi suka gyara zama.

"Assalamu alaikum,"

"Wa'alaikumussalam"

Bayan sun gaisa ya fara masu karatu, suna maimaitawa.

Sai da ya tabbatar sun iya kowanne karatu da ya masu sannan Jameelaa ta masa sallama ta shiga gida.

"Shin dama gidan ku daya da wannan mara kunyar?"

"Ehh ah ah ! da dai ba gidan mu ɗaya ba, amma yanzu gidan mu ɗaya, dan kuwa yayana ke auren ta,"

"Aure? Jameelar?"

"Eh mana ba ta isa aure bane? Sa'ata ce fa"

"To ke ɗin wata babbace? Ke ɗin ma ai baki fi a kira ki da 'yar baby ba,"

"Habaa Malam baby fa,gaskiya ni na fi qarfin a kira ni da baby, Jameelah ta ce masu shekarun mu da yawa an yi masu aure ka ga kuwa mu ɗin ba yara bane"

"Ke kike ganin kan ki wata babba, amma na san dika-dika ba za ki wuce shekaru sha takwas ba,"

"Tabbb ai ka qaramin shekarun ma da yawa, 16 muke, mundai shiga 17 yanzu"

"Ahaff ashe ma cika min ido ki ka yi har naga kamar kin kai 18 years"

"In kun gama hirar ki je Mum na neman ki,"

Da sauri suka kalli inda Jameelah take tsaye hannun ta a qugun ta tana harar Haroon, kad'a kai ya yi saboda Jameelaa ba zata sauya ba sai addu'a kawai.

Sallama ya yi musu ya tafi gida, Umaimah kuwa haka nan take jin daɗin hirar da suka ɗan yi a yau da malam Haroon dik da ba wani abu aka ce ba mai mahimmanci a hirar.

Haka bangaren Haroon ma ba qaramin daɗi hirar tasu ta yi masa ba,a qafa yayi rabin tafiyar shi zuwa gida yana tafe yana hango murmushin ta da kunyar ta tare da kamun kan ta, gaskiya zuciyar shi na son fad'awa cikin damuwa, domin kuwa shi da Umaimah akwai banbancin rayuwa mai tazara,iyayen ta na da hali sosai, shi kuwa dukiya ta yayan sa ce yau idan aka ce me ka mallaka abinda zai nuna bai taka kara ya karya ba idan an haɗa da abinda iyayen ta suka mallaka,kowa kuma ya san mutumin kirki baya taqama da abun wani sai nashi, sannan gashi ba shi da wani zurfin ilimin boko, anya abinda yake ji game da Umaimah zai je mataki na gaba kuwa?

Ko da ya isa gida Hauwaa na zaune a kujera ta ɗora qanqara a goshin ta tana jinya, sanye take da wata iriyar riga ta atampa an yi mata dinkin qananan kaya, gaba ɗaya qirjin ta kusan rabi a waje yake, cinyoyin ta buɗe, ta kuma tattare rigar sama dik da rashin tsaho da take da ita, sai kiran

"Washhhh Allah na.....washhhh zafi..wayyooo Allah na" take.

Kauda kai Haroon ya yi tare da sakin tsaki mai qarfin gaske, da sauri ta juya ta ga shine, itan ma tsaki ta saki sannan ta ce masa,

"Soko mara rabo kawai,"

Shima cike da rashin kunya ya amsa mata da,

"Rabon wahala? Allah ya min tsari da rabon wahala duniya da lahira, in baki sauya hali ba wannan azabar duniya kenan ki ke sha, ta lahira sai kin gwmamace baki san namiji ba ma a rayuwar ki gaba ɗaya,"

"Ah kuna nan kenan,ina can ina duba ki ashe ke kina nan kuna hira abun ku,"

Da sauri ta juya tare da sauke ajiyar zuciya saboda bai ji me suke magana akai ba.

"Yah na dawo daga gidan dana faɗa maka zan dinga yi masu karatu....gaskiya Yah ina ganin ya kamata na koma makaranta ko bangaren kasuwanci ne na karanta,"

"Woww ! yau kuma kai ne ke maganar karatu? Me yasa? Ina ce karatun mahammadiyya ya ishe ka kawai? Meye dalilin son komawar ka makaranta yanzu kuma?"

"Ba komai Yah Ishaq, kawai na ga ya dace ne na koma tun lokaci bai qure min ba, sannan yaran danake koyawa karatu su na da ilimin boko sosai, ina gudun kar a zo a yo min wani turancin ban iya ba na ji kunya,"

Dariya sukai ta yi shi da yayan nashi, can yayan nashi ya kafe shi da ido ya na murmushi ya ce,

"Akwai budurwar ka cikin su ko?"

Zaro ido Haroon yayi sannan ya ce,

"Nii kuma Yaya da budurwa? Habaaaa ni dai kawai ina son makaranta ne yanzu,"

Wani yawu Hauwaa ta had'iya dan sauraro take ta ji ko budurwar ce zata sanya shi komawa makaranta, (ko meye nata a ciki oho?)


Haka sukayi ta hira, Hauwa na zaune kusan tsirara amma ko a jikin Ishaaq, haka tai ta gilmawa a tsakanin su Haroon gajiya yayi da kallon da take jifan shi da shi ya yi ma yayan shi sallama ya shige d'aki, cike da takaicin yanda Yayan nashi sam baya kula da iyalin shi ya bar wajen.


***********************


Rayuwa na ta juyawa yana yi na sauyawa ci gaba ya samu a gidaje da dama, gidan su Umaimah na ɗaya daga cikin gidajen da suka samu nasarori masu yawa, nasara ta farko shine kammala karatun Umar tare da kasancewar shi cikakken likitan mata har ya fara aiki a asibitin Aminu kano, a ta bayan asibitin Aminu Kanon Mum da Dad suka maka mashi ginin gidan shi mai kyau madaidaici, d'aki uku ne da parlour ɗaya mai haɗe da dinning area,sai kitchen a tsakar gida,da toilete ɗaya a tsakar gida saboda baqi, dakin mai gida na da na shi toilet a ciki,ginin ya qayatar matuqa dan kuwa an fitar da fasali mai kyau, ga wasu fulawowi da aka shuka sai suka qarawa gidan kyau matuqa,kowa ya ga gidan sai ya yaba tare da santin ginin,wata na sama ake saka ran tarewar su Umar da Jameelah a sabon gidan nasu.

Umaimah ta kammala secondary school tana zaune a gida, Mum tace ko zata ci gaba da karatu sai a gidan miji, dan haka su na jiran manemin aure ya bayyana kullum addu'ar su Allah ya bata miji na gari mumini salihi.

Ta bangaren su Ishaq kuwa Haroon ya samu nasarar shiga makarantar Bayero dake cikin garin Kano,a bangaren Kasuwanci ya samu gurbin karatu yana cikin shekarar shi ta biyu kenan, sauran shi shekara biyu ya kammala.

Haroon yana son ya bayyana wa Umaimah son daya ke yi mata amma sai yaji nauyi da tsoro sun mamaye shi, Umaimah ji take yi kamar ta furta masa irin son da take yi masa tunda shi ya kasa bayyanawa, amma kunya irin ta 'ya mace ta hana ta, gefe ɗaya kuma wani haushin shi ta ke ji saboda ya kasa furta mata abinda kowa ya fuskanta game da shi akan ta, dan kuwa har Dad ya gane yana son ta.

Yah Ishaaq yayi yayi ya je ya bayyana qudirin shi akan Umaimah ko an san da zaman shi, shi kuma a matsayin sa na babban wan shi makwafin uba a gare shi ya je ya nema masa auren Umaimahn amma sai ya qaryata son da yake yi mata yace shaquwa ce kawai irin ta malami da d'alibar shi mai k'wazo.

A can gidan Malam Jameel kuwa
Ramai kullum naci take yi ma Jameelaa akan ta qoqarta masu ta sama masu gida a wajen da 'yan gayu suke ko da na haya ne,dan kuwa ita ta gaji da rayuwar lungun nasu ta cakud'ed'eniya, ta san Jameela bata da kud'in da zata sai masu gida amma a qalla ko hayar ce su samu su bar wannan gidan, Jameelah kuwa sai dojewa take yi duba da cewa dika-dika auren nasu bai wuce shekara biyu ba amma ace zata fara tatsar miji manyan kuɗi irin haka,wanda har a wannan lokacin ba abinda ya shiga tsakanin su ta bangaren auratayya.

Yau ma kamar kowanne lokaci in zata je gidan nasu takan ci ado ta sa kaya irin na ba raini ɗin nan, yau kuwa adon da ta yi ya fi na kowacce rana qayatuwa da tsada domin kuwa bikin Mamalo ake yi, kuma har yanzu qawancen su na nan ba abinda ya sauya a tsakanin su, wata leda ce a hannun ta wadda ta d'ebi kayan abinci dan kai wa Ramai ta ɗauki atampa da takalmin da zai shiga da atampar ta lullub'e abincin ta yanda ba za a gane ba, dan kuwa ta riga ta sanar da Umar za ta ɗaukar wa Mamalo kaya a nata tinda ba a wani saka mata kaya ba sosai a lefen ta ba, har yanzu iya abinda take aikatawa kenan mara kyau a gidan, wato satar abinci in zata je gida, Mum ta gane amma bata cewa komai saboda ta yi zaton babu ce ta sanya Jameelan d'iban kayan abinci ta kai gidan su ba tare da an bata ba,duk da cewa Mum taga wautar Jameelar ta nan in ta tambaya za su iya bata mafiyin wanda take satar ma amma ta gwammace ta ɗauka ba a bata ba.

Jameelah kuwa jira take yi su koma gidan su ta buɗe asalin rayuwar ta da take son zubawa ta more, ga wata iriyar buqatar mijin ta dake addabar ta a iya tsahon lokacin nan daurewa kawai take yi matuqa dan kar Umar ya gane labarin da ta faɗa qarya ne,ta bangaren Umar kuwa ya kasa sauke haqqin auren dake kan shi ba dan komai ba sai dan alqawarin da ya ɗaukar wa Mum, da kuma ya gama makarantar sai tsoron idan ya kusanceta me zai tarar ya shige shi saboda tunanin fyaden da tace an yi mata a baya,lokuta da dama sai ya fara romancing ɗin ta da zafi-zafi kamar zai zarce sai kawai ya ji wata iriyar fad'uwar gaba ta kama shi ya dakata duk da yanda Jameelar ke maqale masa watarana har kuka take yi amma haka zai qi ci gaba ya bar ta.

Umar na son ya san waye ya yi mata fyad'e ta na qarama yana kuma tsoron me zai ji da zai tarwatsa tunanin shi, a qarshe ya yanke shawarar sai ya kaita asibiti an gwada ta in bata ɗauke da wani mugun ciwon to a sannan ne zai kusance ta, ba zai bari kowa ma ya sani ba sai sun koma gidan su sannan zai keb'anta da ita.

Jameelaah kuwa ta yi duk yanda zata yi ya neme ta abun ya ci tura basirar ta har neman qarewa take yi, shi kan shi ya na buqatar kasancewa da ita amma tsoron mai zai tarar ke dakatar da shi, a yanzu dai ya yanke shawarar kafin lokacin komawar su ya cika zai ce su koma kawai dan ba zai iya qara sati ɗaya ba ba tare da ya san matsayin Jameelaah ba a likitance shin ta na da lafiya ko bata lafiya.

Umar ne ya kai ta gidan bikin bayan ya bata kuɗi da zata yi liqi da su da wanda zata riqe ko da za a buqaci wani abun ta taimaka da shi a wajen bikin kamar yanda ta ke ta yi tunda aka fara shirin bikin,gaba ɗaya hankalin matasa da 'yan matan da ke qofar gidan duk ya tattare ya koma kan Jameelah da Umar tare da motar su dabuwa dal da aka ajiye ta a cikin ta, ko da ya ajiye ta sai da suka ɗan taɓa hirar su ta soyayya sannan ta ja ledar da ta boyo ta ajiye a gefen qafar ta ta busa masa sumba sannan ta fita suna murmushi tare da d'aga wa juna hannu ta shige cikin gidan su ta na taku kamar wata sarauniyar mata, ta na shiga ta tadda qawayen ta da su Mamalo ana zaune a tsakar gida, ihu wajen ya ɗauka Mamalo ta ce,

"Heeeeeeeee shegiya qawata ! kina wutaaaa hajiya ta ina bin ki da fetur, dan Allah ku matsa ku bata waccan kujerar ta zauna qawata ba ta zama a tabarma bace, kuna ganin ta kun ga matar manya,"

Jameelaah kuwa nan da nan ta hau jin kan ta kamar zai fasa gini dan girma,har wani d'age gira guda ɗaya take yi, zama tayi ta harɗe qafa, sannan ta zaro gudummawar wata atampa mai mugun tsada dan neman suna a gaban qawayen su na layin ta bawa Mamalo,

"Ga gudunmawa ta nan na kawo maki,ko yau ki ke so a d'inka maki ita a layin nan sai an d'inka ta saboda tsadar ta na ga dacewar na kawo maki ita a kai ki gidan miji da ita dangin sa sun san basu saka maki kamar ta ba a lefe dan haka kin ga ba raini zaki kankaro wa kan ki aji, ga wannan a kai ɗinki yanzun nan a kawo mana ita an jima a dinke,"

Shewa wajen ya ɗauka da shi ana yabawa da jinjina wa babbar qawar amarya, wasu kuma suka hau fad'in,

"Ji baqauyiya kamar wadda tazo zanen suna, meye na kawo atampa ana bikin aure a matsayin gudummawa? Ko dan a nuna mana an kawo babbar atampa ne oho? Aikin banza kawai lalle a mazaunai,ai dama shi ɗan talaka bai iya samun arziqi ba sai ya nuna daga geto ya fito,"

Cikin turancin ta na 'yan qaramar sakandire Jameelah ta fara magana ta na yatsina hantsi ta ce.

"What say? Say it loudly mana to hear u, ashe ma kuna jin tsoro na har yanzu, ni yanzu kun san i am not ur mate, dan kun samu ma mun gayyace ku bikin ne amma ba laifin ku bane, qazamai kawai"

Tsit wajen ya yi, saboda da damar su gayu iya gayu an sha shi amma ba boko, ga kyau da iya ɗaukan wanka, amma wasu ko arabin ma babu,ba dan ba su zuwa ba ah ah sai dai kawai idan an je ba a maida hankali a yi karatun da ya kamata har a iya turancin.

(Wasu daga yaran cikin gari haka suke,i repeat wasu ba dika ba, kar a ce na zagi 'yan cikin gari nima ita ce, da damar su sunan an je makaranta ne kawai an b'ata lokaci da kud'in makarantar amma ba a maida hankali a koyi abinda ya dace, haka zaka ga yarinya ta gama secodary school amma ba zata iya yin sentence ɗaya kwakkwara ba da kalmar turanci, na sani turanci ba shi ne ilimi ba amma yana daga cikin abinda idan mutum ya na fahimtar shi to an san ba asarar kud'in makaranta aka yi ba a kan shi,tunda karatun namu na Nigeria da turancin ake yin sa idan baka ji ta ya zaka fahimta? Dole sai an fassara maka zuwa yaren ka sannan ka gane me ake koyarwar, gashi da damar maza ba su cika son zuwa islamiyya ba da sun je na ɗan shekaru kafin su balaga shikenan suna balaga ake neman wasun su a rasa a islamiyya, dan haka mata musamman na cikin gari dan Allah mu dage da neman ilimi mu karya record ɗin da aka yi mana mara kyau mu bawa mutane mamaki da kunya akan tambarin da akai mana na rashin ilimin addini da zamani)


Ta na gama zuba masu rashin kirkin da ta ga dama ta miqe ta shiga d'akin su suka gaisa da Ramai, ta bata kayan da ta deb'o mata da kuɗi, sannan ta bata na baban su ta kuma jaddada wa Ramai akan ta bawa Baban nasu dan ta san halin ta, in ma bata bashi ba zata kira shi ta faɗa masa ta bata kuɗi ta bashi, tsaki Ramai ta yi ta hau masifar dan za a bata abu shine sai an yi mata rashin mutunci,Jameelah bata bi ta kan ta ba ta yakice mayafi da jakar ta ta shige cikin 'yan biki aka ci gaba da shagali da ita.

Biki ake ta sha ana tiqar rawa a ɗan tsukukun lungun su Jameelah duk da cewar ango ya hana amma sai da Jameelaa tai uwa tai makarb'iya tasa yaran layin suka samo redio da sipiku manya aka dasa, Bukar da abokan sa ne suke kula da kid'an har magariba ana nan ana abu ɗaya,inda Hajiya Jameelah ta dinga liqa kuɗi ta na taka rawa fili ya zama kamar dan ita aka buɗe shi.

Wayar Jameelaah ce ta fara ruri tana dubawa taga Umar ne, da sauri ta fita daga filin rawar ta faɗa soron gidan su ta amsa wayar, umarni ya bata akan ta fito za suje wani waje daga nan sai su wuce gida, in yaso gobe ta dawo a ci gaba da bikin da ita zai ma raka ta har kai amarya.

Ta ji dad'in hakan kuwa sosai dan kuwa zai qara d'aga ajin ta a wajen mutanen layin su, qawayen ta zasu ga mijin ta kyakkyawa na nuna wa sa'a ga kuma kuɗi ya na da su masu gidan rana,gida ta shiga a guje ta hau tattara kayan ta, cikin sauri ta ce wa Ramai,

"Ramai zan tafi yazo yana jirana a waje,"

"Wai yanzu yarinyar nan ba zaki duba roqona ba da nake ta yi maki na tsahon shekara biyu, dibe ki ki ga yanda kika sauya kin yi jajawur dake kin yi bulbul gwanin sha'awa amma mu muna nan muna ci gaba da dirzar wahala, kin kasa koda sama mana gidan haya ne mu tashi anan mu koma can mu huta da wannan muguwar rayuwa?"

Shigowar Baba kenan daga wajen aikin sa, duk da be so dawowa gidan ba a wannan lokacin duba da yanayi ne na biki mata za su cika wajen to amma yunwa yake ji ba shi da kud'in siyan abincin sayarwa a waje Ramai kuma bata yi hankalin aika masa koda abincin biki bane balle wanda ya bayar a dafa da gumin sa,cikin takaicin jin maganar Ramai ya ce,

"Wai Ramai yaushe zaki yi hankali ne dan Allah? Haqqin ta ne nema mana gidan haya dama ko kuma haqqi na ne a matsayina na mijin ki kuma uban yaran ki?nace banda niyyar tashi anan yanzu saboda banda halin kama wani da ya fi wannan dole ne sai kin yi rayuwar jin daɗi a lokacin da Allah bai nufa ba?"

Cikin d'aure fuska Ramai tace,

"A gaskiya kana shiga haqqina da yawa malam to ni na gaji da irin wannan muguwar rayuwar hakuri na ya gaza, haba ! gida sai kace na gado, tin kan a haife ta muke nan kowa a nan ya sanni, ba zamu samu mu sauya rayuwa ba, ana ta mutuwa sai mu zauna bamu mori duniya ba, qiyamar ma baka da tabbas,"

"In har kina bauta ma Allah da gaskiya, kina kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login