Showing 111001 words to 114000 words out of 118783 words
kayi ne, ina tsoron kar nima wataran kamin haka in ka min haka ina zan sa kaina"
Sai ta sake fashewa da wani mummunan kukan,rikicewa yayi sosai da sosai ya manna ta da qirjin shi yana bubbuga bayan ta alamar tayi hakuri ta daina kuka, shiruuu ya biyo baya na wasu mintuna, can ya gyara murya yace,
"Yanzu ki sanar dani me kike ganin za ayi akan hakan? Inshaa Allahu zan yi maki,"
"Indai kayi alqawarin zaka sauya yanayin zaman ka da matan ka da yaran ka, ba abinda zai hana nima na yi maka alqawarin baka da kuma yi maka dik abinda kake so, indai baifi qarfina ba,"
"Inshaa Allahu na yi maki alqawarin gyarawa, amma yaran ne in ka sake masu raini zai shiga tsakanin ka da su matan ma haka "
"In faɗa maka me yasa zasu raina ka ba zaka ji haushi na ba kuna baza ka d'au hakan a matsayin zagi ko cin fuska ba?"
"Habaa ai ba wannan a tsakanin mu, na tabbata Jameelaah kin fi qarfin aure na ko ta wacce hanya, amma kika hakura kika aure ni, ni kuwa meye ba zan yarda dashi ba indai bai saɓawa Allah ba,"
"Kaga na farko d'aure ma yaran ka da kake baka jansu a jiki baka wasa da su shi zai sa su zama suna aikata abubuwa marasa kyau a bayan idon ka kuma su dinga tsoron ka a gaban ka, sannan matan ka da kake sakarwa cefane wataran har da awo raini zai iya shiga a bayan idon ka su dinga zagin ka, sannan a hankali su daina son ka, na tabbata kuwa kana son su su dikan su, (gyada kai yayi) to ka gani, sannan rashin zama kuyi hira zai dinga nesanta jka da iyalin ka, mu mata muna son ana hira damu, ana jin matsalar mu, ko ba za a biya mana buqatar ba ayi mana alqawarin inshaa Allahu in Allah ya hore za a yi mana, to zaka sami mace tana girmama ka, sanda ka samu in ka mata abu zaka ga girma da qimar ka da kuma darajar ka ta d'agu a wajen ta, ka sani maqo baya daga cikin halin Rasulullah,Annabi yana wadata iyalin shi da abinda yake da shi,abinda bai dashi tinda sun san samun shi da rashn shi basu damuwa, kar na cika ka da surutu dan ni ɗin ba wata malama bace ka fini sani, kawai ka gwada sauyawa akan kan ka zaka ga me nake nufi, sanda iyalin ka suka fara nuna maka so kamar su had'iye ka, sai dai kishi na zai qaru fa in aka janye min kai"
Saqala hannayen ta tayi a wuyan shi ta rungume shi, tana murmushi qasa-qasa, shiru yayi yana ta bitar maganganun da ta yi masa, tabbas maganar yarinyar akwai qamshin gaskiya a ciki, yanayin sana'ar su ɗaya da Malam Jameel sai dai shi shago ma gare shi saboda ya fi su samu sosai, wasu masu gyaran ma har suna zuwa wajen shi ana siyan kayan gyara, amma in ya samu kud'in shi sai dai yaci daɗi shi kaɗai, sai sanda akai kasuwa sosai yayi awo su kuma matan su ji dana cefane. In ya qare kuwa baida kuɗi sai dai su nema da kan su, cikin murya mau natsuwa yace mata,
"Zan duba maganar ki, ki kwantar da hankalin ki ba mai janye ni, ni naki ne har abada"
Sunne kai tayi dan taji kunya, fita yayi ya deb'i ruwan wanka yayi wanka, rabon dayayi wanka sau uku a jere a haka ya manta, tin kafin yayi auren fari.
(Matsalar shi kenan daga uwargida aka faro ta, itace bata tafi dashi yanda ya kamata ba har mai bi mata ta ɗora daga inda ta tarar)
Yana komawa d'akin ya shirya ya ce mata zai leqa kasuwa akwai abinda zai yi, rakashi tayi har bakin qofa tana d'aga masa hannu ya wuce ita kuma ta koma ciki,a tsakar gida ta tadda mero,
"Ohhhni Mero yau naji iyayi iya reto kad'a gado ba miji, ai na zaci tare zasu tafi kasuwar fa Abu,irin wannan kitifi haka?"
Murmushi Jameelaah kawai tayi ta wuce d'akin ta,a ranta ta na ayyana,
'Lallai ruwa ya daki tsohon zakara, in ba dan haka ba har kun faɗan rashin kunya ni?'
Farantai ta d'iba ta d'ebi kayan gara ta zuba dai-dai, ta kuma d'iban wasu a farantai bibbiyu suma ta zuba dai-dai, ta ɗauka ta fita sallama ta yi masu, idon su akan kayan garan Mero me habaici ji kake ta yi difff bakin nan ya mace murus, durgusawa tayi kaɗan ta gaida Abu, ba yabo ba fallasa ta amsa mata,
"Babar Hajjo ga wannan naki ne, wannan na yara su raba ba yawa ayi hakuri da shi,"
Amsa tayi tace
"To an gode, Allah yayi albarka,"
"Ameen"
"Babar Zara'u ga naki gana su Zara'u a basu na sune ba yawa,"
"An gode,"
Miqewa tayi ta koma d'aki yaran su da basu zuwa makaranta suka yo caaa a basu kason su, nan suka karkasa aka aje na sauran yaran da basu nan suka boye masu, sai aka bawa wanda suke gida kuma nasu kason.
Saida ta gama gyara d'akin ta sannan ta yi shirin wanka, wanke band'akin tayi tass sannan ta shiga wankan ta fito, ta shirya cikin wata shadda da tazo da ita daga gida ,ta ware wasu daga cikin kayan ta da zasuyi wa 'yan matan gidan ta aje a gefe sai sun dawo zata siye su da kyutatawa, ta haka zata siye manyan su kuma su taimaka mata da qannen su.
(Wa ya tuna gidan su Umaimah yanda yarinyar nan Jameelah ta dinga zuba mulki? Hummm ka ji tsoron Allah bawa ka zauna lafiya wallahi)
Tsakar gida taje ta saka kujerar ta ta zauna sai qamshi take zubawa, ga kuma uban kyaun da ta yi iyayen suna aiki suna kallon ta,
"Akwai aikin da zan taya ku da shi ne Babar Hajjo? Zaman shirun ba daɗi,"
"Kar ki ce baqar magana nake miki wato ina mamakin abubuwan da kika yi yanzu Jameelaah, saboda ni dai kin san na san ki na san kuma wacece Ramai, kuma na san dik ba haka kike ba a da, ko zaman zawarci ne ya koya maki hankali?"
Jameelaah bata ji daɗin tambayar nan ba amma ta san ita ta jawa kan ta, tinda ita ta b'ata kan ta tin farko,dan haka cikin bata tabbacin ta shiryu tace,
"Lallai a da ban zama daga cikin yaran kirki ba, amma kowa na samun dama ta biyu a rayuwar shi, ruwan mutun ne ya gyara Allah ya dafa masa,in kuma ya samu dama ta biyu ya sake jefa kan shi ga halaka,sai Allah ya barshi da iyawar shi da yake ganin ya iya,"
Shiru suka yi gaba dayan su nan ta miqa mata gyaran wake tace ta taya ta, tana cikin gyarawa ya Malam Tsalha ya shigo tare da wasu yaran a bayan shi, sai shigo da kayan abinci ake yi, dik da rabi-rabin buhu ne amma ba a taɓa yin hakan ba a gidan,abincin sun haɗa da dangin su ; shinkafa, masara, gero, wake, kwalin taliya, kayan su maggi da barkono da mai, sai sabulan wanka dana wanki da omo.
"Wannan fa daga ina Tsalha?"
"Naku ne kowa in ranar girkin ta ya zo sai ta d'iba a girka dan Allah banda almubazzaranci,
Ke Abu da Mero ku samen a dakin Abu ke kuma ki je ki karya, dan da ganin ki har yanzu baki ci komai ba,"
Cike da matsanancin mamaki matan ke bin shi da kallo, ledar da ta rage a hannun shi ya miqawa yaran yace,
"Ku raba harda 'yan makaranta,Allah yayi muku albarka, ya hore kuma a sanya ku a makaranta"
A tsorace suka amsa ya kai hannu zai shafa kan yaron Mero,yaro ya yi saurin kauda kai ya zaci mazge shi za ai, murmushi yayi ya san watarana zasu saba ne amma sai a hankali.
Jameelaah kuwa ta ji daɗi sosai da ya ɗauki gyaran da tayi masa da wuri, sai yanzu take ganin batai gaggawar neman gyara masa iyali ba kuwa, daga zuwa sai gyare-gyare kamar kafinta?
Dan ganin ya yi sanyi sai suka wani tsaitsaya a tsaye ba ladabi suna jiran suji me zaice, tinda suke bai taba tara su ba in ba sanadin rabon faɗa ba,
"Na kira ku ne saboda ina son na baku haƙuri akan irin zaman da muka yi a baya, ban taba kula ina saɓa maku ba, kuma ina saɓawa Allah ba sai yanzu da yarinyarnan ta nusar dani, bana kyauta maku na sani, ku min hakuri inshaa Allahu daga yau komai ya qare ya kuma wuce, zaman jahilci da muka yi a baya ba za a maimaita shi ba, ina fatan zaku bani had'in kai?"
Jikin su ne dik ya mace samun waje sukai suka zauna, suna jin kunyar abubuwan da sukai ta aikatawa.
"Ka yafe mana muma Baban Hajjo lallai zuwan yarinyar nan alkhairi ne a wajen mu baki ɗaya Allah ya yafe mana"
"Ameen sai ku gyara sosai, in ba haka ba ta kwace maku ni, dan dai kunga yanda take ɗaukan wanka da burushi ga kuma uwa uba qamshi,"
"Tabdijam ai mu mutu ka raba ne mu da kai takalmin kaza ba,ba wadda zata kwace mana kai"
Nan sukai ta raha da hirar da suka dad'e basu yi ba.
*********************
Bayan dogon bincike Sapnah ta gano ina ne gidan su Jameelaah, dan haka shiryawa tayi ta d'ebi 'yan kayan Humairah, ta qudurta ko Umar zai yi faɗa sai ta kai ta wajen mahaifiyar ta sun ga juna, itama taji daɗi a ran ta, ta san dik inda take tana kewar d'iyarta rashin ta a gare ta ya na damun ta...............
*Na rantse ba ruwana dik abinda Ummaru ya maki no my water insayiz tammm*
[09/09, 10:39 am] Aunty Hameeda: 💅🏼 *MAZAUNA GIDA* 💅🏼
*WRITTEN BY HAERMEEBRAERH*
Page 49:
Hankalin ta a tashe yake sosai dan bata san me zai je ya zo ba,amma ta riga ta qurdurta ma ran ta yau sai ta kai Humairah wajen Jamewelaah sai dai a yi wadda za a yi haba, koma meye ya faru da su a baya Jameelaah is her biological mother bai kamata ya datse alaqar dake tsakanin ta da 'yarta ba, a qalla ko da hutu ne ana kai ta musamman yanzu da yarinyar tai wayo take jin maganganu wajen yaran maqota da 'yan uwa tinda sunyi zama da mahaifiyar ta.
Tinawa tayi da tambayar da yarinyar ta yi mata a daren jiya bayan ta dawo daga maqotan su kai musu abinci, dan indai suka yi girki sukan kai masu musamman wanda ta san qamshin shi ya karade unguwa sai ta zuba komai kashin shi Humairah ta miqa wa moqota dan fidda haqqin maqotaka.
'Ammi wai dama ashe inada wata Maman Inji su Laure,?'
'Ohhh ni duniya, yanzu daga shigar ki miqa masu abincin nan har sun faɗa mki wannan maganar?
Tabbas kina da wata mamar itace ta haife ki kuma, amma ta koma gidan su itama, watarana zan kai ki ku ga juna inshaa Allahu,'
'Da izinin wa za a je ganin nata?"
Kama hannun shi tayi dan kar yayi b'arin baki a gaban yarinyar wanda har abada Humirah zata na ganin baqin shi, domin kuwa Uwa Uwace koda kuwa mahaukaciya ce.
'Me yasa zaki hana ni yin magana? Ai gwanda ta san wace irin uwa gare ta'
'Lallai kuwa daka zubar da qima da mutuncin ka gaban d'iyar ka har abada wai ni meke damun ka ne? Kai da mahaifiyar ta ku ka samu sab'ani fa ba da ita ba, ita bata san sanda kuka yi cikin ta kuka haife ta ba, da kun san zaku rabu har ya zamar mata tabo da baku haife ta ba, wannan shine sak abinda d'iyar ka zata iya faɗa maka in kanuna tsanar mahaifiyar ta a gaban ta, kar kace bazata iya ba,itama 'yar zamani ce, sannan kuma kai ɗin kai ne sanadin kawo ta duniyar da matar da ka tsana a yanzu, so ba ruwan ta da matsalar ku, wannan shawarata kenan in kaji ka ɗauka ta yi maka amfani a gaba,'
Umar shiru yayi, kamar ba zai ce komai ba,daga baya kuma ya ce,
'Ba za ta je wajen ta ba a yanzu har sai ta mallaki hankalin kan ta,taje da qafar ta a lokacin'
'Yarinyar da ta kai shekara goma ita ce bata mallaki hankalin kan ta ba?yara nawa kamar ta suke zuwa dik inda suka ga dama,ka diba ka gani yanda mutane ke faɗa mata labarai kala-kala na qarya da gaskiya akan mahaifiyar ta baka tunanin lokaci ya yi da za ka manta da baya ka fuskanci gaba? Shekarun fa da yawa ba jiya abun nan ya faru ba ba kuma shekaran jiya ba,amma a gaskiya Abbahn Humairah ka bani mamaki, ka ban mamaki, ashe kai baka yafiya?'
Rintse idon ta tayi a sanda ta tina yanda ta fita tana kuka daga d'akin amma ko bin ta bai yi ba dan ya lallashe ta ko ya bata hakuri,yau kuwa labarin da Humairah ta kai mata ance akan mahaifiyar ta shine dalilin da ya sa zata kaita dan ta tabbatar mata da kwanciyar hankali a ran ta, kuma ta gane me take faɗa mata akan mutane, in dai zaka bi ta maganar su ba zaka yi huld'a da kowa ba, saboda za a kushe mutum ne according to yanda aka tsane shi.
A qofar gidan su Jameelaah tayi parking ɗin kyakkyawar motar ta da Umar ya mallaka mata a ranar zagayowar shekarar haihuwar ta, dan kuwa yanzu likafa ta ci gaba ko gidan su ma da suke ciki Umar ya siye filin gefen shi ya qara faɗin shi ya sai mata mota ya kuma sayi wadda za a dinga kai Humairah makaranta da ita, arziqi sai shukran,Sapnah har yanzu bata samu rabo ba, sai b'ari da tayi sau biyu.
Buɗe qofar motar suka yi tare da ɗaukan kayan sawa na Humairah da suka deb'o,suka nufi gidan da ya sha fenti sakamakon bikin 'yan matan gidan da akai wata ɗaya daya wuce.
Jameelaah na kwashe abinci tana rabawa yaran na miqawa kowa nashi, Abu da Mero na zaune a tabarma babba suna jiran ta gama su ci nasu, kowaccen su ta sha gayun ta dai-dai iyawa da kuma wadatar ta, gaba ɗaya sun zama 'yan gayu sun sauya rayuwar da suke yi a baya mara kyau mai qazanta.
Sallamar su Humairah ne ya sa Jameelaah d'agawa da sauri dan kuwa har abada bazata manta da wannan muryar ba miqewa tayi tsaye sannan ta ambaci sunan ta cikin mamaki,
"Sapnah?"
"Na'am, Jameelaah,"
Maida kallon ta tayi gefen Sapnah ta ga 'yar matashiyar yarinyar da take kyautata zaton Humairahn ta ce,dan kuwa ko a ina ne zata iya gane fuskar gudan jinin ta dik da jimawar da suka yi basu haɗu ba, a ganin Jameelah girma kawai tayi amma kamannin ta na nan tun na yarinta, idanun ta ne suka tara kwalla mai mugun zafi, Sapnah ce ta tura Humairah gaban Jameelah da niyyar taje wajen Jameelaahn, amma sai ta koma bayan Sapnah sannan ta kama hanyar fita tace,
"Ammi muje kawai na gan ta na fasa yin hutun anan,dama dan saboda gaba kar mu haɗu a hanya na kasa gane wacece ta haife ni ko kuma har ɗayan mu ya mutu bai ga ɗaya ba shi yasa na matsu a kawo ni na gan ta"
Da sauri Jameelaah ta tsallake kwanukan dake a gaban ta ta bi Humairah da gudu ta baya ta jata jikin ta ta rungumeta tana kuka sosai, Humairah ma kukan take yi amma taqi yarda ta juya su haɗa ido da mahaifiyar tata da ta nuna halin ko in kula da rayuwar ta,ba dan Allah ya haɗa ta da matar uba mai kirki kamar Sapnah ba da shikenan haka zata watsar da rayuwar ta kamar ba ita ta haife ta ba? Kome ya faru tsakanin ta da mahaifin ta be kamata ta ɗauke qafa a cikin rayuwar ta ba, tana jin son Mahaifiyar ta amma tana jin haushin barin ta da tayi ko sau ɗaya bata taba neman ta ba bata waiwayi rayuwar ta ta ji shin tana lafiya? Ana kyautata mata ko kuma tana zaman qunci a hannun matar uba? Cikin kuka da sarqewar murya Jameeelah ke magana,
"Ki yi hakuri ki juyo ki kalli mahaifiyar ki Humairah, na san ban kyauta ba, shekaru masu yawa sun gushe amma na kasa fuskantar ki balle mahaifin ki, ina da babban tabo a zuciya ta, da jiki na, ina jin kunyar fuskantar mahaifin ki na ce ya bani ke ko da sau ɗaya ne mu kasance a tare, sannan naji labarin yanda Sapnah ke kula dake kamar ita ta haife ki, na san baki da maraicin Uwa, beside ko ina nan bana jin ina da cikakkiyar tarbiyyr da zan baki kamar wannan da Sapnah ke baki, na sani na yi ilimin addini mai tarin yawa amma ban tsaya na yi amfani da shi ba ta hanyar da ya dace, dan Allah Humairah ki yafe wa wannan gafalalliya kuma mai tarin zunubin mahaifiyar taki,"
Da sauri Humairah ta qanqame ta tana kuka,Sapnah kuwa sai lallashin su take yi dan itama sun sanya ta kukan.
"Humairah is time to go home indai har ba zaki zauna anan ɗin ba, coz ur dad is on his way back home yanzu bana son ya san mun fita bai sani ba,sanda kika shirya zama anan ɗin watarana sai mu dawo,"
Da sauri Jameelaah ta kalle Sapnah after all this years bai yafe mata ba dama? Lallai tana da aiki a gaban ta, ko shi yasa har yanzu bata samu rabon aure ba? Allah ya jarabce ta da tsananin son haihuwa, amma bai ba ta ba, dama a kullum tana zargin kan ta akan abubuwan da ta aikata a baya.
Share hawayen ta yi sannan ta shiga d'akin ta ta deb'o wa Humairah dik wani abu data ke da shi wanda ta san yarinya kamar ta zata buqata ta miqa masu, zuciyar ta ta dake sosai.
"Ga wannan maza ku koma gida, Sapnah kar ki qara fita bada izinin mijin ki ba rayuwata babban darasi ne ga kowacce mace, inshaa Allahu da kaina zan zo na bashi haƙuri, har sai ya yafe min zan daina zuwa, kin san dai illar fita ba da izinin miji ba, ko ni na ishe ki ishara, mu mata MAZAUNA GIDA ne ba masu yawo ba izinin miji bane"
Humairah na kuka haka ma Sapnah a haka ta sa yarinyar a mota suka wuce, Jameelaah na soro sai