Showing 51001 words to 54000 words out of 118783 words

Chapter 18 - MAZAUNA GIDA COMPLETE By HAERMEEBRAEH.txt

26 Oct 2025

643

din nasu a gajiye, dan kuwa bayan sun gama komai aika kayan gida 9ja suka yi, suka kutsa cikin garin dan kashe qyayar idon su.

Ishaaq yayi booking ganin likita a gobe, sannan a goben ne yake son ya kai ta Taaj Mahaal, shi ko sanin inane ma wajen bai ba, ita kuwa saboda kallo ta matsu ta je ta bada labari.

Yau ma Ishaaq ya qara ma Hauwaa karatu akan na jiya, Hauwaa fa ta gama gane halal tafi haram alfanu, Ishaaq kuwa ya gama gane ashe da cutar kan shi ya dinga yi bayan cutar da Hauwaan.

Ishaq ne gaban likita yana masa bayanin komai, likita na rubucewa, daga baya ya rubuta masa magunguna da shawarwarin abubuwan da suka kamata ya dinga yi.

A reception ya same ta tana ta danna waya, tana buɗe sabbin account na social net, dan ta rufe na da ta kuma sauya suna daga sunan da aka santa da shi a da,  tana ganin shi ta tashi suka tafi, Hauwaa ta dau hotuna kala-kala a Taaj Mahal, taji daɗi sosai, Ishaaq sai kallon farin cikin ta yake, bai taɓa jin daɗin tafiya irin wannan ba, ashe da tauye kan shi yake yi.

Yau su Hauwaa zasu bar India a wuce qasa mai tsarki dan yin umra.

Hauwaa sai kuka take dan bata zaci zata wannan qasa nan kusa ba duba da yanda mijin nata bai taba zuwa da ita ko ina ba.

Sai lallashin ta yake yana jin ba daɗi a ranshi dan ya san shine silar cire mata ran zuwa duk da cewa ya fi qarfin kud'in da zai kai ta makkan.

Sanda ta ganta gata ga d'akin Allah kuwa a guje ta qarasa ta qanqame ka'aba kamar za a hana ta tab'awa, tayi kuka ta kuma har sai da taji ta kasa kokawa bayan ta gama umarar tadika ta samu waje ta yi nafila raka'a biyu kamar yanda ake yi bayan kammala umara ta hau addu'a sosai tin ina iya saurara a tsaye har sai da na zauna,basu jima a makka ba suka wuce madina sai da suka yi sati ɗaya sannan suka tattara nasu ya nasu dan komawa zuwa gida.

Haroon sai tsokanar su yake yi wai sun sauya gaba ɗaya kamar wasu turawa.

**********************

"Ba zai taba yu wa na bar wannan cikin ba ina fama da karatu, ga shi da na haihu na san dik wannan kyaun jikin nawa sai dai ya zama labari,"

"Me kike nufin zaki yi to?"

"Ina nifin ka taimaka ka zubar min da cikin nan inna kammala karatu sai na haifa maka kantin kwari ma in kana so, dan Allah yah Umar ka tausaya min,"

Kawai sai ta sanya masa kuka, Umar jikin shi dik ya mutu, ya rasa ma tinanin da zai, shin biye mata zai yi ko kuma ya zai yi mata? Ga kukan da take yi masa ya na jin shi har tsakiyar zuciyar shi, baya son ganin koda ɓacin ran ta ne balle hawayen ta.

Ganin halin da ya shiga ne ya sanya ta sake rikicewa da sabon kuka, har tana tari da k'warewa, tare da dafe gefen zuciyar ta ta durqushe a gaban shi tsabar makirci irin na Jameelah.

Umar cikin damuwa mai tsanani ya d'ago ta ya rungume idon shi na zubda hawaye ya ce............


*Thanks to every parson that commented on this novel,ina jin daɗi, ina jin daɗi, ina jin daɗi sosai idan ina karanta comments ɗin ku, Allah ya sa saqona na isa inda ya dace fiye da abinda na ji kuma nake gani a comments din ku, Allah ya shiryar damu dika ya tabbatar damu akan daidai,Allah ya yafe mana kurakuren mu, Ameen*
[11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻   MAZAUNA GIDA  💅🏻










WRITTEN BY HAERMEEBRAERH









PAGE 23:








"My love me kike faɗa ne haka? Bari in tambaye ki, shin waye namijin da ki ke son kasancewa da shi har qarshen rayuwar ki?"

"Kaine😏"

"To me yasa dan kina ɗauke da cikin da nine sanadin samuwar shi kike son zubar dashi? Kin taɓa jin na yi wa halittar ki kushe? "

"A'a"

"To yanzu zan maki wani alqawari, ni Umar na yi maki alqawari ba zan taɓa rabuwa da ke ba saboda lalacewar halittar ki ko kuma rashin ilimin boko mai zurfi ko wata nakasa ko tawaya da zata same ki anan gaba ke har abada ma,ni Umar ina tare da ke ne saboda Allah da son da nake yi maki, dik randa kika ga na rabu da ke to kin saɓawa Allah ne, ko kin yi abinda yake mummuma ainun, wanda na san ba zaki taɓa yin hakan ba,"

Nan da nan idon ta ya yi qifi-qifi ta hau sosa hanci, sai taji bata son a ja maganar ma saboda kar kuma a fara 'yar tone-tone.

Lallab'a ta Umar yayi tayi, tana masa shagwab'ar iya shege har daga qarshe ta nuna masa magana ta wuce ba zata sake tado ta ba.

**********************

Kwanci tashi asarar mai rai, yanzu cikin Jameelaa ya kai wata huɗu,a cikin watannin nan huɗu sau ɗaya ta yarda ta haɗu da Mum, Umaimah ba yanda bata yi da Jameelah ba akan su yi jigilar bikin ta tare amma taqi, ko sanda su Aunty Hauwaa suka kai lefe qememe taqi zuwa, wai bata da lafiya  labarin cikin ta ya baza 'yan uwa da abokan arziqi, tanadi kuwa tini ta fara yi dan yin suna na gararin da ba a taɓa irin shi ba a lungun su,Mum kuwa na ta murna zata samu jika dik tinanin ta ya bata cewa Jameelaa kunyar ta take ji ta ganta da ciki shi yake hanata zuwa inda suke, in tayi wannan tinanin sai tayi murmushi ta ji daɗin yin dace da surukar kirki irin Jameelah da ta yi.

Mamalo kuwa na ganin fi'ili kala-kala dan kuwa kusan koda yaushe Jameelah na hanyar zuwa gidan ta,qaryar kuwa da ta d'ingimo za a yi da sunan nan ba qarama bace, qawayen ta na social media dik sun san tana ɗauke da ciki ta kuma sanar da su irin shirin sunan da zata yi, dan haka dik wanda suke a garin Kano sun yi mata alqawarin zuwa sunan, qawayen ta na makaranta yaran masu kuɗi da 'yan qaryar makaranta dik sai d'igimin zuwan jariri ko Jaririya suke yi.

Bikin Umaimah da Haroon ya taso gadan-gadan, dan kuwa Jibi ne d'aurin aure, Jameelaah uwar bidi'a tinda taji ance ba za ai partyn komai ba ranta yake a b'ace, dan haka ta gama shirya qaryar da zata yi ba zata je bikin ba sai ran kai amarya, ranar kuwa zata kasance kusa da Umaimah dan a bata kud'in siyan bakin amarya.

Motar Umar ce ta tsaya a qofar gidan nasu, tana jin qarar kuwa ta d'iba da gudu zuwa d'aki ta kwanta tare da qaqalo kuka ta hau rerawa, tana ta murqususu kamar me jin naquda, sallama ya dinga yi bai ga kowa ba a parlour ba, kwanon da taci soyayyar kaza da lemun da ta tsiyayo a cup na nan ajiye a saman center table, d'ankwalin ta na yashe a qasa, murmushi yayi dan ya san maybe tana d'aki tana bacci, tinda cikin nan ya shiga wata biyar ta daina laulayi sosai sai bacci da yawan cin abinci.

Yana dosar qofar d'akin nashi ya jiyo kukan ta da sauri ya qarasa ciki, ganin ta kwance tana murqususu ne ya sanya shi shiga damuwa duqawa ya yi a gaban ta ya na shafa ta ya ce,

"Subhanallah My love me ke damun ki?"

"Wayyooo Yah Umar zan mutu ciki na ! innalillahi wa inna'ilaihirraji'una ka kiramin Mamana da Babana ka ce su yafe ni ni tawa ta zo qarshe,"

"Plsss my love ki daina irin wannan maganar tell me, me kk ji a jikin naki yanzu haka?"

Nan ta rasa me zata ce masa saboda sam bata yi wannan tunanin ba ma ta fara wannan iya shegen ta jima bata amsa shi ba sai cann cikin kuka ta hau kiran,

"Wayyoo cikina sai motsawa yake yi da qarfi, Yah Umar ɗan nan so  yake ya fasa min ciki na ya fito,"

"Dan Allah ki daina fad'ar haka, baby ne ke juyawa, ba tin rannan na fada maki ba haka zata faru sanda ya fara girma a cikin ki ko kin manta ne?"

"To ni zafi yake yi min, dan Allah na ce a cire ka qi, inna mutu wajen haihuwa fa?"

Kawai sai kukan gaske yazo mata, dan tana tsoron haihuwar da gaske har cikin ran ta,

"Yah Umar please do something"

Umar gaba ɗaya ma ya kasa cewa komai tsabar yanda ta kid'ima shi, a duniya baya qaunar abinda zai ji ance ya rabu da ita ko menene shi,dan haka ya qanqame ta yana shafa bayan ta, yana ajiyar zuciya,ganin haka yasa ta ji daɗi sosai a ran ta hankalin ta ya kwanta ta san ta gama da shi ya gama matowa akan ta ba abinda ba zata aikata masa ba ya shanye,daga baya ya sa ta kwanta a bayan ta ya hau duba cikin nata da kan shi,ya na gamawa ya tabbatar mata da ba ta da wata matsala ita da babyn suna nan cikin qoshin lafiya motsi ya fara yi shiyasa take jin abinda take ji.

Umar ko tsinke bai barta ta taɓa ba sai abinda ya zama dole, sai nan nan yake yi da ita, ga shi a matse take da buqatar shi, amma dan kar ya ce qalaou take haka ta hakura, sai dai taqi sam ya rab'e ta, dan in ya taba ta tana iya aje ciwon nan a gefe ta mamaye shi.


***********************






Tin da safe ta ke shirin zuwa gidan Mum, dan kuwa ta ci aniyar sai an bata kud'in siyan bakin amarya, ta qara a na sunan da ta d'ingimowa kan ta kamar amaryar ce ta sa ta yin sunan kece raini.

"Wai shirin me kike yi ne haka ke da baki gama warkewa ba? inace jiya da yamma nan ki kai ta birgima a qasa kina kuka, sai da na samu ki kai bacci kika samu sauqi"

"Zan je kai amarya ne mana, da ba zan iya ba ai ba zan ce zani ba ko? Ko baka ga alamar na samu sauqi bane?"

Umar shiru yayi saboda ya kula da wani rashin kunya-kunya take yin maganar, ya na tsoron tanka ta cibi ya zama qari.

Waya yayi ma Mum ya ce mata ga Jameelaah nan zuwa a kula da ita dan bata da ishasshiyar lafiya kwana biyu, ta bashi tabbacin zata kula da ita sosai, dan itama bata son ta wahal da ita din.

Sai da ta gama shirin ta tsaf ta fito,ba qaramin kyau tayi ba kuwa kun dai san mutuniyar taku wajen kyau, sai qamshi take zabgawa kanta daya sha gyara sai walqiya yake yi.

Umar na biye da ita da ɗan qaramin mazubin da take zuba ruwan sanyi da jakar ta, ita kuma tana tsaye tana yafa mayafin ta, yafin mayafin da ta yi irin na 'yan mata ta yi, a zuciyar shi baya son hakan amma yasan in yayi magana yanzu cibi zai zama qari dan haka sai ya kulle bakin sa ya yi gum ya kyale ta .

(Irin wannan soyayyar sai ta kai mijin da matar ma dika wuta)
Suna tsaka da kulle gidan suka ji maganar Ramai a bayan su.

"Ikon Allah Jameelaa ina zaku haka? Ko bikin zaki je da wannan zungurin cikin naki?"

"Ramai me ya kawo ki gidana da sassafe haka?"

"Habaa Jameelaa ya zaki na yima mahaifiyar ki tambayar me ya kawo ta gidan ki da sassafe?"
In ji Umar da ya ji maganar tata ta yi masa girma a kunnen shi.

Yaqe tayi ta sosa hancin ta, sai dai ɓacin rai ne kwance a zuciyar ta game da Ramai da ke son rusa mata shirin ta,washe baki ta yi sannan ta ce,

"Ba nufina ke nan ba, ina nufin naji daɗin ganin ta sai dai na yi mamakin ganin tane dan kuwa kamar ta san tana raina,"

"Allah sarki d'iyar albarka, zuwa na yi dama danna sanar dake mahaifin ki ba lafiya gashi can kwance, ruwan batirin babur ya taɓa masa qafa wajen yayi mummunan rauni, kin san kuma yanayin gidan namu a matse d'aki daya, ga band'aki na gidan gandu jiya da yamma ya shiga band'akin dan kama ruwa ya faɗi, shine ciwon ya sake kwab'ewa, nayi ta kiran wayar ki kuma bana samu, shine nace bari na zo na sanar dake abinda ke faruwa a can gida"

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un,"

Umar da Jameelah suka haɗa baki wajen faɗa, sannan Jameelaa ta fara magana cikin damuwa, dan kuwa uban ta na da matsayi mai girma a wajen ta, yanda take son shi bata son Ramai ma haka, soyayya mai tsafta take yi masa, matsala ɗaya zuwa biyu ne ya sa take jin haushin sa wato bai wuce tsananta mata da yake yi ba wajen bata tarbiyya, da kuma rashin wadata su da dukiya da bai yi ba kamar an faɗa mata shi ke azurtawa,wannan dalilan sune suka jawo take jin haushin shi.

"Muje Yah Umar ka kaini na ga babana, na shiga uku ni Jameelah ya Allah ka hore mana iyaye na su samu muhallin k'warai,"

Umar cikin tausayawa ya ɗauke ta ita da Ramai sai gidan su Jameelaah ,Ramai na ta zayyana masu yanda abun ya faru a hanya.

Koda suka isa gidan Baban Jameelaa na qofar gida a zaune a tabarma, ciwon dik ya kwakkwab'o abin tausayi, da alama yana jin jiki, Bukar na gaban shi ya dawo daga makaranta dan kula da shi, dan tinda Jameelaa ta sashi a makaranta, dan ta kare yawa kar a zagi qanin ta da ita kan ta shi kuma ya ji daɗin makarantar sai ya riqe ta da hannu bibbiyu,Bukar ne ya ce,

"Sannu Baba Allah ya baka lafiya Ramai na nan zuwa da Jameelaah taje ta fada mata,"

Murmushin takaici Baban su Jameelah ya yi sannan ya ce,

"In ba rashin hankali ba irin na Ramai ina wannan halin zata tafi fad'awa Jameelah da kan ta ba zata aika ka ba,ta kuwa san yanda zafin abunnan yake? Ji nake kamar ana yankan nama na, zuwa asibiti ba shine yafi mahimmanci ba? Amma saboda bani da kud'in zuwa shi yasa ba zata kai ni ba bayan ta na da kuɗi ta kuma san na san ta na da kud'in,Kaii Allah ka shirya min iyali na,"

Motar su Umar ce ta parker, Jameelaah ta bude ta fita da sauri, ganin qafar Baban nata ya sa ta saki kuka mai qarfi ta je wajen shi da gudu ta tsugguna tare da fad'in,

"Sannu Babana Allah ya baka lafiya, Bukar Yah Umar ku kama shi mu wuce asibiti yanzun nan dan Allah,"

Bayan Umar ya gaishe shi ya yi masa sannu ne shi da Bukar sai suka saka shi a mota, sai sannu umar yake yi masa shi kuma Baban Jameelah yana amsawa, cike da jin nauyin surukin nashi,dan a ganin shi bai dace ya shiga motar Umar ba, babban takaici da mamakin sa bai wuce na yanda Ramai ke qunshe da kuɗi a qugun ta ba amma ta kasa kai shi asibiti har sai ta kirawo taimako,ina soyayyar da take yi masa a matsayin ta na matar shi? Ina tausayi irin na miji da mata da kuma na musulunci?

A hanyar su ta zuwa asibitin kowa ya yi shiru ba ka jin komai sai tashin kukan Jameelaah, Baban ta ne ya kula da Umar kukan Jameelaah na damun shi, Murmushi yayi dan kuwa ya san yanda Umar ke tsananin son Jameelaah baya son ganin damuwar ta, dan haka sai ya ce mata,

" 'Yar baba ke da bakya kuka ai be kamata ki yi kuka mijin ki na gani ba sai ya tsokane ki bayan na warke, ko ki na so ya dinga tsokanar ki da me kukan banza ne? Rabon ki ma da kuka fa ni har na manta, me zai saki kuka kamar wanda na rasa qafa gaba ɗaya? Dan Allah kwantar da hankalin ki, ki yi min addu'a kawai kin ji?"

D'aga kai tayi, Umar kuwa cikin sauri ya ce,

"Dan Allah ki daina kukan nan haka, zaki iya samun ciwon kai, kina jin dai Baba yace he is fine,so please stop crying kin ji?"

Sai jan majina take yi Bukar kuwa na ta qoqarin taya baba riqe qafar kar ya fama ta.

Ramai kuwa sam bata so aka barta a gida ba, taso aje da ita ta ci gaba da cusa qoqon barar ta na  a sai masu gida ko a kama masu wani su ci gaba da hayar, dan kuwa ta matsu su rabu da wannan gidan da ya zame masu kamar na gado.

Tin da aka shiga da Baban wani daki likita da nurses suka hau duba shi, Jameelaa ta lafe a jikin Umar sai matse hawaye take yi, ganin jini da azabar da Baban ta ke sha ya sa ta jin ba daɗi a ran ta sosai, Mum ce tayo wa Umar waya dan tana son ta ji ya taji su shiru basu je ba kamar yanda suka ce,Jameelah ce ta karb'i wayar ta d'aga ta sanya kuka, Umar ne ya amshe wayar shi ya kanga a kunnen shi ya yi sallama, cikin damuwa mum ke tambayar shi ko lafiya ta ji Jameelah na kuka?

"Mahaifin ta ne ya samu hatsari a qafar shi da ruwan batirin babur, shine muka kawo shi asibiti, dan ya fama ciwon wajen ya samu rauni sama da na da, gamu a asibitin ku ma yanzu haka,"

"Subhanallahi, Allah ya sawaqa inshaa Allahu zamu zo duba shi in aka kai amarya, dan ka san yanz ba a kaiwa da dare zuwa 4 zasu iso su d'au amarya daga nan zamu zo da Daddyn ku inshaa Allahu a gaida mai jikin"

Jameelaah dake manne da Umar tana jin maganar kai Amarya ta kid'ime ta raba hankalin ta gida biyu, ga mahaifin ta a asibiti sannan ga kai amarya, wanne zata ɗauka yanzu?




************************





Mamalo ce jingine da Sadeeq sanda ya gama buɗe masu qofa suka shiga gidan nasu sai sannu yake jera mata, a qasan ledar d'akin su ta zube, shima binta yayi ya kwanta a kusa da ita ya dora ta a jikin shi, hannun shi a cikin zanin ta saman marar ta, sai shafawa yake yana murmushi,

"Sannu maman biyu, Allah ya qara lafiya, ya sauke ki lafiya kin ji Fateena?"

Cike da shagwab'a ta ke murje murje a jikin shi, shi kuwa daɗin hakan yake ji, cikin sassauqar murya irin ta marasa lafiya Mamalo ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login