Showing 42001 words to 45000 words out of 118783 words
ba,"
Kuka ta saka mai ban tausayi sannan ta ce,
"Dan Allah kar ka kashe tsaya kaji, dan Allah ni dai ko dan wasa ne ka dawo muyi, yayan ka kwata-kwata bai iya komai ba, bana samun abinda nake nema a wajen shi, da na san yana da qani kamar ka da ba zan taɓa auren shi ba kai zan aura,.....hello....hello...Haroon?"
Shirun da ta ji ne ya tabbatar mata da cewa Haroon ya kashe wayar shi, kuka ta sa mai qarfi tana dukan kan ta da hannun ta, gaskiya ba zata iya zama gida ɗaya da Haroon ba, ko a sauya masa wajen zama, ko ita Ishaaq ya sake ta habaa, ga namiji tana gani amma bai iya tab'uka komai ba ya dinga abu sai kace ba namiji ba, Haroon yafi Ishaaq cikar mazantaka a ido ma.
'Zuciya ta baki yi min adalci ba, yaushe ma kika kamu da sha'awar qanin mijin ki haka? Ko miji na ban taba sha'awa kamar yanda nake ma Haroon ba,ina buqatar taimako indai ina son cimma buri na'
Tinani ta yi tayi har bacci ya kwashe ta a wajen.
Da safe wajen qarfe tara na safe Haroon ya shiga gidan, ta gyara ko ina kamar yanda ta saba, ta sha kwalliya da qananan kaya matsattsu, wandon iya cinyoyin ta sai qaramar vest mai bayyana baya da qirji, bra din data saka ita ce ta rufe mata qirjin sosai, tare da dago su,tin da ya kalle ta mistakenly bai sake kallon inda take ba, wani kallo ta kafe shi da shi kamar itace miji shine macen tace,
"Ga abincin ka nan sanyin idaniya ta"
"Really? Wai ke Hauwaa baki da hankali ne?"
"Hauwaa? Ina ka baro aunty Hauwaan?"
"Mata da dama suke samar wa kan su mutunci, sannan da daman mata suke saida wa kan su mutunci, ke baki da mutuncin da zan kira ki da girmamawa, matsa in ba haka ba dik abinda na maki ke kika jawo, dan kuwa zan maki dukan da Yah ba zai iya gane ki ba"
Abincin da ya kai hannu zai ɗauka ta dauke, sam ita bata yi fushi da kalaman shi ba, ta ɗauka da niyyar ya bita daga nan suyi ta zagaye wajen dan ya k'wata, shaidan kuwa daga nan ba abinda ba zai iya kimsa masu ba baki ɗayan su, sai Haroon ya bata mamaki kamar koda yaushe.
Tsaki ya ja mai qarfi ya shiga d'akin shi ya barta riqe da abincin ta a hannu, kayan shi ya d'iba masu ɗan yawa ya saka dik wani abu da zai buqata a jakar ya fita, a bakin qofar d'akin shi suka yi karo da Hauwaa, yi ta yi kamar zata faɗi, a zaton ta ya taro ta amma ko kula ta Haroon bai yi ba, aiko sai ji ya yi ta faɗa jikin shi, zuciya ta kai masa ko ina saboda haushi ji yake yi kamar ya zage damtse ya naɗa mata na jaki, amma ya hakura yawurga ta gefe ya fice daga gidan, Hauwaa kuka ta saka mai cin rai, a ranta ta na ayyana,
'Na zaci hakan da na yi zai taimaka min amma inaa, sai ma nesanta ni da yayi da shi, ina zashi oho? Gaskiya ba zan iya rayuwar quncinnan ba, dole ne Ishaaq yayi abu ɗaya acikin biyu, ko ya nemi maganin da zai zama cikakken namiji kuma ya iya soyayya da faranta min rai, ko kuma ya sakeni,gaskiya ba zan iya zama da shi a haka ba,'
Sosai take kuka kamar wadda akai ma mutuwa, bata san iya lokacin da ta dauka ba a wajen, da kyar ta tashi ta shiga d'aki ta kwanta tana jin wani zazzaɓi na shigar ta.
Kwanan Ishaaq uku kamar yanda ya faɗa wa Haroon zai yi ya dawo ya dawo kuwa, Hauwaa shadda ce a jikin ta ta sha aiki daga sama har qasa kalar purple, an mata aiki da baqin zare da golden,ta kafe dauri mai ban sha'awa, abinci ta dafa kala-kala masu daɗi da kyau a idanun mai kallo, ta san dolen Haroon ya dawo gidan a yau.
Shigo wa yayi cikin qananan kaya wandon nan a d'age kamar ko da yaushe ga gemun nan ya sha taja sai kyalli yake yi, baqin shi mai kyau na ta haskawa da annuri, sallama yayi ya zauna a cikin ɗaya daga kujerun parlourn, Ishaaq ya kalle shi cikin kulawa yace,
"An ce min baka kwana a gida ko zan iya sanin dalili?"
"Barka da safiya Yayah, ai ka bari a gaisa ko?:
"Barka dai,"
"Ya kasuwa? Ina fatan ka gama komai lafiya? Yaushe kayan za su iso?"
Nan da nan hirar kasuwa ta kan kama a tsakanin su, suna cin abinci suna hirar irin riba da kuma ci gaban da kasuwar tasu ke samu,Hauwaa takaici dik ya ishe ta ita taso a yi magana akan Haroon da inda yake tafiya ya kwan yanzu, amma sun tsaya suna wani zancen kasuwancin banza,da qarfi ta aje spoon din ta akan dinning din ta shige d'aki fuuuuu.
Kallo suka bita da shi Ishaaq a tinanin shi ko dan ya share ta ne ya maida hankali akan qanin nashi.
Haroon ne ya ke tinani a ran shi.
'Ta ya zan yi wa Yah magana akan rayuwar auren su? Bana son zargin wani abu ya shiga tsakanin su ya gano me matar shi ke aikatawa akaina,'
Ishaaq ne ya tashi dan tafiya d'aki wajen Hauwaa, Haroon ya tsaida shi.
"Yah ina son dama na yi maka wata magana mai matuqar mahimmanci..."
"Haroon ko za ka iya barin maganar zuwa gobe? Iyali na na da buqata ta yanzu,"
Da sauri-sauri Ishaaq ya wuce ya bi bayan Hauwaa.
"Kashhh da ka tsaya kaji ma me zan ce maka, ko kaje ba burge wannan mara godiyar Allahn za kai ba,"
Ci gaba yayi da shan juice ɗin da ya zuba a glass cup, daga baya ya fita zuwa gidan su Umaimah.
Umaimah ce kwance tana danna wayar ta,dana leqa sai naga ashe karatun qur'ani take abun ta, labban ta da suke ta walqiya sai motsawa suke cikin nutsuwa, kira ne ya shiga wayar, ta qarasa ayar da take sannan ta dauka cike da murmushi,
'Ko me zai ce min oho? '
Sallama sukai ma juna tare da gaisuwa, sannan ya sanar da ita yana qofar gidan su, in ba damuwa yana son magana da ita,
"Magana? Akan menene haka?"
"Magana ce akan zuciya ta da taki,"
Nan da nan kuwa zuciyar ta ta ta fara tsallen murna, dan kuwa ji tayi kamar ta gan ta a gaban shi, amma ta dake,
"Indai akan zuqatan mu ne ka makaro dan kuwa wani ya riga ka ya ɗauke tawa, ma'assalam"
Kit ta kashe wayar tana ta dariya , cike da d'imaucewa da gigicewa Haroon ya sake kiran ta, qin ɗauka tayi tana ta yi masa dariya,
'Zaka gane kuren ka ne sai ka nemi Dad da kan ka,dan ko arziqin sanar da kai ka neme shi ba zan yi ba,yanda ka wahal da zuciya ta kaima sai taka ta jikkata,'
Qin d'aga wayar shi da ta yi ya sake tabbatar masa da gaskiyar maganar ta, a wajen ya tsugunna sai ga hawaye na fita daga idanun shi.
Dafa shi ya ji anyi ya miqe da sauri yana goge hawayen shi, kiran sallar da yaji ne ya tabbatar masa da lokacin daya ɗauka duqe a wajen ya na zubar hawaye domin kuwa sallar la'asar ake kira,
"Barka da Yamma Alhaji,"
"Barka dai, Malam ya dai ka zauna anan cikin damuwa,"
Sosa kai yayi tare da maida hannun shi ɗaya bayan shi kai da ganin murmushin da yake yi kasan na dole ne, ji suka yi za a shiga sallah, da sauri suka nufi masallacin,
"In an idar ka sameni a gida,"
"Inshaa Allahu,"
Bayan anyi sallah ya je gidan su Umaimah, yana zaune a kujera a harabar gidan Daddyn su ya dawo, katse azkar din da ya keyi ya yi, ya bi bayan shi zuwa ciki,
Sai da Daddy ya shiga ya zauna bai ga Haroon ba ya kwala masa kira, ya tabbata bai shiga bane saboda yana ganin bai kamata ya faɗa gidan mutane ba kai tsaye ba tare da an yi masa izini ba.
Da sallama ya shiga ya samu qasan kujera ya zauna,Daddy yayi yayi ya hau sama amma yaqi saboda girmamawa.
"Malam Haroonaa me ya faru da kai ka tsaya a gate din gidannan kana hawaye? Ina fatan zaka sanar dani ko meye matsalar ka in ina da halin taimakawa na taimaka,"
Haroon ya dad'e yana kame-kame kafin ya bayyana ma Daddy abinda ya sanya shi kuka, murmushi irin na manya yayi, sannan yace,
"Wannan wasan yara ne a tsakanin ku, amma ni dai ban san na yi ma Umaimah miji ba, kar ka damu kaje gida, zan yi magana da ita, in akwai wanda take so mun ji daga wajen ta, in babu zan baka umarnin ku fito inshaa Allahu,"
Zuciyar Haroon tana a tsakanin murna da kuma damuwa,what if tana da wanda take so ba shi ba? What if ba zai samu auren ta ba.
Godiya yayi, sanan yace zai tafi gida, Daddy ya yi ta roqon shi akan ya tsaya ya ci abinci amma yaqi, zuciyar shi gaba ɗaya ba daɗi.
Umaimah na maqale a jikin kitchen tana leqen shi, sai ta ji bata so yanda ta gan shi ba, sannan bata ji daɗi ba data ji Daddy yace ya gan shi yana kuka, ita bata zaci abun zai sanya shi baqin ciki har haka ba, kamar ta d'au waya ta faɗa masa dalilin ta na fad'in hakan amma taqi, iyaka in an tambaye ta ta tabbatar ma da iyayen ta shi take so, shine zaɓin ta ba wani ba.
***********************
Gidan Mamalo gidan haya ne mai ɗauke da d'aki biyu sai band'aki da kitchen, d'aki ɗaya aka sanya mata kayan gado, d'ayan d'akin kuma sai aka sanya kujeru da 'yan kayan kitchen ɗin ta na gayu, sai ledar d'akin ta mai kyau.
Ba laifi dan bata zaci ma zata samu hakan ba Sadeeq shima yayi qoqari ainun, tinda aka kai mamalo Sadeeq yaqi d'aga mata qafa, dan kuwa a daren ya angwance, Mamalo an kai budurci gidam miji lafiya, ansha kukan shagwab'a kala-kala wanda ya ke burge Sadeeq tsabar jin daɗin hakan ya dage sai lallashin ta yake amma taqi daina kukan, cike da nishad'i Sadeeq ya ce,
"Haba masoyiyar Abubakar mai gaskiya, dan Allah ki daina kukan haka ya isa, har fa maqota na iya jiyo ki, taso muje na taya ki ki gyara jikin ki kin ji? Sai muyi bacci inshaa Allahu gobe kika tashi ba zaki ji ciwon komai ba,"
Cikin kuka da shagwab'a tare da wani irin jin kai da taqama da kuma alfaharin ta kai mutuncin ta gidan aure take magana,
"Ni ba zan iya tashi ba,bayan ka gama min abinda kaga dama, tinda su Jameelaa suke zance da Babawo ban taɓa jin ta koka ba, in ba daɗi da take ce min taji ba, amma kai rana ɗaya ka gama yi min rauni, dubi har da jini fa tsabar mugunta,"
Har cikin ranta take jin daɗin kai budurcin ta da ta yi gidan aurenta dan haka take magana kai tsaye hankalin ta kwance zuciyar ta zaune a qirjin ta.
Sadeeq ji ya ke kamar ya tsaga qirjin shi ya saka ta dan tsabar so, shi talaka ne ba shi da kyautar da zai yi mata irin yanda yake jin ana yi wa wasu matan da suka kai budircin su gidan miji,amma yasan abu ɗaya da zai yi mata zuwa biyu. Kama ta yayi ya ɗora ta a jikin shi yana shafa bayan ta da sigar lallashi ya ce,
"Fateemana ! ba abinda zan ce maki sai dai nace Allah ya yi miki albarka, Allah ya qara min son ki sama da wanda nake maki a yanzu Allah kuma ya biya maki dikkan buqatun ki na alkhairi, dole zaki ji zafi kuma dole na ne na maki dik abinda zai sauqaqa maki, kiyi hakuri kin ji? Na maki alqawarin dik abinda kike so indai bai fi qarfi na ba zan maki shi, zan kula dake, zan kare maki dikkan mutuncin ki, kinga amfanin qin amincewa da na yi muyi soyayyar shashanci ko? Yanzu gashi munyi komai cikin nutsuwa da kuma kwanciyar hankali, ba tsoro ba fargaba, ba tinanin wani zai gan mu, babban ribar kuma babu zunubi sai tarin lada,"
Dik abinda yake faɗa yana mata ma'ana a kwakwalwa da zuciyar ta, yanzu ta fahimci dik abinda yake faɗa mata abaya take ganin rashin wayewa ne, sai gashi a dare ɗaya ya gwada mata shi ɗin kwararren ɗan soyayya ne, ba dan zafin da ta ji ba ai irin soyayyar daya gwada mata bata jin ko a india akwai wanda ya fishi iyawa.
Sun dad'e suna ta hira a tsakanin su, yana mata alqawurran jin daɗin da zai bata wanda har cikin ranshi yake faɗan su, dan kuwa bai ɗaukar wa kan shi qarya ba shi a rayuwar shi, iyakar gaskiyar shi yake fada mata.
Daga qarshe ya fita ya kunna risho ya ɗora ruwan zafi ya juye a bokiti, sai da ya tara wanda zai ishe su sannan ya kai masu dana sirkawa band'akin,wanka ya taya ta tayi ya gasa mata jikin ta sosai, sannan ya riqo ta suka koma d'akin su, zama tayi a saman sallaya ya gyara masu gadon su, sannan ya sa suka sake yin nafila, kafin suka yi bacci, Mamalo dik hakan sabon abu ne a wajen ta, in tai sallahr farilla bata ta nafila sai gashi zama da mutumin kirki ta san ta yi nafila a dare ɗaya.
Bayan kwana huɗu da auren su tana ta bacci ya tashi ya yi masu abin karyawa k'wai ne ya soya sai shayi ya dakko bread din daya shigo da shi a daren jiya ya kai d'akin, ragowar kilishin da basu cinye ba ya juye a plate ya rufe, zama yayi a gadon ya tashe ta, tare da mammatsa mata qafafun ta.
Bude ido tayi tana qoqarin komawa baccin ta dan kuwa tunda aka kawo ta Sadeeq yake nuna mata shi fa ɗan soyayya ne dama lokaci yake jira.
"Yi hakuri ki tashi haka, ki wanke bakin ki mu ci abinci, "
Tana jin abinci ta dire a qasa, zama ta yi zata fara ci ya kad'a kai, tare da kama hannun ta ya ce,
"Sai kin wanke baki kinyi sallah sannan mu ci abinci dan kuwa kin makara, na so tashin ki amma na kyale ki ganin irin gajiyar da ki ka yi , taso muje ki yi alwala ko kina so na wanke maki bakin da kaina ne irin na rannan?"
Tinawa ta yi da daren jiya sai kunya ta kama ta ta miqe ba musu, ya ko bi ta da tsokana har waje, shagwab'a ta fara yi masa tana son yin kuka sannan ya yi shiru ya kyale ta, kujera ya ajiye 'yar tsugunno guda biyu, ɗaya tata ɗaya tashi, toothpast ya sa mata a brush yana jiran ta fito ya bata, Mamalo na ciki ta rasa yanda zata yi tace ya tashi daga wajen, dan kuwa tutu take ji sai kaiwa da kawowa take a cikin band'akin, jin motsin da take yi kamar mai tafiya ne ya sa ya buɗe ya leqa ta,gani ya yi ta haɗa zufa sharkaf, sai matse hawaye take yi da sauri ya isa gaban ta ya riqe ta, a tinanin shi can wajen ne ke yi mata zafi har yanzu.
"Sannu kin ji Fateemaa, bari na sanya maki ruwan d'umi,sai ki kama ruwan dashi,ki yafe ni da na san zaki ji zafi haka da ban yi ba dana hakura"
Wata majinar wahala ta sharce, ko kwakkwaran motsi ta kasa yi,fita yake son yi yaji wani irin mugun warin bala'i, Mamalo ta saki wata tusa mai d'anneman wari, kasa shaqa yayi ya fice da sauri daga band'akin yana fita ya shaqi iska mai kyau ya kalli hanyar band'akin, sai a sannan ne ya gane me ke damun ta.
D'aki ya shiga ya zauna, tanaleqawa taga baya nan kuwa ta zage ta dinga zazzage cikin ta, sai da ta gama tass ta fita ta wanke bakinta ta yi alwala, kunya ta hana ta shiga d'akin, tsaye ta yi a bakin qofar, ganin inuwar ta yayi ya kwashe da dariya,
"Fatee na shigo abin ki kowa ma yana yi, nima dana tashi sai da nayi sannan nai alwala nai sallah wai ke yanzu a yanda muka riga muka zama ɗaya har akwai abinda zaki ji kunya ta akai irin haka? Habaa ai an riga da an zama ɗaya Mamalonaaa,"
Kukan shagwab'a ta fara yi har da hawaye, ita bata san wanne irin mutum Allah ya haɗa ta da shi ba, komai daga zuciyar shi yake faɗan shi ba wani boye-boye, ita dai gaskiya yana bata kunya.
Haka rayuwar su mamalo ta ci gaba cikin girmamawa da qauna tare da soyayyar junan su,yanzu ta fahimci menene darajar kai budurci gidan aure lafiya, da kuma me ake kira da asalin soyayya, dan kuwa Sadeeq A ne har ma zuwa Z, a cikin sati ɗaya da kwanaki da suka yi yanzu da shi ta tabbatar da cewa soyayyar aure ita ce dahir.
***********************
Daga makaranta ta dawo ko abinci bata yi ba kan ta fita, tinda ta saba in ta koma daga school ko kafin ta fita mai aiki ke masu abinci acan shi yasa a cikin kwanakin nan da suka yi da Umar a sabon gidan su ko gas bata taɓa kunnawa ba duk abinda take so koda ruwan zafi ne kuwa shi zai dafa mata ya kawo mata har inda take da buqatar shi, jikin ta dik ciwo yake yi mata sai kawai ta zube a kujera bacci mai daɗi ya ɗauke ta, Umar ne ya shiga da sallama yaji shiru gidan, ya na qarasawa parlour ya ganta a zube a kujera da alama a gajiye take, kuma yunwa na damun ta.
Bai tsaya b'ata lokaci ba wajen tub'e kayan shi ya shiga dafa masu abinci, yana cikin girkin ta tashi ko da ta jiyo shi a kitchen kwala masa kira tayi, da sauri Umar ya fito cikin wani ladabin da ban taba ganin ya yi ma mahaifan shi ba, ta ce,
"Kawon ruwa da maganin ciwon kai, kaina ciwo yake yi,"
"Ina dafa mana abinci yanzu ko zaki bari ki ci abinci sai ki sha maganin, kin san magani ba abinci baya ci,"
Harara ta watsa masa kafin ta ce,
"Kai zaka faɗan me zan yi? Ni ban ruwa da maganin ciwon kai dalla na