Showing 75001 words to 78000 words out of 118783 words

Chapter 26 - MAZAUNA GIDA COMPLETE By HAERMEEBRAEH.txt

26 Oct 2025

634

ɗazu ko? To kice ta dawo ta bamu ɗan makulli in yaso ta dawo ku kwana anan"

"Baba ai nima bata zo ba kuma tin safen nake kiran ta naji Bukar shiru dama nace ta turo shi,"

"Ah ah, to ina taje kuma?"

"Ba ta gida ne?"

"Bata gida tin hantsi na aika a kai mata kayan miya bata nan, ina kuma kyautata zaton halin ta data saba ne dana sa qafa na fita itama ta fice, to ina zata je in bata zo nan ba?"

"Ikon Allah, bari nayi ma Abban Humairah waya ya faɗa ma 'yan sanda a fara binciken inda taje, na shiga uku,"

Kuka ta fashe da shi dan kuwa hankalin ta bai kawo komai ba sai ko ta b'ata ne? Ko wajen sabon bokan da tace zata ta tafi ta b'ata a hanya?

"Daina kuka ina zuwa naje tsohon gidan mu ko taje masu ziyara,"

Kashe wayar yayi ya jira saida Bukar ya dawo sannan ya ce ya jira a qofar gidan in yaga ya dad'e bai dawo ba ya je gidan Jameelaa ya kwana, nera dari ya bashi na abun hawa sannan ya tafi.

Shi din ma adaidaita sahu ya hau sai unguwar su ta da.

Ba binciken da bai ba gida-gida amma kowa sai ya ce ai ta dad'e rabon ta da unguwar ma.

Malam Jameel ya fa fara shiga tashin hankali, bai san yana ji da Ramai ba sai yanzu, ada kullum halayyar ta na sa yaji ta fita akan shi, amma rashin ta ya d'aga masa hankali, ko ba komai matar shi ce kuma abar son shi, halayen ta ne abin qi a gare shi.

Gidan Jameelaa ya wuce shima dan ya san Bukar baya gida yanzu, koda yaje ya tadda Bukar na cin abinci, shima zuba masa Jameelaa tayi amma haka ya kasa ci, ruwa kawai ya sha ya yi jigum.

Umar ne yayi sallama ya dawo daga kai ma 'yan sanda qorafin rashin ganin ta da ba ai ba, Malam Jameel ya shiga matsananciyar damuwa a wannan dare, da kyar sukai ta tausar shi har ya samu ya sha tea kawai, Umar da cewa yayi ya kwana anan gidan amma yace inaa zuwa zasu yi su yanke kwad'on su shiga, in yaso an sai wani.

A mota Umar ya maida su shi da Jameelaa wadda sai kuka take tayi, dan bata san wane hali Ramai ke ciki ba.

Umar ma dik ya damu ganin habibiyar shi na kuka.

Sai da aka buge kwad'on suka shiga sannan suka juya, Malam Jameel bai iya kwantawa ba bayan Bukar yayi bacci ya buɗe qofa ya fita, shiga nan fada can haka yayi ta yawo yana tambayar mutane ko sun ga mace mai kama kaza da kaza.

kowa yace masa bai gani ba, zama yayi qofar wani gida yana zubar da hawaye, dare yayi sosai, dan kuwa 12am tayi a lokacin, qoqarin tafiya gida ya ke, wani mutum a babur ya zo shigewa, sauran kadan ya buge shi, kauce masa yayi yana masifa.

"Ku dattijan nan sai ku dinga tafiya akan hanya, dazu mai babur ya bankad'e wata dattijuwa yau,sai wahalar neman dangin ta nake ban samu ba, asibitin da na taimaka na kai ta an hana ni tafiya yanzu ma gudowa na yi, kana son na buge ka na koma cikin wahalar dana baro daga taimako,"

Cikin sauri Malam Jameel ya bi bayan mutumin yana kwala masa kira,

"Malam dan Allah tsaya ya kamannin matar yake, ni ma nan da ka ganni neman mata ta nake yi a ina abun ya faru?"

Ɗan tsayawa mutumin yayi ya juyo, sannan yayi baya kaɗan inda malam jameel yake tsaye, bayanin yanayin matar da inda abun ya faru ya yi wa Malam Jameel.

Sujjada malam Jameel ya koma gefe yayi yana ta godewa Allah,cikin farin ciki ya cewa mutumin,

"Bawan Allah na gode Allah ya biya maka dikkan buqatun ka na alkhairi, yanzu faɗan inda uwar 'ya'yana take mata ta ce, tin rana ta bar gida yau kusan gaba ɗaya neman ta muke"

Faɗa masa inda ya kai ta yayi sannan ya ce dan Allah yaje gare ta, shi kam ya gama taimakon nasu yau ko wajen nemawa iyalin shi abinci bai je ba, Da sauri Malam Jameel ya dakko wayar shi ya kira no Umar, ya sanar da shi har sun fara bacci a parlour, Jameelaa kwance a jikin shi da Humairah a qirjin ta ta ci kuka har tayi bacci.

Ya so sanar ma da Mum din shi amma ta kafe akan bata son kowa ya san ba a ga mahaifiyar ta ba, har sai nan da kawana uku, ko bayan an ganta bata son kowa ya sani, Umar kuwa ko da wasa bai ji yana son sanar ma da kowa ba tunda gimbiyar ta hana.

Ai yana faɗa mata an ga maman ta ta miqe a firgice sauran kadan ta kada Humairah ya riqo ta, da sauri ta saka mayafi suka bar gidan basu zame ko ina ba sai asibiti.

Ramai ta farfaɗo ciki fal yunwa tin shayin bunu na safe da tasha bata ci komai ba, ta sawa ranta shegen kwad'ai za ta gidan Jameelaa taci me daɗi.

Da gudu Jameelaa ta faɗa a jikin ta ta fashe da kuka.

"Ramai na me ya same ki haka? Dan Allah kar ki qara yin nisa ki bar ni inna rasa ki mutuwa zanyi,"

"Gani ai daina kukan kun zo min da abinci? Yunwa nake ji Jameelah tun safe ban ci komai ba"

"Ah ah bamu kawo komai ba, tinda bamu tabbatar ke ce ko bake bace, munzo dai muga wace ce,dik da Baba yace yana kyautata zaton ke ɗin ce ma,"

Kuka Ramai ta fashe da shi,

"Ni kuka ya kama Jameelaah kin ganni nan wata iriyar mahaukaciyar yunwa nake ji qirjina har zafi yake min, ban jima sosai da farkawa ba, ban ma san waya kawo ni nan ba, dan Allah ku taimakan da abinci kar ku rasa ni,"

Umar da Malam Jameel har rige-rige suke dan fita suje shagon dake cikin asibiti su sama mata abin da zata ci.

Koda suka kawo mata fresh milk da biscuit ci ta hau yi kamar wadda ta shekara bata ci ba.

Tausayin ta Jameelaa tai ta ji Malam Jameel kuwa ba mai gane halin da yake ciki, dan kuwa kallon Ramai kawai yake.

Ramai kuwa sai tinanin qaryar da zata shimfid'a masa take tayi amma ta rasa yau dai qaryar ta ta qare.

A nan Malam Jameel ya kwana Jameelaa kuwa suka koma gida da mijin ta hankali ya kwanta, dan tsagewar qashi tayi tinda an mata gyara sai a jira ya warke kuma.

Ramai ta kasa haɗa ido da Baban Jameela, shi kuma ya qi yi mata magana akan abinda ta yi yana zaune saman kujera a haka yayi bacci.

Washe gari Kulu ce ta kawo abinci ita da Umar, Jameelaa ta tashi da ciwon kai saboda rashin ishasshen bacci da bata samu ba, da kuma kukan da tayi.

Ramai an kwashi garar da ake so, nama ta dinga tsama tana ci na kaza da dankalin turawa da akai mata farfesun su, Malam Jameel dik kunya ta kama shi, Umar kuwa tinani yake ko dan ta kwan da yunwa ne yasa take cin abincin haka kamar mayunwaciya.

Kulu kuwa tsaf ta fara gano halayen su, dan haka ta san tsantsar kwad'ayi ne kawai ba wani abu ba.

Satin Ramai biyu a asibitin aka sallame su,randa suka koma kuwa ta sakan kance Baban jameelaa ya manta da abinda tayi, ta sha gayu ta zauna zaman jiran Baban Jameela.

Bashi ya dawo ba sai goman dare, lokacin dik kwalliyar ta goge yana cin abinci ya watsa ruwa ya kwanta a qasa, cikin mamaki da gatsali ta ce masa,

"Sabon salo, wanne irin abu ne haka zaka kwanta a qasa, na dad'e bana gida yau na dawo shine zaka wani kwanta a qasa?"

Ko lashi kan ki bai ce mata ba balle yace ta ci kan ta, tayi maganar tayi surutun ya mata shiru, daga qarshe ma sai minsharin shi ta jiyo yana tashi.

Haka Malam Jameel ya qaurace ma Ramai a d'akin su na tsahon sati ɗaya akan sati biyun baya da ta yi tana jinya kamar yanda islam yace in zaka qaurace ma mace ka qaurace mata a daki, ga ka ga ta amma ka hanata kan ka.

Ramai fa ta jiga ta matuqa gaya ko hirar da suka saba yi basu yi, bayan sallama da amsa gaisuwar ta baya ce mata ta fasa balle yace sauke.

Bukar daga boko yake wucewa islamiyya, dan haka bai wani kula da sauyawar mahaifin nashi ba, musamman da ya zamana shi sukan zauna suyi hira abun su da shi.

Yau dai Ramai tayi alqawarin sauke ma kanta wannan hukunci da ake mata, dan haka Bukar na tafiya makarantar boko ta zube gaban shi ta fashe da kuka, tana neman gafara, bai kula ta ba dan kuwa so yake ya ga ko da gaske ta yi na dama, kukan ta na taba shi, amma haka ya kyale ta ya fita wajen aikin shi.

Ramai fa har ramewa tayi saboda tsakanin ta da Allah bata son fushin mijin ta, abinda bai taɓa yi mata ba kenan a duk tsawon zaman su, wannan hukuncin na shi ya yi mata tsauri,tun da jajayen sawaye ma ba a hukunta ta haka ba sai yanzu?

Da yamma ta dafa masa abincin da ya fi so ta gyara gidan tsaf kamar ba gidan da ta fara b'atawa da qazanta ba, ta saka kayan ta na qarshen adaka, sannan ta kunna turaren wuta a gidan, tana zaune tana jiran dawowar ɗan dattijon mijin ta ko kwantawa yace tayi yau za ta yi ta ba shi hakuri, ba zata iya jure fushin shi na kusan wata biyu ba dan ta horu ainun.

Abinda bata sani ba shine shi kan shi Baban jameela ya gaji da wannan hukuncin da yake yi mata, dama nema yake ta bashi hakuri ya huce taurin kai irin nata ya sa ta dad'e bata bada hakurin ba, wajen masu gasassun kaji yaje ya sai masu 'yar guda daya ya wuce gida da ita.

Ko da ya shiga sauyin da ya gani a gidan ya sa ya sake samun nutsuwa, daya yi wanka ya koma parlour sai yaga an jera masa abinci a sabbin mazubin da ta zo da su tin sunan Humairah, daya buɗe yaga abincin da yake so ne, ji yayi ya yafewa Ramai dik abin da ta yi masa, ci ya yi ya qoshi ya kora da ruwa mai sanyi.

Ramai ce ta shiga da sallama ta durqusa ta fara neman gafara harda kukan ta, dan abun ya gama isar ta ta matsu su daidaita.

"Ramatu ni na yafe maki tin tini, ina hukunta ki akan halayen da kike aikata min ne shekara da shekaru, ban niyyar amsa maki ba, nayi niyyar rama shekarun da kikai kina min abinda kika ga dama nima kafin na amsa ki,"

Zaro ido ta yi ta fara lissafin shekarun auren su, dan in bata manta ba tinda Jameela ta fara girma suka fara samun matsala da shi, in ya hana abu ta kafe shi za ai tsoro taji ya kama ta,

"Habaa Baban su ba za ai haka ba, dan girman Allah ka yafe min, in dai ni ce ba zan sake aikata abinda dik ka hana ba,"



"To shikenan ya wuce ina maki nasiha da kiji tsoron Allah ni ba wai ina hana ki abu bane dan son rai na, ko dan na b'ata maki rai ba, ina hana ki ne dan Allah ya hana ne, Ramatu waye ya halicce ki?"

"Allah,"

"Me yasa in ya hana abu kike yi? Ko kin manta shi ya halicce ki, kuma zai iya ɗaukan ran ki a dik sanda ya so kin manta da hakan ne? Kin manta cewar dik abinda ki kai akwai littafi ana rubuta maki mai kyau ko mara kyau? Dan Allah yanzu ki zauna na baki minti ashirin ki tina a rayuwar ki kaff me kika aikata da in kin je lahira zai tseratar da ke daga fad'awa wuta, sannan me da me kika aikata na haramun da zai kai ki wuta, in kika bawa kan ki amsa, ki zo ki samen a d'aki bayan kin tuba ga Allah, kuma kiyi qoqarin sauya rayuwar ki daga mummuna zuwa kyakkyawa in ba haka ba qarshen zaman mu ya kusa dan ba zan ci gaba da zama da wadda bata ɗauki sabon Allah a abakin komai ba musamman abinda ya haɗa da shirka,"

K'walalo ido ta sake yi waje ido ya yi mata jawur ga hawaye faca faca, me yake nufi da shirka?

"K'warai shirka nace,ko ji kike ban san kina zuwa wajen malamai yan duba ba? Masu sabon Allah na sani Ramatu, komai da kike aikatawa akan idona yake, idona ya rufe da son ki ne a baya amma yanzu in baki gyara rayuwar ki ba kin qoqarta gyara ta Jameelaa ko zan rasa raina gwanda na rasa dana ci gaba da zama dake, kar ki manta ki zauna sai nan da minti ashirin ki biyo ni ki yi tinani,"

Ko da ya fita ya shiga d'aki, addu'a ya dinga yi Allah ya sa qarshen rashin tarbiyya ne ya zo a gidan shi, Allah ya amsa kukan shi akan shiryuwar matar shi.

Ramai kuwa tinda ta fara tinani daga quruciyar ta zuwa yanzu ta d'au sama da awa biyu a wajen bata sani ba ma, kuka ta dinga yi ta na istighfari, da sauri ta d'aura alwala ta shiga d'aki ko ta kan malam bata bi ba ta sa hijabi ta dinga rabka sallolin da bata san iyakar adadin su ba, tin tana yi a tsaye sai da ta ci gaba dayi a zaune, da taji bacci na neman cin qarfin ta ta yi addu'a da neman yafiyar Allah tare da nemawa kan ta shiriya da iyalin ta dika,sannan ta cire kayan adon da ta sha ta kwanta dan kuwa Malam ya dad'e da yin bacci.

***********************

Aunty hauwaa da Sapnah ke waya tana bata labarin makaranta sannan ta sanar da ita sauran wata ɗaya ta yi jarabawar qarshe ta dawo gida kwata-kwata

"In kin dawo dan Allah ki zauna a nan gidan, kinga wannan cikin nawa shima har ya yi nauyi, na kusan haihuwa, nan da wata biyu inshaa Allahu zan sauka kin san Safiyya mayyar gida ce ba zata zo min ba, ko yanzu inna ce ta dan zo ta taya ni wasu abubuwan ba zuwa take yi ba, ga Umaimah na laulayin qaramin ciki itama kinga ba mun sa matar mutane aiki ba ko?"

"Kar kiji komai ai ni ina son zuwa gidan ku,ina wannan matar wan Umaimahn qazamar nan?"

"Ohhh ni Hauwaa har yanzu baki manta ta ba watanni nawa yanzu da zuwa gidan nata? Inajin 'yar su ma za ta yi wata biyu yanzu fa,"

"Allah sarki Aunty ban san me yasa ba haka kawai sai ina yawan tina Yayan Umaimah, ina matuqar son sake sanya shi a ido na,ban san me yasa ba dik da na kula baya kallon kowacce mace da gashi in ba qazamar matar shi ba,"

"Sapnah kina da hankali kuwa? Kin kuwa san me kike faɗa? Mijin fa wata kike maganar kina son gani?"

"Aunty hawauaa ba laifina bane, ni kaina ina mamakin faruwar hakan,"

"Kinga mu bar maganar nan sai anjima, ki maida hankali akan karatun ki kar ki saka shiririta kin ji ko? Kuma kiji tsoron Allah ki kare mutuncin ki, kar ki biyewa samarin makaranta kin ji,"

"Eh naji na gode Aunty Hauwaa sai anjima a shafan babyna, ina gaida Umaimahn da Yayana,"

"Zasu ji"

Hauwa shiru tayi tana tinanin Sapnah, Ohhh Allah ya sa ba qalatar son maza qanwar ta take da shi ba kamar yanda tayi a baya..........







*Hummmm Allah shi kaɗai ya san karatun bebe*
[08/09, 10:18 pm] Aunty Hameeda: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻














WRITTEN BY HAERMEEBRAERH













PAGE 31:









Shiru ya yi yana jiran amsar ta tare da kafe ta da idanun shi, cikin wata jarumta ta tattaro dik hankalin ta waje ɗaya sannan ta yi masa fari da ido, wanda ta san yana jan hankalin shi ta ce,


"I am sorry Abban Humairah naso na yi maka suprise ne dama, shi yasa ɗazu nace maka ka kaini gidan mu, dama na je na sauya sabon design ne na sarqar da d'ankunnen yanzu irin wanan ake yayi, kuma kasan mu mata yana da kyau mu dinga sauya abubuwan mu, lokaci zuwa lokaci dan birge ababan qaunar mu"

Ta qarasa maganar cikin yi masa wani irin wasan da ya mugun tafiya da shi, lumshe ido yayi tare da sauke numfashi, ya jata jikin shi abun nema ya samu, sai da su kayi romancing junan su sosai sannan ta daga shi,cikin wata iriyar murya Umar yace,

"Ina zaki je kuma Ki qarasa binda kika fara mana ko ladan naki ya cika?"

Ya qarasa maganar shi yana wani lumshe idanu.

"Ina zuwa bari na kaiwa Kulu Humairah na dawo"

Tana kai Humairah wajen Kulu ta koma sai da wasa yayi wasa sanan Jameelaa tayi shiruuu, Umar ya matsu ya kammala abinda ya fara amma 'yannan tai mursisi taqi bashi dama.

"Come on my love, ya kika tsaya,"

"Ni ba komai kawai tinani nake yi ne ina son na ɗora ma Mamana jari amma bani da kuɗi, bata son zama ba sana'a"

"Indai dan wannn ne zan baki 50k ki kai mata zai isa?"

"Anya kuwa kasan fa sai ta sake kayan aiki, ta yi awon dik wani abu da zata yi amfani da shi, sannan...."

"Please love ki bar maganar can a gefe ki qarasamin abinda kika fara, i promise to take care of all her needs, i will give her money to start her business again, please love,"

Jameelaa na jin maganar kuɗi zasu shigo kawai ta ci gaba da gigita Umar hankalin ta kwance bata tsoron Allah bata tsoron cewa mace haramun ne ta amshi kuɗi ko wani abu a dai-dai lokacin da mijin ta ke tsaka da biyan buqtar shi a wajen ta, wallahi dik macen da ke hana mijin ta kan ta sai ta yi ciniki dashi ko sai ta nemi wata biyan buqatar ta ta son zuciya, ko sai ya mata alqawarin wani abu wanda ta san zai cutar da shi to ta sani ko a ina take ko a wanne lokaci za ta koma wajen Allah zata gamu da Allah ta yanda batai tsammani ba, domin kuwa shi zunubi ko wanne iri ne ana son bawa ya bar shi kafin lokaci ya qure masa, mata masu hali irin na Jam Jam a nutsu a ji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login