Showing 27001 words to 30000 words out of 118783 words
ba dik tsawon rayuwar ta,ta na gamawa sai ta fara rera karatun qur'ani da ka, Umar dan daɗi har wani lumshe ido yake yi, sai da ta kai qarshe sannan ta yi addu'a ta kwantar da kan ta jikin gado, hawaye na zuba daga gefen idon ta, Umar ne ya buɗe ido ya gan ta a haka, da sauri ya tashi ya zauna a gaban ta tare da lankwashe qafafun shi, yana mai tambayar ta dalilin kukan nata.
"Yah Umar ka yi hakuri, dan Allah ka yafe min ni na yarda kuma zan hakura sannan zan jure ko da zaka rabu dani a wannan ranar ne, amma ba zan taba iya haɗa shimfida da kai ba,"
"Innalillahi Jameelaah kina da hankali kuwa? Me ya shiga kan ki ki ke kiran kalmar rabuwa a tsakanin mu? ni ne fa Umar naki, me ya same ki? Akan me kike kira mana rabuwa, jiya jiya Allah ya hada mu a bainar jama'a Allah ya mallaka min ke sannan ki so rabuwar mu a yau da na tashi cikin farin cikin kin zama mallaki na,"
Kuka ne ya k'wace mata mai tsanani har tana shessheka, Umar hankalin shi ya tashi ainun, dan haka ya matsa ya jata jikin shi sosai ya na lallashi,aikuwa sai ta shige jikin shi tayi luf tana ci gaba da kukan,cikin zuciyar ta tana ayyana daɗi da laushin jikin shi.
"Dan Allah ki sanar dani me ke damun ki kar zuciya ta ta buga,"
"Yah Umar inna ce maka ni ɗin ba budurwa bace zaka iya ci gaba da zama dani? Na san ba zaka iya ba, kuma babban kuskuren da muka yi kenan nida Mamana, wanda har Babana bai sani ba har yau, dan Allah ka rufa min asiri kan kowa ya ji ka sallame ni na tafi gidan mu, na yi dana sanin rufewa wanda zuciyata ke matuqar so wannan babban sirrin saboda tsoron kar ka rabu da ni tun kafin ka aure ni, zan iya mutuwa akan son ka amma ba zan iya jure ha'intar ka ba,"
Kuka take sosai kamar an aiko mata Ramai ta fece qiyama.
Ji yayi kamar an doka masa guduma a tsakiyar kan sa, amma ganin yanayin da take ciki sai ya sanya shi nutsuwa dan jin me ya faru har ta rasa budurcin ta.
"Zan iya hakuri da dik wani abu a duniya, amma ba zan iya hakuri na rasa soyayyar ki ba, ba zan iya ci gaba da rayuwa in bake a cikin tawa rayuwar ba sanar da ni me ya faru ki ke waɗannan kalaman masu tada hankalin mai sauraro,"
'Wayyooo dadi,lallai maganin mallakar nan na aiki, tin yanzu ya fara ji na kamar wani sashe na jikin shi,'
Cikin tsananin kuka da kauda kai wai ita kunyar bashi labarin da zata faɗa yanzu take yi ta soma magana.
"Yah Umar...........
*A dandana wannan, da babu gwanda ba daɗi, na san wasu zasuce yayi kaɗan, ayi hakuri da ban yi niyyar typing ba ma yau dan babu appetite ɗin taifin ɗin sammmmm*
[11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 14:
"Yah Umar tin....tin....tin inaaa yyyarinya ne.....aka yi min fyad'eeee"
Kuka take mai tsananin ratsa zuciyar wanda bai san wace ce Jameelaa ba, Umar sakin ta yayi ya kafe ta da ido, a hankali idanun shi suke rinewa daga haske zuwa jawur, yawun bakin shi ya qafe kukan Jameelaa ne ya qaru, a hankali ta miqe ta hau ɗaukan akwati ta juye kayan kwalliyar dake ciki ta fara haɗa kayan ta da aka zuba mata na sakawa, tana ninke kayan tana sawa a akwatin tana kuka, sosai hawaye da majina na haɗewa a waje ɗaya a fuskar ta kamar wadda aka yi wa shegen duka, zuciyar ta kuwa nata bugawa saboda tsananin tsoron amsar da zata fito daga bakin Umar,
'Allah ka sa qaryar nan tawa ta karbu, in Yah Umar ya qi Karb'a ta na mutu na lalace, ga samu ga rashi, wannan daula bana fatan barin ta, wayyooo Ramai na wayyooo Babana,'
Ji ta yi an riqe mata hannu an qanqame ta, fadawa tayi jikin shi ta sake fashewa da sabon kuka cike da son a tausaya mata, ta kuwa samu abinda take nema ɗin a wajen Umar, dan kuwa Umar ya tausaya mata matuqa, zaunar da ita yayi a bakin gado, sannan yace,
"Habaa Jameelaa, ya zaki haɗa kayan ki? Ina zaki je to?"
"Ttttaattfiiiyaa zan yiii, na san mun zalince kaa....bamu sanar da kai wannan mummunan abun ba, Mamana bata son ana d'aga maganar......abun ya faru ina da shekaru bakwai a duniyaaa....."
Wani irin kuka ta saki har tana shidewa ga tari da ya sarqe ta, Umar ya rikice ya rasa me zai bata na taimakon gaggawa, da gudu ya fita ya deb'o mata ruwa a cup ya bata, shanyewa ta yi tasss dan kuwa tana da buqatar shi, qoqarin ci gaba da bashi labarin qaryar ta yi ya katse ta, dan zuciyar shi ba zata iya jure ɗaukan labarin fyaden da akai ma matar shi ba,qanqame ta yayi yana sauke wani wahalallen numfashi, tare da jama dik wanda ya mata fyad'e Allah ya isa a zuciyar shi.
"Ya isa haka, ya isa, come on ki daina kukan haka, ina son wannan maganar ta zama sirri a tsakanin mu, kamar yanda maman ki tace bata son kowa ya sani to ki daina tinawa ki daina maimaita maganar, game da mafarkin da kike yi kuma inshaa Allahu zaki daina, ki dage da yin addu'a da azkar, sannan in zaki yi bacci bayan kin gama addu'a ki yi ta tasbihi ga Allah har bacci ya ɗauke ki inshaa Allah zaki daina mummunan mafarkin nan, zo zo ki daina kukan nace ya isa haka, Allah zai saka mana dik wanda ya yi wannan abun,"
A hankali take sauke ajiyar zuciya, ranta fari kwal kamar audiga,hankalin ta kwance zuciyar ta zaune a ta Umar take narkewa a jikin shi,ta tabbata lallai wannan labari zai wa Ramai daɗi.
Gyara dakin suka yi a tare suna yi suna hira sama-sama, dan kuwa zuciyar Umar cike take da takaicin jin wannan mummunan labari, ya ci burin yin aure mai tsafta amma sai gashi zai b'ige da daukan ragowar wani, gwanda da Allah yasa ma fyad'e aka yi mata ba wai da son ranta bane kuma tana qarama hakan ta faru, ta kula da yanayin shi, sai ta saka fuskar tausayi.
Ganin haka ne ya sa Umar ya saki tashi fuskar dan baya son taji wani abu na muzanta tinda ba laifin ta bane.
"Yi sauri mu gama muje gaida su Dad kafin ya fita,"
"Ok to !.... Yah Umar"
"Na'am My love,"
Sunkuyar da kai tayi cike da jin daɗi, sannan tace,
"Yah Umar ka yi hakuri, nima ba a son raina ba ne na kula kamar zuciyar ka har yanzu tana maka zafi akan labarin dana baka, dan Allah....."
Da sauri ya ja ta a jikin shi ya rungume ta, tare da shafa bayan ta, wani iri take ji a jikin ta tinda take hulda da samarin layin su ba wanda tab'in shi ke shigar dikkan wani sashi na jikin ta kamar Umar, lallai rasa shi a wajen ta babbar asara ce, kuma ba zata bari hakan ya samu wajen zama ba.
Sun dad'e a haka sai da Umar ya ji nutsuwa ta gama baibaye shi sannan ya sake ta, kama hannun ta yayi ya sanya mata hijab, sannan ya riqe hannun ta suka fita,suna zuwa tsakiyar parlour taga Mum zaune da Umaimah suna karyawa, Mum da shirin fita asibiti Umaimah kuma da shirin makaranta, Dad ne ya fito ɗauke da jakar shi a hannu yana manna glass din shi a idon shi,zama shima yayi ya dauki mug ya yi bismillah sannan ya kai bakin shi.
Hannun ta ta yi saurin zarewa a na shi ta sunkiyar da kan ta qasa, ta matsa daga gefen shi, Mum ce tayi murmushi dan ganin abinda ya faru,
"Ku zo ku karya mana, ko kunci wanda na sa akai maku ne?"
"Mum Ina kwana? Dad barka da safiya"
"Barka dai Yaron Mummy, ohhh ashe fa yanzu ka fita daga sahun yara,ina fatan kun tashi lafiya? Jameelaa kin tashi lfy ko? Ya kewar gida? Ki saki jikin ki kin dai san nan gidan kune tin da balle yanzu," In ji Dad da ke kallon su cike da sha'awar yanda ya ga kamala a fuskar ɗan nashi.
"Lafiya qlou 'yan albarka, ku zauna ku karya,"
"Mum ni na qoshi tea kawai zan sha,"
"Dad nima yau zan koma school fa, ka san ba wani hutu indai ba so nake a wuce ni ba,"
"Hakan yayi dai-dai, yau inna kai Umaimah zan gama ma Jameela shirye-shiryen kaita makarantar bokon itama inshaa Allahu, dan banga abin bata lokaci ba, sai dai kiyi hakuri da dik ajin da aka kai ki, zan samo maki mai maki darasi a gida dan ki samu gogewa sosai, fatana ki maida hankali ki bawa mara d'a kunya, kema ki zama wani abu a rayuwar ki,"
"Na gode sosai Allah ya saka maku da alkhairi, kun taimaka ma rayuwa ta ta kowanne bangare, bani da bakin gode maku,"
Wasu munafukan hawaye take matsewa, Mum ta shafa kan ta, sannan ta fara lallashin ta,
"Haba Jameelaah ! Ai ke da Umaimah dik daya ne a wajena, kin san dai ina son ki a matsayin d'iya ta, to menene abin kuka da godiya kuma? Muma muna taimaka wa dik wanda Allah ya bamu ikon taimaka wane da abinda muke da shi komai qanqantar shi, shi yasa kika ga muma Allah yake qara bud'a mana kullum, dan haka ki cire komai a ran ki kinji?"
D'aga kai tayi sannan mum ta miqa mata mug din da Umaimah ta haɗa mata tea a ciki, ta hada mata da soyayya. dankalin turawa da ya ji uban kwai yaji kayan qamshi da attaruhu, sai qamshi ke tashi, ga farfesun naman rago, wani mugun yawu Jameelaah ta hadiya,
'Ya Allah kasa wannan ne abin da zamu na karyawa da shi kullum, jar uban nan kayyasa, daɗi kan daɗi kenan,'
"Jameelaa bismillah,"
"Ni dai daga yau Yaya Jameelaah zan dinga ce maki, tinda dai kin zama matar yaya,"
"Kar ma ki soma 'yan aji su ce na tsufa, tinda dai ba wani girman ki nai ba ehe,"
Dariya iyayen nasu suka sanya har Umar,
"Ai ina ga kawai kin daina zuwa Islamiyyar nan Jameelah, zamu samu malami yana koyar da ku a gida zai fi, ko da daga islamiyyar ne ma sai a nemo zamu roqa mu samu ko asabar da lahadi ne sai ana maku a gida da safe ko da yamma,"
"Dad ai kuwa in haka ne akwai wani sabon malamin mu, indai hakan ba zai zama matsala ba ko za a tuntube shi sai yana koya mana a gida, dan shi ke koya min karatu in an fita break dama, ya iya koyarwa,"
Jameelaah bata son a kawo Haroon gidan dan kullum faɗa suke, gashi kusan kullum sai ya dake ta a 'yan kwanakin can saboda rashin kunya da take yi masa,dan haka sai ta yi shiru bata ce komai ba, Dad ne ya kalle ta ya ce,
"Jameelaa yaya dai ko baki son shi yana yi maku karatun ne? Naga yanayin ki ya sauya,"
"Ah ah ba komai, ina tinanin Mamana ne kawai,"
Dikkan su sai ta basu tausayi, kewar gida dole ne dama wajen sabon aure,amma a hankali zata saba watarana, Mum ce ta miqe dan ganin tayi latti, da sauri ta yi masu sallama, ta fita a motar ta, Dad da Umaimah ne suka tashi dan tafiya makaranta, Umar ya raka su har gaban Mota ya koma ciki.
Yana zuwa ya ga har ta cinye abincin ta ta qara wani, murmushi ya yi ya san ɗazu kunya ta ji kowa na wajen shi yasa bata ci ba, in ko haka ne a hankali zata saba cin abinci da su, komawa d'aki yayi kar ya katse ta, dan da alama ta na jin yunwa sosai , wataqila tinda aka fara biki bata samu damar cin abinci sosai ba.
Sai da ta kusan cinye komai sannan ta tattara wajen tana ta sakin gyatsa mai qarfi kuwa,ta qoshi to tayi nak.
Mai aiki ce ta taya ta kwashe kayan wajen sannan ta gyara wajen,Jameelaa bata koma dakin ba sai ta hau goge goge, Umar cikin shirin tafiya makaranta ya fito, da alama wanka ma yayi duba da yanayin shi, ya saka kaya masu matuqar kyau, wani yadi ne mai laushi kalar blue dark, ya amshi jikin shi sosai sai qamshi yake zubawa kafad'ar shi rataye da jakar makarantar shi sai lab coat ɗin shi riqe a hannun sa na dama.
Jameelah ta shagala da kallon shi remote ya faɗo mata a qafa, da sauri ta duqa dan ta d'aga, Umar ya isa gaban ta Shima ya duqa ya kama qafar ta ta yana murza inda remote din ya buge ta. Lumshe ido tayi tana amsar saqon da hannayen shi ke aikawa qafar ta.
Bata san sanda ta dafa kan shi da babu hula ba ta fara murza gashin kan shi a hankali, da sauri ya kalle ta murmushi ta yi shi kuma ya yi kissing qafar ya miqe tsaye,a hankali ta bude idanun ta ta kafe shi da kallo, can kuma kamar wadda aka mintsina ta fara kame-kame ta d'au tsumman, ta aje gefe ta juya ta ɗauki remote ta aje a qasa dik ta rikice, sumbatar goshin ta ya yi,Jameelah ta qanqame idon ta, cikin murya mai sanyi ya ce.
"Sai na dawo ki kula min da kan ki banda bigewa, ni Umar naki ne ke ɗaya har abada inna dawo sai ki ci gaba da kallo na ko?"
Murmushi ta yi mai sauti ta gudu d'aki ita a dole taji kunya,Umar ma cike da nishadi ya fita.
Har ya bude qaramar motar shi da Dad ya sai masa saboda zuwa makaranta, zai shiga ta fito da gudu-gudu, ɗauke da hula a hannun ta kalar kayan shi,
"Kayi mantuwa saboda tsabar kallo na da ka ke yi"
Tana fada ta miqa masa ta koma gida da gudu, bin inda ta wuce yayi da kallo zuciyar shi na tsananin son matar ta shi , tinawa yayi da abinda ta fada masa, nan take gaba ɗaya daya annurin zuciyar shi ya kau.
A haka ya isa makaranta ya na tunani, ya na shiga aji ya ajiye tunanin komai ya maida hankali sosai ya yi karatun shi, abu ɗaya ke d'aga hankalin shi wanda bai wuce na Kalaman Jameelaah da ta ce anyi mata Fyad'e ba.
**********************
Cike da kulawa ya d'aga hab'ar ta ya na kallon fuskar ta ya ce,
"Hauwaa me ya samu goshin ki haka? Me zan gani ni Ishaq Subhanallahi,"
"Sannu da dawowa Yah Ishaaq,"
"Yauwa Haroon, barayi sun shigo ne?"
Da sauri Aunty Hauwaa ta ce,
"Ba barayi bane, bugewa nayi,"
Ta yi hakan ne dan qoqarin hana Harooon yin magana akan abinda ya faru, dan ta ga ɓacin rai a fuskar shi a lokacin da yake magana kar reshe ya juye da mujiya, dan indai ta bari Haroon ya faɗi abinda ya faru tsakanin au yayan shi yarda zai yi ba makawa, saboda ya yarda da dan uwan nashi matuqa, barazana ce dama take yi masa dan kurum ya amince mata.
"Ke dai kina da matsala Hauwaa, watarana sai kin rasa wani sashe a jikin ki, dubi dan Allah goshi kamar an saka maki goribar talatin a cikin shi, haka fa kwanaki na yi tafiya na dawo na ga leben ki a kumbure kamar gandar nera ashirin, wai ke yaushe zaki dinga tattalin jikin ki ne?"
Kuka ta fashe da shi ta fara bubbuga qafa,sannan ta wani harare shi, goshin nan ya yi gaba idon ya yi ciki,
"Yanzu ka ga na ji irin wannan mummunan ciwon amma ka tsaya ka na min faɗa akan ciwon kuma ko irin ɗan lallashin nan kai baka iya ba irin na maza, kayi tafiya kusan wata kenan amma ka dawo ka tirkeni da faɗa,"
Kuka ta sa ta shige d'akin su ta bar su a wajen suna bin ta da kallo, sai ya ji bai kyauta ba tabbas amma ta ya zata dinga zama tana bari bini-bini taji ciwo kamar wata me koyon tafiya ko kuma makauniya da bata kallon gaban ta in tana tafiya,
Kallon Haroon yayi, yace,
"Kai kuma kana ina ta ji wannan mummunan ciwo baka kai ta asibiti ba,"
"Yanda ka gan ta haka na gan ta nima,"
"Baka gidan ne?"
"Ina nan, inna je makaranta na dawo kasuwa nake wucewa abuna, inna dawo daga kasuwa na koma makaranta ta yamma, so banda lokaci, dazu ma baban wata d'aliba ta ya nemi dana dinga zuwa gida ina yi wa yaran shi karatu, za a na biyana dubu biyar a wata, sannan da yamma zan dinga zuwa dik weekend ko da safe, yanda dai naga ya min,"
"To masha Allah, Haroon Allah ya yi maka albarka, ya kare min kai daga dikkan sharri na mutum da aljan, ina jin daɗin yanda ka sadaukar da rayuwar ka wajen bautawa Allah, Allah ya barka a bawan shi na gari har abada, lallai matashin da ya tafiyar da rayuwar shi wajen bin tafarkin Allah ya hakura da soye soyen zuciya da rud'in duniya da na shaid'an ya na da babban tanadi na lada da jin daɗi a wajen Allah ranar gobe qiyama,"
"Ameen Yaya na, nima ina maka fatan alkhairi a rayuwar ka, Allah ya kawar maka da dikkan wani abu maicutarwa a rayuwar ka ko me ne shi,"
"Ameen Haroon"
A dai-dai nan Hauwaa ta fito daga d'aki kuma ta ji sarai addu'ar da Haroon yake yi wa Yayan nashi,kuma ta san akan ta yayi ta, banza ta yi da shi sannan tace,
"Nima a sanya ni a addu'a, Allah ya cikan burina akan abinda nake nema,"
"Ameen idan na alkhairi ne"
Hararar Haroon tayi, ta ja hannun mijin ta, suka shige d'aki daki.
Haroon ya shirya tsaf dan zuwa gidan su Umaimah a matsayin malamin da zai na koyar da su karatu a weekend,littafin da ya rubuta adireshin su ya ɗauka ya duba, ya qara karantawa ya ninke ya sanya a aljihun shi, sannan ya fita,kallon kan shi yayi a jikin windown dake waje komai ya yi kyau acan acan,haka kawai yaji yana son ya yi kyau kafin ya je gidan su Umaimah dan koyar da su karatu......
*Ni kam ban yarda haka kawai bane d'annan, rabani da kitifin yaran zamani ka ji*
[11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 15:
Ya dad'e yana buga qofar