Showing 66001 words to 69000 words out of 118783 words
sake komawa gidan Jameelah ba,haka itama Jameelaah bata neme ta ba, duk wata sutura da sarqa da d'ankunne haɗe da takalmi da jaka da ta so sawa sanyawa take yi ta k'wame k'wam abinta, Jameelah tayi yanda take so har ma fiye da hakan dan kuwa Umar ya tsaya mata, komai an kawo na abincin suna Ramai ta rud'e ta kid'ime k'warai dan ganin kala-kalar cimataku na abinci, Bukar daga makaranta kullum nan yake zuwa yaci abinci har zuwa dare sannan ya tafi gida, da a son shi ne ma idan yazo a dinga bashi renon d'iyar tashi saboda qaunar dayake yi mata, Baban Jameelaa ya zo sau ɗaya ya ga jikar shi, daga nan ne suka je gidan su Umar domin yin godiya akan alkhairin da ake ta yi masu kala-kala da shi da iyalin shi, Daddy ya karɓe shi hannu goma ma ba biyu ba saboda mutuntawa, dan kuwa sai da Baban Jameelaa ya gano inda Umar ya gaji arziqi da mutunci, fatan shi Allah ya gwada masa nashi iyalin sun zama mutanen kirki kamar haka, yanzu dai ya samu Bukar ya kintsu, yana yiwa Ramai da Jameelaah fatan shiriya suma,a tare suka yi sallar Azahar da Daddy sannan suka dunguma dikan su har Daddyn dan ganin jikar su, Daddy ya yi mata addu'a sosai sannan suka yi sallama da Baba ya koma wajen aikin shi, Daddy kuma ya wuce Abuja domin gabatar da aikin shi shima.
Umar akan dole yake zuwa asibiti saboda kula da marasa lafiyar da suka zama dole akan shi, gashi kuma gidan kullum a cike yake da mutane duk yanda ya so zama dole ya basu waje, 'yan uwan Mum da Dad ne yawanci sannan ga 'yan uwan Ramai da Baban Jameelaah gefe ɗaya ga mutan unguwar su da Jameelah ta dinga shigewa daf lokacin da taga ta kusan haihuwa dan su bata gudummawa kuma babu laifi sun bata kuɗi sosai da kayayyakin jinjira.
Ramai har wani ja take a kwanakin nan tsabar yanda ta yi haske ta yi qiba, sai wani bud'a hanci take ita a dole uwar me jego,Jameelaa ta ware mata kaya na musamman tana sauyawa itama dan bata son a raina mahaifiyar ta, ga sarqa da dan kunne masu kyau da takalma duk ta bata ,gaba ɗaya wanda ya san Ramai me shinkafa da wake a da ba lallai ya gane ta ba yanzu, sai a zaci tana da Hassana ko Hussaina ne.
Matan gidan su na da da matan layin da suke dan zumunci a da sai gulmammaki ake yi akan su ita da 'yarta, wasu kuwa murna suke taya su na samun ci gaban rayuwa da suka samu.
(Allah ka sanya mu a cikin masu taya 'yan uwan mu musulmi murna akan ci gaban su ka kare mu daga cikin bayin ka masu yawan qyashi da hassada)
Jameelaah ce zaune ta na doka murmushi saboda kallon kayan da ta baza zata sanya ranar sunan da ya samu halartar manyan mata na dangin su Umar da kuma qawayen ta na social media da yaran masu hannu da shuni na makarantar su ta boko, a wannan rana Jameelah ta yi kuma ta na kan yin yanda ta so dama abinda bata taɓa zaton zata yi shi ba, dan kuwa ko a cikin unguwannin masu kuɗi aka yi sunan da aka yi a nata an kai aya,wani hamshaqin gidan ɗaukan hotuna aka gayyata dan daukan hoton sunan Humairah, duk wanda ya halarci taron nan ya ci ya sha ya yi guzurin abinci.
A ranar Mamalo ji ta dinga yi kamar kar ta je, amma haka ta hakura ta shirya da yamma liss, ta sanya dinkin ta mai kyau abunta wanda Sadeeq ya d'inka mata shi da hannun shi, atampa ce mai kyau ta amshi jikinta ta kafe d'auri mai kyau, koda ta zo mutane dik sun ragu d'aki ɗaya Jameelaah ta ware ta zuba kayan gifts da ta samu, kuɗi kuwa ta same su da yawa wajen qawaye da kuma 'yan uwan mijin ta, sanda Mamalo ta isa gidan Jameelaa na d'aki tana shayar da Humairah dik ta gaji, amma jira take yi yarinyar tayi bacci ta sanya ta a gadon ta, ta sake wasu kayan ta fita ta qara yin barazana, Mamalo na ta gaisawa da mutanen da ta sani ana ta yi mata fatan itama Allah ya sauke ta lfy, tana masawa da Ameen.
Jameelaah ce ta fito ɗauke da Humairah, (sunan da suke kiran A'i'shaa kenan) ta sauya kaya da wata shadda milk da aka zubawa uban aiki ruwan zuma mara duhu, sai ta kafe d'auri mai ban sha'awa ga qamshin turare na tashi, sarqa harda ta qafa sai da ta sanya irin ta mutanen india, qaryar mutum yace bata ratsa shi ba saboda haɗuwar da ta yi.
Mamalo baki sake take kallon ta, dan kuwa bata zaci Jameelaah ta shiryawa sunan har haka ba,nan take zuciyar ta ta raunana ta fara waswasin anya kuwa zata iya kamo Jameelah? Wani yawu ta had'iya mai dumi ta fara gaida Jameelan tare da yi mata barka,sai ta d'akko ledar kayan jaririyar da ta zo da shi ta ajiye mata a gaban ta,a cikin ledar kuwa riguna ne guda biyu, da atampa ɗaya sai takalmin yarinya biyu da sabulu sinqi ɗaya.
Jameelaah bud'a ledar tayi ta kalla sai tayi murmushi ta ajiye a gefen ta tare da yin godiya.
"Ramai ki ce da Khadeejah a kawo ma qawata abinci,a sanya mata komai da komai dan Allah,"
"To shikenan bari na duba ta ina jin tana can tana gyara kitchen,"
Ramai ce ta samu Khadeejaa ɗaya daga cikin dangin Umar ne, da sukai ta taimakawa a sunan dan aikin ya yi ma Ramai yawa, Umar har ya yi magana da Mum a sama masu mai aiki babba wadda zatana kula masa da gidan da iyalin shi, sun tsayar bayan suna za a kawo mai aikin, Ramai tayi iya yin ta dan ta hana a kawo kowa amma sunqi hanuwa sunce in bayan suna ta koma wa zai na kula da su? tace ah ah ai ita zata zauna har bayan sunan Mum tace ai ba za a bar Baba shi ɗaya ba, ta dad'e anan ya kamata ta koma gida,ba dan ta so ba ta hakura dole zata koma gidan nasu.
Babban trey ne aka doro abinci kala-kala akan shi da abubuwan sha sai wata qatuwar leda da aka ciko da abinci again aka dire gaban Hajiya Mamalo, ganin kayan kwalamar da ke gaban ta ne ya sanya yawun ta ya kai maqura wajen tsinkewa, bata b'ata lokaci ba kuwa ta sa a gaba tai ta ci, Jameelaah na murmushin mugun ta, sai da ta kammala ci ta yi nak sukai ta hira, dan kuwa ta sake mata sosai saboda daga ita sai mamalon ne ba wasu important mutane da take jin kunya , sun sha hira ba kamar wancan zuwan ba, har mamalo taji bata kyauta ba data dinga jin kamar Jameelaa ta wulaqanta ta rannan sannan ta janye qudirin ta na son fin Jameelah a abubuwan more rayuwa na yau da gobe dama ba halin ta bane haushin da aka bata ne yasa ta ɗaukan wannan alwashin,sannan ta kulama ba zata iya yin competition da Jameelah ba.
Magrib na gabatowa Mamalo ta ma Jameelaa sallama, Jameelaa ta tashi dan raka ta, a hanyar su ta fita daga gidan ne Mamalo ke tambayar Jameelah Umaimah dan tinda tazo basu haɗu ba.
"Tazo da ita akai suna akai komai da safe ta koma dan kuwa kin san Malam kamar wani mayen ta haka yake baya barin ta ta sake ko kaɗan,tun wajejen 11am ya kawo ta ya dawo around 3:30pm ya ɗauke ta"
"Ikon Allah Jameelaa ina matuqar tayaki farin cikin yanda rayuwar ki ta kyautatu, dibi har turanci kike yi abun ki, Allah nima ya kaini wannan matsayin kema ya qara maku ɗaukaka,"
Murmushin qasaita Jameelaa tayi, sannan tace,
"Mamalo baki da wayo na baki shawarar yanda zakiyi ki tara kuɗi kema kiyi suna irin nawa amma kin qi, yanzu duba ki ga sunan nan dana yi, da kud'in bashin dana faɗa maki da shi na kashe wata yawar ko Umar be sani ba,gashi yanzu na maida kud'in har da riba, na fita kunya ko ban fita ba? dik da dai gaskiya Umar ma da mahaifan shi sun taka rawar gani sosai, amma ba dan kud'in dana ranta ba da tini na san ba zan fita kunyar qawaye na gaba ɗayan su ba,"
Murya qasa qasa sosai suke yin maganar saboda Jameelah bata so aji tana zuga Mamalo, Mamalo ce ta yi ajiyar zuciya sannan tace,
"Jameelaa yanzu inna ce zan yi aro wajen wa zani? Wa zai ara min kuɗi masu yawan da zan shiga na fita kamar yanda ki kai,kar ki manta mijina qaramar sana'a da aiki yake da"
"Kar ki damu indan wannan ne a inda na aro kema a nan zan aro maki, a ajin mu yaran masu hannu da shuni ke yin adashi, dik wata kowa na saka 20k su goma ne, ta haka suke siyan dik abinda suke so, ni kuma da sukaji waye mijina da surikina shine dana nemi aban d'iba na biyu aka bani, na samu Allah ya taimaken na sai kaya na d'inka tun a lokacin, na sai wasu daga abubuwan da aka raba a sunan nan, Umar ma ya sai min kaya masu kyau da tsada dan haka bai ma san nayi ba a zaton shi na lefe na ne na qara da su, in kina so zan iya shige maki gaba dan na tabbata kin kusan haihuwa dan dai ko ki haihu cikin azumin nan ko bayan azumi da kadan"
Tinani sosai Mamalo ta shiga yi, wanne irin yara Jameelaa take tare da su a makaranta da suke adashin kudi masu yawa haka iyayen su basu damu ba? Dan taga dik yaran ta girme su in ba saurin girma irin na yaran masu kuɗi ba.
"Kinga na baro mutane na zo nan muna ta tattuanawa amma kin yi shiru kina tunani, in ba dan amintar mu bama kin ji na faɗa maki sirri na in ba kya so ki fada min tun da wuri na sani,"
"Ina so nima ki nemar min ɗin dik abinda na samu a suna sai na tara na biya, in ma basu cika ba na nema na biya,"
"To shikenan,ki gaida gida, ya kamata ki samu a bin hawa anan, dan kayan sun yi maki nauyi,"
(Kayan suna jameelaah ta sa aka d'ibar ma Mamalo masu yawa dan ta sake kwad'aita mata karb'ar bashin itama a fantama a bikin sunan ta)
Mamalo sai tunanin hirar su da Jameelaa take yi tunda ta koma gida, zuciyar ta ta gama aminta da shawarar Jameelaa dari bisa dari, ita ta san Mai zaman gida ce bata aikin komai Jameelan ma haka, amma a qallah suna da 'yan uwa da abokan arziqi ta san za suyi mata biki zata samu kuɗi, sai ta biya su in an gama suna, ko da kujerun ta ne ta shirya tsaf bayan suna ta siyar ta cika ta basu kud'in su ,in ta samu daga baya ta sai wasu.
Koda ta koma gida gum tayi bata ce ma Sadeeq komai ba akan wannan maganar, yayi tambayar duniya akan me ya sa take yawan tinani taqi magana, dole ya hakura ya qyale ta ya san halin matar shi ba ta da b'oye-b'oye da wani abu ya faru tabbas da ta fada masa.
***********************
Azumi ya kan kama Safnah ta zo hutu gidan yayar ta, dan haka koda yaushe suna tare da Umaimah, tare suke yin girki kullum Safnah na koya mata na zamani dan tafi kwarewa wajen su, ita kuma Umaimah tafi gwanancewa ana gargajiya, dan kuwa Haroon su yafi so, amma a saka kaya yafi son na turawa, yana son yaga matar tashi na d'ame ko ina na jikin ta ya dinga juyawa.
Haroon shi kan shi yana mamakin gano yanda yake da tsananin buqatar matar shi bayan ya yi aure wanda a da da ya kame kan shi kafin yayi aure har tinani yake anya lafiyar shi qalaou kuwa?
Sai yanzu ya gane ashe zina ma waje ta samu, in kai exposing kan ka a gare ta sai ta mamaye ka, amma in ka kame kan ka daga barin ta sai kaji baka da wata doguwar sha'awa da zata kai ka ga halaka duniya da lahira, idan ka biye wa zina sai ka gama jin daɗin lokaci qalilan saita guje ka,Allah na taimakon bayin shi da suke qoqarin nesanta kan su daga zunubi, amma wanda suke kusanta kan su daga zunubi sai Allah ya barsu da iyawar su tin da sun sauka daga hanyar shi, Umaimah ce taje wucewa ta gaban shi da wasu qananan kaya a jikin ta, Haroon ya kauda kan shi da sauri yace mata,
"Dan Allah je ki saka doguwar riga, azumi fa ake yi ni kar ki min targade a azumi na"
Dariya sosai Umaimah ke yi masa, saboda rigar doguwa ce amma mara hannu sai ta haɗa ta da dogon wando, sannan akwai hula akan ta kuma bata shafa komai ba a fuskar ta na kwalliya,kawai kayan sun haɗu ne kuma sun karb'i jikin ta sosai,turare ma baya baya ta sanya, wai amma shi a haka yana jin wani abu game da ita, wanne irin abu ke damun mijin nan nata ne haka?
"Sai dai kuma in barin gidan zaka yi gaskiya tinda dai naga doguwar riga ce a jikina"
"Assalamu alaikum"
"Wa'alaikumussalam"
"Yauwaa Aunty Hauwaa, thank God u ar here, dan Allah me ye matsalar riga ta?"
"As in, ban gane ba ku fahimtar da ni?"
"Ba komai rabu da ita,me zaku yi mana ne yau?"
Murgud'a baki Umaimah ta yi ita kan ta tana mamakin ina ta koyi rashin kunya haka, daya mata abu sai ta murgud'a masa baki,kallon ta ya yi ya qanqance ido ya ce,
"Dani kk?" Ta sake murgud'a bakin tace masa,
"Eh din"
"Ba matsala na yafe maki yanzu, Allah ya kaimu a sha ruwa Lafiya"
"Asha ɗin mana wake tsoron ka?"
"Ba komai bari dai a sha ruwan"
"Kun ga ku bari in ansha kun lalibo mai tsoron wani a cikin Ku kun ji? yanzu ki tashi muje mu fara shirin yin abin shan ruwa lokaci na tafiya,"
Aunty hauwaa har yau kunyar Haroon take ji in ana maganar da ta danganci soyayya, shiru ta yi tana murmushin yaqe ta faɗa kitchen ɗin umaimah, dan yau a wajen ta zasuyi aikin.
Bayan sun kammala ne suka d'ebi abincin suka baje shi a tsakar gidan, inda suke haɗuwa har Ishaaq a ci, watarana kuma a bangaren su hauwaan suke bazuwa a tsakar gidan su sha ruwa.
Umaimah ce tayi wanka ta sanya doguwar riga sannan ta saka qaramin hijabi kalar rigar, ba tare da tayi wata kwalliya ba, mai kawai ta shafa sai turare shima sama-sama, zama ta yi ta dauki qur'ani tana karanta wa tare da jiran dan lokacin daya rage yayi suje wajen shan ruwa, karatu take ta rerawa cikin muryar ta mai daɗin sauraro, Haroon ya shigo sanye da jallabiyya fara sol da hula itama fara, hade take da wandon ta rigar ya dage shi sama ya fito a ustaz ɗin shi sak. Zama yayi suka ci gaba da karatun a tare suna ta yi aka fara kiran sallah, suma suka kai aya suka ci gaba da bin kiran sallah, bayan sun kammala suka yi addu'ar da ake bayan kiran sallah tare da salatin annabi.
Addu'a suka yi tayi wa kan su, kowa da abinda yake roqa na alkhairi akan dan uwan shi.
"To baqaqen larabawa kuzo muje mu sha ruwa Allah ya amsa,"
Tashi sukai suka bi bayan Safnah, Ishaaq na ganin sun fito ya hau kama ciki shi a dole yunwa yake ji, dariya suka yi tayi suka zauna suka fara da dabino, sannan Ishaaq ya sha kunun gyad'a, Haroon kuma baqin shayin da Umaimah ke haɗa masa kamar na ibada ya sha, baya rabuwa da shan shayi matan kuwa da fruit salad suka fara.
Bayan sun gama karya azumin suka koma kan sallaya da suka shimfida Haroon ya ja sallah suka yi magrib.
Suna idarwa suka ci gaba da cin abincin su suna hira, sosai suke hira ana ta nishadi, can Umaimah tace,
"Dan Allah ka barni na koma gidan Yah umar ganin baby, kaga ga Safnah da Aunty Hauwaa ma sunce zasu je, gobe kawai sai muje ko?"
Kallon ta yayi ya haɗe fuska ya ci gaba da cin abinci, mugun kishin ta yake ji baya son tana fita, in ta fita ji yake kamar kowa ma kallon ta yake yi.
"Ni dai na amince maku ku je amma ban san me gidan naki ba ke Umaimah ko ya amince ko yana jin mulki, dan naga mulkin masu gidan ya motsa,"
Bai san sanda ya sa dariya ba wai mulki,cikin dariyar ya ce,
"Yah ni ban san yawan yawo ne fa,"
"Ziyara daban yawo daban, in kana so ba sai kawai ka kaisu da kan ka ba, in sun gama su maka waya ka dakko su, ko me kace?"
"Allah ya kai mu goben yah,".......
❤
[08/09, 10:18 pm] Aunty Hameeda: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 29:
Azumi nada kwana 25 Jameelaa tai wa Mamalo waya dan tabbatar da amincewar ta akan karbar bashin da za su ci bikin suna dashi, a cewar ta gwanda su Karb'a da wuri su sai kayan da zata saka a kai dinki, in yaso daga nan ma sai su sayi duk wasu abubuwan da za a raba abikin suna wanda ba zasu ɓaci da wuri ba.
Mamalo ta tabbatar mata da amincewar ta akan karb'ar bashin, a take kuwa ta bugawa qawayen nata waya ta yi masu bayani kuma cikin qanqanin lokaci kowacce a cikin su ta aminta da a sake bata tinda ba ta yi wasa da wancan da aka bata ba ta dawo da shi akan lokaci,kuma ma dai su basu da wata lalura da shi kamar yanda ita mai iyali take da buqatar kud'in.
Godiya tayi ta masu sannan ta tura account no da zasu tura mata kuɗin, bata jima a zaune ba kuwa ta ga alert na kimanin dubu dari biyu sun shiga wayar ta,Mamalo ta sake kira dan taji ra'ayin ta akan irin kayan da take so, cikin tsananin farin ciki da nuna godiyar ta Mamalo tace,
"Na gode qawata Allah ya saka da alkhairi ya bani ikon biyan wannan bashi,to ni yanzu ai